← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 102

Sashe 95

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da flight d'insu yasafka gabad'aya wajen yarikice da murna musamman ma da Memartaba yazo fitowa tsaye yayi yana d'aga musu hannu cike da jin dad'in ganin jama'arsa yadda sukazo tarbarsa.

Ai suna ganin yarima sai wajen ya ida rikicewa nan aka cigaba da murna dan ma dogarawa sun hana kowa yamatso inda suke nan aka bud'e musu motocin da aka tanadar masu suka shiga dakyar suka samu hanya sai emir palace,

A chan d'inma mutanene dank'are suke jiran isowarsu, nan ma anyi murna sosai da ganin yarima, shaheed ko rugowa yayi yarungume abokin nasa cikin jin dad'i shima yarima yarungumesa.
Shaheed yace abokina ina katafi kabarni? shine katafi kabarmu muna ta nemanka.
murmushi yarima yayi yace kayi hak'uri shaheed yanzu gani nadawo ba inda zan k'ara tafiya inbarka.
cikin jin dad'i yace dagaske?
'Daga masa kai yarima yayi alamun eh.
nan shaheed yayi murmushi yace nagode sosai abokina ammah fa nayi kewarka.
Memartaba baishiga gidaba saida yatsaya suka gaisa da mutane tare da yi masu godia sannan suka rantaya a turakar su Memartaba, rahama da husna dasauri suka nufo dan tarbar iyayen nasu ganin yarima yasa suka rikice suka nufi wajensa har da kukansu, rungume 'yan uwannasa yayi cikin jin dad'i, rahama cikin kuka tace Bro meyasa katafi kabarmu? Baka tunanin halin da zamu shiga, kaduba kaga tun bayan tafiyarka gabad'ayanmu bamu cikin kwanciyar hankali.
shafa kanta yayi yace kiyi hak'uri Lil sis yanzu gani nadawo yayanki zai kasance da ke akowane lokaci,
murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai yayana, nan takoma wajen zarah tarungumeta cikin jin dad'i.

Kallon husna yayi da take ta kuka yace akan me babbar yaya zata dinga kuka bayan ga k'anenta a kusa da ita? 'Dago kai tayi takallesa nan yad'aga mata kai, cikin sauri tafad'a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.
rungumeta yarima yayi yace please sis kukan ya isa haka indai baso kike nima kisanyaniba.

Cikin sheshek'ar kuka tace meyasa katafi kabarni, kai kanacan hankalinka kwance bakasan halin da muka shigaba saboda rashinka.
Murmushin k'arfin hali yarima yayi yace big sis duk inda suhail yakasance toh shima tunaninsa yana a wajenku, daidai da kwana d'aya ban ta6ayiba batare da kuna a raina ba.
toh dan Allah kar kak'ara tafiya kabarmu.
Jan kumatunta yayi yace angama big sis, cikin jin dad'i takai mai peck a goshi sannan suka rantaya zuwa turakar su memartaba.

Gabad'ayansu a saman carpet d'in da yake shimfid'e tsakiyan d'akin suka zauna inda memartaba da dada suka zauna saman cushin.

gyaran murya memartaba yayi sannan yace Alhmdllh godiya ta tabbata ga Allah da yasa cikin ikonsa nasamu lafiya akan ciwon da ni kaina banyi tunanin zan tashiba saidai cikin ikon Allah ayanzu gani garas saidai d'an abinda ba a rasaba.
gabad'ayansu sukace Alhmdllh Allah yak'ara lafiya da nisan kwana.
Shuru yayi nad'an lokaci yacigaba da cewa yarima suhail munatayaka murnar dawowa cikin family d'inka tare da baka hak'uri akan abinda yafaru.
Murmushi yarima yayi yace bakomai ranka yadad'e.
masha Allah sannan magana tagaba itace......shuru memartaba yayi alokacin da yaga sumayya ta shigo d'akin, gabad'ayansu ido suka zuba mata.

daga nesa dasu kad'an tatsugunna tana kuka,,,abban sumayya ne yai k'arfin halin cewa ubanmi kikazo kiyi mana nan? Ko kitashi ko insa6a miki.

Cikin kuka sumayya tace dan Allah kuyi hak'uri kuyafemin abinda nayi maku wlh nayi nadama nadaina bazan sakeba.

Memartaba jinjina kai yayi yace zancen banza koda kikaga na k'yaleki bansa aka had'a da ke aka sa prison ba toh nabarkine yarima yadawo yayanke miki hukunci dakansa saboda shi yafi dacewa yayanke miki ba niba tunda kuma yanzu gashi ya dawo toh alhmdllh wuk'a da nama suna hannunsa dan haka suhail ga sumayya nan kayanke mata hukuncin da yadace da ita.

dada tace tabbas hakane suhail duk abinda kazartas daidaine.

Mik'ewa sumayya tayi tamatso kusa da yarima tatsugunna cikin kuka tace yarima ban damu da hukuncin da zaka zartas ba akaina nidai burina d'aya kataimaka kayafemin abubuwan da nayi maka wlh duk abinda nayi ba yin kaina bane zinat ce silar komai, tasha fad'amin cewa bazan iya rabuwa da itaba saboda akwai abinda tashirya min tun farkon had'uwarmu, indai zinat zatayi magana toh tatanake d'auka inbar ta kowa koda ace ta iyayenace, sannan nasha k'ullah makirci dan inga nashiga tsakaninku da zarah dan ina gani nice nadace da kai ba zarah ba ammah a yanzu nagane cewa zarah ita tafi dacewa da suhail,
Kallon zarah tayi tace zarah nai miki abubuwa dadama ammah baki ta6a d'aga ido kin kalleniba dan tsakani ga Allah kike zaune da ni.

Zarah da tunda sumayya tafara maganar kuka take dan ta bata tausayi sosai musamman ma da taga duk ta fita hayyacinta.

Yarima Kallon memartaba yayi yace ranka yadad'e dalilin da yasa ban fad'a mukuba tun farko saboda nafiso ku ma kugani da idanunku gudun kar kuk'i yarda musamman ma dada da ummah gabad'aya basuson laifin sumayya a lokacin.

Uhm kaidai bari d'annan ai yanzu dai mungane komai,,,cewar dada.

Jinjina kai yarima yayi sannan yace ashe saida k'awartata tak'ara dawowa gidannan,
Memartaba yace yanzu ma haka tana a prison bari insa atafo da ita, nan memartaba yayi waya.

bayan mintuna kad'an saiga wani barde yazo da zinat duk ta yi bak'i ta k'ok'e inba ka kalletaba sosai bazaka ta6a cewa ita bace hatta ita kanta sumayya da taganta saida tafirgita.

Daga nesa dasu kad'an taraku6e tana hawaye, kallonta sumayya tayi cikin kuka tace zinat dan Allah kiwanke ni wajensu susan banda laifi a ciki.

Zinat ma cikin kuka tace idan bakida laifi toh wa yake da laifi? wlh sumayya kin cuceni.

Duk mutanen da suke zaune wajen shuru sukayi sukarasa megaskiya tsakaninsu,,,yarima ne yace bari akira dogarawa suzo atambayesu.

Zinat a tsorace dan ta tsorata sosai da bulala tamanin d'in da akayi mata cikin kuka tace dan Allah kar kakira ni zan fad'i komai ammah kar kasa ak'ara dukana.

Indai har kika fad'amin gaskiya batare da kinmin k'aryaba toh babu wanda zai dakeki sannan zani sallameki kiyi tafiyarki.

Share hawayen fuskarta tayi sannan tace tabbas sumayya batada laifi a ciki nice silar fad'awarta wannan harkar dan tun muna school sumayya tana da wulak'anci bata yadda tayi abota da kowa sai 'ya'yan masu kud'i nikuma tun lokacin da nafara ganinta naji ta burgeni ganin nima d'iyar masu kud'i ce yasa nayi amfani da dadamata muka k'ullah abota nan mukacigaba da wulak'anci saida naga sumayya ta saba dani batada abokiya kamarni sannan nabijuro mata da buk'atata akanta ammah tak'i yadda ban nuna mata 6acin rainaba daga k'arshe naje wajen wani malami yaimin aiki akanta yazamana duk abinda nakeso shi takeyi bata iya tsallake maganata, a lokacin wani saurayina yanuna yana buk'atarta yabani kud'i masu yawa nikuma naimasa silar samun sumayya shima saida taga raina yana neman 6act sannan ta amince har yayi zina da ita.
gabad'aya d'akin suka saka salati cike da al'ajibin abun kowa yana Allah wadai.

memartabane yatsaidasu, nan zinat tacigaba da cewa tun daga lokacin nima nafara neman sumayya har nasaba mata da harkar itama tabi layi.
a lokacin da take fad'amin zatayi aure na nuna bak'in cikina sosai saboda inason sumayya banaso inga abinda zai rabani da ita, daga k'arshe koda tayi aure ni nadinga hure mata kunne akan kar tayi ma mijinta biyayya duk wani abu da sumayya takeyi da sa hannuna a ciki saboda bata iya tsallake maganata, hatta pills ni nasakata tana sha duk dan kar tahaihu saisa kukaga bata ta6a ko 6atan wataba,
ahaka nacigaba da bibiyarta gidan aurenta mukacigaba da harkarmu batare da tsoron komai ba sai gashi lokaci guda dubunmu tacika ankama mu muna aikatawa.
Dan Allah tunda na fad'a maka gaskiya kabarni intafi wlh bazaku k'ara ganin ko k'eyataba nima nadaina.

Gabad'aya matan da suke d'akin kuka suke, sultana sadiya cikin kuka tace Allah ya isa ashe kece kika 6atamin d'iya.
sumayya girgiza kai tayi tace zinat babu abinda zance miki saidai kawai kije munhad'e gobe k'iyama gaban ubangijinmu ammah hakanma nagode da kika wankeni a wajen dangina.

Sultan abbas murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace kema sumayya harda laifinki a ciki nasha kwatanta miki akan kibi rayuwa a sannu ammah rawan kanki ya hana daman ita rayuwa *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka dan haka kije gashinan duniya ta nuna miki hankali daman ita duniya ta ishi kowa riga da wando.

Sultan ahmad da memartaba shuru sukayi kamar ruwa ya cisu

Yarima kud'i yad'auko yamik'a ma zinat batare da ya k'irgasuba yace nabaki minti ukku kifita kibar gidannan ko k'eyarki kar kibari ink'ara ganinki.

cikin sauri zinat takar6i kud'in gudu-gudu sauri-sauri haka tafita.

Sai a lokacin yarima yakalli sumayya yace kije kawai sumayya duk abinda kikayi min dan kanki daman tuni nagano haka kawai dai gudun kar zargi yashiga tsakaninmu shiyasa ban ta6a magana ba ammah yanzu Alhmdllh da gaskiya tabayyana

Rik'o hannunsa tayi cikin kuka tace dan Allah suhail kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko na sami sauk'in abinda nakeji.

Fizge hannunsa yayi, ganin haka yasa zarah cikin kuka tace dan Allah kataimaka kayafe mata tunda ta gane laifinta kuma kunji batada laifi a ciki.
murmushi yarima yayi yace shikenan dear ta ci albarkacinki nayafe mata.

Cikin jin dad'i tace nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, koda taje wajen zarah tunkan tayi magana zarah tace kar kice komai sumayya ni tuni na yafemiki daman ban rik'ekiba.

haka sumayya tazagaya wajen kowa tanemi gafararsa kowa yace ya yafe mata cikin jin dad'i tayi musu godia.

memartaba sai a lokacin yayi magana yace toh Alhmdllh tunda anyafe ma juna, dan haka yanzu wannan ya kamata yazama darasi ga kowa, kekuma sumayya yanzu tunda kin nuna kin tuba kicigaba da neman gafarar ubangiji akan abinda kika aikata sannan kicigaba da zama har Allah yakawo miki miji kiyi aure.

Cikin jin dad'i sumayya tace toh nagode sosai ranka yadad'e.

Memartaba kallon yarima yayi yace suhail ga part d'inku chan nasa angyara maku zaku koma kucigaba da zamanku guards d'inka da ma'aikatanku duk suna nan.

Sosa k'eyarsa suhail yayi yace ranka yadad'e da gidana da nagina naso inkoma da zama idan ka amince.

Girgiza kai memartaba yayi yace a'a suhail kar kayi haka kayi hak'uri kucigaba da zama nan kusa da ni dan hankalina ya fi kwanciya da haka.

murmushi yarima yayi yace toh ranka yadad'e yadda kakeso haka za'ayi.
Chapter 95 · 0% Book details