← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 69

Sashe 60

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daya daga cikin jami'ansu ne me suna Deborah,tana qarqashin jagorancinsa,saidai ita din likita ce,wadda sanda suka dawo yabar kulawar sojojin da suka dawo dasu marasa lafiya da masu rauni ana kula dasu a asibitinsu,itace kuma shugabar likitocin ya buqaci zamun duk wani bayani bayan ya tafi kan ci gaban da aka samu kan marasa lafiyan,babbar macace sosai,don tayi shekara a qalla arba'in da takwas,kaf cikin ma'aikatan mata ita kadai yakewa dariya,saboda yana ganin girmanta kamar yadda take ganin nashi.

Mummunar faduwar gaba hadi da bacin raine suka bijiro mata sanda taji ya ambaci sunan mace cikin wayarsa,hakanan yana wayar cikin sakin fuska,abinda ba zata iya tune yaushe ne lokaci na qarshe data jishi yana waya da wani koda namiji bane cikin walwala haka,wani abu ya taso ya tokare mata maqogaro,har yasa kunnuwanta suka toshe,ta daina ji ko gane maganar da yake,maganganun da hasashen da zuciyarta keta kawo mata su take fahimta,don haka tana dire kwandunan hannunta tayi hanyar fita ba tare data ko kalleshi ba.

Duk takunta daya idanunsa na biye da ita,sai hankalinsa ya rabu biyu,rabi naga wayar da yakeyi,rabi kuma na akanta,karon farko daya taba qarewa tafiyarta kallo,kamar wadda ke rangaji haka takunta suke a tsare,saidai yanayin halittarta ne hakan,batasan ma hakan na faruwa ba.

Ganin ta nufo qofar gadan gadan saiya taka a hankali ya qarasa rufe qofar,ya murza muqulli ya rufeta gaba daya,sannan ya jingina jikinsa da qofar,sai ya zaman shida ita suna fuskantar juna.

Zata iya cewa bataji ya yiwa wadda suke wayar sallama ba,yadai zame wayar daga kunnensa ya jefata gefanshi,tsintar kanta kawai tayi cikin jikinsa,ya mata wata kyakkyawar runguma da taso zabge duk wani baci da ranta yayi kan wayar da yayi yanzun.

Tuni jikinta ya soma mutuwa saboda qamshij da jikinsa ke fitarwa,da wani irin dumi dake fita daga jikinsa zuwa nata,amma duk da haka ta aje wannan gefe,ta soma turashi da yunqurin barin jikinsa,da sauri ya sake yi mata qawanya da hannayensa yana sake yi mata kyakkyawan mazauni cikin qirjinsa yana fadin
"Ke......relax mana,kada kiyi kishi....abokiyar aikina ce fa,nothing else" mamaki ne ya kamata sosai,ya akayi ya karanci haka daga idanuwanta kawai?,kamar me aiki da sihiri,ko kuma wanda ya karanci ilimin sanin halayyar dan adam.

Mintuna a qalla kusan biyar suna tsaye a haka,shuru ba tare da ya sake cewa komai ba,ita dinma haka,kowa na sauraren bugun zuciya da fitar numfashin dan uwansa,ita kanta batasan ke ya debeta taci gaba da zama cikin jikinsa ba,sai taga ya kamata tayi koda pretendin ne,kada ta zubda kanta
"Ka sakeni" ta fada tana tura hannayensa,da sauri ya hannunsa ya birkitota ta dawo tana fuskantarsa,a maimakon dazu data bashi baya,hannayensa duka biyun ya sanya ya kama qugunta ya ruqe yana qarewa fuskarta kallo,cikin wata murya mai laushi da sanyi,can qasan maqoshi wanda koda kana kusa dasu sai ka kasa kunnenka sannan zaka iya jin abinda suke fada yace
"Zahra...." Mamaki ya kusan kasheta a tsaye a wajen,dama yasan sunanta ne?,eh dole tace haka,saboda tsahon rayuwarsu cikin gidan bata taba jin ya ambaci sunanta ba ko a wasa,ji tayi duk duniya kamar yafi kowa iya ambaton sunanta,kamar ya fadi sunan nata ne da wani yaren daban ba hausa ba
"Ke kadai ce rayuwata bata da amfani cikin taki rayuwar ko?" Ji tayi tambayar ta mata nauyi sosai,bata kuma gama fahimtar abinda ya fada din
"Yes....kowa yayi kewata amma banda ke....kowa yana nemana amma banda ke,kyautawa kenan?" Lallai yau mamakin da haidar din yake bata ya wuce tunaninta,da zata iya zata so ta daga kanta ta kalli idanunshi da fuskarshi,don ta samu tabbacin daga bakinsa kalaman ke fita
"Kin kyauta....matsamin daga jiki" kamar me jira kuwa ta janye jikinta,haushi ya cikata taf,ita din ya nemeta?,sau nawa yana kiransu hajja tana wajen ba wanda ya taba bi ta kanta,kwanciyarta a asibiti saboda waye tayi?,ko don ba zata iya gaya masa bane.

Caraf aka riqe hannuta,ta waiwayo da sauri don har ta soma yin gaba,fuskarshi a hade kamar bashi ne yayi maganar da yayin dazun ba,saiya sakar mata hannun sanda take zamewa itama daga hannunsa,ta juya zuwa inda ta ajjiye abincin ya bita a baya,ya samu waje ya zauna.

Duk wani motsi da zatayi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wanda hakan ke sake narkar da ita,kamar zata saki kuka haka takejin zuciyarta na rauni,wani abu mai qarfi yana ratsata loko da saqo,daidai sanda ta kammala zuba mishi abincin wayarsa ta dauki tsuwwa,hajja ce saiya daga kanshi tsaye,ya kuma sanya handsfree
"Zaki.....maza ka turomin innawuro....hadari garin" shuru yayi yama kasa amsawa hajjan,shi abun nata ma mamaki yake bashi,haushi ya kuma cikashi sosai,da gaske wannan karon yaji haushi har ransa,don haka yace
"Gata nan,daga yau a dinga turo min mustapha shamsu ko ibrahim su dinga kawomin abincina" saiya katse wayar,tana jinsa bata waiwayo ba,saita qara wuta,dama neman hanyar tafiyarta cikin sauqi take,don ita kadai tasan yadda yake qara wa zuciyarta pressure,tana jin kamar ba zata iya dogon xama dashi ba.

Tana fita ruwa ya tsinke,saita tsaya cak tana kallon yadda ruwan ke sauka daga sama da gudunsa,shahada tayi ta saka qafarta ta fara takawa cikin ruwan,wata walqiya me azabar haske aka saki,take ta haska ko ina kai kace tsakiyar rana ce,cikin sakanni ta dauke,kafin ta gama mutstsika idanunta da walqiyar ta kashe tsawa mai qarfi ta biyo baya,ai batasan sanda ta juya da mugun gudu ba ta koma ciki.

"Subhanallazi yusabbihur ra'adu bi hamdihi,wal mala'ikatu min khifatihi" ya furta addu'ar tsawa sanda yaji tsawar,yana gama rufe bakinsa tana shigowa a rude,ta jiqe sosai sai diga takeyi,sunayin arba kuma saita daburce,ta karanci abinda ya tsoratatan,amma sai yayi kaman bai gane ba.

Qin zama tayi tana ta leqen ruwan,saidai ba alamar zai dauke,ga sanyin ac ya hadu da jiqewar da tayi yana kadata har cikin jikinta,shima ya lura da hakan,amma yana mamakin dakiya da taurin kai irin nata,ya gama karantar komai daga gareta ta cikin qwayar idanunta,amma taba qaryata kanta da kanta da ayyukanta.

A hankali taji sanyin yana raguwa,data lura ashe kashe acn yayi,ya maye gurbinta da room heater,saita dan samu nutsuwa kadan,ta sake saka kanta tana leqen ruwan.

Ta saman kanta taji an yafa mata wani abu me qamshi,ta daga kanta da sauri sai taga ya bude mata lema
"Muje" kawai ya fada,ta tsaya sosai ta fara takawa yana biye da ita riqe da lemar,hannunta riqe da abinda ya yafa matan,wanda ya kasance qaramin bargo ne mai laushi sosai,kuma yana da nauyin da zai kare maka sanyi.

Tayi mamakin yadda yake tafe cikin ruwan,yana riqe da lema yana kare mata ruwan,shi kuma ruwan yana dukansa kamar bai damu bama,hakanan taji ta kasa daurewa,kamar idan tayi shuru bata kyauta ba,cikin sanyin murya tace
"Da ka saka lemar kai a kanka....ni wannan bargon zai qarasa dani ba tare dana jiqe ba"
"Kada ki damu,an koya mana tsaiwa cikin ruwa da rana kona awanni nawan ne ba tare da mun gaji ba....." Kai ta jinjina tana ci gaba da tafiya yana biye da ita.

Suna zuwa bakin sassan hajjan ya zuge lemarsa ya juya abinsa,saita tsinci kanta da cewa
"Na gode" juyowa yayi kawai ya kalleta sannan yayi gaba,sai dataga bacewarsa cikin ruwan dake sauka farfajiyar gidan sannan ta taka ta shige sassan hajjan.

A falo ta tadda tsohuwar tana shan kunun tsamiya,ta rasa qaunarta da kunun tsamiya,saita bita da kallo sanda take sauke bargon daga kanta,can cikin ranta taji tausayin haidar din,daga yadda ya amsata tasan yaji zafi ne,to amma koma meye tafison sai an aiwatar da komai daya kamata sannan,yadda hankalin kowa zaifi kwanciya,ta tar cikin gidansa,an rakata kamar kowacce mace,ko a baya ma data barsu tayi yaqinin ransu babu komai a ciki,babu wannan abun data gani yana yawo yanzu cikin idanuwansu a da din (hmmm to hajja,Allah yasa dai burin naki ya cika na miqa zahra'u dakinta).

Dakinta ta wuce ta canza kaya,ta dawo falo taci abinci,bata jima ba taji bacci na ziyartar idanunta don haka ta wuce dakinta abinta tabar hajja da husna da ilham,wanda suma wani lokaci nan wajenta suke kwana,abba babba ya tsara hakan,saboda yace zahra'un idan ta tafi xa'a bar hajjan ita kadai ne a sassan,kuma ko yanzun ma idan ta tafi makaranta wajen nata babu kowa,shi yasa suka yo qaura suka dawo,dama kuma sunfi son nan din.

*_BAYAN KWANAKI BIYU_*

Kwanaki biyu kenan da dawowarsa,qarfe sha daya saura na safe ya shigo sassan hajjan,a lokacin abba babba abba yusuf da abban tsakiya duka suna falon hajjan,zahra na kitchen tana wanke kwanukan data hada musu breakfast,don tun safe sukazo suna ta lissafi,na haqqin Allah da za'a fitar cikin kudin hajja da ake juya mata,lokacin fiddawa yayi.

Tunda ta gama ta zuba masa nasa a fulasan da ake zuba masa kamar koda yaushe,kwanaki biyu kenan tun randa ruwan saman ya tareta hajjan bata sake bari taje din ba,saidai ta bayar a kai masa kamar yadda ya fada,ita kam zahra nata idanu ne,saboda tasan halin hajjan,katafila ce sarkin aiki,takan kowa take bi idan aikinta ya tashi.

A ladace ya cire takalmansa ya qaraso gabansu ya tsugunna,daya bayan daya ya gaidasu,yaji dadin samunsu a tare,tunda yaje bai samesu a sassansu ba dama
"A kawo maka abincinne?" Hajja ta tambayeshi,tunda ta lura kwana biyu wani shareta yake,tun ranar nan,itakam ko a jikinta,tunda tasan koma meye qarshe shi zaifi kowa mora
"A'ah...zanyi magana idan za'a kawomin din....magaa nakeso muyi dama" abbansa ne ya daga kai ya dubeshi yana ninke takardar daya gama rubutu akai,abba yusuf ne ya amsa
"To Allah yasa lafiya" qasaitaccen murmushin nan nashi na gefan baki yayi sannan yace
"Lafiya lau abba.....cikin yarjewar ubangiji inason satin nan da zamu shiga in sha Allah mu wuce umara,nida hajja da abba na.....da kuma mama" Wani farinciki ne ya bayyana sosai saman fuskar hajja,burinta a duniya kenan ta koma qasa mai tsarki,duk da cewa taje har sau biyu,hajji daya umara daya,amma wajene da babu musulmin da bazaiso ya dawwama ma a can ba,lallai ba shakka haidar din wata kyautar Allah ce cikin iyalinta,soyayyar da yake mata mahaifi da mahaifiyarsa kai dama ahalinsa gaba daya abarso a sameta ce cikin zuciyar kowanne daga cikin dangi,don samun dorewar qaunar juna da danqon zumunta.
Chapter 60 · 0% Book details