Sashe 6
Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhassan ne ya fara saukowa daga saman bene,yana rike da bindigar sa karama yana gyarawa,tare da saitawa kusan daidai inda su A'indo suke zaune,kamar ance A'indo ta juya aiko taci karo da bindigar, Alhassan sam bai ma lura da su ba,to dama A'indo tana ganin bindiga a tv kuma tasan kashewa take,hakan yasa cik'in ta ya duri ruwa,ta zaro ido,tare da taba Rabi'u daudu,dan ta nuna Masa,ya murguda baki yace"ke dan Allah ki barni nayi kalo na,kin wani zo sai tabani kike😏ya fada da maganar mata.
Carab Alhassan ya dago ya gansu,ransa abace,a ransa yake cewa kenan wanan dan iskan bai bar maganar mata ba ,bai bar daudancin ba,aiko kara ganin A'indo a gun ransa ya Kara tunzura,kara gyara bindigar sa yayi saitin su,A'indo ji tayi cikin ta yayi wani irin kulewa tsabar tsoro,aiko sai ji kake tayi bum ta saki wata irin tusa,"um um wanan ai ko a lahira aka maka hukunci da ita,ka hukuntu, Rabi'u yace tare da juyowa dan ya kalli A'indo aiko ganin wanda baiyi zato ba ya gani wato Alhassan,tuni A'indo tace kafa me naci ban baki ba,gudu take tsakar gida, Rabi'u ma kafin Alhassan ya karaso garesa shima ya takarkare ya arta a guje shida A'indo kai kace gasar tsere suke,kowa a gidan kalon su yake ,basu tsaya a ko ina ba,sai a can k'arshen layin gidan nan suka dakata suna haki.
"Yau ni naga tsiya yar nan ,yau so kikayi wancan mugun ya kashe ni,ai sai kice Rabi'a yi ta kanki,ba sai mu tsira tare ba anma kya gudo ki barni da wanan mugun ya kashe ni."
A'indo tace "tab aradu mugu ne,wanan sai an masa shiri nidai aradu yau saide na kwana anan bazan koma gidan can ba wacan mugun ya kahe ni."
Rabi'u yace "Kanki ake ji bara ki gani,zanin dake d'aure garesa ya kunce ya shimfida,dan dama da riga da wondon sa a jiki,sai ya d'aura zani a sama, yana shimfidawa ya kwanta.
Murguda baki A'indo tayi ,itama ta kunce zanin ta na sama ta shimfida,dan ita dama zane biyu take d'aurawa kamar mahaukaciya.......
Kwantawa tayi bayan ta shimfida. nan barci ya kwashe su ko a jikin su.
Alhassan shi ga yanda suka kwasa a guje abun yayi matukar basa dariya da takaici baibi ta kansu ba,yayi abinda zaiyi ya koma b'angaren sa....
Da misalin k'arfe biyu na dare A'indo da Rabi'u suna barcin su hankali kwance,wata mahaukaciya ce zabgegiya ga tsawo ga jiki,ta kufce daga gidan mahaukata,shine tayo layin,tazo har inda su Rabi'u daudu ke k'wance,ta fara kwaso kasa tana zuba musu,Saida ta musu busu busu,suka tashi, Rabi'u yace "na Shiga uku an fasa aurena mai zan gani wanan abu , mahaukaciya,dariya mahaukaciyar tayi tana Kara nufo su,A'indo ma tashi tayi tana furzar da kasar da ta shiga bakin,taga mahaukaciyar,A'indo ta zaro Idanu waje tace"to bakuwa mukayi, Rabi'u ya tashi a tsorace yace" inafa bakuwa yi ta kanki wanan girbin jiya ce mahaukaciya ce,bari yanzu na dawo nayi maganin ta,tsab ya zame,aiko yana zamewa yace"k'afa me naci ban baki ba ya arta a guje,sai cikin gidan,duk masu gadin sunyi barci,sai mai gadi,yana tambayar lfy ina Rabi'u cewa yake bani wuri bani wuri,da gudu yayi cik'in gidan kitshen ya shiga,ya d'auko muciya,ya kara fitowa da gudu irin na mata,ya fito sai ga A'indo itama ta fito daga gurin da gudu mahaukaciya ma ta biyo ta da gudu,haba ganin haka sai ga Rabi'u ya saki muciya ya yar da ita,shima yace k'afa me naci ban baki ba,wajen shiga gida har buge juna suke ,suka samu suka shiga,kowa a guje yayi b'angaren sa, security na kalon su kawai su sun d'auke su a mahaukatan gidan......
Tun a ranar Latifa ta fara barci da wuka a kasan filon ta,domin kuwa a cewar ta Kar Alhassan ya mamaye ta ,bayan kwana biyu yau ma kwance take ,barci yayi nisa,ta daga k'afa sama ta jingina da bango,tana barci,can dare sai taji kamar ana ja mata k'afa,ta aza Alhassan ne ya biyota,ya duke ta,dan haka cik'in barci ta zaro wukar,ta daga saura kadan ta datsa a k'afar ta Saida taga ta motsa kuma k'afar ta motsa tukon ta tsaya tare da waro idanu tace "tab aradun Allah ni bahuwa ce da yanzu na kahe kaina 🙄."
Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:28] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/
*Page 13-14*
*DEDICATED TO SADJIDA &UMMY ONTOP*
,,,,,,,,,,,,,,,,,Kalon k'afarta tayi dak'yau tace"tab sai ni A'INDO,mtsss nifa yunwa nake ji tashi tayi taci sauran abincin ta ta koma ta kwanta.....
Washe gari Alhassan ne tare da Mahaifin sa,zaune ya dube sa dak'yau yace"Alhassan"
Tunda Alhassan yaji Mahaifin sa ya kira sunan sa haka yasan maganar mai mahinmanci ce,saide ga yanda yaga Mahaifin sa ya hade fuska yasan maganar ba Wasa a ciki."
"Alhassan na jira dogon lokaci na baka dama har sau ba adadi, na tabata wanan dalilin yasa ka daina zuwa gidan nan,sai ka hada shekaru bakazo ba,zan iya baka dama ta k'arshe a yanzu da ka kawo min wada kake so na aura ma,idan kuma baka kawo ba duk wace na aura ma dole ka zauna da ita,kaje na baka sati daya,wly idan baka kawo ba zan hada ka da koma wacece.
Tashi kaje."
Tab duk yanda Alhassan yaso ya shawo kan Mahaifin sa abun yaci tura,dole ya hakura ya tashi,falo ya tarar da Hajiya zaune,zuwa yayi ya zauna kusa da ita tare da aje kansa saman kafadar ta,tunda taji danta yayi haka tasan cewar danta yana cik'in damuwa,domin baya mata haka sai yana cikin damuwa,shafa kansa tayi tace"yadai son lfy ?
"Uhum Unmma plz ki fadama Daddy yayi hakuri,ya kara bani wani lokaci,kinga yanzu ni banida wata budurwar da Zan kawo dan ta zama matata ,ya bani koda shekara daya ce kafin lokacin sai na samo."
Murmushi Hajiya tayi tace"in muna rai ko ?
Ko kai kana Raye.
Son abinda nake so ka gane shine wanan zamanin na yanzu rayuwa batada tsayi ,kuma ko wace rai da buri take mutuwa,duba kaga shekarun ka,anma ace har ila yau bakayi aure ba,saboda Allah idan ba yanzu ba yaushe zakayi,kuma ma ba haka ba mu sai mu zauna mu zuba maka idanu ba aure,kai kasan Al'adan gidan su Mahaifin ku,indai bisa kan wanan kake damuwa gwara ma kabar damuwar kanka,dan wanan karon wly kaji na rantse Ina bayan Mahaifin ka."
A'INDO ce ta shigo taji wanan maganar tace"tab,anma anyi giman banza,muna ganin idi duk girman sa bahida aure ashe ga uban sa nan,idi dai wani katon yaro ne a kauyen su A'INDO shekarun sa ashrin da biyar a duniya ,baiyi aure ba,dan su kansu a kauye namiji bakin shekaru ashirin ake musu aure shi kadai ne yakai ashirin da biyar."
Shine A'INDO ta rike haba,tazo ta zauna kusa da Hajiya,tace"tab anma kaide kam ka zama tuzuru."
Al'Hassan jin yayi wata irin tsanar Yarinyar
na kara shiga ransa, yarinya sai kace mahaukaciya ,tashi yayi a hasale zai mareta Unmma ta dakatar dashi,wani kalo ya watsa ma A'INDO yace "zamu hadu ne."
Sanan yakai duban sa ga Unmma sa yace"haba Unmma me yasa kike ba kowane dan iska damar raina ni,wanan kazamar Yar aikin kinaji take fada min magana,waye ubanta a garin ."
"ai gwara ta fada ma ,sai kayi zuciya kayi auren."
Unmma tace. A'INDO ko kuri kuri tayi itadai fatan ta Kar ya doke ta."
.
Ficewa yayi daga falon ya barsu.
*Bayan sati daya* Alhaji ya kara tuntubar Alhassan da zancan anma sai ya fara kame kame.
Dakatar dashi Daddy yayi da yaga Alamun dai bai fida Matar ba yace tashi jeka."
A tunanin Alhassan daddyn sa ya hakura ne, baisan abun ba haka yake ba.
Daddy Hajiya ya kira yace ta kira masa Anty A'INDO,Aiko Unmma ta Kira ta,tace tazo.anyi sa'a tana garin dan gobe take shirin zuwa kauye,anma gaban ta faduwa yayi da Kiran da tasan wata kila can ma A'INDO tayi ta'asa,ita bazata iya ba tatara A'INDO zatayi ta maida ta kauye.
Ba'a dau lokaci ba sai ga Antyn A'indo bayan tazo ne a falo ta zauna ,Hajiya taje fada ma Alhaji,minti biyar ko sai ga Alhaji da Hajiya sun dawo tare.
Zama Alhaji yayi Anty ta gaida sa ,nan suka gaisa."
Alhaji yace "ba komai yasa na kira ki ba,ila inason kula alaka baba da ku ne,yar wajen ku wada take aiki a gidan nan ita nake so ki kaini wajen iyayen ta,dan nema ma da na auren ta ."
Wata zufa ce ta karyo ma Anty a fuska,tace"anma Alhaji ka ko san ko wacece A'INDO da kake so hada danka da ita, yarinyar da batada nutsuwa ko kadan,kuma Yar kauye,ina Alhaji da dai anbar wanan maganar."
Murmushi Alhaji yayi irin na manya ,yace "ni masani ne,sanan kafin na yanke wanan hukuncin Saida na nemi zabin Allah,karki ga haka kawai daga sama ba wata halaka ta jini ko abotaka haka kawai zan aura ma da na ita ba a'a,inason yin haka ne da karya mumunar akida da yaro na yakeda ita,kuma wanan abu na jima ina istahara naga kuma Alherie ne,dan haka in ba damuwa gobe zaki kaimu kauyen mahaifan nata."
"a to Alhaji ba komai , ALLAH nuna mana,ai mu zamu nuna farin cikin mu muda baka nuna mana kyama ba,ba komai,Nan ya d'auki dubu biyar ya bata dak'yar ta karba.
Tashi Alhaji yayi yabar falon Hajiya ma tabi bayan sa.
Sai ga A'INDO zata shigo falon suka hadu da Antyn ta zata fita,ai kuwa A'indo na ganin ta tayi wata dire a kanta ta mak'alk'aleta,tace"Wayyo dadi anty tazo."
Wata dariya Anty tayi tace "ke ki nutsu muje d'akin da kike."
To A'indo tace taja hannun Antyn tata sukayi d'akin ta.
Bayan sun zauna A'INDO zata fara shirmen nata Anty ta dakatar da ita,tace"A'indo kina son auren namiji irin yaron gidan Nan,akaiki gida Kato har kasar waje inda zaki huta."
Bangalewa da dariya A'indo tayi tace"kaji wani irin shirme irin na Anty kuma,yau ni wane baho ne zai auri marar hankali Irina😁."
Ke ni fa bana son iskanci irin naki ki nutsu ki saurareni ."
Guri guda A'indo ta hade,tare da Rungume hanuwan ta biyu duka a kirji,sanan ta ci uwar fuska,tace"na nutsu.