← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 45

Sashe 36

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikuwa Al'Hassan da sauri ya karasa falon
Yana zuwa" ya daga murya Aisha kina ina ."

Bashir dake zaune saida gaban sa ya fadi anma ya dake yace " kai Malam lfy zaka shigo min gida ba'a koya maka salama ne ba"

Wani mugun kallon Alhassan ya wurgo Masa Wanda ya kadar da Yan hanjin Bashir,da gudu A'indo ta fito ta nufi Alhassan da gudu ta rungume sa tana kuka.

Tace"kaga wanan mugun ne ya sato ni,kara rungume ta yayi yana shafa kanta alamar rarashi, Bashir ya waro idanu waje yace "dama ke Yar iska ce,shine kika Kira kwarton ki to da yazo me zaiyi wallahi A"indo sai na baki mamaki."

A wani irin k'arfi Al'Hassan ya janye A'indo daga jikin sa ya nufi Bashir baiyi wata wata ba yakai ma bakin sa naushi,ba shiri Bashir ya rike Baki Dan tuni hakorin sa daya ya fita baki ya fara jini,cakumo wuyan sa yayi ya makure Al'Hassan yace"kai dan gidan uban waye ? Wane ganganci yakai ka taba min mata,dan uwarka dama inada haushin ka kyale ka nayi in banda akuyanci ka saki mata sanan ka dinga bibiyar ta,to uwar me zakayi mata ,,Bashir zai kuma magana Al'Hassan ya kuma naushin sa,anan ya makure sa ya fara sakar masa duka tako ina nausan sa yake tun Bashir na iya ramawa har yakai ya kasa,jina-jina da jini Al'Hassan ya Masa,yaji haushi ko gani bayayi aikin dukan sa kawai yake,tuni Bashir ya sume anma Alhassan yaki saurara Masa,A'indo ko kadan bata ji tausayin Bashir ba,illa ma wani so da take ji nasa yana mamaye Zuciyar ta,a yau duk wata kiyaya da take masa ta kawar,ta maye gurbi da so ,Hajiya ce ta shigo gidan ita da idrissa abinda ta iske ne ya tsorata ta,da sauri taje ta ririke Alhassan shima Idrissa haka ya rirke Al'Hassan Hajiya tace"kai wai meye haka?
Kashe dan mutane kake son yi ne Bashir ya debo ruwa ya watsa ma Bashir ya dawo hayacin sa,Hajiya ranta a bace ta tambayi Al'Hassan da har yanzu jikin sa ke rawa gaba-daya baya cik'in hayacin sa,ji yake kamar ya kashe Bashir.

A'INDO ta rugo ta rungume Hajiya tana kuka tace"Hajiya sato ni yasa akayi shine na Kira Yaya Alhassan,dama yana Kira na tare da yi min test akan wai nayi hakuri na dawo gidan sa,ganin ya takura min shine nasa number sa a black liss,shine
Yau yasa aka sato ni lokacin da mukaje wajen siyen ice cream,na fito ina jiran yaya Al'Hassan yasa wani mai Adaidaita ya sato ni ."

Su A'indo harda karya wai ta fito tana jiran Al'Hassan🙄

Ran Hajiya kanta ya baci kallon Al'Hassan tayi tace"kayi min dai-dai,sanan takai kallon ta ga Bashir Wanda ya farfado anma idanu kawai yake binsu dashi dan baida ko k'arfin motsa yatsar sa .

"Bashir ada nayi tunanin Kai dan mutunci ne a yanda ka yaudare mu kaje mana da mayaudariyar fuskar ka,wada tasa muka baka yarinya,Ashe ba haka kake ba,munyi nadamar aura maka Aisha da mukayi tun farko, kai ko tausayin maraicin ka baka yi, gargadi zanyi maka Wanda na farko kuma na k'arshe tun farko yara na sun so rufe ka na hana su dan tausayin maraicin ka duk da abinda kayi ma yarinya ta,ka sani Aisha ya ta ce,wallahi Allah duk ranar da ka kara kokarin koda Kallon banza wa Aisha wallahi Allah kaji na rantse sai ka raina kanka ku fice muje."

Hajiya taja A'indo shima idrissa yaja Al'Hassan suka bar Bashir kwance tamkar gawa.

Bayan sunje gida gaba-daya Alhassan yaki sakar ma A'indo fuska domin cewar sa laifin ta ne da tayi hakuri suka tafi bata fito ba da duk hakan bata faru ba....

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[15/11 à 20:06] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*🏵 HAPPY JUMA'A🏵*

*Page 73-74*

Gaba-daya yanzu A'INDO ta damu,Sam batajin dadin abinda tayi masa ,gashinan taurin kai ya ja mata ya fara fushi da ita.

Suna shiga gidan ya fice b'angaren sa,Hajiya tace "A'isha je kiyi wanka kici abinci ki huta,ki fida damuwa insha ba abinda zai kara faruwa."
Gyada kai tayi ta huce b'angaren ta,dan yau acan zata kwana, idrissa ma salama yayi ya koma gidan sa,inda ya tarar da Husseina yake fada mata abinda ya faru.
"Haba ai da kun barsa ya kashe shi ma dan iska duba yanda yazo duk muka d'auka na Allah ne Ashe mugu ne,wallahi Yaya Al'Hassan ya burge ni gwara da yaci uban sa."

Hade fuska idrissa yayi yace"ni kenan ban burge ki ba ranar da na doke sa ko 😕"

"Au afuwa kaima kana burge ni,ai kaima kafi burge ni kaifa jarumin namiji ne,haba dai ya da kishi kuma yayan ka ne fa🤭 "

Rungume ta yayi yace"ba dole nayi kishi da abinci na ba.😉"
"Au nice abincin naka?
Cewar Husseina yace"eh mana kece
Abinci na danye mai dadi ba."

Dariya tayi ya rungume ta tare da fara aika mata sakwanin sa masu rikitarwa.

Dare misalin k'arfe goma sha daya kowa ya kwanta anma banda A'INDO da take da zuwa da dawowa a d'aki,tasan cewar Al'Hassan yayi mata laifi anma kuma ai yanzu ya gane kuren sa me yasa tayi masa haka duk cin fuskar da take masa bai taba bata ransa ba anma yau gashi tanaji a jikin ta kamar ransa ya baci wanan ya hana mata kwanciyar hankali,hijabin ta tasa
Ta fito sadaf-sadaf ta nufi b'angaren Al'Hassan Saida ta isa zata k'wank'wasa sai kuma ta tsaya cak,"me ke damu na ?
Me zanje nace masa,anya nice kuwa?

Ita kadai take tambayar kanta,can dai kawai ta shiga tare da yin Salama,a falo ta iske sa zaune saman kujera yana danna system dinsa, saman carpet ta dan zauna tace"dan Allah kayi hakuri idan na bata ranka,nasan nayi kuskure."

Al'Hassan kamar daga sama yaji muryar ta,abun yayi bala'in basa mamaki,wai yau A'INDO ce ke basa hakuri,tab yau kam yaji dadin sa,ya samu runguma ga kuma bada hakuri,wai yau shine ake bawa hakuri.

aje aikin da yake yi yayi ya tura system din gefe yakai duban sa gareta da kyau,yace"Aisha ba wai nayi fushi bane,nasan duk da ni mai laifi ne a gurin ki anma ki sani nayi miki laifi ne a lokacin ina cik'in fushi,wallahi Aisha idan nace miki ada can wanan abun da nake miki cik'in hankali na nake miki nayi karya,domin kuwa a lokacin ina cik'in fushi abinda iyaye na sukayi min,Aisha ada a shirme na duk macen da ta waye itace komai zatayi ba tare da ta sa ni jin kumya ba ,zan shiga ko ina da ita ,sanan ba wanda zai raina ni a shirme na ,wayewa itace komai,a lokacin bansan so ba ,bansan meye so ba,bansan ya ake yinsa ba
bansan hanyar da zanbi ba na san sa,wallahi duk matan da nake kulawa har ta yanzu wace na aura ba wai dan ina son su bane,nasan zakiyita tunani idan tsakani da Allah nake son ki me yasa tun farko da baki zama haka ba ban nuna miki ba sai yanzu,eh to a zahirin gaskiya a da can ban ma tsaya na zauna dake bare na fahimci so ,ban nutsu ba bare nayi tunanin zan fara sonki,nayi kuskure anma ki yafe min."

Rike hannun sa tayi abun yayi bala'in basa mamaki , murmushi tayi tace"a yanzu kana so na ?

Zaka iya aurena a karo na biyu?
Zaka iya zama dani a ko wane hali"?

Kasa controling din kansa yayi ya washe baki tare da Rungume ta bai shirya ba,"nagode nagode sosai Aisha Wallahi ban taba tunanin zan sameki ba,Allah Kaine abin godiya wallahi nayi miki Alkawarin zaman Amana dake,zan sanya ki nishadi zan zauna dake zama na har abada,zan baki farin ciki,Allah Aisha zaki aureni,zaki sa ni sau daya dai nima na dandana dadin aure.

Kada kai A'INDO tayi tace" Al'Hassan na kuma baka wata dama ta biyu ne dan Allah Karka kara sa na tsani maza,ka nuna min tunani na ba haka ne ba."

Girgiza kai yake yana hawaye na farin ciki tare da kara rungume ta."

Kokarin zame kanta tayi daga jikin sa.
Ta share hawaye da suka zubo mata tace"ni zanje na kwanta dare yayi, murmushin sa mai tafiyar da hankalin yan mata ya sakar mata yace"haba ke kuwa amarya ai kamata yayi ki kwana tunda dai kinzo bikon angon naki😉."

"😳ni din , wato har na zama amaryar taka ,hum karka sa na fasa ma.🙄"

"🙆‍♂ Ki rufa min asiri a yanzu idan kika kara kokarin bari na to tabas gawata za'a d'auka."

"A'a kaiko ana zancan kirki mai ya kawo kuma mutuwa a ciki nidai bana so ka daina."

"😊 To shikenan kiyi min Alkawarin zama dani a kowane irin hali."

"Nayi."

A'indo tace tare da barin gurin da gudu.

Dariya yayi ya koma ya kwanta,ya fara tsale ,rawa kam ranar ya sha ta, gaba-daya farin ciki ya mamaye sa.

Ita kanta A'indo d'aki da ta koma kasa barci tayi sai tunani da nazari take shin abinda tayi yayi ko kuwa tayi saurin bada kanta,anma ita tayi hakane saboda tsoro,tana tsoron kar Bashir ya Kara d'aukan ta dan a zahirin gaskiya a yau kawai k'arfin halin yima Bashir tsiwa tayi anma ta tsorata,tabas yin auren shine zai kare ta daga shairin sa.
Anma zatayi shawara da Yar uwar ta taji.
Chapter 36 · 0% Book details