← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 45

Sashe 5

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Anma Kai Kam anyi rago wly,Kai yanzu har ni zan kayar dakai,anma bazanyi mamaki ba tunda ga kanan ba auki sai kace dan shila,bara na nemo mai gyaran mutane ya gyara ka.".
Ta fada tana shirin artawa da gudu,da sauri Rabi'u daudu yace"ke dan Allah ki dawo ni ki kama ni ki kaini d'aki na,tunda kin kasarani,dan nasan in Kika sa kai kika fita bazan ganki ba."

Dawowa tayi ya dafa ta Saida ya tashi tsaye yana rike da kugu,aiko sai jin jiniyar mota sukayi da gudu A'indo ta sake sa Jin kake Rabi'u ya kara faduwa,yace"wayo Allah na zata kashe ni,ina A'indo ko jinsa batayi,cewa take "ai wly sai na gano bakaji sai wani kuka ake wiwiwi tana rike da siket har ta isa harabar gidan.

Dama kuma yau ne Alhassan ya shirya zuwa,duk da yace ma mahaifan sa sai jibi zaizo anma sai gashi kwatsam.

A'indo a tsakar gida ta tsaya da damarar ta a kugu kamar mai shirin dambe,ga kai a bude,tun kitson da tazo dashi ne daga kauye duk ya tsufa."

Washe baki tayi tace"tab aradu yau zansha kalo,ina husseina kizo kisha kalo aradu,motoci ne take gani sai shigowa gidan suke sunki karewa,kuma duk wada ta shigo sai sodji ya fito rike da bindiga,ga bakin gilashi yasa,fuska tamke ba alamun fara'a Saida motocin kaf suka gama shigowa,sojawan sunkai guda talatin,duk sun firfito , banda motar tsaka wada aka bud'e ma mutumin tun dazu anma bataga ya fito ba,"tab A'indo tace,da taga tsayuwar na gagarar ta sai ta zauna rashe rashe tayi itafa sai taga mai fitowar nan,ankai minti goma sanan ya zuro k'afafun sa,saida yadan d'auki Dan lokaci sanan daga k'arshe ya fito gaba-daya,waya ce a kunnen sa ga duka Alamu zaman da yayi ita yakeyi,ganin da A'indo tayi masa yayi matukar firgita ta,domin ko alama baiyi mata kama da mutum ba a firgice tayi wata irin juyawa,ta fara ihu tana gudu,tare da kwararo Addou'a wa'innahu suleymana wa'innahu bisimillah , Wayyo jama'a ku kawo d'auki rundunar Aljannu sun shigo gidan,Hajiya da ta fito da tabatar da abinda taji,aiko sukayi aran gama da A'indo ta mata wata irin bangaza d k'arfi ji kake tim Hajiya ma ta fadi,ko juyowa A'indo batayi ba taci gaba da gudu,saida ta isa d'akin ta tunkon ta rufe tana karkarwa,har zufa take tana sharewa,jin tayi an k'wank'wasa kofa da k'arfi ,kululu cikin ta ya bada kara,iya tsorata ta tsorata dan ta aza ko aljannun ne suka biyo ta,Jin da tayi an Kara k'wank'wasa k'ofar yasa ta saki fitsari ba shiri,Alhassan ko tunda yaji abinda A'INDO tace dasu ya daina wayar ya daga Kai yana kalon ta,har bangajewar da ta ma mahaifiyar sa,da gudu ya karaso ga mahaifiyar tasa,yasa gard daya yabi A'INDO ya kamo masa ita,Hajiya na cewa a barta anma ina Alhassan ko jinta bayayi kawai burin sa a kamo ko wace Yar iska ce ya lakada mata dukan mutuwa.

Husseina ce tsakar gida sai rusa kukanta take,tana birgima a tsakar gida,kulu mai bakin masifa ce ta fito tace"kaji min hegiyar yarinya,to uwar me zamu Miki? ki matsa mana da kukan mutuwa a gida."

"murguda baki Husseina tayi bakinta cik'e da masifa tace"wly in ba'a kaini wajen yar uwata ba,sai na hada zanga zanga a wanan garin."

"tab Allah iska na wahalar da me kayan kara,yau ki hada zanga zanga mana,ai ni na saba,dan kinyi haka ba zaice min komai ba,shi yasa kuka ki auruwa da keda Yar uwarki,ita Allah ya taimake ta tabar nan din ke kuma sai kiyita fama."

tana gama fadar haka tayi gaba abunta,itakuwa Husseina cigaba tayi da kukan ta ,tana birgima wayyo Allah zan kashe kaina in ba'a kaini wajen yar uwata ba,Wayyo A'indo kina ina,wly in ba'a kaini wurin yar uwata ba zan shiga yawan duniya, yiiiii Wayyo baban mu."

Mahaifin ta ne ya shigo gidan Ado Mai kifi,yana matukar son yaran sa,ganin husseina na kuka yasa ya karaso gareta a rude,yace "ya salam auta me ya faru wa ya taba min ke ne?

"Zumburo baki Husseina tayi tace"ni aikaini wajen A'indo ,😭."

"Wanan ce matsalar?

"Eh"

"To sha kurumin ki duk ranar da A'indo tazo tare zaku tafi,kema a sama miki aikin can kinji."

"Allah babana😁"
Husseina ta fada tare da washe baki tana dariya

"Allah kuwa ya'ta tashi kije kiyi wanka ga kifi na kawo miki da zafin sa,kici Kara tumbure baki Husseina tayi tace"yau ai ga matsalar nan kulum a dinga dura ma mutum kifi,ko tusa mutum yayi saide kaji tace kifiiiii🙄
.......ni wly yau nama zanci."
..... To naji tashi dai kiyi wanka zan sayo Miki."

"ALLAH babana,wo kai wo kai,ta dubi kan na uban sulub dashi sai walkiya yake a tsaka,ba gashi kuma ga kan karami ta shafa kan uban bayan ta tashi tace "tab kwal uba,aradu babana kanka ya kuli kuli,abu gashina dan tsurut,Allah baban mu da Kai mukayo bazamuyi kyan gani ba,to da dadi tunda Maman mu mukayo dan ita tanada kyau,to anma kai baban mu🤔"

"Ke banson shashanci,ana ganin Yar uwarki ce kadai barruwa ashe kema wawancin kinada shi,maza je kiyi wanka."

" Wo wo wo kai baban mu Allah ja zamanin ka eh yane,kasha shagalin ka,Husseina ta fada tare da rike zani tana tafiya irin ta maza.

Uban kam cewa yayi Allh ya shirya,Kulu da ta fito duk a gabanta abun ya faru tace"wly Kai ke bata wanan yarinyar, yarinya sai batanci mtssssss."

Baice da ita komai ba yayi ficewar sa d'akin sa dan Yasan in ya biye mata sai ta watsar dashi yanzu.

Alhassan Kama Mom dinsa yayi yakaita d'aki,tace"Sodja na dan Allah nasan ka karka sa ayima wanan yarinyar komai,batada cikak'en hankali,kuma ta tsorata ne,Yar kauye ce bata san komai ba."

baice komai ba anma ransa a bace yake da wanan yarinyar ."

Sodja shiko sai bugan k'ofa yake A'indo ta bud'e dan yasan in har bai tafi da ita ba,ogan sa zai hukunta shi."

"A'indo fida toro tayi ta d'auko wuka a hankali ta bud'e k'ofar,ta nuno masa wuka ta d'aure ta cije ,ta bud'e Idanun ta sai taga bakin mutum ne ,kuma mumuna tace"au kai kuma sufar ka ta munana ce,shi wancan ta kyawawa ce,to wly naci dubu sai ceto,ni A'INDO Baku Isa ku tsorata ni ba,runtse idanu tayi ta fara wurga wukar da hannun ta soja tsoro yaji ya koma baya,dan bai d'auke ta a mai hankali ba,yace"dan Allah kizo muje oga na yace na kamo ki."

"Ka kamo ni sai kace fara🙄" A'indo tace,"Eh kizo
Waye shi"?

Ta tambaya dan mai gidan nan ne." tunani ta tsaya yi yau ko shine dan Hajiya sodja, tab to aiko bari taje taji bashin sa taci bata biya ba😗 "mtsss ya sani inata zabga gudu nayi tunanin mutanen boye ne."

"Muje to ka wani tsareni da Idanun ka kamar na mujiya."

Sojan ransa yayi matukar baci kawai ya raga Mata ne dan tanada wuka a hanun ta kuma ga dukan Alamu batada cikak'en hankali,"shiga gaba yace da ita."
"kaji wauwta yau ni in higa gaba ka damke ni ,Kai nima fa da wayo na,shiga gaba kai muje ai nasan wurin hajiyar."

ba yanda ya iya ya shiga gaba itako ta sanyo sa gaba da tsinin wuka,yanayi yana waiwayowa karta nakasa shi,kai kace shine mai laifin ba ita ba .

a haka suka karaso falon Hajiya ,soja yace" oga gata na kawo rai a bace Alhassan ya taso zai nufo A'indo,wata irin zabura tayi ta bud'e k'afafu,kai kace mai shirin dambe ,tace"aradun Allah ka iso nan sai an kwashe ka ta nuno sa da wuka ,tace"yau wace magana ce baza'a min ba daga nesa sai an taso😏 Kai kasan matsayina kuwa? Kasan ko.ni wacece?."

Aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:28] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/

_Wanan litafi gaba-daya sadaukarwa ne gareku my Ummy Ontop (takwara) da Sajida, Marubuciyar (Yar Mahaukaciya),sadaukar ne gareku ga yanda kuke kaunar book din A'INDO tun farkon sa_😍😍😍😘

*DEDICATED TO Sadjida & Ummy Ontop*

*Page 11_12*

"""""""To nice Nan A'INDO Tantagariyar Yar Aiki,😏 kuma baka isa ba kace zaka dakeni,dab da zai karasa gareta Hajiya ta daga murya tace"Alhassan nace maka karka taba yarinyar nan ko,wly ka taba ta sai ka hadu da fushi na."dole ba yanda ya iya ya yarfar da hannu ya bar wurin,rai a bace."

Gyara tsayuwar ta A'INDO tayi tace"aradu hajiya kin cece sa yau da na jibgi kayan banza,dan yagan sa Kato an fada masa tsoran sa zanyi,ta juya ga wancan sojan dake tsaye tace"to kikam sai a tafi dawa batayi mai ba 🙄."

Juyawa yayi ya fita shima cik'e da haushin ta,yana tunanin wacece wanan ko wacece tanada matsayi a gidan.

"A'indo dawowa tayi wajen Hajiya ta zauna ta Shiga tunani tare da daga Kai sama🤔 can tace"yauwa na tuna,kamar zata fadi abun arziki tace" nikam Hajiya Dan Allah dazu naji na buge abu kamar buhun hatsi ko na masara lokacin da nake gudu oho ,Hajiya sai Naga abun kamar yamin gizo,sai nake ganin kamar ke na buge,Allah Hajiya gidan Nan cik'e yake da mutanen boye, dan ma nidin nasha na kohi ,Hajiya dan nan naki ma inaga sune sauye aka miki,mutum sai mayen kyau,Niko Hajiya na tambayeki dan Allah Ina sonshi zai aureni😁"

"Kalon ta Hajiya tayi tace "nikam Hajiya Saude na debo ruwan dafa kaina,wai dan A'indo yaushe zakiyi hankali?

"Gobe dasafe"

A'indo ta bata amsa tare da kamewa wuri daya.

Girgiza kai Hajiya tayi tabar wurin."

Sam Rabi'u daudu nacan na fama ko kadan bai san cewar Alhassan ya dawo ba.

Dadare wajen k'arfe Tara na dare akoi wani serie film da suke kalo shida A'indo wanda Rabi'u ya koya mata kalon itama,duk irin wanan ranar ake yinsa sukan zo falo baba suyita fade faden su da kalo.hakan ce ko, Rabi'u yaji sauki yazo kalo Hajiya na sama,Saida ya biya ya Kira A'INDO dan suyi kalon dan duk da suna fada yafi jin dadin kalon da ita,duk da shirme da kauyancin da take zabgawa."

Zama sukayi kamar abun arziki suka fara kalo.
Chapter 5 · 0% Book details