← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 45

Sashe 35

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ya fara tuki suka fita daga gidan,can sun fara tafiya Farida tace"anm yaya Al'Hassan nace wanan wacece acikin dangin ku,Farida ta fada cik'in siyasa da dariya,baikai gayin magana ba A'INDO tace"kekam kin damu kanki sai kin san ni ko wacece,meye ruwanki ne wai?
Kinga ki fita harka ta na fahimci yar rainin hankali ce ke,bana son shishigi."

Waro idanu Farida tayi tace"ke ni kinsan ko wacece kuwa,ni kike fada ma wanan banzar maganar ."

idanun A'INDO tuni sukayi ja ,ganin shi Al'Hassan baya ma kareta,ko dazu ta fada mata magana anma bai tsawatar mata ba ,da k'arfi tace"ajeni nan,bazan iya tafiya da wanan karyar ba."

A tsorace ya taka burki ganin ran wace yake kauna ya baci yace"haba Aisha me yayi zafi haka kiyi hakuri mana, bud'e k'ofar motar tayi ta fita,wani haushin kanta take ji me ma yasa ta biyo su,gashi yanzu ba abinda zai ja mata bayan raini,ganin da gaske take yasa Alhassan jin zafin Farida ya juyo rai a bace yace"kin gani ko zaki ja min kimin asara ,fitowa yayi daga motar ya bud'e gidan bayan yace"Kinga malama fice ki shiga abun hawa ki tafi gidan ku,dama ni nace zan kaiki yanzu na fasa,kudi ya fido ya jefa mata yace gashinan shiga mota,sa'a kikayi da yanzu bana wulakanta mata saboda wani dalili anma wallahi yau da sai kin raina kanki ,sakaka da baki Farida ta tsaya tana kallon sa cik'e da bakin ciki da takaici,tare dajin muguwar tsanar A'INDO,sanan ta d'auki alwashin sai ta d'au fansar abinda A'INDO tayi mata.ganin ba zata fito ba ya finciko ta tare da watso mata kayan ta.

Ya rufe motar sa tare da janta a tsiyace yabar wurin ya tarar da A'INDO wace take tafiya. bisa hanya,yana isowa daidai wajen ta ya tsayar da motar ko rufe k'ofar baiyi ba ya fito ,"Dan Allah kiyi hakuri,wly banyi haka ba dan wulak'anci ko tozarci,kawai sanin da na miki ne nasan zaki iya gyara ta da bala'in ki ,shi yasa nayi shiru na barki da ita."

"Au dama ka d'auke ni uwar bala'i kenan ."

"Dan Allah kiyi hakuri ba haka nake nufi ba,ina nufin ki mata bala'i,dan Allah ki dawo kamar yanda na d'auke ki na mayar dake."

Ganin yanda ya marairaice yasa ya dan bata tausayi ta juya ba tare da tayi masa magana ba.

Sauke ajiyar zuciya Alhassan yayi,tare da jinjinawa so haka so yake,duba yanda yake rokon ta kamar zai duka mata,tana wulakanta sa anma sam baya ganin laifin ta,saida ta shiga mota da sauri shima yazo ya shiga ya tuka suka fara tafiya,sun fara tafiya tace"zan siye cream glass ."

"To to akoi inda ake saidawa yanada dadi sosai muje na kaiki.",share sa tayi ba tare da ta kuma kulla sa ba,kai kace yar mulki ,suna zuwa wajen suka fito,sukaje inda ake siyarwa,nan yace a basu,ya bada kudi aka basa Glass din kallon sa A'INDO tayi tace"kaga nifa bance ka Siya min ba,me zanyi da abinda ya fito daga hannun ka,juyawa tayi ta fido dubu daya a jakar ta ,ta ba mai saidawa tace a bata.

A wanan karon kam ran Alhassan ya baci, gaba-daya ji yayi kamar yayi kuka ko ya samu saukin abinda yake ji ,me yasa Zuciyar sa ke kaisa inda ake wulakanta sa,shin Allah ma ba ana masa kuskure ba ya yafe,me yasa ita bazata yafe sa ba,ko wanan masifofin da yayita shiga ai ya isa ace zuwa yanzu ta hakura tunda

taga irin masifofin da yayita shiga ta dalilin ta.

Tabas zaije wanjen malami a dinga masa rubutu Allah ya sa masa dangana game da ita,Allah ya raba sa da sonta ko zai huta."

Yanaji yana gani ta siya. gaba-daya tunani ya tafi da hankalin sa,,wanda ya gusar masa da hankali bai ma san ta gama ba,shekeke A'indo ta kalle sa,ganin baida alamun gusawa taja tsuka ta fito waje,keke napep ta tara ta fada masa inda zai kaita ta shiga.

Jin ana fadin "ranka ya dade ga sauran canjin ka,wanan maganar ta dawo dashi daga dogon tunanin da ya shiga,firgigit ya dawo hayacin sa,nan ya fara dube dube da waige waige,yana neman A'INDO anma bai ganta ba,.

Da sauri ya tambayi masu saida S.cream sukace ai ta fita daga nan,da sauri ya fito suna cewa ga canjin sa anma ina ba tasu yake ba.

Fitowa yayi yanata waige waige inda zai ganta anma bai ganta ba ,hankalin sa yayi bala'in tashi dan a tunanin sa ko sace ta akayi,tuni cik'in sa ya kada,nan ya fara duduba gurin da gudu gudu lungu da sako bai ganta ba, nan ya fara tambayar mutane yana nuna pic dinta dake wayar sa,kowa sai yace bai ganta ba,yana ta neman ta aka kira sallah magariba ,gaba-daya ya rikece,wani tunani ya Fado masa ya d'auki waya yayi kiran Hajiya tana d'auka yace "yauwa Mom Aisha ta dawo gida ?"

Hajiya tace"nima kiran da zan maka kenan na tambaye ka me ya tsayar daku har warhaka."

Kashe waya yayi ya aza hannu bisa kai.

itako A'INDO fitarta ta shiga adaidaita, ta fada masa inda zai kaita,wato gida.shigar ta keda wuya ya fara gudu da ita,nan tace" haba malam na fada maka inda zani anma kabi wata hanya sai gudu kake dani.

"Sorry Madam kiyi hakuri,wata tsohuwa ta ce ba lfy shine zan dan bada magani a bata sai na kaiki dan Allah kiyi hakuri da ban fada miki ba."

A'INDO ko jin tsohuwa ce ba lfy yasa ta tausaya ,tace ba komai,abun mamaki suna isowa ba inda suka tsaya sai gani tayi an hangame gat mai adaidaita ya shige da ita,a matukar tsorace take kallon mai Adaidaita ,ji tayi an jawo ta shiko mai Adaidaita ya juya ya fita daga gidan a tsiyace,aka rufe gidan."

Cik'in tsoro A'INDO ta daga kai taga Wanda ya finciko ta a firgice ta ja da k'arfi tayi baya waro idanu tayi a gigice ta nuna mutumin da yatsa tace" dama kaine....."

_Oh Nagode sosai Wanda suka tambayi jiki na da na yarinya ta ,Allah yabar zumunci_🤝🏻🤝🏻
[13/11 à 21:15] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Page 71-72*

Murmushi Bashir yayi ,tare da kokarin matsowa kusa da ita,da sauri ta kara ja baya tayi tuntunbe da wani dutse ta Fadi a gurin k'afar ta ta fashe.

Anma sam bataji zafin ciwon ba saboda a yanzu ji take wanda ke gabanta yafi zafin ciwon sau dubu.

Dukawa yayi tare da sakin murmushin sa ,yace"welcome baby nayi kewar ki."

Ya fada tare da shafa fuskar ta,runtse idanu A'INDO tayi tare da fadin"karka kara sa wanan banzan hannun naka ya taba min jiki na fada ma mugu."

Gashin kanta ya kama ya jata kiiiiii har saida ya isa da ita k'ofar falo sanan ya sabe ta da k'arfi ya shigo da ita.

Ihu A'INDO take dan neman agaji anma ina ba Hali.

"Bashir kai wani irin mugu ne dan iska,wanda baisan darajar dan Adam ba,kai bunsurun ina ne,to bara kaji na rantse da Allah tun muna shaidar juna ka bani hanya na tafi idan ba haka ba kuma wallahi lahira zatayi bako."

"Hahaha , yarinya kinada abin Dariya,sai ya marairaice fuska kuma yace"haba Aïsha na kira

ki baki d'auka ba nayi miki message bakiyi reply ba, a k'arshe ma kika sa ni a black liss,haba dan Allah Aisha kizo muyi zaman mu,nan Kinga ke ba wani dangi ne dake ba bare a wani damu da bacewar ki,kizo mu zauna na Miki Alkawarin zaman farin ciki a gidan nan kiyi yanda kike so."

Murmushi A'INDO tayi,ta tashi kamar ba ita ba ,tayi dariya tace" Allah ko karka damu anma bara na dan sama mana abinda zamuci yunwa nake ji."

Washe baki yayi yace"Alhamdulillah kin hakura kenan."

"☺me zai hana kuwa Bashir bara dai yanzu na dafa wani abu idan na koshi sai muyi maganar."

Kitchen ta nufa,yayyin da shi kuma yayi wani tsale ya haye saman kujera yana tsalen murna tare da kecewa da dariya yace"ai dole ta so ni kodan kyau na,wly zaman mu zamuyi ba ubanda ya isa ya raba mu.

A'indo ko tana shiga da ma rigar ta doguwa tanada aljihu koda taga yanda mai Adaidaita ya rugo da ita ta d'auki wayar tasa a aljihun rigar ta ,a lokacin da ta shiga kitchen kuka ne ya kusa kufce mata, tayi sauri tayi shiru ta kama bakin ta,sai ta fido wayar daga Aljihu numbers Al'Hassan tasa har mamaki tayi ya akayi ta hadace ta haka.

Kira daya biyu Al'Hassan ya d'auka bayan ya samu gefen titi ya tsaida motar sa dan tunda ya rasa inda A'INDO take yaketa yawon garari Yana neman ta kamar mahaukaci.

Number ta ya gani wace dama yanada ita
Yayi saving dinta,da sauri ya d'auka har bakin sa na rawa wajen magana "hello!

Aisha kina ina kin tada min hankali."

"Yaya Al'Hassan plz kazo ka raba ni da wanan mugun Bashir shine yasa a sato ni gani nan gidan sa ina kitchen plz kazo ka d'auke ni."😭

Idan ran Alhassan yayi yayi dubu to a lokacin ya baci, gaba-daya kansa hayaki ma yake masa, jijiyoyin kansa har tashi suke,Kiran Idrissa yayi bayan idrissa ya d'auka yace"maza ka bani adreshin wanan dan inskan tsohon mijin Aisha."

"Yaya lfy?"

"Kaga nace ka bani ko."
Saurin basa yayi Yana basa ya Kira Hajiya yace"Hajiya maza kije gidan tsohon mijin Aisha dan inaga brother yau Zuciyar sa ta tashi Kar ayi kisan Kai ba alamun lafiya."

"Ya Salam Hajiya tace ta tashi ta hau sama dan d'aukan hijabin ta.
Shi ko Alhassan a dari ya ja motar kamar zai tashi sama,sai gashi a unguwar, k'wank'wasa gidan yayi sai ga Mai gadi ya bud'e ,bindiga ya dungura ma mai gadi ba shiri yayi mazan bashi hanya yana rawar jiki,yana shigowa Mai gadi ya arta a guje yabar gidan.
Chapter 35 · 0% Book details