← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 69

Sashe 42

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta shirya cikin atamfa riga da skert da suka zauna sosai a jikinta,don bata da wata tufa data wuce atamfar,saboda tafi sonta sosai,gashinta ta gyara saita ware dankwalinta kawai ta yafa,tana jin yadda hanjin cikinta ke nade waje daya,dole tana buqatar abinci,sannan charging wayarta yayi low,tana da buqatar jona chargy,hakan ya sanyata dole fitowa falon.

Chargyn ta jona sannan ta nufi saman dining din,taja kujera daya ta zauna,ita kam gaba daya takaicin yadda namiji ke shiga kitchen godai godai da sunan kuku yayi girki take,namijin ma kafiri,dyk tsantsamin ya haidar din ya tashi a banza kenan take rayawa aranta,yanzun ma banda mahaukaciyar yunwar da take ji da kanta zata shiga kitchen din tadan dafa wani abu,sai ta janyo ruwan zafi ta hada tea kawai ta soma kurba,lokaci lokaci tana tunanin gida da abinda sukeyi yanzu,wani sashe na zuciyarta kuma tunanin makaranta takeyi.

Tunanin da take ne yasa bataji tahowarsa ba,sai qamshin turarensa daya cika mata hanci,hakanne ya ankarar da ita ta daga kanta,ashe tsaye yake a wajen yana buda kwanukan gami da duba abunda aka dafa din.

Sanye yake da wata fara qal din shirt cotton mai gajeran hannu,sai wando three quarter shima fari tas dashi,hakama slipper din qafarsa,duk wanda yasanshi ya sanshi dason farar tufa tun asali,saita ajjiye cup din hannunta tana fadin
"Ina kwana?" Ba yabo ba fallasa ya amsa,saidai bai dubeta ba,kana yaja kujera ya zauna ya fara kurban tea din shima.

Zata bar wajen yana duba uban saqonnin taya murna da suka cika mishi waya,yana amsa wasu wasu kuma ya wuce,don yawan saqonnin da 'yammatan sukayi mishi ma yasa sa yaga alamun mace bai budewa saiya wuce gaba
"Ki zauna ki rubuta duk abunda zaki iya buqata" ya fada a taqaice,saita amsa tana yin gaba,ta qarasa wajen wayarta zata dauka,dai dai sannan Williams ya buda qofar kitchen din zai fito,haidar dake cin chips ya kalli qofar ya maida idanunsa ga farantinsa,sannan yace masa ya koma ya fita ta baya,ya jirashi a waje zai sameshi a can,a ladabce ya amsa ya maida qofar ya rufe din.

Tana cire wayar saiga kira ya shigo,dr nasreen ce wadda tun a jiya sukayi musayar numbers na juna,sai taji taji dadin kiran nata,don haka ta wuce da a hannunta zuwa daki.

Sai data shiga ta samu waje ta zauna sannan ta daga
"Mrs dabo....an tashi lpy" murmushi zahra tayi,yanayin faran faran dinta kamar na hindatu,saidai nata maturely yake kamar yadda take nutsatstsiya tun daga fuska
"Lafiya lau amaryar jafar" dariya tadan saki
"Amarci ai mun bar muku,muda muka kwan biyu" sosai suka gaisa a sake kamar wasu tsaffin qawaye,sai tace da ita
"Ya shirye shiryen anjima kuma?,kin ganni a wajen gyaran kai,kantin wata babbar makeup artist ce,nace ko a nan za'a mana makeup na anjima iyi mana booking?,sai su biyo su daukemu daga nan mu wuce ko?" Idanu zahran ta waro waje,danqari!.....yo ita aita manta ma da wani zancan dinner ta anjima,baya ga haka ma ina ita ina saka kanta inda Allah bai kaita ba,shi kansa uban gayyar bata ga fuska ko alama ba bare ma aje ga batun zuwa makeup,waya aiketa bare yaga ta dade?,Allah ya taimaketa take qaryan da zatayi ta qwaci kanta ba tare da dr nasreen din ta fuskanci komai ba yazo mata,saita karyar da murya
"Ayyah....zanso hakan,amma kinsan halinshi fa,banjin anjiman nan zai yarda naje"
"A'ah....ya zai min haka,amma da bai kyauta min ba oga haidar,kuma ai ya sani mr and mrs ne.....let me call jafar ya masa magana ya barki..." Tana qoqarin tsaidata tuni har ta katse wayar,saita bita da sauri saidai an shaida mata busy,hakan ya tabbatar mata harta kira din.

Wayar ta aje ta dora hannu saman ka
"Innalillahi" ta fada jimantawa kanta,saita damu gaba daya,ta kuma zauna zaman jiran jin abinda zai biyo baya.

Minti biyar minti goma ashirin talatin awa daya biyu uku shuru dr nasreen bata kira tace komai ba,hakan sai yasa hankalinta ya kwanta taci gaba da sabgarta cikin dakin.

Cikin awa ta hudu taji ana knocking a qofar falon,saita share saboda tana tsammanin yana cikin gidan,jin knocking din na sake daduwa saita aje wayarta ta miqe.

Shuru falon babu kowa,saman table dinma babu komai duka an kwashe,dauke idonta tayi ta isa qofar ta bude,macace a tsaye sanye da uniform na sojoji,fara ce 'yar tsamurmura mai qaramin jiki,gefanta wata ce sanye da kayan gida,saidai ita waccan din tana da garin jiki,cikin fara'a suka soma gaidata,ta amsa musu fuska a sake sannan suka fara mata bayani
"Oga ne ya aikomu,za'a shigar da kaya,sannan kuma idan kin shirya zamu kaiki" matsawa tayi suka fara shiga da kayan abincine dasu lemuka da drinks,saidai kuma bata gane idan ta shirya ba,don haka ta jawo wayarta saiga kiran dr nasreen
"Dear yace zakizo....amma fa ki hanzarta,wata takewa,daga ita saimu"
"Ok to" ta fada badon ranta yaso ba,dondai kawai bataso tayi wani abu dazai fallasa abinda ke tsakaninsu ne da haidar din,sannan bugu da qari idan ta fitan ko banza taga gari,ta huta da wannan zaman kurkukun data wuni yi.

Daya daga cikinsu ce ta bude mata bayan lafiyayyar motar ta shiga,sannan suma suka shiga suka tada motar suka fice,mai gadi yaja qofar ya rufe.

Babban gurine wanda kana kallonsa kasan ya tattara mata masu aji da wayewa,tana shiga masu karbar custumers suka tareta,ta tambaya inda dr din take suka mata jagora.

"Oyoyo....kinyi sauri amma" dr nasreen din ta fada cikin fara'ar nan tata,sai zahran itama tayi murmushi tana zama inda ta matsa matan suka shiga hira kafin azo kansu.

Dr nasreen din tace a fara yiwa,tana ta addu'ar Allah yasa lokaci ya qure kafin azo a kanta,don har ga Allah bata so,saidai addu'ar tata bata ci ba,nan da nan aka gama yiwa dr din akazo kanta
"Lite makeup pls sis" ta fadawa me yi mata kwalliya
"Ok" tace tana gyada kai.

Cikin qalilan din mintuna saiga zahran kamar an sauyata da wata ne,bakin dr nasreen yaqi rufuwa,cewa take
"Kefa kada ki bada 'yan maza yau,wallahi kada kisa oga haidar yayi abun kunya gaba mutane,kinganki kuwa?" Murmushi kawai tayi bayan ta kalli fuskar tata a mudubi itama,tana sake dubawa nasreen din ta aje mata wata leda gabanta
"Ga kayanmu da xamu saka.....tunda ba'a gayyacemu biki ba da dear yacemin sun hadu dasu hajja tace masa kinzo na tanadar mana don mu saka iri daya...."
"Kai kai,duka dai dr?"
"Haba babu komai,mu saka sai suyi mana dauri,don naga tex din dear yace suna hanya" tayi maganar tana ware zaninta.

Wani irin lace ne mai azabar kyau da daukar idanu butter colour,dinkin da aka masa yayi masifar dacewa dashi,hakanan zahran kamar don ita aka dinka shi,kamar yadda ya zaunawa dr nasreen din sosai itama,sai duka kallo ya koma kansu sanda aka gamawa nasreen dauri aka fara yiwa zahra nata.
[10/8, 5:53 PM] Anty Rabi'at: 29
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
_______________________________

Dai dai sanda aka gama kira ya shigo wayar dr nasreen,ta dauka da hanzari
"An gama dear....gamu nan" saita sauke wayar tana duban zahra
"Ke....oganki ya matsu....yanata mita,muje" duk yadda zahra taso dr nasreen ta barta ta biya kudin kwalliyar qememe taqiya,haka ta biya sannan suka dauka kayansu suka fito.

Yaja saki gami da kallon agogon hannunsa yafi a qirga,idan banda kada jafar yaga kamar ya watsa masa qasa a idanu baiga abinda xai dakatar dashi xaman jira ba,shi totally ma bai shirya zuwa wajen dinner din ba gaba daya,hakanan yakejin baison yadda matansu ke karakaina a tsakiyarsu,sai yakega sam hakan bai dace ba.

Karo na qarshe daya kalla agogonsa,ya yanke ma ransa indai basu fito ba zaiyi tafiyarsa ne,saidai shi jafar din da ya daurewa qaryar zuwan qarqashi ya daukosu,ya daga kai da niyyar duban bakin qofar,saiya hangi fitowarsu sun jero a tare,dauke idanusa yayi daga kan dr nasreen ya maida kanta,murmushi ne kwance saman fuskarta,har fararen haqoranta na bayyana,da alama wata magana dr nasreen din ta fada data bata dariya.

Janye idanunsa yayi ya maida daya side din,har cikin zuciyarsa yaji inda ya maida din baiyi masa ba,ya sake canza waje,nan ma yaji baiyi masa ba,saiya dauke idonsa ya kuma maidawa inda suke tahowar.

Zuwa yanzu sun iso dab da motocin,kana iya ganin fuskokinsu tarwai ta hasken fararen qawayen da suka haske wajen,haka kawai ya samu kansa da xubawa fuskarta idanu,wane sashe na ranshi yaji yana baci ba tare da yasan dalili ba,saiya dauke idanunsa daga wajen,yama rufesu gaba daya sanda take qoqarin bude gidan baya ta shigo.

A tunaninta yana gaba,sai data shiga ta zauna ta maida murfin ta rufe sannan ta lura dashi,duba daya tayi masa ta kauda kai,kamar mai bacci,saidai kuma yanajin komai,fuskarsa kamar ko yaushe a hade dai,tabe baki tayi cikin ra ta tana mita,tana kallo motarsu dr nasreen ta wuce gaban tasu kadan,sai suma suka tsaya,dai dai sannan wayarsa dake aje tsakiyarsu ta dauki kuwwa.

Bai buda idanun nasa badai still ya laluba hannunsa ya dauka ya kara a kunne,murya can qasa taji yace
"Kuje kawai" sai kuma yayi shuru yana saurare na sakannin da basu wuce biyar ba sannan ya kuma magana
"Banjin zamu iya zuwa" still dai wayar tashi tana kunnensa na wasu sakanni,da alama akwai abinda ake gaya masa,saiya sauke wayar,ya bude idanunshin kana ya shiga ya rubuta gajeran sms ya tura sannan ya maida wayar inda take,shi kuma ya gyara zamanshi,kamar wanda dama can ya shiryawa zaman cikin motar ne.
Chapter 42 · 0% Book details