← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 69

Sashe 5

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naira hamsin ce tayi ragowa a layin nata,ta tuna zahra takwararta ce ta mata transfer kyauta ana ya gobe xasu koma hutu,tunda tace ga wanda ya tura mata kudin ta raba musu 50/50 a ciki sai taji credit din bai burgeta ba,amma yanzun zai mata amfani,don haka kai tsaye ta shiga rubuto lambobin nuraddeen daka wanda ta jima da haddacesu ta danna kira,take sunan my happiness ya bayyana saman screen dinta,ta kalli sunan ta saki murmushi tana kuma sauraron yadda wayar ke ringing.

Dab da zata katse aka daga,sallama ya fara yi mata,saita sauke a jiyat zuciya cikin shagwaba tace
"Nayi fushi"
"Afuwa,kaina bisa wuyana,kina raina inata son na karki,damac ce ban samu ba". Duk da uzuri ya nema amma sai taji banbarakwai,don wannan shine karon farko daya soma neman uzuri irin haka a wajenta,amma saita saki murmushi
"Nayi maka,amma fa lasam nayi kewarka da yawa"
"Nima haka princess,an dawo lafiya?"
"Lafiya qalau alhmdlh"
"Ya makarantar,ya mutan gidan?"
"Kowa lafiya lau" zai soma magana taji ana mata warning cewa kudinta sun kusa qarewa,daga bisani ta tambayeshi me yace
"Nace ne ina hajja da ummi"
"Duk lafiya na samesu....." Ta kasa kunne taji yace xai shigo a yau din,saidai tuni kamfanin waya suka katse kiran saboda qarewar kudin wayar tata,saita aje wayar gefanta tana dan dubanta,tasan cewa babu jimawa xai biyo sawun kiran nata,don haka ta zauna daura da wayar tana dan gyaran kayanta tana dakon kiran.

Harta gama gyaran bataji shigowar kira ba,sai data miqe tana shirin shiga bandaki ta watsa ruwa taji sautin shigowar saqo,ta miqa hannu da hanzari tana dubawa,saqon daga nuradden dinne
"Zan kiraki" abinda ya qunsa kenan,saita maida wayar ta ajjiye ranta tana cewa
"Lallai yau wanne irin busy happiness ya shiga haka" ta wuce bandakin bayan ta daura towel din wanka.

Aqalla minti goma sha biyar ta shafe a bandakin sannan ta fito tana mita
"Haba,babu inda yakai gida dadi,me za'ayi da makarantar kwana,babu abinda yakai gida dadi wallahi,inda a school ne ina ka isa ka dade haka,da tuni an matsanta miki daki fito,mtseww...wallahi badan yaaya da kuma ummi da bazan koma ba" da wannan qananun mitocin mata ta qarasa gefan qatuwar kafitar dake dakin ta zauna,wanda daura da ita 'yar drower ce dake jere da kayan shafe shafenta,zahra ba daga baya bace wajen son ado da kwalliya,hakanan idan ta fannin yawan sutura da kayan qyale qyalen rayuwa ne tana sahun gaba cikin 'yammatan gidan,saboda ta kowanne fanni yi mata ake dalilin maraicinta,qannen mahaifiyarta mata da yayan mahaifiyar nata dake matuqar qaunarta,wanda dukkan abinda xaiwa yaransa to lallai fa saiya yiwa zahran,hakanan 'yan uwan mahaifinta dake gidan,duk sanda wani xaima iyalinsa saiya hada da ita,ga hajja a gefe itama da ba'a barta a baya ba.

Sa'annan uwa uba wani irin farinjini da Allah ya yiwa zahran tun tana mitsitsiyarta,don mahaifanta ma sam basa yarda a karbi abun hannun kowa akan yarinyar,haka halittarta take,tun abun na baiwa mamanta mamaki harya koma bata tsoro,hakan ya sanya tun kan ta mallaki hankalinta ta tsaya kai da fata wajen mata addu'ar samun kariya da samun miji na gari,don ita kanta tasan Allah ya yiwa diyartata baiwar wani asirtaccen boyayyen kyau,tana tsoro n kada hakan ya zama wata sila da za'a shiga rayuwar diyartata a cutata mata babu dalili,ta sani cewa sautari baiwar kyau jarrabawa ce,qalilan ne kuma cikin mutane ke iya cinyeta,musamman mata.

A nutse ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar atamfa cotton mai budadden dinki,ta gyara kanta da ribbom wanda da wahala kaga kitso a kanta,duk wanda ya santa yasan bata qaunar kitso tun yarinta har zuwa yanzu data girma,duk sanda xa'a mata kitso saita tarawa mai kitson jama'a saboda tsabagen kuka,daya daga cikin abinda ya sake sawa basa jituwa da yayanta kenan,yana ganin kamar an bata ta ne an sangarta ta.

Tana tsaka da fesa turarenta mai sanyin qamshi wanda ta saba ta soma jiyo sautinsa.

Sassanyar murya mai zaqi,amma cike da kaushi da kuma fada yake magana,da alama wani abun ya faru ne,baki ta tabe tana aje turaren nata,maimakon ta fito yadda tayi niyya da farko sai kawai ta fasa,ta koma gefan katifar ta zauna tana sauraren fadan nashi,duk da cewa bata iya fuskantar me yake fada.

Baki ta sake tabewa karo na biyu
"Ayi mutum sai shegen kaushin hali da fushi,Allah ya kyauta" ta fada tana jawo filo bayan tayi rub da ciki saman katifar,sannan ta janyo wayarta tana sake duba kira ko saqon nuraddeen,saidai har yanzun babu ko daya,saita maida ta aje tana ayyanawa wala'alla bai gama uzurinsa bane.

Shigowar hafsat dakin kamar wadda aka tunkudo ya sanyata miqewa ta xauna,fuskarta a hade da alamun kamar ma hawaye ta gama yi
"Yaya?" Zahra ta jefa mata tambayar tana gyara zamanta idanunta kan hafsan
"Yaa haidar mana......shikenan da zarar ya dawo mutum bashi da sauran sakewa,kome kayi baka masa dai dai ba,haba?" Koda bata tambaya ba tasan kwanan zancen,don halayyarshi ba baquwar halayya bace a wajensu,don haka baki ta tabe
"Hmmmm,ai ni shi yasa nake godewa Allah dasu abba basu dauko aqidar sai munyi karatu ba kafin aure,inda haka ne Allah kafin mubar gidan nan saiya sa mana hawan jini" dubanta hafsa tayi
"Ni kuma kinsan hakan baimun ba,nafison naci gaba da karatu kafin ayimin aure,inda xasu sauya shawara wallahi hakan yafimin,amma ya haidar kusan yafi kowa na'am da wannan tsarin tun xamanin su ya khairiyya" hararara zahra ta jefeta dashi tana cewa
"Bakinki ya sari danyan kashi,ni da kike gani na nan ba'a da candy qalilan ce inji 'yan arabiyya,babu wani karatu da xan tsaya wahal da kaina inayi,me yafi aure dadi?,kaida masoyinka?,ka samu 'yanci babu me takuraka?,tabdijan,ke ai saikita zama kici takarda da biron" ta fada tana komawa zuwa kwanciyarta ta daxun.

Dariya hafsa ta saki tana daka mata duka,tana sane ta sako wannan zancan,don duk cikinsu kowa ya san ra'ayin mahaifansu ya dace da ra'ayin zahran,kuma ita hakan yayi mata dai dai
"Allah ya shiryeki zahra"
"Amin....ai dan sunna bayaqi sunna ba ko"
"Wannan haka yake malamarmu"
"Kyaji dashi" ta amsa mata tana sake jawo wayarta ta fara buga game,jifa jifa suna hira,tana kuma dakon daina jin motsinsa a falon hajjan data samu ta fita taci wani abun kafin ta dawo ta kwanta tadan matse gajiya.
[9/6, 9:32 PM] Anty Rabi'at: 04

*KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾,KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
___________________________

*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kintaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* *@turare_by_awwaba mungode*
_______________________________

Sake maimaita tambayar yayi a karo na biyu dai ba tare daya kallesu ba,sanin hali yasa suka fara yunqurin nunata kawai,saidai basu kai ga aikata hakan ba tsawarsa ta mamayesu wanda ta rudasu,ba shiri kuma suka nuna zahra dake tsakiyarsu.

A hankali ya dora birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza a kanta na sakan daya kana ya janye yana cewa
"Itace ta dawo yau daga boarding ba?" Haushi tambayar tasa ta bata fiye data dazun,baqo ne shi,ko yau ya soma zuwa gidan nasu,tuni suka amsa masa da eh
"Good" ya fada yana kashe wayarsa ya zurata a aljihun wandonsa na baya,idanunsa dake ladabtar da mutum na bisa kanta.

"Daga dawowarki yau shine kikeson maida mana qofar gida tasha?" Ya jefa mata tambayar da batasan amsarta ba,hakan yasa tayi shuru tana nazari,tare dason gane me yake nufi da hakan
"Am asking you!" Ya kuma fada cikin tsawar data dan razanata,wannan karon bai jira amsarta ba ya dora da
"Wato kaiko boarding da akayi baisa komai ya canza ba ko?,su samarin da sukazo suna son mana tumasanci qofar gida duka ina kika sansu kina kulle cikin makaranta?,koko malaman naki ne soma biyo sawunki?,duka duka shekarunki nawa?tun baki tafasa ba zaki qone?,to i wil deal with u,bazan dauki wannan iskancin ba tun baki riqa ba,ba zaki fi qarfinmu ba,ki gayawa kowanne shashasha duk randa ya sake zuwa qofar gida ya mana fada saina masa daurin da za'a kasa ganeshi,ba gidan 'yan iska bane nan,hope kin haddace abinda nace?" Tuni hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa mishi,har sai daya maimaita mata cikin tsawa
"Kinji ko bakiji ba?"
"Naji" ta amsa cikin muryar kuka
"Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!" Ya kuma fada cikin tsawar.

Tuni suka miqe har suna rige rigen barin wajen,sai da suka tabbatar sun bar inda zai iya jinsu suka fara bawa zahra dake kuka haquri,kasa amsa musu da komai tayi,ta kuma kasa zuwa tura watsapp da zuwa sassan umminta don tayata dora girkin da mafi yawancin lokutta nata girkin dana hajja take hadawa,duk da itama hajjan idan tayi sha'awar wani abun tana dafa abinta,sai kawai ta juya ta koma sassan hajjan da sassarfa kuka Na sake qwace mata,maganganunsa na dawo mata.

Me yake nufi kenan?yana mata kallon 'yar iska ne koko meye?,bin maxa take a makarantar kenan har suke biyota gidan ubanta yake nufi?ko ita ta kirayesu tace suzo,bayan batama san kosu waye sukazo din ba,fatanta daya Allah kada yasanya da nuraddeen dinta akayi hakan.

Saman kujera ta zube a falon tana qoqarin tsaida qwallarta duk da taqi tsaiwa,daidai lokacin hajja ta fito daga dakinta tana riqe da carbi,da alama zikirinta data saba takeyi.

"Ke lafiya?,kukan me kike bayan qalau kuka fita?" Hajjan ta jero mata tambayar tana tsaiwa kan zahran tana rungume da hannunta fuskarta cike da damuwa da fargaba.
Chapter 5 · 0% Book details