← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 45

Sashe 38

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zumburo baki yayi yace"daddy so ne ,shi ba ruwan sa da jarumta, zuciya ba'a iya controlling dinta game da so."

Girgiza kai daddy yayi cik'e da farin ci yace"to ai sai ku fara shiryawa tunda batada idda a kanta za'a sa wata daya ayi a d'aura muku mu huta da rashin kumyar ku."

Hajiya ma murmushi tayi yanda taga yanzu suna son junan su matuka,nan suka juya suka haye sama ita da Alhaji."

Kallon ta yayi yace"ashe kina so na haka shine wancan lokacin kika nemi kasheni,da yanzu na jima a kabari."

"Shiiii🤫 bana son haka ,ya zaka mutu bayan baka bani baby ba, k'yakyawa irin ka ,kuma ma ai sai na riga ka mutuwa,nafi so mu mutu tare,ban ma so na riga ka,dan idan na barka mantawa zakayi dani ka auri wata kusha soyaya."

Dariya yayi yace"anya kin barni ma nayi magana da mata ma kuwa?
Wanan kishi,ranar haka kika sa na kori Farida a mota ta."

Ya fada yana tsokanar ta.

Wani nishadi yake jin kansa ji yake kamar ya dawama a cinyar ta,Dan yana jin dadin yanayin.

"To tashi muje muyi shirye shirye Kinga Alhaji yace wata daya za'ayi auren mu,muje musan abin yi ko."
" Har ka warware?"

Ta tambaye sa
lakuce hancin ta yayi yace"ai dama ciwon naki ne, tunda an bani ke ai na warware ko."

Dariya tayi tace"tashi mubar wurin Allah yau nayi rashin kumya fa."

"Share su Mom ai duk cik'in so ne su wa yasan me sukayi tashi muje ,anma sai kin kama ni bana da k'arfi sosai."

Tashi tayi ta kama sa ,suka bar falon cik'e da so da kaunar juna .

Alhaji zaune shida Hajiya a d'aki.

Alhaji yace"a gaskiya yaron mu ya kamu da so sosai fa ,dariya Hajiya tayi tace"hum wa ya fada masa ai ni na jima da sanin son da yake Mata tun fa zuwan sa da yayi,ka manta yanda yazo yana rokon mu kafin auren ta,da yanda ya kwanta rashin lfy,ni ko auren nata na tabata rabo ne ya raba ta da mijin wancan."

"Hum ni ai ban taba tunanin yaron nan zai mana haka ba,anma in halin sa ne zai gani."
. Nan sukayita tataunawa bisa kan auren, daddy ya bada kudi masu yauwa yace"a sayi duk abubuwan da ya kamata.

Koda su Al'Hassan suka isa b'angaren sa suka zauna a falo, A'INDO ta bud'e fruits ta kawo musu suka zauna kasa suka kunna kalo ita ke basa yana sha tana sha, Al'Hassan yace" babyn na 1millions ya ishe ki sabgar biki ko?

"😳 Haba kaima wani irin abu ne haka duk inkai wanan kudin ina haka,gaskiya a'a sunyi yauwa sosai."

"Nidai abinda zan baki kenan idan ma basu isa ba sai a kara, in yayi saura can kisa a account din ki,kina matsayin matata bana son a raina min ke."
. "🙄 to wai kai kudin sun maka yauwa ne?
Idan sun maka yauwa karka ma yara na albazaranci ka bar musu idan sunzo suci dadin su dasu."

"Wai ni sai maganar yara ake min ince dai za'a Haifa min su masu yauwa ko,dan yan biyu biyu Zaki dinga Haifa min,Kinga har na tsufa anma banida dan kaina😔."

"Tab wai ka tsufa a hakan ,ka ganka kuwa wly kamar dan shekara ashirin ,ni baka tsufa ba gaskiya ban yarda ba😙."

Dariya yayi yace"to naji yaushe zamu fara sayaya,ni Paris ma nake so muje ko kuma indiya ko wata kasa daban dai inda zamuyi sayayar mu,anma nasan Mom bazata yarda ba."

*Bayan sati daya*
Cik'in Khalissa kanwar su Al'Hassan ta tashi da bala'in ciwon ciki cik'in dare wanda ya zubar mata da ciki ko kafin idrissa yayi wani abu akai ciki ya zube.....

Su hajiya da A'lhassan A'INDO duk sunje, Khalissa nan tayita neman gafarar iyayen ta ,tare da fadin a Makarantar su ne akayi mata fyade,Nan iyayen suka amshi k'addara suka yafe Mata,aka maido ta gida kamar ba abinda ya faru.

Mijin Halissa ma Ya dawo garin Zinder kullum cik'in zuwa bada hakuri yake,anma anki ma sauraran sa,so ake a tabatar da ya gane kuren sa tukon.

Al'Hassan da A'INDO sun koma tamkar Romio da Juliette,kullum cik'in soyaya suke,har mamakin soyayar su ake.

A yau Mina ta sauka A Niger inda ta sauka a b'angaren Al'Hassan,wanda gaba-daya A'indo ta d'auke wuta jin da tayi wai Matar Alhassan tazo.

Takai ta kawo ko kulla sa ta daina yi,wanda hakan yana bala'in cutar da A'lhassan,yanzu haushin kansa ma yaji ya akayi yasa Mina tazo duk shi yaja gashi Aisha na fushi dashi shikam bai taba tunanin hakan
Take da kishi ba.

Yau suna zaune kowa ya halara,ana farin cikin wanan bikin da za'a hada ,Alhaji ma da Hajiya suna zaune.

Mina ce ta shigo kamar kullum cik'in kayan ta na tsiraici riga da wondo,Alhaji da hajiya
suka kalli juna yayin da A'lhassan ke zaune yana takaicin wanan shiga ta rashin da'a da Mina keyi.

Hajiya ce ta d'aure tace"yauwa Mina zo ki zauna kema."

Zuwa Mina tayi yayyin da Hajiya ta umarci sauran yaran da su bar wurin.

Suka tashi yayi saura daga Alhaji sai Hajiya da A'lhassan sai kuma Mina.

Alhaji yayi gyaran murya yace"ya ta Mina kiyi hakuri ,munsan munyi Miki laifi da bamu fara fada miki ba tun farko,anma kasancewar baki wuri daya damu shi yasa bamu samu damar fada miki ba,Mina kiyi hakuri Mijin ki Alhassan zai maido tsohuwar Matar sa Aisha ,dan haka nake mai baki hakuri,ku zauna da mijin ku lfy,na tabata insha zaiyi Adalci a tsakanin ku."

Hajiya ta k'arbe da cewar"kwarai Mina kiyi hakuri nasan kishiya ba dadi,anma kuma idan kukayi hakuri komai mai hucewa ne.".
.
"to tsohuwar najadu,da tsohon najadu,ni zaku Raina ma Hankali,ku d'auke ni Yar tasha, dan kun Raina min hankali ku kawo karuwa a gida suna iskanci dan ku yanzu wai ku dawo kuce zai maida ita,oho Ashe shi yasa kuka rike sa anan...........

Ayi hakuri da wanan

Comment din ku ya rage,nima zan dinga rage yawan page💃
[17/11 à 20:35] Mai Waina: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Page -77-78*

Bata gama maganar ba ya d'auke ta da mari,ya kara sharara mata wani,babu wanda yayi kokarin hana sa, kwalar sa taci tace"dan iska idan ka cika dan halak ka sake ni,yarfe ta yayi daga jikin sa Jin kake tim ta fadi kasa,nan ya dinga ball da ita,ya kwalo,saida mahaifan sa suka rike sa saboda ransa yayi bala'in bacewa,nan yace",wallahi daddy ku yafe min bazan kuma iya zama da wanan jahilar matar ba,Mina kije ni Al'Hassan na sake ki saki uku."

"Alhamdulillah Allah nagode ma,dama na jima ina jiran wanan ranar,acan ma na barka da ita ne saboda kaga ishara,saboda bijire ma zabin mu,anma yanzu da Allah ya ganar da kai nafi kowa farin cik'in rabuwar da kayi da ita,ke kuma idan Halin ki ne yima manya rashin kumya kije kin hadu da daidai ke."

Hajiya ce ke wanan bayanin Zuciyar ta fess,shi kansa Alhaji abun ya masa dadi ,domin tun can dama yarinyar ko kadan tarbiyar ta da ta ubanta bai mishi ba.

Mina tana kuka.

Ta tashi ta duka ta fara rokon Alhassan domin yanzu take kara Jin wani son sa na kara shigar ta.

"Dan Allah kayi hakuri karka rabu Dani ina son ka,wallahi bazan Kara ba."

"Kinga malama yanzu babu auren ki a kaina ki tatara inaki inaki ki barmin gida."

Haka ta tashi ta fita jiki ba kwarin gwiwa, A'indo da take labe wace da shigowa zatayi taji wanan abun,da gudu ta koma b'angaren ta,wani b'angaren na Zuciyar ta bataji dadin sakin ba,saboda koba komai mace ce Yar uwar ta,anma kuma wani b'angaren taji dadi koba komai abinda A'lhassan yayi ya burge ta,tunda dai batada mutunci har take zagar mata mutanen da take kallo a matsayin iyaye,bayan hakan yanzu zasu zauna hankali kwance suci soyayar su ita da mijin ta ba fargabar zata raba kwana da wata,har rawa tayi ranar,Mina kam Alhaji ya cirar mata ticket na jirgi dan komawa, shirye-shiryen biki sai kankama yake,inda Hajiya ke gyara A'INDO da ingantatun maganunnuka na mata masu inganci da kyau ,tare da d'auko mai gyaran jiki,inda take Kara koya ma A'indo kisoshin kala kala na zama da miji ,da kuma yanda zata saye zuciyar sa,da koya mata kalolin kwanciya,yayin da ta kara amsar number wayar ta tasa ta a group group nata wanda take wayar ma da mata kai yanda zasu kula da mazajen su,tana koya mata tsarin iya kwanciya,da inda zata kulla da jikin ta ta sanya turaruka
Lungu da sako da kuma kalolin turarukan da ya kamata tayi amfani dasu.

Yau ma kamar kullum A'INDO na zaune bayan an gama mata wankan turaruka,da kuma abubuwan da take sha, na Karin ni'ima da ciciko gaba da dadi.
Tana zaune da book dinta wanda take d'aukan note na abubuwan da zata dinga gyara jiki dasu,,
Ladi Mai gyaran jiki tace"Aisha maganin mata ga mace yanada matukar mahinmanci a jikin mace ,rayuwa ce yanzu ta lalace zakiga mata sun haukace shan maganunnuka wa'inda basuda inganci bare kuma kyau,to shan maganin mata ba laifi bane,anma shi ba'a maida shansa ya zama kullum.
Chapter 38 · 0% Book details