Sashe 7
Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yauwa ya ta,shin kina son auren yaron gidan nan yanzu idan akace zai aureki Zaki yarda."
"Da gudu ma,nayi rawa harda tsale ,ai ni Addou'a neke Allah bani miji irin sa,wly da ma ace hajiya zata aura min danta da naji dadi🙈."
Yauwa Yar Albarka gobe zamuje kauye Alhaji zai nemi ki auran ki."
" Nashiga uku ni A'INDO ,aiko sai gata ta kece da kuka,Yi take ba k'ak'autawa,tana dira k'afafu,niko na shiga uku a rasa wanda za'a aura min sai kanton ciki wayo Allah ni A'indo🙆😭."
Lura da yanda A'indo bata fahimci maganar ba yasa Anty sakin dariya,tace "ke uban wa yace miki Alhaji zaki aura ,Ina ke ina Alhaji ,Zaije Nemo ma dansa sodja nan auran ki."
Nan danan sai ga A'indo ta washe baki tace"aradun Allah da gudu ma,ai wly Ina son shi kuma ni bana jin tsoron sa,dan tsab zan gyara masa zama😁."
"Yauwa yar Albarka haka ake so to sai ki shirya gobe zamuje kauye ."
Nan sukayi Salama ,Anty na tafiya A'indo da gudu tayi wajen abokinta Rabi'u daudu ,yana hada abinci a kitchen ,zama tayi kamar ta kwarai ,juyawa Rabi'u yayi ya ganta,ya kyabe baki yace"kyaji dashi,ke wly A'indo ki fita idona na rufe,kawai haka zaki zo ki wani shigo haka gandan gadan har kinsa zuciyata na bugawa😗,nikam naga ranar da zaki nutsu A'indo."
"Kai dan Allah.....
"a'a kinga dakata,yau ya Zaki kaini jinsin nan, dan Allah kidan dinga sakayawa mana,casss ma kuwa."
"Mtssss kaji dashi,Kai aure zanyi kuma mai kudi,shine nace bara na fada ma ko kaje kayi min zaman d'aki🙈."
"Ke dan Allah kice abun yazo,ke ko wane gara ne wanan da zai kwasa ya kaima kanshi,a wly in dai yanada kudi ai wly zanyi miki zaman d'aki,har ma na wata biyu kuwa cassss."🙄
"Allah bani mu kashe nawan ✋ tafawa sukayi Rabi'u daudu yayi fari da idanu yace to fadamin waye angon?
Soja ne,dan Hajiya."
"🙆♂ Na Shiga uku mai kika ce Yar nan rufa ma kanki asiri,kar a jiki,wly ki barni maza su kaini ba mata ba,inaga ciwon ajali ya kamaki da Kika ambacin wanan mutumin duba harda fitsari ya Kama ni,ke ni kinga tafiya ta,ke kin cika hauka,na tafi bazan iya d'aukan wanan karyar taki ba,kedai kin shiga uku yar nan bayan hauka da kauyancin harda karya kika koya."yana magana Yana tafiyar mata .
Washe gari tun dasafe Anty tazo,shima Dady kanin sa yayi ma waya yazo,itama Hajiya ta shirya,harda A'indo aka dunguma
Aka kama hanyar kauyen su motar Hajiya da A'indo da Anty daban,dreba na jansu.shima Alhaji da shi da abokin sa dreba ke jan su.A'indo sai ihu take a mota wai bishiyoyi na gudu suma.
Sorry fans yau dai ina typing ne anma bana jin dadin typing din kuyi hakuri da wanan😌
[10/10 à 17:28] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*Ya mace Kowace da irin Ni'imar ta*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
*Page 15-16*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
A haka suka isa kauyen su A'indo,ai tana ganin kauyen su ne ta fara ihu,wani ihun da ta buga tace"la ha'ila aradu wancan idi Kato ne."
Ta zuro Kai ta window din mota waje ta kwala ihu tace"Kai idi kato nice A'indo idi!!!!!
Da k'arfi Anty ta jawo ta tace "ke wai A'indo yaushe zakiyi hankali dan Allah ."
"Gobe dasasafe"
Ta bada amsa tare da daka fuska,Hajiya ta girgiza kai tace"hum ai ni yarinyar bansan wace iri bace sam batada nutsuwa,nasan wata kila tayi auren ta nutsu .
A haka suka isa k'ofar gidansu A'indo suna tsayawa sai ga Husseina ta karyo daga kwana taci uwar damara a kugu,sai huci take ga dukan alamu fada tayi,ai A'indo ko bari batayi ba mota ta ida tsayawa ba ta fara kokarin fitowa ta k'ofar window na mota,Saida Antyn ta ta jata,mota na tsayawa bayan Anty ta bud'e k'ofa da gudu A'indo ta fito ta kwala Kiran husseina aiko husseina Jin muryar yar uwarta yasa ta juyo tana ganin A'indo ta kwala Kara,a guje ta taho itama A'indo da gudu ta taho suka rungume juna sanan suka saki juna suka fara gaisuwar su da suka saba,wato suka tafa da hannuwa,suka hada k'afafu nan ma suka tafa,kowace ta dangwala yatsa a kan yar uwarta sanan suka hada kugu suka bada kwamatse irin na yan daudu ,wanan gaisuwar haka suke yinta,sanan suka kece da dariya suka kara rungumar juna.
Alhaji da da abokin sa,sai su Hajiya duk sun fito , sunyi bala'in mamaki da ganin cewar wai A'indo dama yan biyu ne,Anty ce tayi murmushi tace"ai yan biyu ne dama,kowa saide yace Masha Allah, domin yaran sunada kyau,kawai matsalar su rashin natsuwa ga kuma fada.
Anty ce ta fara shiga gidan,A'indo Kam ta manta da su wa sukazo taja yar uwarta suka shiga gida,aiko tana zuwa da gudu ta auka d'akin mahaifiyar ta kulu,itama ta fito ta rungume yarta, cik'e da farin ciki,Anty ce ta shigo ta shaida Mata da baki suke tare,maraba tayi musu cik'e da farin ciki,Ado ya fito shima yayi farin cikin ganin Yar sa,aiko Anty ta fada musu da maza suke tare,uwayen gidan A'indo ne.
"To to keko kin barsu a waje Safiya,tashi shigo dasu Bari na samo tabarma mu mu zauna a zaure.
Husseina ce taja A'indo gefe tace "ke A'indo wai su waye kuka zo dasu,harda wani na gani mai irin cik'in Mai gari,shima ya kusa haihuwa ko?
Allah dai yasa ba irin cik'in Mai gari bane dan kinga har yanzu bai haihu ba."
"Tab A'indo tace kinga wanan fa har gudu yake har bai tsoron ma cik'in ya zube."
Husseina tace "tab to ai da zai bari mu taba da mun taba."
Wai kus kus kus din me kuke ma mutane,maza ku tashi ku shiga d'aki kun wani tsaya manya na zaune kuna gindin su cewar kulu ta katse musu zance."
Dan tuni Hajiya ta shigo Suma su Alhaji suna zaure.
Hajiya dai kalon su A'indo take gwanin sha'awa sai suka tuna mata yan biyun ta su Alhassan lokacin da ta haife su da abokiyar tagwaitakar sa,kama suke sosai ,haka su A'INDO suka shiga d'aki sunata kus kus din su.hajiya sun gaisa da kulu nan Anty ta gabatar mata da Hajiya tare da nufin su,acan zaure ma Abokin Alhaji ne suke magana da Ado mai saida kifi,ya yaba da kamalar mutanen ,sanan yace tunda harka ta aure ce bari ya Kira mai gari,bayan an Kira Mai gari shiko ya shiga cikin gida tare da kiran Anty da kuma matar sa ,sai kuma A'indo a d'aki,nan Husseina ta fito ta zauna kusa da Hajiya tayi tagumi tana kalon Hajiya ,bayan Kulu sun shiga d'aki Ado ya tatara nutsuwar sa zuwa ga Anty yace"Safiya mu bamu san mutanan nan ba ke Kika san su ki fada mana tsakani da Allah mutanen kirki ne ,me yasa suka tsalake birni suka zo kauye dan neman auren ya ta,wanda kowa yasan halin A'indo,batada nutsuwa."
"Yaya wly wa'inan mutanan ko a birni ansan irin mutuncin su da kuma son talakawan su,ko a birni da kaga yanda A'indo take musu tabara Kai kace Yar su,basu taba nuna kyamar su ba gareta,saima sanyata a jiki da sukayi,suna son dansu ya daina kyamar talaka da kuma yan kauye shi yasa sukace A'indo itace daidai shi,shi yasa yake son ya masa aure ,anma wly yaya basuda matsala."
"To shikenan,ke kulu ya Kika gani."
Nima na yaba da hankalin Matar,kuma ko baya ga haka kaga yaran nan yanda sukayi bakin jini a kauyen nan wata kila dama can haka Allah ya kadarta,dan haka kawai ni a gani na ayi auren ,Allah sanya Alherie."
"A'indo ado ya Kira ta."
"Iye babana!!!😁 A'indo ta fada da k'arfi,girgiza kai yayi yace" kina son wanda akace za'a hadaku aure?
"Hahhh kaji babana da wani zance,ka gansa kuwa,Allah ko maman mu ta gansa sai tace bata son ka shi take so🙄."
Kulu ce ta rank'washe ta a kai tace"ke wai dan ubanki yaushe zaki nutsu ne.?
"Yau"
A'indo ta bata amsa,shiko ado girgiza kai yayi yace"kina son shi."?
Marmadi da idanu A'indo tayi tace"casss ma kuwa Ina son sa😁."
To Alhamdulillah ku tashi kuje wurin hajiyar ni bari na fita waje,Yana fita kuma Yan uwan sa sun zo wanda ya aika su zo,kowa yayi na'am da wanan auren,dan matsawar yaran suka zauna kauyen Nan to komin kyansu baza'a aure su ba,hakan yasa ma auren A'indo mutane dayawa sun amince,sudai fadan su a rage wanan irin,inda mutane wasu suna gulmar cewa wai Ado yaga kudi ya Saida yar sa,wasu kuma suce ai yan mafiya ne,yan yanka Kai wa zai fito daga birni yazo kauye neman aure,haka dai akayita Yan dumumuwa.
Su Alhaji dama tafe suke da komai nasu goro halawa dabino,a k'ofar gida mutane diyawa sun taru Kai kace an jima da fadin aure ,k'ofa ta cika tambal,su Alhaji basu wani nuna kudi ba ,dubu hamsin aka bada a matsayin sadaki abokin Daddy ya bada dubu hamsin kudin sadaki,anan take aka shaida d'aura auren Alhassan,da Hassana,wato A'indo.
Anyi farin ciki Nan maroki ya shaida,da gudu A'indo ta fito tsakar gida,nan fa ta fara rawa,tana girgizawa,tare da fadin an d'aura,an d'aura."💃💃💃💃,
Mutanen da suke gidan kowa ya Kama haba ana kalon A'indo,itama Husseina fitowa tayi ta fara rawar nan fa suka fara rawa,suna fadin "an d'aura 'an d'aura."