← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 69

Sashe 50

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai idanunta suka nuna razana muraran,da hanzari ta juya a sukwane ta durfafi qofa,taku uku qwarara ya cimmata,ya sanya hannu ya cafkota tare da birkitota gaba daya,sai gata tayi kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa,damshin ruwan dake jikinsa ya ratsa fatar hannunta da wuyanta,tsigar jikinta ta zuba,saiya matseta yana fadin
"Nutsu mana,ina zaki koma a haka kamar wadda wani mugun abu ya biyo,ba baqi mukayi ba?" Ya fada a dake,kasa furta komai tayi sai jikinta dake rawa,saiya yasa hannu ya janyeta daga jikinsa yana ladabtar da ita da kaifaffan kallonshi.

A nutse yake qare mata kallo tun daga yatsun qafarta har zuwa kanta dake gyare cike da baqa qirin din suma,fuska a hade yake dubanta
"Uhummm....,me yasa ko yaushe kike firgita kanki?,tell me,meke baki tsoro a jikina?" Gam ta rintse idanunta,don har ga Allah ba zata iya kallonshi a yadda yake tsaye a gabanta ba,don ita a wajenta bashi da maraba da tsirara,gashi hanya takeso ta samu ta tsere,saiya kada yatsanshi saman fuskarta
"Niba dodo bane?....kinji ni?" Kai ta gyada,sotake kawai ya bata waje ta fita,amma a maimakon haka ma sai taji yana saka lock na jikin qofar yana rufe qofar,saita bude idanunta da sauri,sai kuma ta sake kauda kai,cikin rawar murya tace
"Pls....zanje wajenta....jira take" baiko bi ta kanta ba yayi gaba abinsa,ya bude ma'ajiyar kayansa ya dauko wanda ya dace da ra'ayinsa,ya dawo gaban mudubin yaci gaba da shiryawa,tilas taci gaba da tsaiwa tana jiran tsammani,saidai kuma ta bashi bayane tana duban qofa,hakan ya bashi damar qare mata kallo,lokaci lokaci,yana dubanta yana shiryawa.

Batasan ya gama ba duk da qamshin turarensa mai laushi daya addabeta,har sai data ji yana bude qofar sannan ta ware idanunta a hankali,sannan ta tako ta nufi qofar,dab da shi ta tsaya ganin shima yana tsaye bai fita ba,cikin husky voice dinshi yace
"Ko yaya iyayenka suka yanke maka hukunci,duk boren da zakayi kada ka yarda ka nunama duniya....aikata hakan kamar kana gayawa duniya ne how valueless they are",sai ya fara takawa yana ficewa daga dakin.

Magana yayi mata me harshen damo,saidai ta fahimceshi sarai,don haka tabi bayansa itama tana gyara yanayin fuskarta.

Ta taras suna gaisawa da nasreen din,daga yanda suke gaisawa kawai ya isa ka gane tana ganin girmansa sosai,cikin 'yar dariya kasancewarta mai yawan barkwanci tace
"Ai cewa dear nayi yazo muje dubiya....Allah yasa qaruwa muka samu" dan murmushin gefan baki kawai yayi,saidai ya maida dubansa ga zahra,sannan yace
"Wata qila,gatanan kya tambayeta" saiya miqe yana ficewa daga falon.

Dan tabota nasreen tayi
"Kai qawata daga zuwa kiransa yanzu fisabilillahi shine aka shanyani?" Murmushi tayi
"Ayimin afuwa...." Tun kafin ta qarasa tace
"Anyi miki....tun kafin boss yayi aure munsha yin gulmarsa nida dear...mun gode Allah ma da gidansa ke shiguwa,saboda irinsu ko.....basu iya qonewa a love ba,ki gansu a waje kamar gaske,amma a gida...uhmmm" dariya sosai ta baiwa zahra,lallai batasan ya haidar ba da bata fadi haka ba,batajin irinsu so na shagaltar dasu haka,amma saita share zancen kawai suka shiga wata firar.

Tunda ya isa farfajiyar gidan yaga tare suke da major ya sake tamke girarsa sosai,duk da cewa akwai saif a wajen
"Yallabai....irin wannan shanyamu haka?" Major ya fada yana washe baki,wani kallo haidar ya masa sanda yake bawa jafar hannu suna gaisawa,sai da yazo kansa sannan ya amsa mishi
"Da kasan kana da abubuwan yi da yawa ma da baka zo ba,incase nan gaba kaga irin haka ka dinga tafiyarka kawai" saif dai na danne dannen waya yana boye dariyarsa,shi yasan qarshen alewa qasa,don major ya dage ne kawai saiya biyosu,amma yasan haidar din bazaiyi maraba da zuwanshi ba,jin amsar daya bashin sai yayi shiru baice komai ba.

Daga nan inda suke tsaye haidar din ya qwalawa mai gadi kira,ya bashi umarnin bude guest room sannan suka dunguma zuwa ciki.

Zuwan dama ya shafi ayyukansu ne,tattaunawa zasuyi ta musamman,don haka kai tsaye haidar ya shiga abinda ya tarasu,don shi sam bai farinciki da zuwan major,shima daya lura da hakan suna gama maganar data tarasun ya musu sallama,yace yana da wani uzuri,akwai inda zashi.

Yana fita saif ya qyalqyale da dariya yana kallon yadda haidar din ya hada girar sama da qasa
"Mai master....wannan wai duka kishin ne haka?,lallai fatima ta ciri tuta...wannan so ba qarami bane" dashi da saif din duka sunsan magana yake gaya masa a fakaice,saiya masa wani irin kallo ya bude baki
"Sosai,ko laifi ne hakan?....akan me ma zaku daukomin wannan kwarton ku shigomin dashi gidana....kai J,haka ka hadoshi da matarka a mota daya kuka taho?" Ya jefawa jafar tambayar,bai amsa mishi ba shima illa danne dariyarsa da yakeyi,sai haidar din ya jijjiga kai
"Next time zan gaya mata,duk sanda zaka dauki wani qato a motarka to saika sama mata abun hawa,koka bata motar tayi driving ku kuje ku hau ta haya....kai kuma" ya nuna saif
"Ka kiyayi haduwarmu wallahi" saiya miqe yana ficewa don sawa a amso musu drinks.

Sun dan jima don basu tafi da wuri ba,sai daya sallamesu sannan ya koma cikin gidan.

Cikin sauri take kammale falon da kwashe kwanukan zuwa cikin kitchen,don bataso yazo ya risketa,nauyi yake sanyata ji haka kawai duk sanda suka hada wajen zama.

Kallo daya ya mata ya dauke kai ganin yadda ta zumbula uban hijabi
"Ki shirya jibi zamu wuce gida" ya fada sanda take qoqarin wucewa kitchen,daidai sannan wayarsa ta dauki ruri ya soma qoqarin cirota daga aljihu.

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin dadin zancan komawarsu,tayi kewar 'yan gidansu gaba daya,musamman yasira dake ranta,wadda sukayi sallama randa zasu koma haihuwa ko yau ko gobe,tana ta zuba idanu amma shuru bataji ance ta sauka ba,wayarta kuma ya rasa me matsalarta yau kwana uku taqi daukan layi,so take duka saita koma ta bayar a duba mata.

Sunan hajja daya gani saman wayar yasa ya samu waje ya zauna sannan ya daga wayar,a aladabce yayi sallama kana ya soma gaidata,saida suka gama gaisawa sannan tace
"Kai daga baka aron diyar mutane sai ka yiwa mutane dif?,an gaya maka haihuwar yasira yau kwana uku ba'a samunta a waya amma banji daga gareku ba,halama baka shaida mata ba.....to ka dawomin da jikata maza maza ayi taron suna da ita" ya soma gajiya da rigimar tsohuwar,yana ji cewa zai fara nuna mata shima dan yaune ko zata dinga shafa masa lafiya,don haka cikin dakakkiyar muryarsa yace
"Zamu dawo,amma ba yanzu ba"
"Me kace?,to baka isa ba,ai dama aro na baka,na taimaka wa wannam shegen baqin ran naka,wala'alla idan kanajin motsin dan adam kusa dakai ka rageshi"
"Nidai dawowa ba yanzu ba,matatace....kuma qarqashin ikona take" daga haka ya yanke wayar,saboda iya tsiya ma saiya kashe wayar gaba daya,yadda ko zata sake kira ba zata sameshi ba.

Yana sane yayi mata haka,kuma a niyyarsa a wasance ne,amma sai yaji zancan daya gaya matan ya zauna har cikin zuciyarsa,saiya tsinci kansa da yin mita shi daya
"Wai aro....kaman wani yaro" ya furta qasa qasa a fili,wannan karon shima sai yayi wasa da hankalin tsohuwar,zata ga dan zamani kuwa,da haka ya miqe ya dauki duk abinda yake buqata a falon ya wuce.

Har zai shige dakinsa saiya tuna hajjan ta gaya masa ba'a samun wayarta,don haka ya sauya akalarsa zuwa dakin nata.

Daga bakin qofar ya tsaya yayi knocking,ba'a jima ba aka bude qofar a hankali,fuskarta tarwai a hasken qwan dake corridor din,tayi rolling da wani pink mayafi saman doguwar rigar baccinta mai kauri da laushi data sauka har qasa,sosai mayafin ya haska fuskarta,qamshin turarenta na busowa tun daga cikin dakin da kuma wanda ke jikinta zuwa inda yake tsaye,saiya sauke boyayyar ajiyar zuciya,muryarsa tayi laushi qwarai qwayar idanunsa cikin nata yace
"Me ya sami wayarki?" Dan yamutsa fuska tayi wanda hakan ya qara mata kyau ba tare data sani ba
"Hakanan ta daina daukan layi"
"Me yasa baki gayamin ba?" Yayi mata tambayar dashi kansa yasan batayi ma'ana ba,qila hakanne ya sanyata yin shuru itama tana juya maganar,saiya waske da fadin
"Daukomin ita" juyawa tayi a nutse ta koma cikin dakin,yabi takunta da kallo.

Batayi koda minti guda ba ta qaraso da wayar,hannu biyun data sanya ta miqa masa yasa ya bita da kallo,garin hakan bai kula ba ya hada da hannunta,ta zame hannun nata da sauri sai wayar ta subuce zata fadi a qasa,cikin zafin nama ya tarota da hannu daya yana ambaton
"Bismillahi" dan ja baya tayi kadan,sai taga ya juya kawai yabar wajen ba tare da yace komai ba.

Maida qofar itama tayi ta rufe tana sauke numfashi,wanne irin taushi hannunsa keda shi haka?,take tambayar kanta,sai tasa yatsa ta dungure kanta da kanta tana fadin
"Shiga hankalinki".

_ZAFAFA BIYAR_🤙🏽🤙🏽🤙🏽🤙🏽🤙🏽

_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_34

Bayan ya shiga daki saiya aje wayar a gefan bedside drower dinsa,ya shiga bandaki yayi shirya kansa,sannan ya dawo ya shimfida abun sallah ya tada sallah,yakanyi sallah raka'a biyu ko hudu duk sanda xai kwanta,musamman idan yana jin gajiya a jikinsa wadda yake saka ran zaiyi wuya ta barshi ya iya tashi cikin dare yayi sallah.

Ya dan jima yana addu'o'insa,wanda ya tabbatar da cewa sune makaminsa a rayuwa,su suka hana a cimma sa,banda hakan yasani cewa da tuni tarin maqiya abokan gaba da masu neman irin matsayinsa sun dade da kwantar dashi.

Sai daya sauya kayan bacci sannan ya isa gadonsa bayan ya kashe qwan dakin,yana shirin jan duvet dinsa ya rufa idanunsa suka sauka kan wayar tata,saiya saka hannu ya daukota ya kuma kunnata,ta daidaita sanda ya kwanta sosai saman gadon,yasa hannu ya budeta,don babu passoword ko security pattern.
Chapter 50 · 0% Book details