← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 45

Sashe 4

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hahhh Hajiya ai dan tare ne na fara ,gobe ma zan tafi na sayi dusa in kika Kara bani wani ragowar canji ko ta naira ashrin ce."
"To naji me zakiyi dasu ?
Cewar Hajiya da ta fara tsoron Al'amarin A'indo.
"ai Hajiya kiwo zan fara Nan da shekara nake so na sayi Rago guda daya ya fara haihuwa,shine nake so na tanadi dusa da igiyar."
"😳 Waro idanu hajiya tayi tace"wai ni kam A'indo bakida hankali ne ?
"A to wa ya sani Hajiya sai an Kira mai gyaran mutane ya duba ni dan nima banida tabaci😁"

"Uhum naji Allah ya kyauta bani katin wayar ni."

ai kuwa Naso miki mai kyau Hajiya bara ki gani,nan ta zaro kwalin waya ta bata,.

Amsa hajiya tayi ta duba tace me zan gani niko Hajiya,duba kwalin tayi bayada komai kwongo ne,Hajiya ta zaro Ido tace A'indo meye wanan shine katin wayar A'indo.?
Hahhhhh kaji Hajiya da wani shirme kuma to meye in ba shi ba🙄................

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love
[10/10 à 17:27] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/

*Page *7_8*

*________* Saurin tufe hanci hajiya tayi tace "um um ke wai A'indo meye hakan ,kina min tusa a falo duk kin ruba min falo."

Yi hakuri Hajiya kinsan ita tusa in zatazo bata wani burki kawai saide kajita ta manya irinku Hajiya saide kajita buuuut bururut burut ,ta yara sai kajita piiiit pit pit ,ta daidai mu kuma saide kaji muna bum bum,ai bata karasa ba wata tusar tazo,Hajiya tace"Dan Allah karki saketa,sai ji kayi ta bada buttttutu ,tana matse fuska tace"haba Hajiya in banda abinki kin taba Jin inda aka matse tusa,ai ko na danne ta bata dannuwa ,dan Allah Hajiya ki taimaka min da ko langa ce na juye wanan bala'i na ciki na😖."

"Kinga dan Allah fitar min a falo idan bazaki je kiyi can ba,ki shafa min lfy."
Rabi'u Rabi'u zo dan Allah sa min turare falon nan duk tabi ta bata min falo.

Da gudu A'INDO ta fita,tabar gidan Saida tayi tafiya sosai sanan taga wani dan daji anan ta duka ta zaka kashin ta,har zufa take ,tana gamawa ta katse,ta tashi ta maida wondon ta,da zanin ta,sai hada uwar zufa take tace"kai aradun Allah kahi yayi a rayuwa kaji yanda nake jin kaina sak'ayau aradun Allah,ta rike kugu tace to yanzu ciki ya zazage ya kamata kuma na masa sabon lodi dan yunwa nake ji buguzun buguzum tabar wurin.

Tana zuwa wanka tayi,taci abinci,ita yanzu kusan babu abinda take yi a gidan Dan Hajiya har tsoron bata aiki take,yayyin da Hajiya haka kawai take jin A'indo cik'in ranta tamkar Yar ta.kodan yaran ta basa nan suna har Niamey wajen karatu .

Zazaune suke a falo A'indo da Hajiya da Rabi'u daudu da yake zaune yake faman cin shuiwingwom.

,,,,,,,,Wayar Hajiya ce tayi kara tana murmushi ta daga,tace"Soja na kana lfy,Kai Masha Allah ashe da na ya kusa dawowa gida,to Allah kawo ka lfy,a'a indai zaka taso kayi min magana sai a hada maka kalolin abincin da kake so."

Nan sukaci gaba da magana daga k'arshe sukayi salama,A'indo tace "Hajiya wa zaizo ?

"Baban da na ne Alhassan zaizo Yana kasar waje baban Sodja ne,sanan baya d'aukan wargi ko shirme,Rabi'u kaida A'INDO nasan ku sarai kuyi hankali ,anma Kai kasan sa shekaru hudu da suka huce da yazo ganin gida."

"Tab Hajiya bara kiga na tashi dan zama bai same ni ba,wanan mugun dan naki in yazo wanan karon ai nasan kulikulin kubura zaiyi dani,haka wancan karon dole saida yasa na koma jinsin da ba nawa ba Ina maganar kati,na koma jinsin maza,a'a wly bada ni ba in kingan ni Lahira kaini akayi,bara na tatara Yan komatsaina na kara gaba."
Cewar Rabi'u daudu,dan yayi matukar tsorata da yaji Wanda zaizo,hakan ko ta faru ne wani zuwa da Alhassan yayi , watarana yana hutawa akewayan sa ,kusa da swimming pool yana shan iska,yayi Kira a kawo masa juis sai ga Rabi'u daudu ya kawo masa,yana kawowa ya juya zai tafi carap Alhassan ya gano tafiyar da Rabi'u keyi irin ta mata,ransa ya baci dan in akoi abinda Alhassan ya tsana bai huci abu biyu ba,dan kauye da kuma yaga namiji na abun mata ,dan haka Rabi'u na juyawa ya daka masa tsawa,dama Rabi'u na tsoron sa,da sauri ya dawo Alhassan yace"Kai dan daudu ne,Rabi'u jiki na rawa ya daga kai,Alhassan yace "wly nasake ganin ina gidan nan kayi maganar mata ko kayi wani yanayi irin na Mata sai nasa an baje min kai,"to" ranka ya dade ayi hakuri Rabi'u yace."

Nan ya salame sa,bayan kwana biyu sai ga Rabi'u dashi da wata tsaye daya daga cik'in yan aikin yana maganar mata,yana fari da idanu,tar akan Idanun Alhassan Nan Alhassan yasa gards dinsa suka kamo masa Rabi'u aka lakada masa duka na fitar hankali,tun a lokacin indai Alhassan na gidan dole yake sa Rabi'u yin maganar maza Saida ya tafi sanan Rabi'u ya koma daudun sa......

Alhassan yana gama waya da Mom dinsa,sai ga Mina tazo budurwar sa,Alhassan dai ,na daya yana neman mata,anma baya Kai kansa saide mace ta kawo kanta,yana shan taba,yanada zafi,sosai baya d'aukan raini,kulum iyayen sa na masa maganar aure anma shifa har yanzu baiga Matar aure ba,domin gani yake yanzu matan babu na aure,masu mutunci duba da irin yanda suke kawo masa kansu.

Mimi ce ta shugo falon sa,zaune yake daga shi sai karamin wondo daidai cinya,ko riga bashida,kirar nan ta yan maza ta fito, Alhassan badai kyau ba,da cikar sura ,duk inda cikak'en namiji kuma k'yakyawan namiji yake yakai,saide ance dan Adam tara yake bai cika goma ba, matsalar sa shan taba da neman mata.

Mina na shigowa ta gansa a haka ta haye saman jikin sa,tare da" fadin sodja na"ta shafi fuskar sa,bata rai yayi yace"wai Mina yaushe zan dinga fada miki idan zaki shigo ki dinga salama,sai kace ba musulma ba haba."
"Haba sodja na Kai kulum sai ka dinga cika mutum da fada,ni ba fada ya kawo ni ba,bakin su ta hade wuri daya,dama shi sex mutumin sa ne dan haka ya biye mata.

Rabi'u dak'yar Hajiya ta lalabe sa ya hakura da barin gidan, A'INDO kam ko a kanta,dan ita bataga dalilin da zata wani shakar sa ba.

Yau dadare Hajiya da Alhaji suna zaune ,Hajiya cikin damuwa tace "haba Alhaji ya ma za'ayi haka,akoi yayan dangi ya zakace haka Yarinyar da baka san asalinta ba,baya ga haka ma mahaukaciya ce kace zaka hada ta da da na, kayi hakuri Mana shi aure ai lokaci ne dashi."

"Hajiya kinsan Sarai Al'adan mu tun yaro yanada shekaru ashrin da biyar muke Masa aure,anma,na kekashe idanu na naki aurar da nawa,wajen shekara tara Ina ba Alhassan dama yayi aure anma kulum magana daya ce bai samu wace yake so ba,a family mu kinsan babu Mata,duk sunyi aure haka kema naki,nasan Sarai yanda Alhassan ya tsani Yan aiki,sanan ya tsani Dan kauye .
domin tun ranar da na fara ganin ta naji ta shiga raina, yarinyar,duk da wawancin ta da shirme,wanan itace daidai da Dan mu Alhassan ,ki amince nayi wanan jihadin ."

Nisawa Hajiya tayi domin itama yarinyar ta shiga ranta,anma kuma abinda take gudu karfa dansu ya cutar da Yar mutane Alhaji yace karki damu bazan yi hakan da sauri ba zan basa dama ya kawo wada yake so ya aura nan da dan lokaci idan bai kawo ba ji zan basa wada naga dama.............

Aci gaba da gashi😘
Maimou love🍇
[10/10 à 17:27] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/

*Page 9-10*

,,,,,,,,,,,,********Hajiya ni dan Allah ki bani na goge miki falon Nan,Allah masu aikin nan basu iya aiki ba,ki bani na goge miki shi kal kal,Allah ai kinga aikin da nayi ranar har yanzu babu wace tayi irin wanan aikin,🙄."
Cewar A'INDO da ta matsa ma Hajiya dole sai ta barta ta gyara falo."

😳 waro idanu Hajiya tayi tace"tab A'indo so kike ki ida kashe mu da sauran kwanan mu ko ?
to bada ni ba wly,ranar duk kinsa munyi rauni,to yau idan kikayi inajin gawar mu za'a d'auka ,idan aiki kike so kije can kitchen ki koyi girki yafi miki."

"Tab anma wly Hajiya kin maida ni marar Hankali,anma Koda yake ba shi ke gareni ba,to ni na zauna ba aiki gani nan sakam ,wata waka akasa ta ado gwanja a tashar hausa ,Yana sama mata, A'INDO taji kidan na Kai mata, aiko tace Ina ai sai na danna,kugu ta d'aure da wani dankwali,nan fa ta fara girgiza,tana kalon yanda yake rawa itama tanayi,har wata irin lankwasa take Kai kace macijiya,da kida ya Kai mata ta dubi wurin da Hajiya take tana ma A'INDO kalon mamaki tare da tarin mamaki tace"aradu hajiya wanan waka da dadi take,zo mu taka hajiya,yanda take rawa Kai kace dambe take, Hajiya ko sakaka da baki tayi tana kalon ikon Allah,ashe shima Rabi'u daudu yaji kidan yana isowa kidan ya Kai masa,aiko shima ya d'aure kugu ya fara rawa yana karkada kugu tare da kwaso shoki, sai suka koma ma Hajiya Tv ita Kam ta kwaso ma kanta,anya ba zasu tafka kuskure ba kuwa ita da Alhaji🤔tashi Hajiya tayi ta bar musu falon dan abun yafi k'arfin ta,sosai suke Shan rawa da A'INDO da Rabi'u,A'indo na koyan shauki wata irin lak'wasowa take kamar macijiya sai ta kwaso,a garin kwashe kwashe ta kwaso da k'afafun Rabi'u daudu dama gashi siriri ba kiba ba,kafafuwan kamar na sauro,ji kake tim Rabi'u ya fadi,ya rike kugu yace"wai wai nashiga uku ta kasarani ,Wayyo k'wank'waso na,Hajiya ki kawo d'auki,wanan mahaukaciya zata takaita ni."

Ina Hajiya bata jinsu,A'indo bata tsagaita rawar ta ba saida ta kawo k'arshe,ta juya taga Rabi'u zaune rike da kugu,salati ta fara,tace "kaiko meye haka,🙄

"Ke kam Allah shi debe miki Albarka so kike ki kasarani,ki maidani miskini,dan na rasa mai aure na,wanan duniyar da lfy ka ma baka tsira ba bare bakada lfy,ya fada yana kara rike kugu.
Chapter 4 · 0% Book details