Sashe 26
Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me haka ke kuma kamar wadda aka biyo?" Ta fada cikin masifa tana qare mata kallo
"Ina kwana yakumbo" ta fada kamar yadda suka saba gaya mata,ko amsarta bata tsaya ji ba ta qara wuta zuwa ciki,sai anty uwanin ta bita da kallo ta kuma fara masifa
"Eyeee....ni zaki gaisar a haka?,lallai yarinyar nan iskancinki kullum qara gaba yake,koda yake kina da daurn gindi ne shibyasa,amma zamu hadu dake bari naje na dawo" ta fada tana buga cinya gami da yin gaba.
Sam bata kula da umminta dake falon hajjan ba sai data isa gaban hajja,saboda abune baqo a wajenta,ba kasafai ta saba ganinta din ba
"Lafiya?" Hajjan ta jefa mata tambayar tana duban qwayar idanunta,saboda yadda ta ganta kamar a birkice,yayin da ummin tata itama hankalinta gaba daya yake kan zahran a fakaice,don a zahiri ba zaka ce hankalin nata yana kanta ba.
Ko kafin tace komai haidar yayi sallama,a nutse yake takowa zuwa cikin falon,yana qoqarin rage zafi da radadi da yake ji daga cikin qirjinsa zuwa maqoshinsa,kallo daya ummin ta yiwa fuskarsa tasan ba lafiya ba,don idanunsa nakan hajjan da zahran,hakan ya sanya ta miqe don basu waje,duk da can qasan zuciyarta hakanan ya cika da zulumi da fargaba,sai taji batason tafiya,amma saita tanqwara zuciyarta ta duqa ta dauki carbinta ta fice ba tare da sun ankara bama.
Tana barin cikin falon taji ta kasa sake daga qafarta,abinda bata taba yiba kaf tsahon rayuwarta ta tsaya sauraren zancan wasu koda kuwa ya shafeta,amma a yau din sai taji tabbas tana son jin me ya faru?,wanda jikinta ya bata kan zahra ne,don ba haka ta saba zuwa gida weekend ba.
"Kai zaki.....lafiya?" Hajja ta jefa masa tambayar ganin yadda idanunsa suka sauya launi,ya kafeta da ido ya kuma kasa cewa komai
"Gata nan hajja,a hotel na daukota" idanu hajjan ta zaro sosai,hannunta dafe a qirjinta
"Kai haidar,banason shirmen banza da wofi,kasan kuwa me kake fada?,otel fa kace!" Kai kawai ya jinjina mata alamun tabbatarwa
"Kai!,haidar.....na gaya maka banason sakarci ko?,ka gayan gaskiya" wannan karon sai yaqi tanka mata,illa lumshe idanunsa da yayi kawai bai sake furta komai ba,sai hajjan ta waiwaya inda zahra ke tsaye,tana jin kamar zata saki fitsari
"Innawuro....abinda ya fadi gaskiya ne?"kamar ta dora mata dala da gauron dutse haka taji
"Eh hajja....amma...." Salatin hajjan shi ya katse sauran magana da bayanin da tayi niyyar yi mata,yayin da umminta dake tsaye daga can bakin qofa ta soma maimaita
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,Allahumma ajirni fi musibaty,wa'akhlifni khairan min ha" daga haka ta ja qafafunta da take jin sun mata nauyi ta soma barin wajen cikin matsanancin tashin hankali,wani hazo hazo take gani a idanunta,a haka takai kanta bangarenta cikin mawuyacin hali.
"Zahra'u....hotel fa zahra'u,hotel aka ce fa?" Ta fada tana duban zahra wadda takejin inama ana iya maida hannun agogo baya ta maida ta goge dukkan wani kuskure data aikata nabin su hindatun da tayi
"Hajja....ki tsaya na miki bayani,wallahi ba abinda kuke zato bane,ba abinda kuke tunani bane....na rantse d...."
"Rufemin baki....zahra'u ai yau ni kika kunyata,ni kika baiwa kunya wallahi,oh ni fadimatu" hajjan ta fada cikin matsancin firgici tsoro da kuma tashin hankali
"Matsa daga kusa dani,tashi ki ban waje nace" karon farko da hajjan ta taba korarta daga inda take tunda suke a rayuwarsu,hakan yasa taji wani sabon tashun hankalin ya rufto mata,saita kasa jurewa ta kwasa da gudu tayi daki.
Shikam haidar na tsaye,sai a sannan ya bude idanun nasa,ya juya ya soma takawa zaya bar falon
"Haidar....zo nan" hajjan tayi kiran sunansa tana qoqarin binne tashin hankalinta,baice komai ba ya dawo ya tsaya daura da ita,ta masa kallo na tsaf,ta karanci yadda ranshi yake masifar bace
"Bana son naji maganar nan a bakin kowa haidar....banaso" idanunsa ya bude sosai yana kallon hajjan,kamar ba zaya tanka sai kuma ya bude bakinsa
"Me yasa zakice haka hajja?,sai yaushe xaki daina bata kariya kan dukkan laifin data aikata koda kuwa muninsa yakai wannan?,wannan kariyar ita ta zame mata rigar da take iya shiga ta buya a ciki,taci gaba da aikata abinda ranta yaso a sanda taso ba tare data samu wata tirjiye ko kuma shamaki da zai hanata kaiwa ga ci gaba da aikata mara kyau ba....don Allah hajja wannan karon....ki cire soyayya ko qauna,ki kuma kauda kai,ki bari ayi hukuncin dashi yafi dacewa"
"Haidara" hajjan ta sake kiransa karo na biyu
"Nasan zahra'u ciki da bai,na santa sanin dako mahaifiyarta bata sani ba,ni ina ji a jikina,ina jin cewa zuwanta ko ganinta a wajen baya nufin ta aikata ko tana aikata wani mummunan abu ne,kuma nasan bayanin da taketa qoqarin yimin kenan,saidai naqi bata dama da wuri tayi bayanin,har sai rashin bata damar ya zama wani hukunci mai zaman kansa a gareta,nayi imanin jinina bazai taba aikata wata mummunan alfasha har kamar haka ba,addu'a ba qarya bace" shuru yayi ransa yana baci,yana ganin hajjan tana bata kariya ne kawai saboda kada ta fuskanci hukunci,wanda hakan ya jima yana bata masa rai,shin ita hajja bata ganin sauyi qarara tattare da yarinyar ne?,har sai yaushe sannan zata ankara su yiwa tufkar hanci?,duk wasu doka da qa'idoji na gidan hajjan da karan kanta tasha karyasu indai akan yarinyar ne,wannan shine dalilin da yasa sam yarinyar bai hada idanuwa da ita,saboda yana da yaqinin duk sanda ta masa wani abu mai kama da sangarta ko rashin kunya zai iya ɓaɓɓalata ya zubar.
Saiya juya kawai yaci gaba da takawar,hajjan nada wani irin girma da qima a idanunsa,amma yana jin sam hukuncin bai kwanta masa a rai ba,saidai kodon saboda girmanta da matsayinta bazai iya tsayawa yayi ja'inja da ita ba,a haka ya fice ba tare daya sake cewa komai ba.
************
Kwana uku da dawowartata amma sam hajja taqi tsaiwa ta saurareta ko taji bayaninta,wanda hakan yayi mugun daga mata hankali,don hajjan itace last chance dinta,tana da yaqinin koda kowa yaqi saurarenta,koda kowa yaqi yarda da ita zata samu dukkan wadan nan abubuwa daga wajen hajjan tata.
Cikin kwana ukun ta rame ta fada saboda fargaba,sai a rana ta ukun hajjan ta tsaya da qyar ta saurari bayaninta,ta yarda da ita ta kuma gamsu,saidai tasha fada da masifa daga wajen hajjan irin wadda bata taba yi mata irinsa ba,duka bai damu zahra ba,tunda ta samu abinda takeso,sai data gama fadanta tsaf ta miqe sannan tace cikin dari dari da tsoron amsar da zata bata
"To hajja makaranta,anata CA bana nan" wani kallo mai kama da harara tayi mata
"Saiki jira kiji abinda yayanku zaice,don shurun da yayi kan zancan bazan sake tilastashi kan makomar makarantarki ba"
"Sai kace shine uban kowa cikin gidan nan?,koshi ya haifi kowa?" Abinda zahra keson fada kenan,amma tasan fadin hakan shi zai sake dagula komai,bata ma isa tace din ba,haka taja bakinta tasa masa zip ta zuge ta zubawa sarautar Allah ido,cike da fargaba kada ta rasa abubuwa masu muhimmanci acan makaranta.
Har hajjan takai bakin qofa ta waiwayo
"Waye haisam?" Tambayar data daurema zahra kai
"Haisam kuma?" Zahran itama ta maimaita sunan ta sigar tambaya wa hajjan
"Eh shi" nazari kadan zahra ta fada,tafi kowa sanin cewa ta jima da yiwa kanta shamaki da duk wani da namiji bare tace ko yana da alaqa ne da rayuwarta,don haka ta girgiza kai
"Bansanshi ba hajja" kai ta jinjina
"Bari yayankun ya dawo" bin hajjan kawai tayi da kallo saboda ta kulle mata kai,waye haisam din?,kuma meya hadinsa da yaa haidar?,data kasa canka saita tattara tunanin duka ta watsar,koma waye kuma koma.meye matsalarsu ce,itakam ta jima sa cire sabga ko sha'anin maza daga tsarin rayuwarta,hakanan ta dade da ciresu daga cikin jerin matsalolinta da zasu dameta.
Tun randa ta dawo a daren hindatu ta nemeta basu ganta ba,washegari tazo gidan,ta gaya mata lafiya lau,kada ta damu karsu nemeta,zata nemeta da kanta.
Tunda hajjan ta fita take kwance tana saqa tana warwara kan yadda lamarin zai warware mata cikin sauqi ba tare da wata matsalar ga sake sawo kai ba,tunda tana fatan wannan ta mutu,a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita.
*_ABINDA KA SHUKA_*
A nutse take tafiya kan hanyarta zuwa gida,tun daga nesa take hango mutum biyu,daya a tsugunne daya a tsaye bisa saman kansa,haka taci gaba da tahowa tana matsar inda suke harta qaraso dab dasu,sai a sannan taga fuskokin mutum biyun sosai.
Na tsugunnen abdulyassar ne,na tsayen kuma auwal ne,sam babu alamu na walwala ko farinciki kan fuskar abdulyassar din,face ma uban gumi da yake hadawa,fuskarshi amurtuke sosai.
Kai ta dauke zata gotasu taji an riqe hijabinta,saita juyo da sauri,auwal ne,ya soma magana cikin zallar damuwa kamar zaiyi kuka
"Haba zahra....yanzu kina ganin abdulyassar haka zaki wuceshi ba zaki kulashi ba?,don Allah ki dawo ki tambayeshi me yake damunsa?,wallahi kinga munyi munyi ni da hajiyarsa ya gaya mana abinda yake damunsa yaqi cewa komai tun daxu,babu yadda bamuyi dashi ba,munyi munyi ma ya tashi daga nan amma yaqi" hijabinta ta fincike daga hannun auwal din tayi gaba abinta,tana jin auwal din na kiranta,tana kuma hangen yadda abdulyasar din yaci gaba da zama awajen.......
(Exactly haka yarinyar tayi mafarkinsa kwana biyar da rasuwarshin,na manta ban kawoshi tun a sannan ba saboda ajizanci na mantuwa).
Firgigit ta farka daga baccin daya dauketa din,ambaton sunan Allah ta shiga yi tana tunawa daya bayan daya dukkan abinda ya faru cikin mafarkin,a yanayin da taga abdulyasar din yana cikin damuwa babu ko shakka,saita miqe ta soma cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya,har a sannan mafarkin na maqale cikin ranta,saboda haka koda ta fito falo ta zuba abinci tana ci hajja ta soma baiwa labari.
"Zai iya yiwuwa haqqinku ke tambayarsa,ki yafe masa idan kinsan a baya baki yafe masa ba" baki zahran ta tabe
"Ni na yafe masa mana hajja,yaji da haqqin sauran da bansan adadinsu ba,da marasa zuciyar tausayi da zasu kasa mancewa bare su yafe masa".