← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 45

Sashe 25

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wani shirye-shirye yana gabata yanda ya kamata,inda khalissa tazo itama autar su Alhassan,suna bala'in sonta,komai take so yi mata suke basa takura ta,da kwana biyu,khalipha yazo shima mai bima idrisa,sai halissa itama a tatare sukazo mai bima khalipha ,wato wada take aure a Niamey,kai gaba-daya family an hadu,kuma dukan su akoi su da son jama'a,ga wani'irin so da suke ma su A'INDO tamkar jinin su ,dan dama koda su A'indo sukayi waya,suka saba da khalipha,Halissa,da khalissa,abun burgewa dukan su, sun d'auki su A'indo tamkar jinin su,hakan yasa da sukazo gida ya d'au hayaniya,domin Suma yan sharholiya ne,akoi su da son sho,Halissa da khalissa kusan kullum suna tare da yan matan amarya wato su A'indo.

Yau kwana biyar kenan da zuwan Alhassan anma abun nasa sai a hankali,dan kuwa kullum cik'in bin A'indo cik'in Siri yake,wani yanayi yake jin kansa wanda ya kasa gane masa, kamar kullum yau ma wajen k'arfe goma na safe suna zaune duka a falo harda Hajiya,da khalipha, Halissa,da khalissa da Idrissa sai Alhassan dake zaune yana duba computer baya ko jin hirar su, Hajiya tashi tayi ta tafi saman ta dan shirye-shiryen su dan bazata iya biye ma shirmen su ba.

A'indo ce ta shigo cik'in siririyar salamar ta, dukan su suka juyo harda uban gayar wato Alhassan,da ya ture cumputer gefe ya zuba ma k'ofar idanu,jin wace yake ishirwar ganin ta shigo,sanye take da dinkin doguwar rigar na bakin less,daga sama matse anyi mai gidan nono,matse yake har wajen bra sai aka sake sa daga sama har kasa ya bud'e ,dinkin yayi bala'in yi mata kyau,ya mata das ,ta dan yafa wani dan shara-sharan gyale,fuskar ta tayi simple make up,sanye take da dogayen takalma masu tsini,bakin ta yasha lips sai walkiya yake,da yar karamar jakar ta,sai ni'imatacen kamshin ta ke tashi a duk inda ta huce sai tabar sanyayan kamshin."

Khalipha yace"hum my sis tun kar ki shigo nasan kece,domin ke dama turaren ki ke fara ma mutum salama kafin ke.

Dariya A'indo tayi,duk da taga Alhassan ta dake tayi kamar batasan yana gun ba,yayyin da shi kuma Alhassan yaji gaban sa ya fadi lokacin da yaji kanin sa yayi wanan maganar.

Wata muguwar harara ya banka ma khalipha,anma ina khalipha ko ganin sa baiyi ba.

Kallon A'indo yake a kaikaice,ina kuma zata tayi wanan Shirin mtsss,salon ayita kalle ta,shi kadai yake wanan maganar a zuciyar sa ,idan ka gansa zaka rantse cewar aikin sa lake bisa laptop,anma ina ba wani aikin da yake sai ma rubutun sakin layi yake yana bata aikin da yayi yana rubuta shirme duk a rashin sani.

Wani kallo A'indo tayi ma khalissa na marairaicewa tace" da khalissa Bashir fa na jiran mu tun dazu ashe ke zaune ma kike baki shirya ba."🙄

"Bashir Alhassan ya ambata a zuciyar sa,tuni Zuciyar sa ta fara kai kawo."

Da sauri khalissa ta tashi tace"just five minutes my sis wallahi na sha'afa ne."
Halissa tace"to nima ku tafi dani man."

Waro idanu A'indo tayi tace"ki rufa mana asiri kina matar aure Zaki bimu,kekam ai saide a kunkume a cik'in gida,😂
Kinga zamuyi reunion ne da samarin ango,kaima surikina baka shirya ba,anma ba matsala ko kaje ko baka je ba ai duk daya ne,tunda abokan kazasuyi abinda muke so dan haka ka ma yi zaman ka."

Dariya idrissa yayi yace"au abin hakane,ba'ama so dama naje,to bara naje wurin amarya ta Nima,ya tashi ,yabar gurin, khalipha ne yace"tab abin yar wariya ce ,hum ya kalli halissa yace"sis taso muje yawo harda shopping kyale wa'inan."
"Yauwa bro muje kawai."suka tafa A'indo tace "to aso diyawa."

"Anki "
. Sukace da ita tare da yi mata gwalo suka fita suma.

Alhassan kam tunda yaji tace da halissa abun na Yan mata da samarin ango ne yaji Zuciyar sa na tafarfasa,wato itama yan matace kenan.😡kuma uban waye Bashir dinnan?

Ganin duk sun watse sai ita dashi yasa ta tashi zata fita ,yace"da ita kema kenan yan Mata ce,ai inaga dake da halissa matsayin ku guda,Dan me ke zakije cik'in kata wai da sunan reunion."😡

Ya fada kansa na hayaki,Idanun sa har sun canza coulor tsabar masifa.

Mamaki ne ya kama A'INDO,zatayi magana kuma ta fasa dan ba amfanin masa magana,ganin ta kama hanya ta fice yaji wani irin bala'in zafi da Zuciyar sa ta masa, ta ya ma za'ayi ta tafi yana mata magana,a haka take son zuwa cik'in wasu kata,tashi yayi da zafin nama ya fito waje da gudu ,ganin ta yayi zatayi part dinsu,da gudu yazo ya sabe ta,bayan ya rufe Mata baki, yayi saurin yin b'angaren sa da ita.

A'INDO na wule-wule tana ihu,bai dire ta ko ina ba sai d'akin sa ,ya rufe,wata irin faduwar gaba A'indo taji,ranta yayi mugu-mugun bacewa,Idanun ta har sun canza,tsabar masifa da bala'in dake cinta, gaba-daya taji ta kara tsanar sa,tsanar da ko makiyin ta bata fatan tayi masa irin ta.

Alhassan yace"bakida hankali ne Ina miki magana zaki wani share ni dan ki raina min hankali,dan iskanci a haka zaki fita,kuma wai wajen samarin ango uban wa kika tambaya,ke ko kumya bakiji ba zaki fita a haka har kina ikirarin kanki a Yan mata,a haka kike son fita maza suyita kalle ki."

Takaici bakin ciki suka yima A'indo tsaye a zuciya,wuka ta hango a bisa tire mai d'auke da lemo,d'auka tayi rai a bace tace"wallahi Allah idan baka bani hanya na huce ba zan caka maka wanan wukar,an fada ma A'indo ta da ce da ko wane sakarai zai nemi wulakanta ta ,to bara kaji idan acan farko kayi kaci bulus wallahi yanzu bazan barka ba,da kake cewa meye ni Yan mata ce,kwarai kuwa ni yan mata ce tunda har yanzu ina tamaka da abinda yan matan ke tamaka,dashi,har ake kiran su da budurwa,banida igiya,ko nauhin wani a kaina,dan haka dole nayi rayuwa ta yanda nake so,sanan Wanda zan aura ma baiyi min wanan takurar ba sai Kai! kai a su wa.?

"Wallahi ka bani waje idan ba haka ba zan caka maka wanan wukar ."

Ke har kike tambaya ta ni a su wa,dan kin raina min hankali ina matsayin mijinki kike kiran wani zai aure ki."😡 gaba-daya cik'in tunzura da bacin rai yake wanan maganar.

"Miji miji,tuf ta tofar da yawu ,tace "Allah ya kiyaye,ai wallahi da ace har yanzu ina matsayin matarka tabas da ko saide na kashe kaina,dan da in zauna dakai gwara zama da bakin kumurci ina umartar ka da ka bani wuri na huce,dan wallahi idan ka nace zan caka maka wanan wukar.",ko gezo baiyi ba,ya tsaya cak gurin kamar an dasa sa,ji yake ga daya duniya bai tabajin ciwon abu ba, da zafin abu kamar yanda tayi masa wanan maganar wai gwara ta zauna da bakin kumurci da zama dashi,aiko yau zaiga k'arshen kiyayar da take masa,dan bazai gusa a gun ba sai ya tsaya yaga zata caka ko kuwa,a matukar haukace A'indo tayi saiti da wukar ,dan ta d'aukan ma kanta matsawar bai gusa ba wallahi sai ta caka masa ita.......

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[22/10 à 21:02] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Assalamu Aleykum,zanyi kira ga wasu marubuta,wa'inda kuma yawanci sababin marubuta ne ke irin hakan,a gaskiya bana jin dadin abinda kuke yi min,ace kaf online kunfi d'aukar min sunan book, duk idan zan rubuta sunan book to sai na zauna nayi nazari nayi bincik'e naga idan ba'a taba irin sunan ba sai na rubuta,ban taba d'aukar sunan book din wata marubuciya ba ko daya ba a Online na rubuta,wallahi duk sunan book din da zan sa babu taimakon kowa ni ke aje hankali na kirkiro sunan book dina,anma abun mamaki shine da farko an d'aukan min sunan book dina Mai sunan *(MAKIRCIN, )anyi sa.nayi shiru banyi magana ba,aka kuma d'aukan sunan book dina (YAN MATAN ZAMANI,)shima nayi shiru,aka kuma d'aukan (HASSADA GA MAI RABO),shi nayi ma marubuciyar magana kuma ta fahimce ni,an d'auki Ina (MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN),shima nayi shiru,kwanan nan daga fara tala book zan fito dashi wata ta gani ,a lokacin ta fara rubuta sa,nayi hakuri,kwatsam yau kuma sai naga an kuma d'aukan saunan book dina mai taken (KAICONA),shi nayi magana anma tace bazata iya canzawa ba,to a gaskiya a wanan karon bazan iya hakuri ba,ya kamata ace wasu marubutan su dinga tunani da lissafi kafin su fara abu, bai kamata ba ace ana rubuta sunayen book sama da uku ba,kuma duka sunaye iri daya,hakan zai sa mu ruda kan Makaranta,ina mai bada shawara ga masu irin wanan abu,idan zaku rubuta litafi kuyi bincik'e da kyau ku tabatar ba mai irin sunan litafin sai kuci gaba,anma ba wai ku d'auki sunan litafin wani ba,gaskiya hakan baiyi ba, idan akaci gaba da haka kunga zan d'auki sunan book din wada ta d'auki nawa Nima na rubuta book din da irin sunan book din da takeyi akafi sanin ta dashi na kunga hakan ba dadi ,dan haka dan Allah mu gyara tun kafin mukai ga haka.*🙏

*PAGE 51-52*

Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo,alhakikanin gaskiya wani irin tararin bala'in sonta yakeji ,wanda shi kansa abin tsoro ya fara basa,bai taba son wata mace ba haka,sanan baisan lokacin da son ya shige sa ba,tafin hannun sa yasa zai janyo ta ,itako idanu a rufe ta yarfar da hanunsa,a inda tsotsayi yaja ta yanka tafin hannun nasa,take jini ya fara zuba, bud'e idanu tayi jin yayi yar karamar kara,jini taga yana zuba a hanun sa,duk da bataji dadiba a k'asan zuciyar ta,saboda har ga Allah bataji dadin abinda tayi ba,saboda ita ba irin sa bace,d'aurewa tayi ta dake,tare da cin fuska ,tace"Wallahi kadan ka gani ma ,idan ka kara gangancin koda taba hannuna ne to wallahi abinda zan maka sai ka kwanmace baka doron duniyar nan."
Chapter 25 · 0% Book details