← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 45

Sashe 3

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kaina nayi mamakin ci irin nata,Hajiya ce ta fito ta sauko daga matatakala tana kwala Kiran Aindo ,anma sai me tana saukowa daga matatakala sai ji tayi kamar an d'auke ta an yado,wata kara ta saki wanda ya tada Hankalin Yan gidan suka fito gaba-daya ,anma duk Wanda ya shigo falon saide kaji suuuuuuu ya fadi,wasu kuma kamar an jefo su haka zakaji suna faduwa,harda yan aikin gidan,dukan su daga mai rike kugu sai me rike kafa,wasu kuma reran suke kwance,daya saman daya a hankali Aindo ta fito ,kamar yanda ta fita,wato da rarafe,har ta karaso falon ,ganin mutanen gidan duk zazaune wasu a k'wankwance ,wasu na hawaye ,sai zama itama tayi ta aza hannu bisa kai ta kece da kuka,"yiiiii yiiiiii,Allah jikan ka hanma Allah jikan ka hanma,Wayyo Allah bango ya fadi.
Gaba-daya sai suka tsaya suka zuba Mata,ido duk da sunajin radadin faduwa da sukayi, Hajiya ce tayi k'arfin halin cewa"ke wai lfy waye ya rasu mutane na cik'in wani hali kizo kina mana kukan mutuwa."

tsayar da kulan Aindo tayi ta zuba ma Hajiya idanu,tace"to ba zaman makoki kuke ba,in ba hanma ya mutu ba ai bakunzo kuyi wanan zaman ba ,harda masu kuka,yiiiiii Allah ya jikan ka Hanma , Alhaji ne ya fito yana cewa wai lfy ko " waro idanu hajiya tayi tana cewa Alhaji karka karaso Kar ka karaso akoi matsala a kasa."
"Nikam Hajiya kinada shirme watarana kema me kuke yiiii ai bai gama fadar abinda yake shirin fada ba sai ji kake suuuuu ya jibgo kasa sai saman Hajiya,wata Kara sukayi a tare ta wahala,anma Hajiya tafi cin wahala ,me Aindo zatayi in ba dariya ba harda rike ciki,sanan tace"Alhamdulillah ashe ba mutuwa akayi ba,kardai kuma faduwa kukayi,to ku dama in Banda abunku da waw ta irin ta yayan farin wa zai taka wanan guri ba tare da ya bushe ba,woooo wooooo Alhaji Alhaji yasha kasa🤣"
Rarafawa tayi har ta fito waje duk sunyi sake suna kalon ta,har ta fita tana fita tayi ajiyar zuciya tace "wai Alhamdulillah Kai anma nikam wly yar baiwa ce na iya dabara, bari na fita na nemo magyari ya gyara su wai likita shine magyari🤣,da gudu ta fita tabar gidan,tana fita ta gyara d'aurin kugun da tayi,da dankwalin ta tayi ture kaga tsiya, zane daban riga daban dankwali daban,Yar kauye sak👌ga wata kwaliya da taci kaf ta rikita fuskarta da wata rikitaciyar kwaliyar ta.bazaka taba gane yanayinta ba,wani ta hango yana tafiya,gyara tafiyar ta tayi,Dan wai Kar ya rainata ,dan tasan mutan birni da raina yan kauye,tace"Kai dan mutume kai tsayawa yayi,ganin kamar dan birni ne wayaye sai tace"ke Aindo kema fa yanzu kinada matsayi karki manta a bini kike,kuma kowa da aikin sa yake tinkaho,to aike baban aiki ma gareki dan haka karki kwafsa,duk ita kadai take maganar ta cik'in Zuciyar ta,yamutse fuska tayi kicin kicin Kai kace mai jin kashi mutumin Yana kalon ta tsoro ma ta basa tsayawa yayi har ta karaso yaji ikon Allah ,tana wani Fadi tana kumbura,ta karaso tace "hi gaye wai irin na Yan birni ya kake dan Allah a Ina ne ake zuwa a d'auko mai gyara mutum idan ya lalace."
Kalonta ya tsaya yi ,sai ganin ta murguda masa baki yayi,aiko ransa ya baci yace
"Ke Dan kin raina min hankali kinsan ni waye zakizo kazama dake wa ya sani ma ko mahaukaciya ce zakizo kina wani tambaya ta kodan kinganin a kasa,to ni dan Minista ne,motata ce ta samu matsala badan haka ba ke kin isa kimin banzan tambayar ki Yar kauye kawai."

Tunda ya fara magana Aindo take masa gatsine tana murguda masa baki,tace "mtsss Ashe ma ba wani matsayi ne da uban naka ba,ina wani gadara a aikin masai ko me,yau Kai uban naka ma aikin kwasar Kashi yake ko,to bara kaji ni sunana Aindo ya a gurin ado Mai Saida kifi ubana babu wanda bai sanshi ba,uwata kuma babu Wanda baisan kuluwa Mai bakin masifa ba ,nikuma matsayina wly in kaji sai ka sara min,to matsayin da na taka ko wa yaji sai ya saramin."

" Meye matsayin ki ya katseta ganin Alamun kamar batada hankali?

Niko keda matsayi,domin ni tantagariyar Yar aiki ce,Mai zaman kanta.

Kuma kaf wanan k'asa babu Wanda baisan A'indo Tantagariyar Yar Aiki ce ba."

Sakin baki yayi sakaka yana kalon ta duba da yanda take zare zaren idanu tana kade Kaden idanu ya tabatar masa dacewa wanan batada hankali,shiko a duniya in akoi abinda yake tsoro to mahaukaci ne,domin tun Yana yaro wata mahaukciya ta taba fashe masa Kai,aiko ganin zare zaren da A'INDO takeyi yasa ya tsorata,tare da hada wani yawu makwat,ja da baya baya ya farayi adan tsorace tana binsa,ganin da yayyi kamar zata kamo sa yasa ya arta a guje,itama da gudu ta bisa,tare da ihu bisa hanya,tana cewa"wayyo jama'a ku kawo mana agaji gudu take tana waywayawa, duk a tunanin ta ko wasu suka biyo su,sosai take tikar gudu har ta fita daga unguwar,can ta tsaya tana haki,ta juya ta buga tsaki tace"mtsssss ashe ma bahon ba komai ba ya gani yasa ni inata tikar gudu kamar wata mahaukaciya 😏"

Saida ta gama gararanmar ta a gari bata samu mai gyaran mutum ba kamar yanda tace,tukon ta dawo gida can wajen yanmma,a lokacin tuni doctor yazo ya duba mutan gidan,inda akayi sa'a basuji rauni ba.....

tana dawowa ta shigo falo,ta kalli Hajiya dake zaune ta washe baki tace"wo wo Hajiya yau anji jiki aradu,Ashe manya ma na faduwa.😁

Kallon ta Hajiya tayi rai a bace tace "yanzu ke A'indo haka ake aiki so kike ki nakasa mu,wa yace miki ana zuba man gyada ayi guga?

"Yau Hajiya ke kikace falon yayyi walkiya har sai ya koma tamkar madubi,to shine Naga Man gyada kadai zaisa d'akin yayi walkiya,kuma ke Hajiya banda shirme irin naki,Aou 🤭na manta ashe ke baba ce,to Hajiya in banda wauwta irin ta yayan fari me ya kaiki taka gurin ba tare da ya bushe ba."

Sake da baki Hajiya ta tsaya tana kalon A'indo wada take magana tsakaninta da Allah , Hajiya tace nice "mai wauta irin ta yan fari, kuma uban waye yace miki man zai bushe?wai anya A'indo kinada cikak'en hankali kuwa?

"To wly Hajiya nima haka ake cewa a kauyen mu inajin dai sai an kawo mai gyaran mutane ya bincik'e ni ya gani dan wly ko a kauye haka ake cewa banda shi.🙄

Sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi kawai A'INDO ta Shiga ranta ne da yau sai tabar gidan."..

"Jeki ki huta gobe an nuna Miki aikin."

"Yau Hajiya wane hutu zanyi inajin yunwa."
"Je ki zuba abinci can kitchen ."

Hajiya tace Dan ta dan fara jin tsoron A'INDO.

Anma Hajiya langa nan zan cika dan wly tunda nazo gidan nan ban taba koshi ba."

"Kije ki zuba iya cinki."

Hajiya tace tana mamakin irin ci irin na A'indo

Bayan kwana biyu Hajiya ta Kira A'indo tace tazo taso mata kati na waya A'indo ta amshi dubu biyar Hajiya tace kiso min na dubu hudu da dari biyar,ki d'auki dari biyar,din kisha halawa."

Kai Anma Allah zungura Miki Albarka Hajiya wly,Bari naje na sayo Miki.
Da gudu ta fita."

Hajiya ta girgiza kai tace "Allah ya shirya,tana fita kofa da gudu har taje bakin hanya akoi wani shagon waya,Nan ta nufa to,A'indo dai batasan meye katin waya,itadai ta taba ganin gidan waya wurin Yar aikin gidan Hajiya da zuba kayan kwaliya a ciki,A'indo tace meye sai tace mata ai gidan waya ne ,to shine ta rike,dan ta manta abinda Hajiya ta aiketa siya tana zuwa tace"mai shago abani gidan waya na dubu hudu da dari biyar."

Waro idanu Mai shagon yayi yace gidan waya kuma"

Murguda baki A'indo tayi tace "kaga Malam ka bani gidan waya meye na wani tambaya,baga irinsa ba ba can na gano ta nuna wani kwali.

Yace"Au kwalin waya zakice ,yau ai ba'a saida kwalin waya,saide ,in wayar Zaki saya....

" kaga Malam wly banzan gusa anan ba sai ka bani kwalin nan na dubu hudu da dari biyar casssss ma kuwa." ta murguda masa baki,ganin yayi bari kaway ya amshi kudin ya bata, dan ga dukan alamu batada hankali."
"Kawo kudin to na baki."
"Hahhhh kaji dan rainin hankali cewar ta,😏 ta kunto kudin da tayima kuli ta basa,kuma ka bani canjina eheee kar ayimin halin bera."
Bata yayi dariya kunshe a bakin sa,Saida ya bata tace "yauwa dan gari,a haka dai gaka kamar ka waye anma katon bakauye ne kai,way Malam dan Allah na tambaye ka mana?
" Inajinki"

"Dan Allah Ina ake saida igiyar kaba ta d'aure awaki da raguna 🤔?

"Kije can ga wani tsoho can zaune sune yake saidawa."

"😁 Kai anma wly Allah ya maka Albarka ta kunto wata tsohuwar naira biyar dinta a zani tace"gashi ka fida nera biyu kaban naira uku canji na,na baka kyauta halak malak,saboda ka nuna min wurin Saida igiya."
"Kada kai mai shagon yayi yace a'a jeki nagoda."
"🙄 Inba shirme irin naka ba wa yake kin k'arbar kudi,ai sai kayi ni na tafi,tafiya tayi taba tsohon dari biyar din duka tace" baba ka bani wanan igiyar ta dari biyar.
"Kai yata duk ina zaki da wanan igiya."

"Dariya tayi tace "baba ka bani."

"Yanzu ko yata ,ni ai na ma saida bari na baki,duka ya zuba Mata a buhu ya bata, ta jawo kayanta tana waka har ta karaso gida duka mutanen gidan kalon ta suke,babu Wanda ya d'auke ta mai hankali.

Karasowa falon tayi ta aje buhun kusa da Hajiya tace"wai Hajiya na gaji wly.
Kallon ta Hajiya tayi tace"keko meye wanan Kika jajubo a buhu.?

Washe Baki A'indo tayi tace Hajiya ai igiya ce"😁

"A'indo igiyar me kuma me zakiyi da ita?
Chapter 3 · 0% Book details