← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 102

Sashe 90

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dada fashewa tayi da kuka tace hakane ranka yadad'e ammah ai ubangiji bai safkar da cutaba saida yasafkar da maganinta dan Allah kataimaka aje asibitin kaga bamu kad'aiba hatta sauran mutane hankalinsu atashe yake.

Cikin dauriyar ciwo memartaba yace shikenan na amince muje ammah ubangiji ya gama tsara komai akan lamarinsa.

Cike da jin dad'i tare da neman gasgata kalmar da kunnuwansu suka jiye musu nan suka shiga kallon juna suna murmushi.

Sultan Abbas ne yace dagaske ya amince muje?
Shima sultan ahmad murmushi yayi yace nima kusan abinda kunnuwana suka juyo min kenan.

Dada share hawayen fuskarta tayi tace Alhmdllh yanzu kuje kusa ashirya motocin da zamu tafi da shi, asibitin suhail kawai zamuje.

Cikin jin dad'i sukaje sukasa aka shirya motoci nan aka fito da memartaba aka shigar da shi motar da aka tanada dominsa Dada kawai tashiga cikinta.

Su kuma cikin d'ayar motar suka shiga ahankali ake tuk'in duk inda aka wuce talakkawa d'aga masu hannu suke suna ma shugabansu fatan samun lafiya.

Koda suka isa Prince.S hospital, cikin gaugawa akazo aka tarbesu dan motocin kawai da suka gani yasa sukagane daga inda suke,

Dr khalil da sauran manyan likitocine tsaye akan memartaba a cikin wani k'ayataccen room suna ta bincike bayan anyi masa scanning d'in, inda shi kuma yake ta baccinsa.

Gabad'aya hankalinsu ya tashi saboda basusan yadda zasuyi sushawo kan matsalar ba nan sukayi 'yan maganganunsu.

Dr khalil ne yafito jiki ba k'wari yanufi inda su dada suke zaune, ganinsa yasa gabad'ayansu suka mik'e suna tambayarsa jikin memartaba.

Murmushin k'arfin hali yayi yace Alhmdllh dasauk'i sannan yasamu waje yazauna, ya umurcesu da suma suzauna bayan sun zauna, kallonsu Dr khalil yayi sannan yace Alhmdllh mun gano abinda yayi causing d'in ciwon cikin ba komai bane face 'yan hanjinsane da wasu suka nad'e,

Gabad'ayansu saida gabansu yafad'i sukace 'yan hanjinsa sun nad'e?

Ganin yadda hankalinsu yatashi yasa Dr khalil yad'anyi murmushi yace kar kudamu ba wata babbar matsala bace tunda daman ana samun masu shiga wannan condition d'in kuma suna rayuwa saidai ta hanya d'aya za'a bi.

Gabad'aya suka had'a baki wajen cewa ta wace hanya kenan?

Ajiyar zuciya yasafke sannan yace ta hanyar yin theatre.

Sultan abbas ne yace toh Dr indai ta hakan za'a samu sauk'i toh mu relatives d'insa mun amince ayi masa kawai.

Jinjina kai Dr khalil yayi yace abbah saidai wani hanzari ba guduba jinin memartaba ya hau sosai babu yadda zamuyi mu iya yin wannan aikin batare da jininsa ya d'an yi low ba.

Salati suka sanya cike da tashin hankali, dada kuka tasaka tace yanzu khalil babu yadda za'ayi a iya yin komai?

Cike da jin tausayinta yace ranki yadad'e kar kidamu zamu duba mugani.
Yauwa Dr dan Allah kubincika sosai.
Dr khalil yace kar kidamu ranki yadad'e zamuyi iya bakin k'ok'arinmu.
Yafuto sultan Ahmad yayi da ido sannan yamik'e yace ina zuwa.

Saida yafita sannan sultan Ahmad yamik'e yabi bayansa.

A office d'insa suka je, bayan sun zauna Dr khalil kallonsa yayi cike da damuwa yace daddy adai cigaba da yi masa addu'a dan jininsa ya hau over, kuma a wannan condition d'in da yake ciki baikamata ad'au lokaciba batare da anyi masa aikinba, ammah a yanzu zamu d'aurasa akan wasu drugs tsawon kwana ukku idan har jinin baiyi low ba toh saidai afitar da shi abroad.

Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un daddy yashiga nanatawa cike da damuwa.

Dafe kai Dr khalil yayi kamar mai tunani sannan yace yauwa akwai wani mai irin wannan condition d'in da aka kawo mana bamuyi aikinba sai dagabaya akace mana ankaisa a wani gari wani likitane yayi masa aikin saidai ban tambayi wane gari bane ammah gaskiya ance yanzu haka mutumin yana nan lafiya lau ya warke.

Cike da damuwa sultan ahmad yace dan Allah khalil kataimaika kagano wane garine inyaso sai muje.

Murmushi Dr khalil yayi yace insha Allahu daddy zan bincika yanzu dai bari inje infara kawo drugs d'in da zai fara amfani da su mugani, Indai har akayi kwana ukkun bai safkaba sai kutafi chan.

Jinjina kai daddy yayi cike da gamsuwa da maganar Dr khalil yace Allah yashige mana gaba.

Ameen,,cewar Dr.
Sannan suka tashi suka fito tare inda sultan ahmad yakoma wajensu dada yai musu bayanin rik'esu da za'ayi tsawon kwana ukku ad'aurashi akan magani, ammah bai fad'a musu sauran bayaninba gudun kar hankalin tsohuwar tasu yatashi sosai.

Haka Dr khalil yaje yakawo drugs d'in, tun daga wajen d'akin dogarawane aka zuba suna gadinsa, sultan ahmad ne yace zai dinga kwana da mahaifin nasa ahaka su dada suka amince suka koma gida.

Kulawa sosai memartaba yake samu daga ma'aikatan asibitin ba a awa d'aya batare da anzo anduba lafiyarsaba, abinci dakyar ake samu yana d'an ci kad'an kafin yasha magani, su dada kullum suna hanyar asibitin sai dare suke komawa.

Mutanensa dadama sunzo dubasa dan ma ana hanasu shiga wajensa saboda ba aso ana damunsa dayawa.

*BAYAN KWANA UKKU*

Nan likitoci suka k'ara taruwa akan memartaba aka k'ara bincikawa ammah har a lokacin jinin nasa bai yi wani low ba saidai d'an ragewa da yayi kad'an.

Gabad'ayansu hankalinsu ya tashi, nan Dr khalil yakira sultan ahmad da sultan abbas cikin damuwa yasanar da su,

Su dukansu hankalinsu ya tashi, ganin haka yasa yace ammah Alhmdllh na binciko garin da kwararren doctor d'in yake ance min garin Abuja saidai sunce bazasu iya tuna sunansaba ammah yana aiki a babbar asibitin garin, insha Allahu inaji a jikina za'a dace idan akaje chan.

Cike da gamsuwa suka ce insha Allahu zuwa gobe zasusa ayi masu komai sukama hanya dan yanzu ma dare ne kuma sunaso suyi shirye-shirye saisa bazasujeba a lokacin.

Dr khalil yace Allah yasa adace.

Nan sukaje suka sanar ma dada akan batun zuwansu jihar abuja, saida ta jinjina ma lamarin sannan tace toh shikenan Allah yakaimu goben yanzu muzo mutafi gida muyi 'yan shirye-shiryenmu.

Koda suka koma gida kayansu suka shirya nan sultan abbas yaje yayankar musu ticket, su sultana bilkisu da sultana sadiya sunso subi aje dasu dada tace a'a subari sai daga baya sai suzo ammah yanzu in suma sunbi wa za'a barma gidan.

Haka suka hak'ura suka zauna tare da yin fatan Allah yasa adace.

Da dare koda waziri yashigo duba jikin memartaba, rik'o hannunsa memartaba yayi cikin muryarsa da bata fita sosai saboda zafin ciwo yace ga amanar gari da talakkawana nan na damk'a maka.

Rik'e hannunsa waziri yayi kwallah duk tacika masa ido yace na amsa ranka yadad'e Allah yabani ikon cikawa kaikuma Allah yabaka lafiya.

Cikin jin dad'i memartaba yayi murmushi tare da maida idanunsa yalumshe.

Wanshe kare tun dasafe motoci kusan guda goma sukayi layi suna jiran fitowar su memartaba, wajen k'arfe goma suka fito, inda su sultana bilkisu sukayi musu rakiya har airport, inda dandozon mutane suke tsaye ahaka suka shige jirgin mutane na d'ago musu hannu tare da addu'an Allah yaba shugaban nasu lafiya, saida sukaga tashinsu sannan kowa yakoma gida.

*GARIN ABUJA*
Suna isa garin nan sukatarar da motoci da shi kansa sarkin garin tsaye suna jiran isowarsu, kasancewar daman tun jiya sun sanar da shi akan zuwan da zasuyi.

Cikin karamci da jin dad'i suka tarbesu daga nan suka d'unguma wani k'ayataccen gida da aka tanadar masu dan suzauna a ciki, sunso sufara wucewa asibitin ammah sarkin garin yace sufara zuwa su huta sannan.

Haka suka hak'ura saida sukaje suka kimtsa suka ci abinci sannan sukafito suka shiga motocin da sarkin ya aje musu aka jasu zuwa asibitin.

Koda suka isa yanayinsu kawai aka gani da motocin da suke ciki yasa aka gane daga inda suka fito, koda daman sarki kabir ya kirasu ya sanar da su akan zuwan sarkin gazban.

Tarbarsu akayi sosai inda aka wuce da memartaba a amenity, nan suka duba history taken d'in da ke cikin folder d'insa na chan garin, saida suka k'ara yi masa scanning d'in dan tabbatarwa nan kowa yai shuru.

Sultan Ahmad ne yasanar da su abinda Dr Khalil yafad'a musu akan wani mai irin condition d'in da aka ta6a yi ma theatre kuma BP d'insa yayi high.

Jinjina kai MD Dr Muhammad bashir yayi sannan yace shikenan zanje intuntu6i Dr S domin nasan shine kawai zai iya hakan.

Cikin jin dad'i sukayi masa godia nan yatashi yanufi office d'in Dr suhail da baisan wainar da ake toyawaba.

Lokacin da M-D yashiga zaune yatarar da shi yana research a cikin system d'insa.

Nan yamik'a masa hannu suka gaisa, bayan sun gaisa nan yake sanar da shi akan zuwan wasu da irin condition d'in da patient d'in yake ciki.

Shuru Dr suhail yayi na d'an Lokaci sannan yace zan iya ganin file d'in patient d'in?

Nan Dr muhammad bashir yayi waya, ba a wani dad'eba saiga wani Dr hannunsa rik'e da file nan yabud'o yamik'a ma Dr suhail, saida gaban Dr suhail yafad'i ammah yadake yana karanta history taken batare da ya duba sunan me file d'inba.

Saida yagama karantawa nan gabansa yai wani irin fad'uwa lokacin da yaga sign d'in Dr khalil, cikin sauri yajuya bayan folder d'in, baisan lokacin da saki folder d'inba lokacin da yaga sunan da yake jikinsa, nan gabansa yacigaba da dukan ukku-ukku tashin hankali yabayyana k'arara a fuskarsa.

Bai san MD yana masa magana ba saida Dr muhammad bashir yata6osa tare da cewa Dr S lafiya.

Ajiyar zuciya suhail yasafke cike da damuwa yace ba zan iyaba kusami wani yayi.

Kallonsa Dr muhammad bashir yayi cike da damuwa yace ammah ai an tabbatar min da cewa kaine kata6a yi ma wani mai irin condition d'in.

Dafe kansa yarima yayi yace ni ba zan iyaba kakyaleni.

Cikin d'aga murya Dr muhammad bashir yace haba Dr suhail baidace kace haka ba bayan aikinka ne kuma inaji a jikina zaka iya.

Mik'ewa suhail yayi tare da kife system d'insa yace bazan iyaba nafad'a maka!.

Cikin jin haushi shima yamik'e yace zaka iya man, dan haka umurni nabaka a matsayina na shugabanka dole kacika umurni na.

Wani irin kallo suhail yawurga masa yace shugaba kuma?

Murmushi Dr muhammad bashir yayi yace eh shugaba kaga indai kanaso kacigaba da aiki a k'ark'ashina dole sai ka bi umurni na.
Chapter 90 · 0% Book details