Sashe 20
Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
_wanan page Naku ne Yan group din Latifa sabon salo & A'INDO Tantagariyar Yar Aiki fans saboda comment din ku na sa ni nishadi_
*Page -41-42*
Dariya A'INDO tayi cik'in aji tace"Rabi'u kanada abin dariya kana nan da halin ka." Cewar A'indo.
"😨iyeee tab wai A'indo kece da wanan maganar cik'in jan aji,jar uba,kai yau ni naga abinda yafi k'arfi na,anma Hajiya dan Allah ya akayi wa'inan suka gyaru suka waye." Cewar Rabi'u .
Dariya Hajiya tayi tace" lokacin nutsuwar ce tayi ."
Ka fara shirye shiyen girke girken da za'ayi da na na biyu mai bima soja zai dawo ya gama karatun sa na doctor dan haka zai dawo yau yana bisa hanya."
Husseina ce naga tayi murmushi wanda bansan ma'anar sa ba,A'indo ta dan buge ta ta daga mata gira tare da cewa" ya dai Yan mata🤨."
Murmushi Husseina tayi ta rufe fuska tare da barin gurin da gudu,tun a lokacin A'indo ta fahimci wani abu,anma kuma a take ranta ya baci hankalin ta ya tashi ,tana tsoron Kar ya uwarta ta fada irin cik'in yanayin da ta fada ,wanda har yanzu take fatan Allah ya yaye mata shi ."
bin bayan Husseina tayi dan tabatar da zargin ta, shikam Rabi'u har yanzu zaune yake sakaka da baki,abun har yanzu bai bar basa mamaki ba,shi kawai gani yake kamar an canza su.
"Husseina!
Husseina !
Husseina! ki fadamin tsakani da Allah me yasa ki farin ciki haka."
Cewar A'indo.
"Wallahi A'indo nima bansan me yasa ba idan an ambace sa nakejin nishadi,watakila ya danganta da shakuwar da mukayi,da kuma yanda baya nuna kyama,ko shi wani ne a tare da ni."
"Waye shi"?
Cewar A'INDO."
Shine mai bima mijin ki, wallahi A'indo idrissa yanada kirki,kinga yanda yake ja na da fira,yanzu haka kullum sai munyi wathapp dashi,yau wata daya kenan da yace yana so na,tun lokacin ban kara yarda munyi ko magana dashi ba,nayi blocking dinsa,a tsoro na,Kar shi ma yayi min irin na Mansoor da abinda mijin ki ya miki,anma sai ya bullo da wata hanya da kansa yake kiran Hajiya ya matsa ta bani waya,ita kanta nasan a yanzu tasan abinda danta ke nufi,ni kaina zuwa yanzu inajin wani yanayi daban a tatare dani anma ina tsoro,ina tsoro,A'indo da naga ya matsama Hajiya da kullum ta kawo waya sai na fida sa daga blocking din nasa da nayi,a jiya ya furta min kalmar so tare da cewar yana so na zai aure ni."
"Masha Allah indai har shida kansa yake son ki,kuma kin tabatar da cewar yana sonki to wallahi ina mai farin ciki,domin kuwa Hajiya ta mana hallacin da ba kowa zaiyi sa ba,ta d'auke mu tun lokacin da bamuda cikak'en nutsuwa,ta zauna damu duk da asarar da mukayita jawo mata,Kinga ko auren danta da zakiyi idan har yana son ki shine hanya mafi alkairin da zamu saka mata,anma kuma hakan bazai hanani amsar takardar saki na ba ga wannan azalumin dan nata ba."
"Kinada gaskiya A'indo Dan ko ni ban goyi bayan ki zauna da Alhassan ba."
.........a ranar idrissa kanin Alhassan ya dawo , cik'e da nasarori na zama kwararan doctor,a inda su hajiya sukayita farin cik'in,shi kam a lokacin ba wace yake muradin so da gani kamar yanda yake Jin son ta tun rana ta farko da ya ganta a yar kauyen ta,lokacin da Hajiya take videos call dashi a cumputer,inda Husseina ta shigo fallon tana shirmen kuka wai sai an kaita gun A'indo.
Shine da Idrissa yaji ya tambayi Hajiya wacece wanan ?Hajiya ta fada masa,ko wacece Husseina.shine Husseina ta basa dariya,yace a basa ita suyi magana Hajiya ta kira ta aka basa Husseina,yanda tayita shirme ya burge sa,shi sanyi garesa gashi bashida kyama,yanada raha wanan abin da yaga Husseina nayi cik'e da shagwaba yasa yaji lokaci daya ta shiga ransa,tun daga lokacin idrissa har mafarkin Husseina yake wai sunyi aure,to bare da yaga ta waye anan yaji kaf duniya ita yakeda muradin aura.
A gidan Hajiya da Alhaji sunyi matukar murnar dawowar dansu idrissa,
An masa tarba da kayan ciye ciye kala kala,wanda harda Husseina akayi komai,suna zaune a dinner ne Yana cin abinci yake tambayar su hajiya ina hausseina akace tana school,a matse yake da son ganin husseina,yayyin da Hajiya ta kashe ma Alhaji ido data,yasan mai hakan yake nufi,domin sun dai gano dan nasu ya fada son Husseina.
Idrissa dogo ne,madaidaici,baki ne shi anma ba irin bakin nan ba wuluk,bakin sa mai kyau ne,yanada kyau shima,dan yafi kama da Alhassan, anma Alhassan yafi sa kyau,bayan sun gama cin abincin ya tafi d'akin sa yayi wanka ya kwanta anma ya kasa barci ,sam ji yake idan baisa Husseina a idanun sa ba bazaiji dadi,gashi ance yan biyu ce ,dayar ce Matar yayan sa,shi bai ma san an raba auren ba,domin ba'a fada masa ba.
Tashi yayi yaci shiri,wajen k'arfe biyar ,ya fito ya zauna a tsakar gida,dreban su A'indo ne ya shigo gidan,tunda motar ta shigo idrissa ya kura ma motar idanu,nan A'indo ta fara fitowa,bata lura dashi ba tasa kai, tayi gaba abunta ,yayin da shi kuma yaketa kallon ta,a tunanin sa Husseina ce,can husseina ta fito tana waya,cak ta tsaya , sakamokon Idanun ta da ya hadu da na idrissa,da dan gudu ta karasa wurin sa,tana murmushi,tare da cewa"yaya yaushe kazo,sai a lokacin yasan cewar wanan itace husseina sa.
Shima farin ciki ya mamaye sa,tare da tasbihi a Zuciyar sa,domin yaga Husseina ta ma fi kyau a waje fiye da hoto.
A takaice dai tunda idrissa ya dawo suka dinke soyaya mai tsabta a gidan,yayyin da suke burge A'indo,sanan yana kara musu sani bisa kan wasu abubuwa da ya shafi karatu,tsaraba kam sun sha ta,ta kaya, na kasar waje,anma tsarabar husseina daban take.
Bai jima da dawowa ba dama mahaifin sa ya Gina masa katon asibiti ,Wanda harda turawa ke ciki,shine mai asibitin gaba daya,abu ga manya nadanan ba bata lokaci ya fara karatun sa.
Wata rashin lfy da Mahaifin Mina yayi wanda ya fida rai da zai rayu ,hakan yasa ya buga ma Mahaifin Alhassan cewar yazo a d'aura auren Yar sa tun yana raye,kar ya mutu baiga auren yarsa ba,hakan yasa aka kira Alhassan aka fada masa, ya amince, da a d'aura ,aiko ba'a wani ja lokaci ba aka d'aura Auren Alhassan da Mina.
Duk da d'aura auren da akayi bai hana Mina tsayar da sharholiyar ta ba,duk wata shiga da take tana yan mata bata bari ba ,a cewarta ai mijin baya kusa.
A inda kuma Mahaifin ta ya samu lafy yaci gaba da harkokin gaban sa.
Rayuwar A'INDO da Husseina a school,rayuwa ce da duk wata daliba rayuwar su ke burge ta,a inda suke komai cik'in aji da class,bazaka taba gane cewar daga kauye suka fito ba,sanan suna sityl ne cik'in tsari da ban sha'awa.
*Bayan shekara daya*
,su Alhassan sun dawo daga Mission dinsa Wanda acikin mutum ashrin su uku suka dawo da rai,Wanda Alhassan ne ya karkashe yan ta'adar tare da kamo shugaban su,wanan nasara da ya samu ba karamin girma da mutunci ya kara samu a kasashe ba,domin yan ta'ada ne da suka damu duniya , aka kashe,tare da kama baban su .
Yayyin da za'a shirya musu baban taro domin kara musu girma, anason kuma duk wani makusancin su ya zo wanan baban taron dan tayasu murna nan da sati daya za'ayi wanan gagarumin taron.
Iyayen sa sunyi matukar jin dadi da Allah ya maido musu da yaron su lfy.a inda suka shirya tafiya domin taya dansu murna.
*A wanan lokacin kuma ba karamin wayewa da cigaba,tare da haduwa ba ,su A'indo sukayi ba,a inda turanci ya zauna dam a bakin su ko gargada babu ,gashi sun Kara wayewa,ilimi ya shige su,sunyi bala'in kara wankewa,idan ba kayi da gaske ba a gaskiya ba lalai ka gane su ba,a inda sukayi nasara suka huce aji na na gaba,jss2,abun ba'a cewa komai,samari dai ne basa kulawa,duk da irin yanda samari ke hauka akansu ,dan har akoi masu masu kuka,Kai abun saide ace Masha Allah,dan yanzu mota ma da kansu suke tukawa ,wada idrissa ya Saya musu,mai tsada,abin ba'a cewa komai,dan ni kaina mai rubutun busoshin kaina nema suke su kunce,yanda su A'indo suka rudani da kyansu da ajin su,abun sai Wanda ya gani,yayin da Mansoor a yanzu har kuka yake yana rokon Husseina ta so shi,anma ina Husseina tace yayi wasa da damar sa,ita yanzu ta idrissa ce .......
Bayan Alhassan ya dawo Mina taji cewar yau yake zuwa anma babu abinda tasa a masa,na tarbon miji,abun takaicin ma da ya dawo gidan bai tarar da ita ba,domin ta tafi birthday din kawar ta.
Ransa yayi bala'in bacewa,ace mutum yanada mata ya dawo daga irin wanan tafiyar ko tarba bazai samu ba, gaskiya ba haka yaga Matar Abbas nayi ba,dan bazai manta ba,sun taba irin wanan tafiyar na watanni ne ma, shida Abass ,anma da zasu dawo Abass ya matsa suje gidan sa yaci abinci acan,
tunda Alhassan nason Abinci na Nigeria,sukaje abinci kala-kala yaga ta dafa ma mijin ta,sanan ga gida da yasha decoration,ga ko Ina kamshi yake,kamar za'ayi wani party,gata itama tasha shiri,anma shi sai ya iske akasin hakan."
A cewar sa yanada mata yanzu ba sai ya Kira cucu ba,dan dafa abinci baisan abun ba haka yake ba.
Wanka yayi ya shirya,yasa cucu ya dafa masa abinci yaci,shi ke jiran yaga Mina ta dawo anma bata dawo ba sai k'arfe sha daya na dare ta dawo.
Ran Alhassan idan yayi dubu to ya baci,idanun sa tuni suka canza coulor tsabar bacin rai, shigowa Mina tayi da dan gudu ba ko salama tazo zata rungume sa,tsawa ya daka mata tare da daga mata hannu, ya dakatar da ita,yace"Mina daga ina kike"?
Kayan jikinta ya kalla ransa ya kuma baci duk da yanason wayewa anma ba irin wanan ba,shifa yanada bala'in kishi,ace matar sa tana yawo da wondo iya gwiwa,riga kuma daidai cibi,
Kai ba dankwali,tasha gashin attachement,ga faratan hannun ta zako zako,kamar ba Yar musulmi ba,ransa yayi bala'in baci,baisan lokacin da ya daga hannu ya zabga mata mari ba,dafe kumci Mina tayi tace"ka mareni ban maka komai ba."