← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 69

Sashe 7

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin tayi lomar farko ta soma da bude data dinta sannan ta aje wayar gefanta ta soma cin abincin tana kallon wayar tare da jiran saqonnin su gama shigowa,duk da wasu sun yayyanke,wasu kuma waiting suke nuna mata,don haka basu jima ba suka gama shigowa tsaf,sai tasa hannun hagunta ta dauki wayar,daya hannun kuma tana diban abinci dashi.

Duk yawan saƙonnin dake kan wayar bata bi ta kansu ba,sunan data sanyawa nuraddeen taje ta lalubo ta shiga inbox din tana qoqarin duba last seen dinshi ko kuma yana online.

Ga mamakinta saita ganshi online,dole tayi mamaki,don bata taba ganinsa online ba ba tare da ta tarda saqonshi ba koda kuwa na sallama ne.

Ba jinkiri ta rubuta slm ta tura mishi,yayi mata tick guda biyu alamun yaje,saita tsaya ta zubawa sallamar data tura din idanu kamar ba ita ta rubuta ba,tana jiran taga ta sauya launi zuwa blue,saidai kafin hakan ta faru ta lura daya sauka.

Goshinta ta dafe,sam sai takeji banbarakwai,wannan karon kamar nuradden din ya canza,tunda sam basu saba haka ba dashi,zama tayi sosai ta tura masa saqon cewa tayi fushi dashi,daga haka ta kashe data gaba daya ta maida hankalinta ga abincin,tana son ta gama ta wuce daki kawai ta kwanta gaba daya.

Da wayar da kwanon ta miqe gaba daya a hannunta,hajja ta dubeta
"Yau babu hirar dare kenan?" Fuskarta tadan yamutsa
"Wai so nake nadan huta,tun dazu nasoyin bacci ban samu dama ba" kai hajjan ta gyada
"Ya kamata.....yau banji duriyar nuraddeen ba?" Sai data dubi wayar hannunta sannan ta maida dubanta kan hajjan
"Nima yau na rasa me ya riqeshi haka,kwata kwata bamuyi waya ba"
"Ai yau da gobe sai Allah" bata ce komai ba ta juya ta wuce kitchen ta aje farantin sannan ta wuce dakinta,tasan me yiwuwa su salma nacan na jiranta zaman hirar dare yadda suka saba,idan kuwa basu jita ba zasu biyota ne sassan hajja ayi a nan yadda sukanyi mafi yawancin lokutta,ita kuwa yau sam bata jin wani karsashi.

Kaman jira yake ta gama gyara kwanciyarta saiga kiranshi ya shigo,murmushi ta sake cikin zumudi ta daga kiran
"Kimin afuwa ranki ya dade tuba nake" cikin shagwabar nan tata tace
"Aini tuni nayi fushi ma"
"Kimin rai,karkisa cikin daren nan na kamo hanya"
"Na yi maka" ta fada murmushi na qwace mata,yayin dashi kuma ya saki ajiyar zuciya yana cewa
"Kinsan duk duniya ke daya ce fushinta ke daga min hankali,gwara ran kowa ya baci,hankalin kowa ya tashi indai naki yana a kwance"

Farr tayi da idanunta cikin jin dadin yadda take da girma da matsayi cikin zuciyarsa,kullum kwanan duniya sake nuna mata matsayinta yake a wajensa,hakan yana mata dadi qwarai,tana jinta cewa itama takai mace,ba kamar yadda ko yaushe ya haidar ke nuna musu suna mata bane.

"Baby ina zuwa,minti biyu,mama tayi kirana zan kiraki"
"Kace ina gaisheta" ta fadi,bata ji amsarsa ba amma taji qit wayar ta katse,saita sauke wayar daga kunnenta tana murmushi,soyayyarsu da nuraddeen koda yaushe ta dabance a zuciyarta,gyara kwanciyarta tayi ta bude inbox nashi tana bitar saqonninshi da ita,fuskarta wadace da murmushi,ta jima a haka sannan taji hayaniyar 'yammatan gidan,tasan zuwan zasuyi su dasa hira,wala'alla ma idan nuraddeen ya kirata su hanata dagawa,don haka ta cusa wayar qasan filo ta runtse idonta ta gyara kwanciyarta kamar me bacci,tana jinsu suka shigo suka qaraci nacin tashinta suka haqura suka shiga hirarsu.

Tun tana jinsu sama sama har har bacci ya kwasheta.

Bata tashi farkawa ba sai da aka kirayi sallar asuba.

Misalin sha daya da rabi na safe ta gama dukkan abinda zatayi,tana gaban madubi tana qarasa kwalliyar fuskarta,bayan ta shirya kanta cikin wasu riga da skert na atamfa da suka yi mata cif a jikinta,abu na qarshe datayi gaban mudubin shine feshe jikinta da turare,ta kalli kanta ta tabbatar komai yayi,saita sakarwa kanta murmushi,saboda ita kanta tasan tayi kyau.

Hankalinta ta maida kan wayarta dake gefanta,tun daxun take trying number nuraddeen,tana son gaya mishi xata fita,don kada yace zayazo kuma bata nan,gwadawa ta sakeyi tana fatan ta sameshi,tun jiya da yace zaya kira bai biyo din ba,amma ta masa uzuri,mai yiwuwa basu gama magana da maman nashi da wuri bane.

Cikin sa'a wannan karon ta sameshi,sai daf da zata tsinke aka daga,muryarshi can qasa kamar mai bacci suka soma gaisawa
"Zan je gidan abban gwammaja ne nace bari na gaya maka kada kazo gida baka sameni ba"
"Ok,babu matsala,na tarad dake acan kawai"taji dadin hakan don tana da muradin ganinsa,amma saita boye murnar tata da cewa
"Ok fine,yayi" daga haka sukayi sallama ta aje wayar tana sakin murmushi tare da sake duban kanta sosai,nufar ma'ajiyar sarqoqinta tayita cire dan kunnen kunnenta ta saka sarqar da dan kunne harda abun hannu,wanda ada batayi niyyar sanyawa ba,data sake duban kanta sai taga kwalliyar ta sake qawatuwa fiye da daxun.

"Kince karna bata mana lokaci,kuma naga kamar kedin xaki bata mana" ta jiyo mitar salma daga can falon hajja
"Ina zuwa" ta fada da sauri tana daukar mayafinta dake saman katifa ta yafashi saman kafadunta,ta maqala hand bag dinta a hannu ta zura takalmi ta fito.

"Wannan mayafin fa salma?" Zahra ta fada tana duban salma
"Hmmmm...kin manta yaa zaki yana nan,baki nan ranar daya kora mana warning kan saka irin wadan nan mayafan,wai bama ganin zahransa,ita bata ishemu darasi ba" baki zahra ta tabe,zata ce wani abu hajja ta fito
"Ma sha Allah..." Ta fada tana duban kyawawan jikokin nata
"Amma innawuro ki koma ki canza mayafi" baki ta tabe kamar xata saki kuka tace
"Ni bani da wani babba irinsa da zai shiga da kaya na,don Allah hajja ki barni"
"Ni ina dashi,kije kibude adaka ta ki dauka nawa" dariya sosai zahra ta qyalqyale da ita,salma na dan tayata,sai data tsagaita sannan tace
"Haba hajja,haba don Allah,mayafinki fa?ai sai a nannademu duka nida salma a ciki,ki qyaleni don Allah,wannan ma meye aibunsa tunda ya rufemin duka baya na,kuma ba mai shara shara bane"
"To Allah ya baki sa'a,idan kuka hadu dashi ai kya dawo ki dauka ko ba don Allah ba" daga haka tayi gaba ta barsu
"Muje don Allah salma,su na fuskanci kowa ma bin dokarsa da tsoron fushinsa yake,kamar shine uban gidan gaba daya" ta qarashe xancan tana barin falon,salma tabi bayanta tana dariyar zancan hajja na zahra ta yafa aron mayafinta.

Sassan umminta ta nufa don gaya mata zata wuce,sai data tsaya daga baya ta bawa salma riqon mayafinta sannan ta shiga ta mata sallama ta fito suka wuce,salma nata tsokanarta Allah yasa su hadu da ya haidar,ita kuma tana ramawa
"ƴar baqinciki,bakinki ya sari ɗanyen kashi" suna hira kadan kadan har suka isa bakin titi suka tsaya don samun abun hawa.

Tun daga nesa salma ta hangi motarshi,damqe hannun zahra tayi
"Xahra,ya haidar" ta furta idanunta na kan motar dake qara kusanto inda suke tsaye,duban wajen tayi,tabbas motarshi ce,to amma su ina ruwansu dashi,don haka ta zame hannunta daga na salma
"Ina ruwanmu dashi?,share kawai,karma ki nuna kin ganshi" daga haka taci mur ta maida fuskarta wani sashe,saidai kuma zuciyarta na dan bugawa saboda tsoro.05

Masoya ga abdulrahamaan❤️
K’aramin yaro masoyi kuma mahaddaccin alqur’ani mai girma
Yana matuk’ar son karatun alqur’ani duk kankancin shekarun sa, Ya haddace surorin alqur’ani da dama hizb biyu na ammah.

Dan Allah a shiga a danna masa subscribe, Aunties, uncles 🥰🥰 A saurara a kalla a kuma sanyawa channel dinsa albarka ❤️❤️

Yaro k’arami yataso da zuciar son karatun Al’Qur’ani mai girma. Kullum burin sa bai wuce a kyalla shi a camera yana rangada karatu cikin kira’arsa mai dadi, 👏🏻👏🏻
Toh yan uwa dan Allah a hanzarta a danna kararrawar subscribe ta tashar YouTube na ABDUL-RAHMAAN... ❤️❤️Domin samun sabon karatun da yai a duk sanda Aka dora 💝💝

Mungode kwarai da zab’in zafafa biyar..👏🏻👏🏻

https://youtu.be/NgqdCTVKOF8

Channel name Abdul-rahmaan.

He's a very young boy who's passionate about becoming one among the huffaz, he loves reciting the Holy Qur'an even at his younger age. He has memorized so many surahs within juz ammah.

please help him grow his channel fisabilillah and also pray for him to be come a Hafiz in future in sha Allah. Jazakumullah khair..

*KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*

5

Cikin nutsatsen tuqi motar tazo ta giftasu,wata ajiyar zuciya zahra ta saki,can qasa muryarta tace
"Thank god....Allah ya tsaremu daga masifar wannan masifaffen" tayi maganar a afili sanda tasa hannu tana tsayar musu da dan adaidaita sahu,ba tare da tsayawa dogon ciniki ba ta shiga salma ta bita a baya tana cewa
"Addu'arki taci bai ganmu ba,Allah ya tsallakar dake".

Tafiyar minti talatin da mintina suka isa gwammaja gidan abban gwammaja,matarshi daya da yara tara,gidane na masu rufin asiri qwarai,matarshi hajiya halimatu macace mai mutunci da zumunci gami da son dangin mijinta,hasina itace kusan sa'ar zahra,tsiransu watanni biyu kacal zahra ta bawa hasina,daga khadija mahaifiyar zahra saishi iyayensu suka haifa,su biyu kacal a duniya,hakan ya sanya abban gwammaja yake kulawa da ita sosai,ya zame mata tamkar uba,kamar yadda itama take girmamashi sosai,duk wani hukunci daya yanke ko ya zartar a kanta ko yaranta dai dai ne,shi take dauka a matsayin uba,kamar yadda yaranta suma suke daukarshi haka,shi ya dauki nauyin karatun zahra da yayanta tun mahaifinsu ma yana raye,yanzu haka yayan zahran dake a ji daya a jami'ar ibadan shike masa komai da ya kamata uba mahaifi ya yiwa yaransa.

Da sakin fuska kamar kullum umma ta tarbesu,saida suka gama gaisawa sannan suka wuce dakin hasina suka kafa tasu hirar,wanda kusan rabi tambaya hasina take mata kan makaranta bayan ta dawo gida jiyya
"Wallahi ji nayi nima kamar nayi cutar qarya a maidoni gida,amma nasan halin ummi da abba,tsaf xasu gane,kuma raina saiya baci fiye da kima,shi yasa kawai na haqura,don Allah sis ki warke mu koma tare" dariya hasina ta danyi
"Sanin hali....shi yasa nima duk tunanina yana kanki,ai naji sauqi sosai,in sha Allahu tare xamu koma" daga haka suka shiga hirarrakin da suka shafesu,sai da akayi sallar la'asar sannan nuraddeen ya kirata yace yana hanya,tuni ta isa bakin mudubi ta soma gyara fuskarta,su hasina nata tsokanarta,ita dai bata kulasu ba taci gaba da abinda takeyi.
Chapter 7 · 0% Book details