← Book details Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 45

Sashe 17

Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan ubanki har tambaya kike in kinmin laifi,agidan uban wa kika taba ganin an wanke computer."
Duk Mina na tsaye tana kallon su tana dariyar jin dadin bugun da yake ma A'indo,itakam A'indo neman gudu tayi dan ta ceci kanta ,ganin haka ran Alhassan ya kara tunzura,ya kara damko wuyanta ta baya da k'arfi ya buga kanta da bango wata irin razananar kara A'indo ta buga sai gata suuuuu ta fadi,jini ya fara zuba daga goshin ta,salati yaji an buga daga bayan sa,wanda yayyi matukar razana sa,juyawar da zaiyi aiko wa zai gani idan ba Hajiyar sa ba,wato Momyn sa,a matukar ruduwa da firgita ya zaro idanu,da gudu Hajiya ta karaso ita da Mari dan dama a tare suka shigo talabo A'indo Hajiya tayi,ta fara jijigata tana ambatar sunan ta anma ina A'indo ta suma.
"Mari taimaka mukaita asibiti.".

Hajiya tace da Mari,d'aukan A'indo sukayi,aka kaita wata asibiti daban,ba wacan ba,taimakon gagawa aka ba A'indo awa daya aka d'auka a kanta,sanan aka samu ta farfado,anma kuma ga dukan alamu akoi matsala a kanta,domin kuwa har k'wak'walwar ta likitoci suna tsoron idan bata samu matsala ba saboda buguwar da k'arfi ne akayi mata.hajiya na hawaye ta dafa Mari tace nagode ya ta,da Kika kirani,anma dan Allah ki fadamin gaskiyar duk abinda kika san ana mata a gidan,domin na tambayeki a waya kince sai nazo to ki fadamin yanzu."

Sauke ajiyar zuciya Mari tayi,ta fadama Hajiya duk wani abinda ta sani.

Goge hawaye Hajiya tayi,tabas sunyi kuskuren yin wanan hadin,ashe haka Alhassan yake bashida imani,tabas zai gane kuren sa,dafa Mari Hajiya tayi sanan tace "Mari ki kula min da A'INDO zanje na dawo fita Hajiya tayi,ta shiga taxi gidan Alhassan ta koma,yana falon har yanzu, yana nan inda yake, Mina kam ta gudu ta bar sa dan tsoro ,tunda ta fahimci Hajiyar sa ce tazo .

A tsaye Hajiya ta iske sa,bata ko masa magana ba ta basa takarda da biro tace"amshi ka saki A'indo a yanzun nan,idan ko kaki bin Umarni na zan iya tsine maka,hannu na rawa ya amsa ya rubuta ma A'indo saki daya,ya ba Hajiya takardar hannun sa na rawa,"Mom dan Allah tsaya kijiiiii."

"✋ya isa!!! tsayar dashi Hajiya tayi a tsawace,tace"a yau ka nuna mana mu bamu isa dakai ba,cewa nake ko Kashi muka aura ma ka zauna dashi ba tare da ka zalunce sa ba bare dan Adam,ni bazan maka baki ba,anma ka sani wallahi alhakin baiwar Allah nan kadai ya ishe ka,yanzu sai kayi abinda kaga dama ,A'indo insha Allah ta rabu dakai har abada."

Hajiya na gama fadar haka tabar gidan ta nufi asibiti,anma tana zuwa asibiti ta tarar da mumunan labari,zaune suke daga ita har Mari gaban doctor inda yake musu bayani game da matsalar A'indo kamar haka........

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_kuyi hakuri na rubuta Latifa ina tsaka da editing ya goge_😢

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*Page 33-34*

Fita yayi ya barsu,a kyamace Mina ke nuna mata abubuwa cik'in yanga,tanayi mata magana tana done hanci wai wari take,duk A'indo na lura da ita,tabas duk abin A'indo bata zama da kazanta bare wani abu wai shi wari,kaya ne kawai na lefe bata sawa Wanda aka mata,anma tana amfani da mayukan da aka hada mata na gyaran jiki da kuma kamshi,sanan tana amfani da turare,wanda ko ita karan kanta Mina bazata nuna mata kamshi ba....

Girgiza kai kawai A'indo tayi cik'e da takaici,nan ta zuba komai yanda ta nuna mata ta duka ta fara wanke mata kafa,"wai ke wace irin daba ce stupid bakya da laka ne,wawiyar banza ,kina wankin kafa kamar kina susa."

Cewar Mina ta daka ma A'indo tsawa."

"Yi hakuri"

Abinda A'indo tace kenan,nan ta dinga wanke ma Mina k'afa tana zagin ta,bayan ta gama tace A'INDO tayi mata tsifar kitson kanta,mai hade da gashin attachement,kalon ta A'indo tayi tace"kiyi hakuri hannuna daya bayayi ya samu karaya ne."

Fadin haka ya bata ran Mina tace"dan uwarki bakiji abinda mijina yace ba,cewa yayi ke baiwata ce,koda hannun ki yana jan kasa ai kinyi abinda nace,anma tunda naga dama ku yan kauyen nan baku iya samun guri ba,bara kiga."

Waya ta d'auka ta danna kiran Alhassan aiko cik'in yan sakanni sai gashi sai muzurai yake,yace"my wife wa ya tabaki."
Kyabe baki Mina tayi tace"haba my Man ace wai yarinyar nan na sa ta aiki anma taki yi min ,wai taji ciwo a hannu dan munafurci,kamar ni yarinyar nan ta nemi zagi na."

Waro idanu Alhassan yayi tare da cewa "what"? cik'in zaro ido,ransa in yayi dubu to ya baci,dama neman hanyar da zaibi ya bata ran A'indo yake,ya kalli A'indo yace"ke dan ubanki kina matsayin yar Aiki ni zaki kalli Matar da nake so kice bazaki mata abinda take so ba,wai ke hannu, sallon munafurci,hannu ko ,hum bara kiga,hannun ya rike wanda ya karye din,yayi masa wani irin ja da k'arfi,wata razananar kara A'indo ta saki tsabar azaba,sai gata ta fadi sumamiya.

Waro idanu😨 Mina tayi cikin matukar tsoro tace" Man ka fa kashe ta!
"Yau ta mutu mana wa keda asara,kinga fice muje,na kirawo masu fida min ita,ni dama zata mutu da naji dadi mtsssss."
Cewar Alhassan,da k'arfi yaja Mina suka fice daga wurin,gards dinsa Mata yakira,Mari da Jenifer,su suka d'auke A'indo sukayi d'akin ta da ita a some.

Mari Kam yau kuka take sosai,domin tasan cewar matukar A'indo nada rai to ga yanda taga hannun ta sai ta Allah,domin gwiwar hannun ta dan lank'wasa,yau Mai gyaran hannun ta kira direct ,bata nemi saurayin ta ba,ba'a jima ba yazo,a sumen ya duba hannun A'indo ya zaro ido yace"ranki ya dade ya haka ,me yasa aka bari hannun ta yana samun matsala haka,to a gaskiya cik'in biyu za'ayi daya,kodai idan ba'ayi sa'a ba hannun ta ya lalace wanda dole sai an yanke sa,idan kuma na duba Allah ya so ta to ba lallai hannun ya daidaita yanda take a da ba."
Duk a turanci yake wanan bayanin.

"Mari da duk jikin ta yayi sanyi tace"ka taimaka ka duba hannun a yanda take a some domin idan ta tashi zatafi cin azaba."

Nan ya kunce karayar ,ya duba,hannun ya lank'wasa,haka dole ya sake sabon d'auri,wanda azabar hakan ya farfado da A'indo a gigice,ta fara kiran sunan Alhassan da yayi hakuri,tana kara fadin wayyo babana ka taimaka ka kwato ni daga hannun azalumi,Wayyo Allah,Mari ce ta rungume ta,Saida aka kara gyara karayar,saide hannun bai koma dai-dai ba, saboda ya dan gusa,bayan an gama mai gyaran yace"a gaskiya a dinga taka tsantsan da wanan hannun domin anyi sa'a tanada kyan jiki,badan haka ba da wani jikin ne saide a yanke hannun ,anma yanzu ma a kiyaye,domin kuwa idan hannun ya kara tabuwa to za'a iya samun matsala,dan ba fata nake mata ba za'a iya yanke hannun."

Ga wanan maganin a bata tasha."

Mari ta masa godiya ya tafi ,kallon ta takai ga A'indo tace"wai ke me kikema oga yake miki irin wanan horon,ki daina matse masa,ko yi Masa musu dan wly kinji abinda akace idan hannun ya kara tabuwa to fa za'a iya yanke sa,ko kinfi son a yanke,kinga ni yanzu sati yayi min saura na bar kasar nan in koma kasata Niger dama ina sha'awar aikin soja shi yasa mahaifina ya turo ni wanan K'asar domin Karin ilimi bisa kan karatun soji,shine aka hadani da oga Alhassan a wajen sa nake karin koyan abubuwan da ya danganci soji."

Dan Allah ki roke sa ya mayar dake gida,kinga duka gidan nan kusan arna ne,ba wani tausayi garesu ba,suna kallan ki ko zaki mutu ba zasu taimake ki ba."

Kada kai A'indo tayi cik'e da tausayin kanta,zataje ta roke sa ya mayar da ita,anma kuma yanzu mugu mugun tsoron sa take ji ,nan Mari ta barta ta koma taci gaba da aikin ta,A'indo taci kuka kamar ranta zai fita....

Washe gari da zazabi mai zafi A'indo ta kuma tashi,wanda yasa ko tashi bata iyayi,sai tayi yunkurin tashi sai jiri ya d'auke ta,dan haka take kwance,ga muguwar yunwa da ta adabe a,ga amai da yake zuwar mata,tun tanayin na garin rogo har takai in ta duka bata anma komai,saide tayita kakari anma ba abinda ke fitowa, ,cik'in ta ya kulle,a haka da asuba kamar yanda Alhassan ya saba idan ya fito daga Sallah a masalaci yana ganin ta tana wanki motar da zai fita da ita anma yau yaga wayam ba ita ransa a matukar bace,yayyi b'angaren ta,kwance ya isketa tayi lamo,dan yanda taga dare haka taga rana,bai tsaya lura da yanayin da take ciki ba yana zuwa yayi ball da ita dai-dai Allah ya taimaka bai samu hannun ba , saide cik'in ta da ya buga,da kyar A'indo ta iya yin kara wace duk azabar da take ji karar ba zata fito ba saboda ba k'arfi a jikin ta,kuma gashi ba komai a cik'in ta ga bugun da yayyi mata dama ciki ya kulle.

"Dan uwarki ubanwa kike so ya miki aikin naki,kinsa da bana son a saba magana ta shine dan ubanki yau baki tashi Kika wanke min ba."

Kuka A'indo take da kyar muryar ta ke fitowa tace"dan Allah ranka ya dade kayi hakuri wallahi banida lfy ne,nasha kokarin in tashi anma jiri yana diba ta,kayi hakuri ka yafe ni😭😭😭."

Ko kadan bata basa tausayi ba,saima dukawa da yayyi ya ja kunnen ta da k'arfi yace"wallahi baki isa ba ko Zaki mutu sai kinyi ayukan nan."

Cik'in zafin ciwo da kunar zuciya A'indo tace"dan Allah idan abinda nayi maka ne a baya kayi hakuri ka yafe min,wly Allah yanzu a shirye nake da fasa auren ka,wly Allah zan fada ma Hajiya,dan Allah kayi min rai ka maidani kasata."
Chapter 17 · 0% Book details