Sashe 44
Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nutse ya bude murfin motar ya shiga sannan ya rufe,yana shirin saka key ya kunna motar idanunsa suka kai kanta,ya dubi yadda ta cure waje daya,sai haka ya tuna masa da zahra....lokaci na qarshe a rayuwarta daya dauketa cikin motarsa,lokacin da take nemam agaji a sanda bashi da abinda zai iyayi mata,a haka a cure waje daya a sit din da wannan zahran ke kai,sai yaji wani abu ya tsarga masa tun daga kanshi har zuwa qafafunsa,sai daya furta can qasan maqoshinsa
"La haula wala quwwata illa billah" sannan ya bude idanun nasa ya tada motar suka fice daga wajen cikin tuqi a hankali saboda yadda ruwan saman yake qara qarfi.
Sannu a hankali suke tafiya bisa titin,haka kawai ya samu kansa da waiwayawa ya dubeta lokaci zuwa lokaci,time by time takan motsa ta kuma cije labbanta saboda ciwon da take jinsa har gadon bayanta.
A qalla sun shafe kusan minti talatin sannan suka qarasa unguwar tasu,yayi horn aka bude musu ya sanya motar tishi ciki ya ajeta a wajen adana motoci na gidan,saiya kashe motar,ya zubawa waje idanu ta cikin glass din motar yana kallon yadda ruwa ke gudu yana sauka da qarfinsa,a irin wannan yanayin da lokacin zuciyarsa na masa wani irin fes,tamkar ruwan na sauka ne saman zuciyarsa,saiya sanya hannunsa ya bude murfin motar ya fita,ya ware lemar hannunsa.
A kasalance itama ta bude murfin motar ta zura qafafunta tana rufe ido saboda yadda ruwan ya soma feso mata,duk da haka bata fasa fitowar ba,don babu abinda take buqata a yanzu irin ta samu waje ta kwanta sosai ko zata rage azabar da takeji.
Qanqame jikinta tayi waje daya ta soma nufar cikin gidan,saidai batayi taku biyar cikakke ba taji an lulluba mata abu saman kafadunta.
Kanta ta dago sanda yake dora mata lemar hannunsa tsakanin hannayenta,kafin takai ga kallon qwayar idanunsa tuni yayi gaba,cikin kuma ruwan saman dake saukowa yana dukan suit din jikinsa daya cire 'yar saman ya rufa mata,mamaki ya tsaidata,sai kuma tasoma takawa itama zuwa cikin.
Kamar wanda ya tuna wani abun saiya kuma ya tsaya,sannu a hankali ta iskeshi harma ta wuceshi sannan ya rufe mata baya,tana gaba yana bayanta har suka isa qofar falon.
Zagayeta yayi ya matsa bakin qofar ya sanya key din ya bude,sai yaja baya ya tsaya,taja qafafunta ta shige,da qyar ta qarasa dakinta ta zube saman katifa tana juyi.
A qalla ta kusa minti talatin babu wani sauqi,kadaici da zama ita kadai ta qara ta'azzara mata ciwon,sai qwalla ta cika mata idanu,nan da nan suka fara gangarowa,tana rayawa a ranta inda yanzu ace tana gida babu shakka da tuni an sama mata magani,koda babu magani akwai kai kawon jama'a da zai dauke mata wani abu daga ciwon komai qanqantarsa.
A nutse yake takowa cikin falon bayan yayi wanka da ruwa me dumi sosai ya sanya kaya masu dan kauri saboda ruwan daya dakeshi daga gun ajiye mota zuwa cikin gidan,har yanzu ruwan ake tafkawa bai tsaya ba bai kuma sassauta ba,garin gaba daya ya fara daukar sanyi,saman dining ya qarasa ya samu abinci yaci,ya gama yana sauko ya nufi daki don sanyin daya soma busawar ya fara sashi jin takura,bargo kawai yake da buqatar shiga.
Har zai shige dakin nasa kuma saiya dakata
"Amanar Allah ce a hannunka" ya tuna zancan mamanshi,saiya sauya akalarshi zuwa dakin nata.
Yana shiga ya sanya hannu da sauri yana kashe fankar dake faman wulwulawa kamar babu sanyin ruwan sama,sannan ya dauki remote yayi controlling sanyin da acn ke bayarwa sa'annan ya waiwaya saman katifar dakin.
Can ya hangota cikin bargon tana mutsu mutsu,duk da baka iya ganin koda kanta
"Wayyo Allah na" daya kasa kunne yaji tana fada qasa qasa,saiya qarasa da sauri ya haura zuwa saman katifar ya tankwashe qafafunsa,sannan ya saka hannu yana yaye abun rufar dai dai sanda ta qaraso dab da ita yake zaune garin mirgin mirgin din da takeyi
"Ya Allah" ya fada a hankali yana duban yadda take riqe da qirjinta,tun asali shi mutum me mai tausayin mara lafiya,abu na farko dake daga masa hankali,lalura da kuma raunin 'ya'ya mata.
Miqewa yayi tsaye da sauri yana ciro wayarsa daga aljihunsa,idan bai manta ba ya taba zuwa hutu gida lokacin bata da lafiya irin haka,yaji hajja tana cewa ulcer ce,da alama yanzun ma itace.
Kai tsaye number jafar ya kira,bugu uku ya daga
"How far oga?" Ya fada a sake
"Nasreen tana kusa?"
"Eh....Allah yasa lafiya"
"Lafiya.....amm...." Saiya rasa sunan da xai kira zahran dashi,daga qarshe yace
"Madam ce ba lafiya,ulcer dinta ta tashi....ko zata turamin medication da zata iya sha da zasu bata relief koda zuwa safiya ne?"
"Ok hold the phone" ya fada,sai yajishi yana magana duk da baijin me yake cewa,da alama tana kusa dashi ne,tsahon second talatin sannan yaji muryar jafar din,ya gaya masa magungunan da zata sha din,ya masa godiya sannan ya kashe kiran,ya sake kiran wata number sukayi magana,ya tura sunan magugunan sannan ya katse kiran nan ma yana maida dubanda dai a kanta,har yanzu babu wani canji da sanda ya shigo,yana tuna yadda ummi ke damuwa isan bashi da lafiya,ta miqa dukkan kulawarta akanshi,ya kamata shima ko yaya a yanzu ya kamanta akan jininta,saiya koma bakin katifar yadan tsugunna,yasan cewa bataci komai ba,yakan ji wani lokacin yadda suke daga da hajja idan bata da lafiya kan cin abinci,don haka yace, mata
"Tashi ki samu wani abun kici kafin a kawo magani" kaita girgiza masa alamun ba zataci ba,saiya dan xuba mata idanu na wasu sakanni,ba tare da yace da ita komai ba ya tashi ya fice.
Kusan minti talatin ya sake dawowa dakin,hannunsa dauke da wani irin mazubin abinci mai kyau,mai dauke da tambarin wani waje,ya qarasa ya janyo table din dake dakin ya dora akai,yana shirin miqewa wayarsa ta dauki ruri,ya daga yana amsa sallamar,wanda ya aika siyo magani ne ke shaida masa dukka pharmacies din a rufe suke
"Ok....thanks" ya fada a gajarce yana katse kiran
"Tashi kici abinci" ya kuma fada yana juyawa ya fice a dakin.
Bai wuce minti biyar ba ya dawo dauke da wata butar shayi me qananun kofuna,ya ajeta inda ya aje wancar ledar a hankali yana furxar da iska daga bakinsa,saiya dubeta still dai tana kwancen bata tashi ba,sake maimaita mata yayi ta tashin,saita girgiza masa kai alamun a'a
"Ki tashi nace....ina wasa dake ne!" Ya fada a dan tsawace,wanda hakan ya tilastata yaye bargon da take ciki,hawaye ne jage jage a idanunta,da gumi daya jiqe mata fuska,da alama zazzabin daya soma rufeta ne yake sauka,saita zauna sosai ba tare data miqe din ba.
A hankali yake takowa direction dinta,fuskarshi a dinke idanunsa a kanta,ya isa gabanta ya duqa a hankali ya riqo hannunta ya dagata cak ya miqar da ita tsaye,duk sai tajita wani irin a mugun takure,duk da ciwon da takeji,don babu mayafi a jikinta bare dankwali.
Taku biyu yayi ya hade tazarar dake tsakaninsu,kafin ta ankara ya jata zuwa qirjinsa kamar mai shirin rungumeta,ajiyar zuciya ta subuce masa a sirrance,ya dora hannunsa a hankali a bayanta yana lalubar zip din rigarta,saita sandare a tsaye tana raba idanu,jikinta ya dauki rawa gaba daya lokacin da taji ya kama zip din ya soma zugeshi zuwa qasa
"Zzzzzan...." Take fada bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yakeyi,ko harafi daya ya kasa fitowa daga bakinta,har sai da taji yakai zip din qasa,rigar ta rabe gida biyu,taji hannunsa saman kafadarta,yana nufin sabule mata rigar xaiyi?,ta tambayi kanta da kanta,ai batasan sanda ta cafe tsintsiyar hannunsa ba cikin hawaye tace
"Zanc.....zan cire da kaina" nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana zame hannunsa daga cikin nata,don dama yana tunanin ta yadda zai qarasa aikin da yake pretending din yin,saiya taka da baya da baya,sannan ya juya bayansa,ya tafi zuwa window din dakin ya yaye labulen ya bude glass din ya saka kanshi a ciki yana sake sauke ajiyar zuciya gami da fidda iska daga bakinsa zuwa hancinsa,yana jin wani irin yanayi cikin jikinsa.
Kamar wata sakarya ta riqe wuyan rigar gam,tana tsaye tana rawar sanyi,tana kuma satar kallon yadda ya juya mata baya,yana nufin yana dakin xata canza kaya kenan?,idanunta ne suka sauka kan qofar toilet,sai tayi sauri ta nufi bandakin itama tana sauke ajiyar zuciya.
Bata jimaba ta fito sanye da hijabi,kamar yaji takunta ya waiwayo a hankali,Ya qarasa inda ya aje kayan,sannan ya biya ta gaban mudubi ya dauko wiper da yakan ajjiye saboda goge busashen abu,sosai ya zauna a gabanta har gwiwarsa na gogar tata,ya ciro daya daga cikin wipes din ya kamo fuskarta tsakiyar hannunsa sannan ya fara dauke duka powdern dake fuskarta.
Idanunta ta rufe gam,sanyin wiper din na ratsa fatarta,numfashinsa dake fita anutse na dukan fuskarta,yayin da kuma takejin nauyin idanunsa dake yawo saman fuskarta.
Kowanne waje idan ya saka wiper ya goge saiya kalleshi,sosai yake ganin kamanninta wanda a baya ko za'a tsireshi baisan ya fuskarta take ba,manyan idanu dake qawace da gashin ido dogaye,daga samansu kwantacciyar gira ce mai yalwar suma itama wadda ta kusa hadewa da juna,a hankali harya gangaro kan lips dinta da suka jambaki,saiya sauya sabuwar wiper,ya saka dan yatsansa a cikinta ya dora saman lips dinta ya fara gogewa.
Jikinta ta qanqanme saboda ji take kamar yana mata tafiyar tsutsa,ta gefan aliyyu kuwa haka ya dinga goge jambakin ainihin kalar labbanta na fitowa,baisan cewa ya jima yana gogesu ba sai da zahra da har yanzu idanuna ke rufe tace
"Zafi"saiya janye hannunsa da sauri yana sake daure fuska,sai yaja tsaki qasa qasa sannan ya aje abincin gefanta,ya miqe ya fice yana yarfe hannu,gami da tuhumar kansa,me yasa bai bar mata kwalliyarta ta goge da kanta ba?,daga bisani ya aza hakan a matsayin kyautata zai gwada yi mata kamar yadda mahaifiyarta ta gwadawa tashi rayuwar.
A hankali take cin abincin kamar ta rusa kuka saboda yadda sam baya mata dadi a bakinta,ga numfashinta dake wani irin nauyi,bata ci da yawa ba ta ture kwanon ta koma rub da ciki,a yanzu duk yadda taso ta daure dauriyarta ta qare,ta soma raki a bayyane don ta kasa yin shurun.