← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 45

Sashe 32

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana Gama fadar hakan yabar wurin ,durkushewa tayi tana kuka a gun,saida taci kukan ta mai isar ta sanan ta tashi ta koma d'akin ta ,wayar ta ta d'auka ta fido number hajiya ta fara kokarin kira,wayar na ringing anma ba'a daga ba,kira yakai goma tanayi,daga k'arshe sai hakura tayi ta nemi layin Husseina shima a kashe,ta nemi na idrissa,anan ta same sa,tana kuka ya daga ,"idrrisa ina su hajiya, idrissa a b'angaren sa yace"Aisha basa kasar jiya suka daga kinsan bro yayi accident,to shine nace su barsa a nan asibiti na za'a duba sa shine Mom tace a'a ya Bari su tafi dashi waje."

Share hawaye A'indo tayi tace "Allah ya basa lfy,ya ita kuma khalissa fa?

"Tana nan ita a asibiti na ba lfy,Husseina na kulla da ita da Sauki yanzu."

"Ok to Allah bada Lfy zanje insha Allah."

"Allah ya yarda ."

Cewar Idrissa,kashe wayar tayi hawaye na zubo mata na tausayin hajiya,.
"Na yafe maka Alhassan idan har Alhaki na ne ke taba ka da kaida hajiya ta na yafe maka duniya da Lahira."

Bashir ne tsaye k'ofar d'akin tun lokacin da ta fara wayar yake tsaye yana sauraran ta rai bace ba kamar da yaji ta ambaci Alhassan."

Murmushi yayi wanda baikai ciki ba yace"hum ashe kwarton ki kike son gani shi yasa Kika matsa kina son tafiya,munafuka kawai,mtsss amshi nan yace da ita juyowa tayi ,abinda ta gani a hannun sa shi ya bata mamaki,juyar dakai tayi tare da yin tsaki.

Yace"ba ke nake ma magana ba kika min tsaki ki karba kisha inada bukatar ki".

"Yau ai banga abinda zan karba bane,kaga malam wallahi bazan kara shan wanan kwayar ba,yau Allah na tuba na safurce duk da ba dadin abunan nake ji ba ai wallahi nasan ba haka maza suke ba,jarumi kuma gwarzo a gidan sa shine wanda za'ayi ma biyaya ayi duk abinda yake so ,anma ba wai muna maza ba yan rakiya."

Ransa ne ya tunzura fita yayi sai gashi da katuwar wayar TV dagawa yayi tare da zaro idanu zai lafta mata ita tayi saurin tashi tace"kut wallahi karka saki ka kara tunanin fara dukana domin ni ba jakar gidan ku bace."

"Au haka kikace,to bari na nuna miki cewar jaka ce ke din. Janyota yayi da k'arfi,kunsan cewar k'arfin namiji da mace ba daya ba dan haka yafi k'arfin ta,duk yanda taso tarewa abin yaci tura,nan ya daga bulalar ya fara lafta mata a jiki,tana kuka tana neman agaji,anma Ina ko jinta bayayi duk inda ya samu bugawa yake , saida yayi mata liss tukon ya barta ,ya kuma dagota ruwa ya debo a cub ya ririke hanuwan ta ya take da k'afa,sanan ya bud'e bakin ta ta k'arfi ya danne mata hanci yanda bazata iya shedawa ba sai ta baki,aiko yayi saurin jefa mata maganin tare da kwarara mata ruwa ,ba shiri ta shanye,nan ya sungume ta sai bisa gado,baiyi wata-wata ba da kokowa ya kekece kayan jikin ta ,saida ya rabata tasss dasu sanan ya kware mata cinya,ya bud'e zif din wondon sa,nan ta k'arfi ya shige ta ya fara sukuwa a kanta ko minti biyu baiyi ba ya kawo,ya kwanta gefe yana fida numfashi, yayyin da ita kuma take kwance kamar gawa tana kukan bakin ciki.

*Bayan sati daya*

Ta tuntunbe sa da maganar komawar ta school ya rufe ido yace baisan da wanan ba,salon taje tayita haduwa da samari ,ba yanda batayi ba tana rokon sa anma yaki yace wallahi bazatayi karatu ba,haka ta hakura badan taso ba.

*Bayan wata daya*

Haka rayuwa taci gaba da zuwar ma A'indo cik'in kunci,Sam Bashir baya mata da kyau,yayyin da har lokacin ya Hanata zuwa gidan Hajiya taga su Khalissa saide suyi waya,a inda su hajiya har a wanan lokacin suna kasar waje,har lokacin Alhassan za'a iya cewa dai jikin da dan sauki,har bisa yau Mina bata kira ba taji ya jikin sa,sau daya tayi kira shima zata tambaye sa kudi ne Hajiya tace mata suna asibitin Paris anma ko ta leko ganin sa,bata ma yi kokarin kara Kira ba,wanan abu ya kara kullar da Hajiya,suna waya da A'indo,kuma tana jin dadin kulawar ta garesu,saide tana lura da cewar kamar A'indo na cik'in matsala,tasha tambayar A'indo saide tace mata ba komai a haka suke rabuwa.

Zaune take a fallo,duk tayi baki ta rame,shigowa yayi ba ko salama,yayi mata wani irin kallo sama da kasa ya buga tsaki tare da fadin Ina abinci na"?

Kallon sa tayi tace"kayi hakuri ban samu damar girkawa ba,saboda bana jin dadin jiki na,Wallahi aikin gidan ma da kyar nayi,dama jiran ka nake kazo ka kaini asibiti."

"What bakiyi me ba?
baki girka abinci ba,saboda kin tsari wani sabon iskanci,dan haka ki tashi kije ki dafa min abinci ,inada mata bazan zauna ba naci wani abinci a waje ba,dan haka ki tashi ki girka min."

ba yanda ta iya duk da jirin da take ji yana diban ta haka ta tashi zata tafi kitchen dan dafa abincin,anma sai me kafin ta karasa ji kake tim ta fadi a gurin sume,da sauri ya taso ganin ta haka ya d'auke ta ya nufi mota da ita,sai asibiti ,bayan sunje aka k'arbeta,taimakon gagawa aka bata,inda aka debi jinin ta,akayi gwaje gwaje,bayan awa daya doctor ya fito,ya umarci Bashir da ke danna waya kamar ba shi ya kawo matar sa asibiti ba,hankali a kwance doctor yace yazo ya same sa a office,tafiya yayi doctor yace ya zauna,nan ya basa result da gwajin da akayi ya miko ma Bashir hannu yace"congratulation daga yau nauhi ya kara hawa kanka,domin Matar ka na d'auke da cik'in wata biyu."

Wata irin zabura Bashir yayi ya tashi tsaye a matukar razane,tunawa da yayi a asibiti yake yasa ya daidaita kansa,duk da Zuciyar sa na masa zafi.

Murmushin yake yayi,yace da Doctor "zan iya tafiya da ita."

"Eh zaka iya tafiya da ita anma a bita a sannu,ta daina yawan aiki a barta ta huta kwana biyu,sanan a dinga bata abincin da zai Kara mata jini da lafiya,kamar su anta koi,da fruits......

Bai tsaya ida sauraran abinda doctor ke fada masa ba yayima doctor salama ya tafi,jan A'INDO yayi sai mota ya jefa ta,sanan ya shiga yayi ma motar wuta yabar asibitin,idan kaga yanda yayi kicin-kicin sai abun ya baka tsoro, a haka suka isa gida,yana rufe mota,ya jawo hannun ta kiiiiiii sai falon su,nan ya jefar da ita,Rai a bace ya d'auko wayar radio yace"dan ubanki ki fada min wanan cik'in na uban waye ,domin kuwa wanan cik'in ba nawa bane,duk in zanyi sex dake sai na baki magani,kenan ban sani ba cin Amana ta ,to bara kiji matsawar baki fada min kwarton nan naki wallahi sai nayi ajalin ki ,ganin bazatayi magana ba ta zuba masa idanu cik'e da bakin ciki yasa ya daga wayar ya fara zabga mata,kuka ta fara tana rokon sa yayi hakuri dan batada wani k'arfin kwatar kanta,anma ina ya ki hakura sai ma kamar kara tunzura sa take haka ya mata likiss sanan ya ja ta kiiiii zuwa wani d'akin ya jefata ya fito ya rufe d'akin da key ta waje yace"wallahi idan baki fadamin dan iskan da ya miki ciki ba bazaki fito daga wanan d'akin ba,saide ki mutu......

Oh!!!!!!!!!!🤦‍♀
[31/10 à 21:05] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Page 65-66*

Ihu take tana ya bud'e mata anma ina ko sauraran ta baya yi,ficewar sa yayi daga gidan ya nufi wajen Salman........

Salman na zaune a office dinsa Bashir ya Shigo rai a bace ya zauna .

"kaiko lfy kake?
Ka shigo ba ko salama."

"Ruwa Bashir ya d'auko a firge yasha ,sanan ya furzar da iskar bakin sa,yace"wai yar rainin hankalin yarinyar nan ni zata yaudara,taje can wani kato yayi mata ciki wai tazo tace ni na mata ciki ta ya ma za'ace ciki nawa ne bayan ina bata maganin hana d'aukar ciki kullum idan zan sadu da ita."

Salman yace"ban gane ba,dama Matar ka ba a budurwa ka same ta ba?

"A budurwa na same ta mana."

"To cik'in wata nawa ne da ita" ?
Salman ya jefo masa tambaya .

"Doctor yace cik'in wata biyu ne,kuma auren mu wata biyu ne da kwana uku a yanzu."

Salman yace "tun yaushe ka fara bata magani kafin ka sadu da ita."?

" Bayan kwana uku da auren mu."Bashir ya basa amsa kuma nan take ya tsaya cak da zancan sa yace" kenan a cik'in kwana ukun nan ta d'auki ciki na,tab wallahi bazata sabu ba,kodai ta zubar da cikin nan ko mu rabu,ni bazan iya zama da ita ba har na haihu da ita ba,kai wallahi a ma fida mahaifar gaba-daya yafi,zan bata duk wani kwanciyar hankali,da duk wani gata da take so ."

Salman zaiyi magana Bashir ya tashi ya bar Office din ya shiga motar sa yajata da gudu yabar wurin,gidan sa ya nufa,ya nufi d'akin da ya kulle ta dazu ya bud'e,kwance ya same ta ,kallon ta yayi ta dan basa tausayi yanzu yace"ki fito zamuyi magana ne."

Batada k'arfin jiki anma haka ta tashi ta fito,nesa da inda yake zaune kadan ta zauna,kallonta yayi da kyau,sanan yace"Aisha idan kina son farin ciki a gidan nan da kwanciyar hankali mu koma tamkar lokacin muna saurayi da budurwa,ki yarda mu zubda cik'in nan."

Share hawaye A'indo tayi tace"indai zan samu farin ciki daga wajen ka na yarda a zubda,in har ka yarda yanzu naka ne."

Murmushi yayi yace"haba ko ke fa masoyiyar ,ai haka ake so anma da kin tsaya taurin kai, yanzu shirya kici abinci
Akoi inda zamu inda za'a zubda."

Murmushi tayi tace"Bashir dagaske zaka koma kamar da idan aka zubar."

Murmushi yayi yace"fiye da da ma."
Chapter 32 · 0% Book details