← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 45

Sashe 13

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Masoya na asali kuma magoya bayan mu,ni Maimouna Matar_ _Abdoulahi ina nan tafe tare da baban kuma mashahurin litafi na Mai suna *YAN GATA NE*,wanda yake d'auke da abubuwa mai matukar amfani garemu_ _Mata,litafi ne mai cik'e da abubuwa,wanan litafi ya kunshi abubuwa kamar haka ,👉iya kwanciya a gidan auren ki,iya kula da mijin ki,kissa,kishi cik'in ilimi,ba tare da mace ta maida kanta_ _mahaukaciya ba saboda kishi,magance matsalar da ta adabe ki ta namiji,kama da komai ma da Mata ke fuskanta a wanan zamanin,a gaskiya tsayawa zana abinda wanan litafi ya kunsa bata lokaci ne,shi yasa na baku kadan daga ciki,duba ga yanda idan har na fara rubutasa a_ _Free to nasan abinda zai biyo baya,dan nasan za'ace ina rashin kumya,nayi batsa,hakan yasa duk wada take son karanta wanan litafin zata biya Naira dari biyu,sanan wanan litafi na matan_ _aure ne kadai,dan Allah duk wace tasan budurwa ce bana gayatar ta ,sanan bana bukatar kudin ta ko shigar ta wanan group din,in ko kika shiga ba ruwa na🤷‍♀ Allah yana gani na fita hakkin ki,domin wanan litafin ,na karuwar matan aure ne kawai sai kuma wa'inda zasu shiga daga ciki ma'ana wa'inda aka kusa auren su,karku bari a baku labari,Naira dari biyu kacal zaki biya ki more rayuwa tare da_ _gyara halakarki gami da zamantakewar auren ki,Litafin_ _*YAN GATA NE*_
_Yana nan tafe_💃💃💃

*Page 29-30*

Tunda Alhassan yaga yanda A'INDO ke dariyar keta,yasan da sa hannun ta a wanan danyen aikin....
Dan haka ya kama Linda ya d'auke ta ya kwantar da ita saman doguwar kujera,a lokacin tuni A'indo ta Kama bakin ta tayi shiru gudun kar ya gano ta,bata san ta makaro ba....

Cik'in dabara Alhassan ya koma inda sulbin ya ja su duk da yana jin zafin faduwar da yayi,dukawa yayi yasa yatsa ya dangwalo man da ya gani ya shinshina,ya tabdatar da mai ne aka sa a gun,wata dariya gefen baki yayi mai cik'e da ma'anoni daban daban ,hadi da bacin rai, gami da takaici.
Wata kararawa
Ya danna nan danan sai ga sojawa Mata sun shigo falon,nuna musu A'indo yayi yace"ku duketa har sai ta suma,idan ta suma ma ku kwara mata ruwan sanyi ta farfado ,idan ta kuma tashi ku kara lafta mata dukan,sanan ku rufe min ita a d'akin wancan na tsohon dog wanda ya rasu na gidan nan."

Wuki wuki da idanu A'INDO tayi dan taji abinda Alhassan yace musu, kasancewar da hausa yayi maganar,soboda suna jin hausa .ta aza hannu bisa kai ta fara ihu tana rokon sa dan Allah yayi hakuri bazata kara ba,ina Alhassan Linda ya saba yayi d'akin sa da ita,ya kira doctor dan a duba mata k'afar ta.

Acan k'asa ko A'INDO tsere ta fara dasu,idan sukayi gusun tayi arewa,in sunyi arewa tayi yanmma, gaba-daya wana su take a falon,su kansu saida suka fara gajiya,a Hankali A'INDO ta biyo ta inda ta zubar da Mai ta dan hau matatakalar tayi hakane dan su biyo ta suma su samu rabon su,aiko hakan ce ta faru,domin kuwa suna biyo gurin da zafin nama,irin na sojawa,cikin bacin rai dan kamota anma sai me ji kake suuuu sun bada tim sun fadi,dayar har saida ta fashe baki,su kam ba karamar faduwa sukayi ba ,dan kuwa kasa tashi sukayi.

Sama A'indo ta haye inda taga Alhassan ya shiga anan ta shiga d'akin, tsaruwar d'akin yasa anan take ta sulale ta fadi tamkar wada ta suma,jin kamar abu ya fadi yasa Alhassan juyowa dan ganin wane dan iska ne ya shigo masa d'aki babu izini,yasan dai ba mahaukaciyar da aka lakaba masa bace,dan yasan zuwa yanzu ta ladaptu wata kila tana can an rufe masa ita kamar yanda ya bukata,anma ga mamakin sa sai yaga A'INDO, ta tashi zaune ta kalli d'akin ,ta koma kuma ta kwanta wai ta suma, gaba-daya ta rikice da ganin tsarin da daular da aka shimfida a d'akin,shi kam Alhassan abun d'aure masa kai yayi,tare da mamakin ina sojawan da yasa su kama ta su duketa,🤔, gaba-daya yanzu Al'amarin yarinyar ya fara basa tsoro,anya ba mahaukaciya bace kuwa?

Husseina ce tsakar gida taci damara,sai masifa take it kadai, Rabi'u daudu dake zaune kusa da ita kadan yace"wai ke masifar me kike ma mutane duk kinbi kin adabe mu😏."
"Yau ba dole nayi masifa ba,ace duk wanan katon gidan ba kasa,inason nayi rame nayi yar carabke anma ba hali,dan Allah muje waje ka rakani nayi carabke😁"

"Ke dan Allah rabani da zancan banza,andai ji kunya ace kamar ki kina wani carfke,a'aaaa wly anyi girman banza aradun Allah,ke ni fa sai naga ma kinfi A'INDO rashin hankali,yanzu ke katuwar ki guda rusheshiya dake zabgegiya kike wani zancan carafke,to wanan badala bada ni ba,a nemi
wani makidin,ni kinga tafiya ta ,ya kama hanya yana tafe yana murguda duwawu....

Cik'e da takaici Alhassan ya iso inda take cik'in hargowa yace"ke wai me yasa kin raina ni?
Uban wa yace"ki shigo min d'aki ni sa'an ki ne?

Shin inama wa'incan sakarkarun da na basu horon ki?

Wanan karon ransa yayi mugu mugun baci,ganin kalon da take masa na rainin hankali,k'afar sa yasa ya fara ball da ita kamar ya samu jaka,jin wanan dukan yasa A'indo tashi a rikice tamkar mahaukaciya,zata gudu,damko ta yayi ya yarfar,nan ya fara jefa ta,yana ball da ita har ya fido ta daga d'akin,kuka A'indo ta fara tana rokon sa gafara,saboda zafin bugun da yake mata,ina ko jinta bayayi,ran maza ya baci,dukan ta yake a duk inda ya samu,haka yayita tila ta kamar ya samu k'walo, cik'in azaba A'indo tana son tashi anma abun ya gagara,saboda zafin dukan .wani irin bugu da yayi mata daga matatakala sai gata tana gangarowa ihu take tare da dafe wajen cikin ta,a haka har ta fado kasa,ganin gards dinsa Mata zaune
Ko wace tana rike da kafa,abun ya kara tunzura sa dan yasan suma faduwa ne sukayi ,kara buga ma A'indo kafa yayi,ta saki wata razananar kara sai gata ta sume,koda ta suma bai barta haka ba dukanta yaci gaba dayi har saida ya karye mata hannu daya,azaba ce ta kara farfado da ita,tun muryar ta na fitowa tana basa hakuri har takai muryar ta bata fitowa, gaba-daya jikin ta yayi jaga-jaga da jini,ya bata mata kamanin ka,dukan da yake mata kamar ya samu kato,babu alamun imani a tatare dashi,saida yaga ko motsin kirki bata iyawa sanan yasa sojawan da su cicibeta suyi d'akin tsohon karen da yace su sa ta dazu,sanan yace kar a bari ta dinga fitowa,abinci ma a dinga bata sau daya a rana, aiko haka akayi d'aukan ta sukayi sai daya ta lura da karyewar da tayi a hannu sakamokon yanda hannun ya lank'wasa."

"Sa ina ganin fa kamar hannun ta ya karye."

"Mtsss kai bana son zancan banza kuje kuyi abinda na sa ku,ina ruwa na da wata karewar ta,ta mutu ma ina ruwana,duk wanan maganganun A'indo na jinsa,kuma azaba na cinta,tunda take a rayuwar ta bata taba tsanar wani abu ba sai yau,lalai Alhassan bashida imani,wasu hawayen takaici ne suka zubo mata,d'aukan ta matan sukayi,suka kaita d'akin da akace,dayar ce tace"Jenifer ni fa kiran Doctor zanyi bazan bar yarinyar nan haka ba fa,kinaga hannun ta ya karye,idan aka barta a haka yayi tsami zata iya ma rasa hannun ta."

Dayar wace aka Kira da Jenifer saboda Crista ce ,tace"ke kikaji kina iyawa,ni kam ba ruwana,duk abinda ya biyo baya kece sila ,kina dai ganin abinda yarinyar nan ta mana,anma dan bakida Zuciya kike son taimakon ta."

dayar Mari wada ke son taimakon A'indo musulma ce,dan haka tace zata d'auki wanan kasadar,domin kuwa
Ita dama tausayi gareta,ba karamin tausaya ma A'indo tayi ba,dan haka ta kira saurayin ta doctor ne,yana bala'in son ta,dan haka tace yazo da mai gyara hannu,dan itama ta taba karyewa shi ya kawo mata wanda ya gyara ta,nan ta fada masa kanwar ta ce ,ba'a jima ba sai gashi,A'indo tayi kuka sosai wajen gyaran da aka mata,sanan ya bata magani,anan suka bar A'indo tayi barcin wahala.

Hajiya zaune ita da Alhaji,ya dube ta yace"hajiya nayi tunani hakika kin fadi gaskiya game da dawowa da matar Alhassan A'indo,anma ba yanzu ba,akoi lokacin da dakaina zan sa kije ki d'auko ta,karki damu."

"Shikenan Alhaji yanda kace ,anma dan Allah kar a d'auki dogon lokaci,kaga A'indo ba kai ne da ita ba bare Wayyo, Alhassan kuma ga Zuciya,Kar yaje ya halaka ya mutane...."
Cewar Hajiya.

Ayi maneji fans😍😘

*Page *
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*And Now*👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Masha Allah kawata,Mrs Adam Yar Mutan kagara,ina matukar tayaki murnar kamala litafin ki mai suna( Labarin Amira),litafin ya bada baban darasi wanda ya kamata Al'ounma su karanta kuma suyi amfani da wanan darasin,domin mata irin su Nafissa matsawar basu tuba ba to makomar su wuta,Allah ka mana tsari da ita,hakika labarin Amira cik'e yake da baban darasi,ya koya mana hakuri,da juriya,ya hane mu da shirka,cin zalin, wulakanta miji,Allah ka mana mai kyau,wanan litafi ya fadakar,ya nishadantar,ya ilimintar,Allah ubangiji Ya baki ladan dake ciki kuskuren ciki kuma Allah yafe miki,up up up my kawa kawar kirki,kawar arziki,kawa har a gidan Aljanna, Insha Allah.ina Alfahari da ke,a kulum kuma sonki karuwa yake a zuciya na,ban hadaki da kowa ba aradu idan aka cire iyaye da oga🤪🙈,Allah ya barmin ke my heart,ya Kara ma oga sonki linkin ba linkin,ya raya miki zuri'a,ya karama mahaifan mu nisan kwana,ya basu lfy ingantaciya,sha shagalin ki kawa daga ke sai ke a gurin oga ba kari*😍😘💃

*Page 27-28*
Chapter 13 · 0% Book details