← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 45

Sashe 27

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hum Soja na kenan ,ai ka makaro,domin kuwa A'INDO yanzu baza mu taba tarbon ta ba da wanan maganar,dan a yanzu haka ta kuma zama ta wani,bayan bikin yar uwarta zamusa auren ta itama.ni da kake gani wallahi ni na haife ka anma a yanzu nafi son A'indo sama dakai ,domin ita din marainiya ce gaba da baya ,iyayen ta sun rasu shekaru biyu da suka huce,nice uwar su,kuma wallahi bari kaji ko ni bazan ba A'indo shawarar ta koma gidan ka ba,domin kuwa ba dan Allah kake son ta ba,a Koda yaushe zaka iya kuma rabuwa da ita,idan so na Allah kake mata tun acan da bata zama mutum ba ya kamata ka nuna hakan anma ba yanzu da ta zama mutum ba.ada can ma ita tabi umarnin mu duk da bamu haife ta ba ta aure ka,kai da muka Haifa ma kaki bin Umarnin mu,dan haka ni shawarar da zan baka kaje kayi hakuri da matar ka,ka dinga mata Nasiha
Wata killa ta shiryu,anma zancan rabuwa bamu amince maka ba.

Kallon daddy yayi a matukar razane,da gigita,ba komai kuma ya sashi a wanan halin illa jin da yayi cewar yayi hakuri yanzu kam A'INDO ta wani ce,wanan abun yasa ganinsa da jinsa na neman d'aukewa,biyu biyu ya fara ganin su,
Tun yana gane abinda suke cewa har ya daina jin komai,sai gani sukayi ya fadi a gurin ba alamun numfashi.

A matukar razana da rikicewa hajiya tayi kansa,ta kama sa ta fara girgiza sa,tana fadin" Alhassan dan Allah ka tashi ,ka taimaka,meye haka,Alhaji baya numfashi fa,shima Alhaji a rude da ganin halin da dansa ya shiga ya d'auki waya ya Kira idrissa ,ko minti goma ba'ayi ba sai ga idrissa da kayan aiki,nan ya fara duba sa,ya gano matsalar,jinin sa ne ya fara hawa,sanan kuma yanzu wanan hali da ya shiga Zuciyar sa ce ta buga ,jin abinda baiyi zato ba,ko kuma zuciyar sa bazata iya d'aukan abinda taji ba ruwa ya hada,ya sa masa.ya samu numfashin sa ya daidaita anma bai farfado ba.

Hajiya tayi tagumi shima Alhaji hankalin sa ya tashi kawai dan yana namiji ne yasa yafi hajiya dauriya.

Idrissa ya dubi daddyn nasa yace Daddy wai meye aka fada masa da ya sashi a wanan mumunan halin?."

"Gaskiya ce kawai muka fada masa"

Cewar Hajiya,domin bazata so yaran ta suji wai saboda A'INDO ya fada wanan halin ba,dan zasu iya fara jin haushin Yar ta itakam abinda bazata iya jurewa bane,bazata so ba ace daya daga cik'in yaran ta basu samun jituwa ,dan haka tace"so ne yake ya saki Matar sa,shine mu kuma muka ki amincewa."

Cewar Hajiya,duk da tasan ba shine musababin fadawar sa cikin wanan halin ba.

"Gaskiya Mom dad ku barsa yayi abinda yake son yi mana, haba wanan ai ba Mata bace,ku duba fa a matsayin ta na matar aure shigar da take yi,sanan ko kadan bata mutunta brother,gaskiya nima ina bayan sa,Mom kawai ku barsa yayi abinda yake so."

"Wanan kuskuren shi ya tafka a farko wanan kam bazan yarda ba,domin kuwa shi namiji idan ya saba da saki kullum hakan zata dinga Faruwa,dan haka zabin sa ne yayi hakuri ya zauna da ita."

Hajiya na gama fadar haka tabar d'akin.

Idrissa ya kalli Mahaifin sa alamun ya tausaya, murmushi Mahaifin yayi yace"idrissa kasan ban taba juyama mahaifiyar ka baya bisa kan gaskiyar ta ba,sanin kanka ne cewar abinda take so shi nake so,domin kuwa duk abinda zatayi da gaskiya take yinsa,dan haka abinda tace nima shi zance ban amince ba da abinda Alhassan ke so ya aikata ba."

A'indo ko yinin ranar cik'in nishadi da farin ciki ta shiga,ganin cewar yau an mari Alhassan ,me yafi wanan dadi a wajen ta.

Yau gaba-daya cik'in nishadi take."

bayan an gama fulani day da misalin k'arfe goma na dare su A'indo suna zaune suna tsara yanda za'a tsara Arabian day gobe , Salma daya daga cik'in kawayen su tace"a'a yau ko kunga abinda na gani kuwa?
Hum wai wanan sojan yayan ango wata ta mare sa,nace tooo duk fuskar sa,da miskilanci ace mace ta maresa."

Mimi tace "hum ai ance Matar sa ce ta maresa."
Salma tace" kai haba dan Allah ,gaskiya batada tarbiya batada mutunci,ace mace da ita ta daga hannu ta mari mijin ta."

"Hum shi mijin ai baku san halin sa ba,baku san abinda yake ba kawai a dai yi sha'ani." Cewar A'indo,da gaba-daya ranta ya fara baci da taji ana maganar makiyin ta.

"Nikam A'indo naga baki son ana maganar sa,ranar ma nace miki nifa ya min,anma naga kin bata rai,kince Kar na kara miki wanan zancan yadai🤔cewar Salma."

"Mtsss dako kinyi zabon tumun dare,domin kuwa wanan Zuciyar sa baka ce ko kadan bayada imani, kamar fir'auna yake, sanan ga wulakanta dan Adam kai wanan yanada mugun hali wly ni dan Allah abar wanan zancan nasa mu kwanta zaifi saboda kunsan gobe munada aiki.."

Shiru sukayi suka kwanta,yayyin da A'indo take ta juye juye,tunanin marin da Mina tayima Alhassan take,daga ta tuna sai tayi murmushi.

Washe gari haka akayi Arabian day,Masha Allah nan ma yayi kyau, Alhassan nacan kwance saida yasha ruwa leda biyu,ya farfado anma duk da haka bashida k'arfin jiki,da ya rufe idanu A'indo yake gani tana masa murmushin ta mai tafiyar da tunanin sa,da nutsuwar sa .

Zaune yake saman gado,yana tunanin A'indo yau kwana biyu bai ganta ba,so yake ya saba ma kansa da rashin ganin ta,ko zai samu sasaucin Zuciyar sa,anma ina abin ba sasauci domin kuwa ji yake idan har bai ganta ba to zai iya samun matsala,tashi yayi da k'yar duk ya rame kwana biyu kwance,duk ya fige ya rame shi kadai yasan radadin da yake ji a zuciyar sa,yana dafa bango haka ya isa falon Hajiya,da yake duk bakin suna falon baki dan haka ba kowa,sai A'indo da take cin abinci bisa table,sanye take da jar atamfa dinkin riga da siket,dinkin yayi bala'in yi mata kyau,irin rigar nan ce mai gidan breziya sanan daga saman wuyan rigar sai aka bud'e sa ya zamana wuyan yakai kafadar ta,tasa yar karamar sarkar gold a wuya sai ta hau wuyan tayi das da yake wuyan nata a cik'e yake bul-bul gwanin sha'awa,sai yan kunnen sarkar,tayi kyau sosai kamar ita ce amaryar,domin kuwa ita kanta gyaran amaren take sha,ga wani ni'imtacen kamshin da yake tashi a jikin ta,tasha d'aurin d'ankwali irin na zamani,zaune take tana cin abinci tana gamawa ta d'auki fruits tana sha dan tabi'a ta ce, shan fruit bayan cin abinci,shigowa yayi falon juyawa yayi Aiko ya ganta zaune,ba karamin sanyi yaji a zuciyar sa ba, gaba-daya ya nemi ciwo ya rasa illa wani sanyi da yake ji yana ratsa zuciyar sa,lumshe shanyayun idanun sa yayi tare da dafa saitin Zuciyar sa jin yayi gaban sa na faduwa,kamar ana jansa yana murmushi ya isa wajen ta,yana zuwa ya duka kasa har gwiwa tuni wasu hawaye suka zubo masa,ace wai shine yau yake zubar da hawaye ,kuma duke gaban mace,macen ma wada ya wulakanta,gaskiya so bai masa adalci ba,tabas Alhakin A'INDO ne yake kama sa tabas lalai abinda ka raina wataran shi zai tsole maka ido ji yayi sonta ya kara shiga Zuciyar sa.

A'indo tun daga dan nesa ta jiyo kamshin turaren sa,tasan sarai shine shi yasa ko juyowa batayi ba taci gaba da Shan fruit dinta,ganin ya duka kasa dai-dai gurin ta,abin yayi bala'in matukar bata mamaki da tsoro,zaro idanu tayi tana kallon sa cik'in tsiwa tace"Malam wai meye haka"?

"Na roke ki da girman Allah kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi miki na tabata alhakin ki ne ke bibiyata,dan Allah Aisha ki taimaka ki bani dama a karo na biyu ki tausaya min ki tausaya ma rayuwa ta."

" Mtsssss kaga Malam dakata✋ karka zo min da wani zancan banza ,ba wani dadin bakin da zakayi min,ni a lokacin kaji tausayi na ne,ko an fada ma Kaine da namiji kadai,to bara kaji wallahi ko maza sun Kare a duniyar nan na k'wanmace na zauna ba aure,kai wallahi da komawa auren ka gwara na koma da bakin kumurci,mtssss........."
. Tana gama fadar haka tabar wajen,wani tari ne ya tunkuro ma Alhassan,sosai yake tarin abin tsoro tare da kiran sunan ta,tun yana ganin ta har ya fara ganin ta biyu biyu,daga k'arshe Idanun sa suka rufe rufffff..........
....

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[25/10 à 21:33] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Page -55-56*

Halissa ce ta shigo falon,ta ga yayanta a haka,a tsorace ta karaso inda yake,tana jijiga sa,tare da fadin" Yaya yaya plz ka tashi ,me ya same ka?
Wayyo Allah ,da gudu taje ta d'auko ruwa a firge ta yayafa masa,nan take numfashin sa ya dawo,a hankali ya fara bud'e idanun sa,har ya sauke su akan kanwar sa, murmushi yayi wanda yayi nuni da iya lebo kawai ya tsaya,ya tashi da k'yar da taimakon Halissa ta taimaka masa suka idasa saman kujera,tace"yaya bakada lfy me ya fito da kai haka"?

"Oh kanwata na gaji da zama d'aki ni kadai ne,kuma kinga bikin dan uwana ake."

Mina ce ta shigo falon sanye da riga da dogon wondo,tasha Attachment na gashi,ga farata zako-zako da tasa,tasa yar karamar hula,ga uwayen takalma dogaye masu tsini da tasa,da alamun fita zatayi.

Tana cin shuiwingwom irin na yan duniya,tsohin karuwan nan wanda suka shahara a bariki,kallon sa tayi shekeke,tace"key zaka bani na motar ka,dan ita nake son shiga yau zanje salon."

Daga kai yayi ya kalleta,ya girgiza kai cik'e da takaici,yace"fita da zakiyi kin tambaye ni ne?,sanan kina yar musulmi zaki fita haka bugu da kari da auren ki,wai Mina me kika d'auke ni ne?
Chapter 27 · 0% Book details