← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 69

Sashe 64

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari shi da ita kadai suka fita wani waje,bayan sun biya sun gaida su hajja,yadda ta dinga sussunne kai da jin nauyinsu su duka ya alamtawa hajja me afkuwa ta afku,duk da ba haka taso ba,taso sai bayan anyi taron biki an kaita amma ba abun damuwa bane,tunda already matarsa ce.....da fatan alkhairi ta bisu sanda suke ficewa,saita lura mama ma idanunta yana kansu fuskarta na nuna farincikin dake qasan zuciyarta.

Karo kusan na hudu kenan tana hada ido dashi sanda suke zaune saman table din daga ita saishi,waje ne me kyau,wanda kallonshi kawai ya isa ya sanya zuciya ta debe kewar dake damunta,gabanshi shi babu komai face ruwan roba,sanda aka kawo menu ita ya zabarwa abubuwan da za'a kawo mata,wanda kusan duk abubuwan kwadayi ne,yatsunsa ya sarqafe kawai cikin na juna ya zuba mata idanu yana kallon duk wani motsi nata,kyau take qara yi masa,qaunarta yakeji har babu iyaka.

Karo na qarshe da suka hada idanu tadan kwabe fuska kamar mai shirin yin kuka,murmushi ya sakar mata yana girgiza kansa,gyara zamansa yayi still dai baibar kallonta ba,a hankali yace
"U r my first love" cikin mamakin furucinsa ta dakata daga kai ice cream din data debo bakinta ta zuba masa idanu alamun son qarin bayani,kai ya gyada mata
"Yes u r"Saita samu kanta da tattara dukkan hankalinta a kanshi,cike da mamaki take dubanshi
"Tun lokacin da aka haifeki na fara sonki,a lokacin da nike tamkar ɗa a wajen ummi,duk da na fara samun qanne a lokacin,amma sanda aka haifeki ji nayi sai a lokacin na samu qanwa,a sannan ni kadai kike yarda dani baya ga ummi kaf fadin gidan" yana fadin haka saita tuna sanda hajja ke bata wannan labarin,amma a lokacin ta zata hajjan na fada ne kawai saboda taji dadi a ranta,kota rage kaifin jin haushinsa da rashin jituwar dake tsakaninsu
"Sannu a hankali kina qara gama inajinki cikin zuciyata da gangar jikina,hakan yana yiwa ummi dadi,amma takan kwabeni kan...nayi a hankali,kada kulawar da nake baki tasa ki sangarce,saina fara sanya lura da nutsuwa,a sannan sai na lura da kin fara tabara saboda gata da kike samu daga wajen hajja itama,duk gidan kece ta gaban goshinta fiye da kowa,saboda sunanta da kikaci,sannan kuma cikin jikokinta kinfi kowa wuni wajenta,tunda jima sashenta shine wajen zamana a yawancin lokuta.

"Lokacin da kika fara girma a sannan na zama saurayi" saita kalleshi,murmushi ya subuce mata,saboda fadar hakan da yayi ya tuna mata da abubuwa masu yawa,ta kuma gane dai dai lokacin da yake nufi din,shima murmushin ya sake mata mai sanyi sannan yaci gaba
"A lokacin na fuskanci kaf cikin sa'anninki da tsararrakin kin fisu tsiwa.....kafiya...rashin tsoro da kuma taurin kai,kuma kamar hakan ya faru ne saboda kulawa da hajja ke nuna miki,kinsan dalilin da yasa na aje soyayyarki?,wanda ya zama musabbin da har yau babu wanda yasan ina sonki?" Kai ta girgiza a hankali cike da daukin son jin ci gaban labarin
"Abu na farko da ya sanya naji ya cancanci na ajeshi shine ummi....ummi na nuna miki qauna da soyayya qwarai,hakanan ta azani a matsayin yaya a gareki,wanda ya isa da duk lamuranki,ya isa ya yanke hukunci cikin rayuwarki fiye da sadiq.....sai nayi tunani a karan kaina,matuqar naci gaba da sonki har aka kai sanda zaki sani koki fahimta....to ya zamana babu me tsawata miki kenan kan kiyi koki bari?,idan har na aureki kenan babu sauran wanda zai dinga taka burki akan al'amuranki?,komai zakiyishi yadda kike so?,hakan zaiwa ummi dadi?,ko kuma zaifi mata dadi idan naci gaba da tsaiwa kan rayuwarki ne?.....hukuncin na aje din shi nafi ganin dacewarsa,saboda haka na ajjiye dukkan wata soyayyarki da nakeji a cikin raina,na shiga treating dinki kamar sauran,na kuma qara matsa lamba fiye da baya,abunda ya kuma sawa naji na gamsu da hukuncin da na yiwa kaina,sabon suna da suka miki inna wuro,uwar masu gida ko?,hakan na nufin kiyi abinda kikeso,sannan lokaci qalilan daga dan fara tasawarki samari suka yiwa rayuwarki caaaaaa.....naso hajja a lokacin ta yarda da tsarin da naso kafawa a kanki amma fur taqi,saboda tana ganin na fiya matsantawa,bana duba maraicinki.....kinsan wani abu?" Saita girgiza kai a hankali,labarin da yake batan yana mata dadi sosai
"A duk sanda wani yazo ya kuma yaudareki ya gudu.....na fiki jin ciwon faruwar wannan,nakan jima ina jin raina yana baci,duk da nakanji kishi,nakanji bacin rai duk sanda kike tsaye da wani da sunan saurayi,to amma sai zuciyata ta gayamin,tunda ka aje soyayyarta ka zabi bata kariya,dole zuciyarka taqi ji taqi gani,dole ka daure ka zama jajirtacce,ka fuskanci dukkan wani qalubale,na karbi wannan magana,na kuma sake jaddadawa kaina hakan,dalilin da yasa na karbi zahra takwararki kenan,na soma nazartarta da halayyarta....."sai yadan tsaya yana aje numfashi idanunsa kan zahran yadda ta nutsu tana saurarensa tana kuma fahimtarsa
"Am sorry to say....tana da haquri....tana da sanyin hali,uwa uba nutsuwa da kamewa,sannan kuma sunanku daya,wadan nan dalilai sune kadai suka sanya na miqa mata wuyana,saboda nasan wadan nan halaye zasu dai dai da tawa dabi'ar da halayyar,zatona da hasashen saiya zama gaskiya,ta fahimceni fiye da yadda na zata,ta kuma banbance abinda nakeso da wanda bana so,a hankali sai zuciyata ta fara samun nutsuwa da sukuni,na kuma gamsu zahran ta dace dani,saidai duk da haka baki fita daga zuciyata ba....sau tari nakan tura mata saqo wanda a zahiri sanda nake rubutashi dake nake,saidai nasan cewa koda baki sani ba kai tsaye,kuna karbar wayarta,kuna kuma shiga inbox nata,idan akayi katari kika karanta to kamar na rage wani nauyi dake zuciyata,na kuma isar da saqona,don yawancin lokuta tana gayamin yadda kike nuna zallar mamaki idan kikaci karo da daya daga cikin saqonnin dana tura matan.....bazan boye miki ba....nayi missing zahra'u,na kuma shiga tashin hankali na haqiqa sanda na rasata,har nakejin ma kamar bani bane....kamar zan zauce....na jima....na jima ina dorawa kaina alhakin mutuwarta,saboda ta rasu ne a sanda naje makaranta ganinta,da wani yammaci,na dawo daga gwambe,na tsaya ta wudil ganinta,saboda munyi waya tun ina hanya.

"Sanda na shiga makarantar na sameta shuru,kamar irin anyi hutu dalibai sun kokkoma gida,to amma nasan ana tsaka da zangon karatu ne,ba lokacin hutu bane,waya na daga na kirata da zummar bata mamaki,don batasan da zuwa na ba,na gaya mata inda nake tsaye,cike da zumudi da mamaki tace gata nan fitowa,saina maida wayar aljihuna ina duban inda nake tsayen,wajene mai yalwar bishiyoyi dogaye da kuma tarin ciyayi mai tsaho,tunda nake zuwan mata makarantar lokaci zuwa lokaci bamu taba tsaiwa a wajen ba sai ranar,ina cikin karantar yanayin wajen naga bullowarta ta gefena,kamar kowanne lokaci cikin hijabinta,tana tafe tana murmushin ganina,saina bata dukka hankalina harta qaraso.....
"Me ya faru yau naga makarantar taku yau so silent" tambayar dana fara mata kenan
"Wallahi tun jiya da aka samu fitowar macizai ne,sai kowa ya tsorata ya lazimci zaman daki,don yau ko lactures ma ba'ayi ba" kai na jinjina sannan nace
"Amma da kin gayamin da bazan shigo ba bare na fiddoki daga daki" dariya tayi
"To na godewa Allah da ban gaya maka ba bare ka haramta min ganin fuskarka....komai muqaddarine ai daga ubangiji,koda ina daki duk abinda ya qaddara zai sameni saiya samenin"basai na gaya miki sauran abinda tace min ko nace mata ba...saboda tsaro ba don tsoro ba" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi tana girgiza kanta,idanunta a kanshi,ajiyar numfashi yayi
"Yau soyayya ta sani dogon magana.....a taimakamin da ruwa" hannunta ta sanya ta bude masa gorar ruwan sannan ta ajjiye masa,ya dauka a nutse ya soma sha,yana sha yana ajewa yashaqi numfashi har ya gama,ya aje robar yana sauke numfashi tsahon minti daya sannan ya dora.

"Bari na samo maka abun sha a wani kanti nan" ta fada ta soma takawa,da hanzari na tsaidata
"A'ah....ni ganinki kawai nazoyi,bana buqatar ci ko shan komai" kafada ta maqale
"Ban yarda ba....saboda nima irin karamcin nan naka nakeso na koya,saboda haka saina samu ladan baqona" daga haka ta soma takawa ta cikin ciyayin nan tayi gaba,a cikin zuciyata inason tsaidata amma kamar wanda aka daurewa baki na kasa,inasin ince kada tabi ta wannan ciyayin amma na kasa fada mata,inason ince mata ta tsaya na rakata amma dukka kamar wanda aka daurewa baki duk na kasa fada,ashe ajali ne,ajali ne ya kirata,don batayi wani nisa da idanuna ba naga gilmawar wani abu ta bayanta,na fuskanci maciji ne,idan nayi magana kuma zata iya rudewa,don haka na fara takawa da wani irin hanzari da zafin nama,dai dai sanda ta waiwayo tana kallona,sai fuskarta ta nuna mamakin ganina ina tahowa inda take da mugun gudu,bansan ya akayi ba saijin ihunta nayi ta durqushe cikin ciyayin.

Sanda na isa na sameta riqe da qafarta,ta hada gumi sharkaf tana juye juye,dana dauke hannunta saiga inda macijin ya sareta nan,na bata taimakon daya dace,na riqeta zuwa asibitinsu na cikin makaranta,saidai abun haushin abun takaici basu da allurar kashe gubarsa,raina ya baci sosai,amma ban tsaya biye musu ba,saboda kada bata lokaci ya jawo asarar ran da naketa gudu,na sanyata a mota kawai muka wuto zuwa kano.

"Irin gudun dana dinga tsalawa ni kaina nasan Allah ne kawai yayi motar ba itace ajalinmu ba nida ita gaba daya,tana cure waje daya set din gaba taba murqususun ciwo da azabar dafin daya zuba matan,hankalina rabi ga titi rabi a kanta,qarin abun haushin asibiti manya guda biyu mukaje suma basu da allurar a dai dai lokacin ta qare,sanda muka dauki hanya zuwa asibitin mu a sannan ta kalleni,launin idanunta yana canzawa
"Kayi haquri ya haidar....kayi haquri,kuma naga ranka ya baci,duk abinda Allah ya shiryawa bawa bai isa ya tsallake mishi ba" saita maida kanta ta kwantar,kalamanta suka dagan hankali,na tsaya gefan hanya sanda naga yanayin jikinta ya saki gaba daya.

Nasan a sannan ta mutu don zuciyata tana gaya min haka.....amma idanuna a rufe suke,saina tashi motata da mugun gudun da yafi na dazu na nufi asibitin,saidai abinda nake tsoro dai shi aka gayamin,zahra ta rasu,dafin yaci jikinta yakai inda ba'a so yakai......"saiya tsaya da bata labarin yana duban yadda hawaye ke zuba a idanunta,a wancan lokacin sam batasan yadda mutuwar zahra ta kasance ba,kawai dai tasan saran maciji ne,hakanan tana ganin haidar yaqi daukan qaddara ne kawai,amma data kwatanta mutuwar masoyi ko aboki gaban idanun abokinsa sai taga abun ba mai sauqi bane,dole ya shiga irin yanayin daya shiga din,kasa jurewa tayi,sai tayi qasa da kanta kuka na kubce mata42
Chapter 64 · 0% Book details