← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 45

Sashe 19

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aci gaba da gashi😘
Maimou love🍇
[12/10 à 20:42] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Page -39-40*

"ba matsala matata zanyi ma malamin islamiya magana da na boko su sai a fara koyama A'indo harda Husseina tunda itama ta fara zuwa . Cewar Alhaji

"😊yauwa Alhaji na ,nagode bara na dan kwanta na huta."

"Ok anma nifa yaran nan sun jima basu dawo gida ba,ba kamar khalissa yar auta ta,nayi missing dinta sosai."cewar Alhaji.

"To Alhaji ai kai kace tunda sun zabi yin karatu a wata K'asar karsu sake su dawo gida sai sun gama karatun su,saide mu muje mu dinga Kai musu ziyara,yau shekara daya kenan fa da suka tafi wanan karatun kuma muje can wajen sau uku."

"Hakane."
Cewar Alhaji.

Duk wani abu da ya kamata ace anyi bisa kan karatun A'indo anyi,a d'auko musu malami wanda yake kara fahimtar dasu bisa kan karatun su,yayyin da acan Makaranta akayi ma A'indo gwajin.
Aka sa ta a jss1 , aka saya mata uniforms da komai,ranar Monday A'INDO ta hade cik'in uniform dinta,tayi bala'in kyau ,abun ba'a magana,domin kuwa Hajiya ita da kanta take sa A'indo gaba ta mata wanka,duk da A'indo na Jin kumya,yar shekara Sha shida ,anma Hajiya ke cewa ta fida kumya ita kamar yar cik'in ta ,ta d'auke ta,kuma baya ga haka ai bazata iya wanka da kanta ba saboda karayar ta."

Wanan dalilin yasa duk inda wani dati yake saida ya fita daga jikin A'indo,sai gata farin ta ya fito,mai bala'in kyau,domin kuwa ita ko a cik'in fararen farinta daban yake,irin mai kyau din nan ne,yayin da gashinta ma saida aka kaita salon aka gyara mata Kai,sai ga gashin ta ya zubo har a gadon baya abun sai Masha Allah,a yanzu ne naga asalin kyan A'indo,tanada fuska madaidaiciya,mai d'auke da idanu masu kyau da sheki ,wa'inda cik'in fari kal suke gasu in ka gansu ya Mai jin barci,tanada hanci mai kyau, dai-dai yake shi ba tsawo ba,kuma ba gajere ba ,yayin da takeda matsakaicin baki dan karami,kai wly wanan gyaran jikin da hajiya take mata anan asalin kyan A'INDO yaketa fitowa,wanda ko kai waye idan ka kura mata ido kana kalon ta bazata taba sauya maka ba,sabanin wasu da sai ace idan aka cika kalon su sai a gano munin su itakam A'indo abun ba haka yake ba,domin ita saide ta Kara maka kyau.ashe can ma shirmen ta yasa ban tsaya na gano muku asalin kyanta ba,sai yanzu da ta nutsu.

Ita kanta hajiya yanzu tayi matukar yabawa da nutsuwar A'indo ,ba wai dukan da Alhassan bane ya nutsar da A'indo a'a ,dan duka ko zagi baya nutsar da yaro saide ya Kara tunzurar dashi,kawai ta zauna ne tayi tunanin wukanci dacin kashin da Alhassan yayi mata,da kuma yanda taga jahili bayada wani galihu hakan yasa take son itama tayi karatu ko dan d'aukan fansa.

Malamai biyu aka d'aukar musu na isilamiya,da na Makarantar boko,kulum da dadare suke zuwa,Idan malamin islamiya yazo yau to gobe na boko zai zo,kuma daidai gwargwado suna fahimta,domin ko wani dogon hutu sun hana kansu,burin su a yanzu bai huce suyi ilimi ba,shima mai zurfi.

Abin burgewa anan basuda k'wak'walwar kifi,Allah ya basu ko yaya aka fada musu abu to ya zauna kenan a kansu,turanci shi ke basu matsala,Dan haka aka dage da koya musu sosai,tun basa ganewa har suka kai suna ganewa.

Yau sati uku kenan da fara karatun su A'indo,yayyin da a yanzu idan kaga A'indo yanada wuya ka gane su,domin sun fara wayewa,kuma duk abinda suka gani idan basu sanshi ba zasu tambaya ,kuma su koya.

A yau ne Mari tazo gidan,ba karamin dadi ba A'indo taji ba,kamar ta hade Mari dan murna,bayan Mari ta gaida su hajiya,ta fito A'indo ta ja ta b'angaren su,ita kanta Mari tana mamakin canzawar A'indo,aiko tana ganin husseina ta rude ,tace da A'indo dama ita din yan biyu ce,A'indo tace Eh ,nan suka gaisa da Husseina ,A'indo tace "Anty ya batun mu na inason aikin soja."

Mari ta nisa tace"A'indo me yasa kike son aikin soja"?

"Soboda in rama dukan da mugun Nan yayita yi min."

Murmushi Mari tayi ,sannan tace"A'INDO ai ko kin zama soja shine sama dake,ba zaki iya rama komai ba,saide kisha takaici,akoi ayuka gasunan birjik Wanda ya kamata ki zabi daya daga ciki ,ko baya ga haka a soja bazasu d'auke ki ba,saboda karayar hanun ki."

"Anty ai zan warke."
"Ai ko zaki warke bazasu d'auke ki ba,idan suka bincik'a suka san kin taba karyewa,anma kinga akoi karatun asibiti,akoi karatun zama Malamar Makaranta,akoi karatun sasanta iyali,gasunan da yawa ko wanne mace zata iya ,Anty meye karatun sasanta iyali.?

A'indo ta tambaya,
"A'indo karatun sasanta iyali ya kunshi abubuwa diyawa,ana ce masa Droit,acikin droit ma akoi wani b'angare daban wanda zakiga miji da mata suna samun matsala a tsakankanin su,ko kuma mata tana cutar miji,ko miji na cutar Mata,to anan za'a iya bima kowane hakin sa,ko kuma idan wa'inda za'a sasanta ne a sasanta su,
Za'a iya kiran sa da (Humain right)."
Akan wanan aikin har kasar waje idan kin kware a aikin ki,zasu iya fitar dake."

Kai wly Anty ni ya ma burge ni aikin,zanyi shawara."

"To ku dage da karatu ku zama wasu abu,wa'inda za'ayi Alfahari daku,a kasa."

Fira sukayita yi har dare sanan Mari ta tafi.

Duk wani abu da ya kamata Alhaji yayi,yayi bisa auren Alhassan da kuma Mina,domin kuwa yaje yaga Mahaifin Mina,shi dama ita kadai garesa ,kuma mahaifiyar ta ta rasu,ganin karta ja Masa abun zagi ga bataji yasa yayi farin cikin auren.

Inda akasa wata shida zuwa lokacin Mina ta gama school dinta,kuma auren a Nigeria za'ayi sa."

Alhassan da yaji iyayen sa basuyi fushi dashi ba,tunda idan ya kira su zasu d'auka,suyi komai kamar yanda suke ada ,yasa ya saki jikin sa kamar ba'ayi komai ba,ya sakankance,sunata shirye shiryen auren su shida Mina."

Mina dai irin matan nan ne da ba diri,Mai ma kuma bilichin take shafawa, yanayin zaman turai ne yasa ta caje ta zama fara tas,baka gane tana shafa mai,anma batada wani kyau,gata kulum cik'in attachement take,dan ba gashin,ni har mamaki nake me Alhassan ya gani a jikin ta yake son ta haka

*Bayan wata hudu*

Wani mission ne ya taso ma su Alhassan zuwa K'asar Maleshiya inda zasuyi shekara daya wajen wani kama wasu yan daba ne,kuma yan daban sunada yauwa,dole sai an d'auki lokaci mai tsawo kafin a kakama su,domin k'wak'walwa ce zatayi aikin,hakan yasa aka daga auren su shida Mina aka maida sa bayan shekara daya da wata biyu.

Ita Mina bata wani damu ba,tunda tana holewar ta,shikam iyayen sa ya Kira,suka bisa da Addou'a sanan ya tafi."

Anan ne Su A'indo karatu ya d'auki zafi saboda excam da zasu fara,wallahi Mai karatu idan kaga A'indo zaka rantse ba ita bace,domin zuwa lokacin karayar ta ta warke,komai normal,ga uban gayu da take ci,ga kuma ilimi da ya fara zama a kanta,ita kanta Husseina a yanzu ta waye,kaf Makarantar kowa burin sa yayi sityl irin nasu A'indo da Husseina,samari kamar su cinye su dan so.

Abinda zai burge ka dasu ko a gida yanzu sun daina yin hausa sai turanci,in suna wani abu kamar diyan turawa,wanan kuma duk da taimakon Mari da wasu yan class dinsu cewar su dinga turanci ko a gida,ko a tsakankanin su ne,hakan zai sa su kware sosai.

Hata iyo cik'in ruwa sun iya,Mari ta koya musu,a inda yanzu idan suna hutu to suna swimming pool na cik'in gidan ,wanda dama yaran gidan ke shiga yanzu basa Nan su A'indo ke hutawar su acan,har kawayen su mata suke ja suyi pic nik a gurin,in ka gansu cik'in ruwa ko kifi Albarka,bazai fisu iya ruwa ba ,ita kanta hajiya ji take dasu,sosai tana matukar Alfahari dasu,jinsu take kamar yaran ta na cik'in ta, Alhaji ya Saya musu manyan wayoyi,da computer aka koya musu yanda ake aki dasu, kullum cik'in search suke idan sunga sabon abu su koya .
a lokacin da Rabi'u daudu ya dawo shi kansa bai gane su ba,saida hajiya tace"Rabi'u bakaga mutanen ka ba.?

"Su wa kenan Hajiya.?

Su A'INDO mana."

Hajiya ta basa amsa,
" Yau ni wallahi Allah da tambayar ki zanyi ina Husseina ,Dan ita A'indo nasan tana kasar masu jajayan kunnuwa."

"A'a Rabi'u A'indo ai ta jima da dawowa ."

Ana tsakar magana sai ga A'indo da Husseina sun shigo,sanye suke cik'in dogayen riguna abayoyi,sunyi bala'in kyau,ba ma kamar A'indo dan tafi husseina diri , cik'in turanci suka gaida Hajiya a nutse,sanan A'indo ta juya ga Rabi'u tace"Hi Rabi'u tun a bakin k'ofa muke magana ka tsaya muka gaisa kayi gaba Alamun baka ganemu ba,yanzu kai saboda Allah ace ka huce baka gane mu ba , su A'INDO ne fa."

"La'illaha ilalahu,kai jama'a A'indo ,
Hajiya ki tayani dubawa,dan nidai ban yarda wa'inan sune ba, Hajiya ta tabatar masa da sune,tana dariya,ita kanta bata taba tunanin ba yaran haka suke kyawawa tamkar yaran turawa,sai da suka fara gyara kansu asalin kyansu ya fito."

"Tab wanan kyau haka,aradun Allah babu Wanda zai yarda idan akace daga kauye kuke,tab,cashi,a wallahi kun zama yan gayu,yau ni Allah ban Gane ku ba,ca nake bakin turawa ne Hajiya tayi,da naji kunyi hausa sai nace to wata killa rabawa ne,koyon hausa kukayi,wai Ashe kune."....

Wo fans sai a hankali kuyi maneji domin typing akoi wuya aradu.
[13/10 à 21:37] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
Chapter 19 · 0% Book details