← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 69

Sashe 62

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare mata kallo yake tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya cimmata,saiya jera da ita,suka ci gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar wadansu masu shirin film,lokaci lokaci saisu waiga kallon juna,kowanne saiya kama dan uwansa,sai kuma kowa ya dauke kansa,saidai shi haidar yana maida kansa gefe daya ne ya murmusa,komai nata ya gama fallasa kanshi,wai amma dole saita ja masa aji?,saiya samu kansa da wassafa yadda zai qure jan ajinta da kuma kunyarta,qaramar dariya ta kubce masa.

Kafin su qarasa provision din haushi duka ya cikata,ta dinga jin ba dadi saboda yadda ake binsu da kallo,abun haushinma yadda duk 'yammatan da zasu gifta sai taga sun bishi da kallo,yau aiport din a dan cike take,alamun akwai yawan matafiya kenan a ranar.

"Kai....nasma,kinga sojan nan,wanda ke zuwa gidan general hamza" daya daga cikin fararen 'yammata uku sanye da baqar abaya ta fada qasa qasa tana tabo ta kusa da ita,wanda hakan ya faru a kunnen zahra wadda ke tsaye daga qofar provision din tana jiran fitowar haidar da ya tsaya biyan kudin ruwa da lemon da suka siya,wani abu ne ya takore wuyanta,ta juya a hankali tadan kallesu,dogaye ne don sun fita tsaho,hakanan farare ne ba kamar ita da take chocolate ba,hannun kowacce tsadaddar waya ce,wadda aka kira da nasma ta bada attention dinta inda haidar din yake tsaye,saita fidda ido
"Wow....wallahi shine,don Allah heedaya,yau ko ya za'ayi mu samu number dinsa please" daya ce ta zaro idanu
"Waye zai tunkari wannan?,ban taba gaya miki yadda muka taba yi dashi ba,tsinannen girman kai ne dashi,kulashi shine great mistake da zakuyi,ku nema number dinsa dai ta wata hanyar daban,koda cikin gidan general ne"
"Gidan general ba kowa sai matarsa,duka yaransa sunyi aure,ita kuwa ban tsammanin tana da number dinsa"
"Quiet sis....gashinan fitowa fa" dayar ta fada,duk sai sukayi shuru har zuwa sanda ya fito din,ya qaraso inda zahra take,wadda kishi ya cikawa qirji,ranta ya dinga suya.

Jerawa yayi da ita,kuma ta tabbatar yammatan nan sun bisu da kallo,a hankali ta saka hannunta ta lalubo nashi,saita hade tafukan hannunsu waje daya ta matse gam,taqi kuma duban fuskarsa.

Mamaki ya kamashi dajin faruwar hakan,saiya bi hannuwan nasu da kallo,laushi da dumin tafin hannunta yana ratsashi,ya dinga qoqarin lalubar qwayar idanunsa taqi bashi dama,har sai da sukaje kusa da inda su hajja suke sannan ta fara qoqarin zame hannunta,shi kuma yace baisan zance ba,hakan yasanya ta dakata da tafiyar da sukeyi,ta juyo tana dubansa,matsowa yayi gab da ita zai hade tazarar dake tsakaninsu,taja baya da sauri,cikin salon marairaicewa ta shagwabe masa tana masa inkiya dasu hajja da ido
"Idan kika sake lasa min zuma a baki ko?hmmmm....." Saiya gyada kao ya zare hannun nasa a hankali,ya soma yarfar dashi,kamar wanda wani abu ya maqale masa.

Cikin jirgi ta kasa ta tsare,saboda ta lura ashe jirginsu daya da 'yanmatan,number din set dinsu dama daga nashi sai nata,don haka harda qirqirar baccin qarya saman kafadarshi.

Bai fahimta meke faruwa ba sai daga baya,cikin ranshi ya dinga dariya sosai,shikam zuwan yammatan ma kamar taimakonsa yayi,saiya tallafeta sanda take kwance kafadar tasa yana tayata,ta dinga zare ido a boye tana tsoron kada fa ta wuce gona da iri.

Hotel me kyau suka sauka,dab da harami,don daga window dinsu suna iya hango masallaci,su shida harda wata 'yar qawar hajjan da suka hadu a jirgi,itama umara ta kawota
"Daki daya mas'ud da halima su zauna daki daya,daki daya kaida zahra,nida rabi mu zauna a daki daya" hajja ta tsara yadda zasu zauna,duk da mama najin nauyi amma haka suka amsa,hakanan itama zahran nauyinsu takeji,ga haidar kuwa sai yaji nutsuwa,yaji har ransa hakan yayi masa,amma saiya basar bai nuna ba saboda yasan tsiyar hajjan,don haka kowa shida kayanshi ya wuce dakinsu.

Dakine madai daici mai kyau,wanda yake dauke da duk abinda xasu iya buqata a kwanakinsu,itace qarshen shigowa don tuni haidar shi ya shigo,tana ajjiye qaramar jakar hannunta taji ya riqe mata hannu,dubansa tayi,ya kafeta da idanunsa har wani lumshewa sukeyi,saiya matsa hannun da qarfi har sai data dan saki qara
"Badon hajja tace haka ba,da bazaki ce komai ba kenan ko?,saiki bita gotai gotai ki dinga kwana a bayanta?" Kasa amsa masa tayi,saboda wani nauyinsa kunya da qimarsa data dadu a idanunta,da kansa ya sakar mata hannun yadan ja da baya sannan ya dauke idanunshi,order din abinci yayi musu sannan ya wuce bandaki.

Cikin kwanaki biyu suka gama ibadar umara,sai sauran ziyarce ziyarce da suka biyo baya,sun ziyarci gurare masu yawan gaske wadanda suke da alaqa da tarihin musulunci,manyan gurare da suke da tarihi da kuma alfarma.

Sosai imani qaunar Allah da manzansa suka sake shigarsu,a kwanakin ibada sukayi ba kadan ba,hakanan tsakanin haidar da zahra kowa ya tsinci kansa da yin addu'a cikin zuciyarsa kan katari da kyakkyawa kan tarayyarsa da dan uwansa,dukkaninsu babu wanda yasan dayansa yana addu'a dominsa.

A kwanakin da suke cikin ibadarsu duk da suna daki guda kowa yana kwancinsa,da sun dawo daga masallaci ko xiyara kowa zaiyi wanka ya samu wajen kwanciya,kusan duk kwanciyarsa a qasa yakeyi,yabar mata gadon,yayin data dinga jin nauyin hakan,duk sanda ta daga idanu ta ganshi kwance saman carfet sai taji kamar bata kyauta ba,a hankali ta tsinci kanta yana burgeta matuqa,baya ga soyayyarsa data shigeta ba tare data ankara ba,ta yi mata shigar burtu.

A wannan tafiyar ta sake gasgata zancan mahaifiyarta,duk abinda ta fada dangane da haidar din haka yake,yana lura da damuwar kowa cikinsu,baga mamanshi ba,baga hajja ba,baga abba babba ba,baga ita ba,kullum kwanan duniya saiya tabbatar babu me buqata ko matsala a cikinsu,bugu da qari ta fahimci yadda yasan addininsa yadda ya kamata,duk da ta sani cewa sam gidansu basa wasa da karatun addini,amma kuma bata tsammaci samun sani da fahimtar addini har haka daga wajen soja ba,ta manta cewa suna suka tara,iya zamansu bataga yayi fada ko fushi ko sau daya ba,kamar ma walwalarsa aka qara yawanta,ya qarfafesu dukkansu sun ribanci abunda suka je aiwatarwa,basu sake ba sai da suka gama ziyararsu kaf inda zasu iya zuwa,sannan suka soma kuma yawon ganin gari.

Ranar farko da suka dawo daga tafiyar ganin gari da sukayi,miqaqqiyat tafiya ya kaisu wani waje,a gajiya suka dawo,don a qafa yace zasu taho,yana yi yana kwasar hajja,don ma Allah yasa yana ganin idanun mamanshi da abbansa suna kwabarsa,haka ya sanyasu tafiyar qafa yace kowa ya wasa jininsa,hajja kam ta dinga masa mita,saiya dinga dariya yana cewa
"Cikin irin tafiyar da muke wannan ba komai bace,kamar kaje qofar gida ka dawo ne" sai suka hada ido da zahra,wadda ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah yau haidar din ke dariya?,saiya waske ya dauke fuska,wanda ta fuskanci kamar haka halayyarsa take,ya iya waskewa mutum.

A hanya suka ga wani kantin saida kayan qwalam da maqulashe,zaka iya siya ka tafi dashi,zaka iya kuma zama kaci a nan,hajja kam cewa tayi bata shiga,zasu tsaya a waje ita da mama,don dama shi abba babba tashi tafiyar daban,ya hadu da abokan kasuwancinsa a can tun zuwansu,don haka shi tare dasu yake,su hajja ne haidar din ke jagorantarsu,ganin haka yasa yace zahra ta biyoshi suje su siyo,su suka samu abun xama nan suka zauna su kuma suka wuce ciki.

Kamar kowanne lokaci ta gefan idanu suke satar kallon juna,jallabiyya ce a jikinsa irin ta maza harda hirami,ita kuma baqar abaya tayi rolling daya lullube mata fuskarta da rabin hancinta.

Ita ta dinga dauka musu abinda take ganin zasu iyaci,hannunta ya cika saita rasa inda zata sanya,tana waiwaya ta ganshi gefanta riqe da kwando,suka hada idanu saiya saki qaramin murmushi ya miqa mata kwandon,ta zuba a ciki,ga mamakinta binta kawai yaci gaba dayi tana zaba tana zubawa,kai kace yaro ne da uban gidansa har suka gama.

Wajen biyan kudin akwai dan layi,saiya duba daura dasu yace ta zauna anan kada ta gaji,idan ya biya zai mata magana ta taso su tafi,murmushi ya subuce saman fuskarta,mutum ne shi mai nuna kulawa qwarai,tana sane da yadda yakema mamanshi duk safiya,dama ba'a maganar hajja,duk wanda ke qarqashinsa yana samun kulawarsa yadda ya dace.

Dukka hankalinta na kansa a fakaice,yana tsaye kusa da wani balarabe suna hira,tana mamakin yadda yaji larabci har yake iya mayarwa yadda za'a fahimta tun zuwansu,kwatsam ta hangi wata matashiyar balarabiya ta iskosu,saita tsaya tsam,tun daga sanda ya waiwaya ya ganta,zuwa sanda taga alamun hira yakeyi da ita,fuskarshi da fadada da fara'a wadda ta qara masa kyau sosai.

Ƙirjinta ne taji ya quntat sosai,saita miqe tana cire earpiece din kunnenta dai dai sanda yake juyowa shida yarinyar suna kallonta,yana kallo ta miqe daga gurin ta fice da hanzari,zuciyarta na mata zafi,tana hango yadda ya sake mata fuska sosai kamar ba haidar data sani ba.

"Ke lafiyarki kikema mutane tsaki?" Hajja ta tambayeta sanda ta isa inda suke,shaf ta manta data isa dab dasu,kishi kawai ke nuqurqusar zuciyarta
"Eh mun gama siya,na barshi a can zai biya kudin,wajenne akwai layi"
"Ai dama....su da basu rabo da siye siyen irin wadan nan abebaɗen".

Tunda ya fito har suka qarasa hotel a tsume take,taqi ma koda kallonsa bare ta nuna tasan da wanzuwarsa,cikin ransa hakan ke masa dadi gami da burgeshi,ko banza yasan ya gama kama zuciyarta TABBAS! baya ko shakka kan hakan.

Shima baice ba har zuwa sanda ya dawo daga dubasu mamansa,ya tabbatar basu buqatar komai kafin ya kwanta.

Sam bata tsammaci dawowarsa da wuri ba,saboda tasan yanayin awa daya a qalla idan yaje musu sallama kafin ya dawo,itama yau gajiyar da sukayi ne ya sanyata bata kuma fita ba,saita shige wanka ganin ya fita,donta samu ta shirya a nutse,tunda yawanci idan yana nan saidai ta shirya cikin hijabi,fitar tasa ne ya sakata fitowa daga wanka daga ita sai towel a daure a jikinta,ta kuma tsaya gaban mirrow tana shafa turarukan da take amfani dasu,sannan ta ware gashinta daya jiqe da shower tana son yadan sha iska kadan kafin ta maida ta kulle,dai dai lokacin daya turo qofar dakin kunnensa maqale da waya yana amsawa.

A badini ta tsorata,amma a zahirance saitaqi motsawa,saboda batason ta motsa ma ya dauka ta damu dashi,gwara ta nuna masa haushinsa takeji koda ba zaya fahimta ba,don haka taci gaba da tsaiwa gaban mudubin tayi kamar batasan ya shigo din ba.
Chapter 62 · 0% Book details