← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 102

Sashe 19

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shima murmushin yayi tare da zama kusa da ita, rik'o hannunsa sultana bilkisu tayi cike da kulawa tace daddynsu suhail barka da dawowa muje daga ciki.

sultan Ahmad tallabo fuskarta yayi yace sultana ai banje ko'inaba yau ina fada daga chan naje wajen dada munata shan hira.

Sultana Bilkisu tace Allah sarki, ya wajen memartaba duk kwanan nan bamu gaisa da shiba duk lokacin da zanje gaishesa toh yana chan fada.

sultan Ahmad yace lafiya lou, daman nima sawa yayi aka kirani yayi min magana akan wata walima da aka gayyacesa shine yace ni inwakilcesa inje tunda gobene zaya fita, kuma babu dad'i ace babu Wanda yaje daga wajensa.

Sultana Bilkisu tace tabbas hakane k'ara ko kaine kaje, murmushi sultan yayi yace ai tare da ke zamuje goben, yarima ma zan kirasa domin yashirya muje tare.

Sultana Bilkisu cike da farin ciki tace Allah yakaimu da rai da lafiya.

Sultan Ahmad yace Ameen, taso mushiga daga ciki akwai maganar da nakeson muyi,

dariya Sultana Bilkisu tayi tace kai Abban suhail kawai dai kace mushiga ciki ammah nasan babu wata magana da zamuyi.

wanshekare chan makarantarsu zarah cike take mak'il da mutane, daga wajen islamiyyar aka kafa rumfuna inda daga tsakiya aka tanadi wajen da za'a gudanar da walimar.

Rumfa d'aya aka fitarma da Yarima Suhail, Sultan Ahmed da Sultana bilkisu dukkansu sanye cikin kayan alfarma sai dogarawansu da kuyangi da suka zagayesu, nan aka cika musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,

shi dai yarima suhail tun da yazauna dannar wayarsa kawai yake ko da sau d'aya bai d'ago kai ba, domin tun da yazo yaga anzuba masa ido mata da maza suna kallonsa saisa yajawo wayarsa yashiga dannawa.

inda daga bisani mai gabatar da shiri yafita yafara bayan ankira shugaban makaranta ya bud'e taron da addu'a nan aka fara gabatar da kowa, bayan angama aka fara kiran d'aliban da zasuyi walimar da d'ai-d'ayansu suna fitowa sugabatar da karatu.

Daga chan gefe nahango zarah da k'awarta khairy zaune cikin anko d'insu sunsha dogayen hijab d'insu.

zarah kallon khairy tayi da take ta kalle-kalle tazungurota tace ke wai mekike kallo tun d'azun kin zuba ma waje guda ido?

Murmushi khairy tayi tace wlh wancan yarima din nake kallo ya burgeni sosai kiduba kiga yadda ya hakimce, harararta zarah tayi tace kekuma rashin aikinyi miye abun kallo, ke nifa tunani nake anya zan iya fita inyi karatun nan? wlh jikina yayi sanyi sosai kuma nasan ganin mutanen da nayine.

Dariya khairy tayi tace nifa tsiyata da ke tsoron mutane gareki, kidaure kisa ma ranki babu kowa wajen insha Allahu zakiyi karatunki batare da fargaban komai ba.

zarah murmushi tayi tace nagode sosai khairy Allah dai yasa zan iya.

khairy tace Ameen.
kiran khairy da akayine yasa tamik'e tanufi filin tazauna bisa kujerar da aka tanadar masu nan aka mik'a mata lasifika tafara karatu.

tunda aka kira khairy zarah hankalinta ya tashi sosai nan gabanta yashiga fad'uwa, addu'a tashiga yi cikin zuciyanta ahankali taji nutsuwa tazo mata.

bayan khairy ta gama kiran sunan zarah aka yi, k'in tashi zarah tayi saida aka maimata kiranta sannan tamik'e ahankali tana tafiyarta a nutse, duk wanda yake wajen kallonta yakeyi yanayin yadda take takunta a nutse ta sadda kanta a k'asa ahaka ta isa filin taron tazauna, nan aka mik'o mata lasifika.

amsa tayi nan tad'anyi shuru na d'an minti biyu saida tasaita nutsuwarta sannan tafara karatun cikin muryarta mai dad'in saurare inda take karanta suratul bak'ara daga izif na ukku _Sayak'ulus-sufaha'u minan-nasi ma wallahum ank'iblata humullazi kanu alaiha_...... cike da nutsuwa take karatun, wajen yad'auki tsit kowa saurarenta yakeyi, yarima suhail tunda aka fara bai d'ago yakalli kowaba ammah lokacin da zarah tafara ji yayi yanason ganin wadda ta mallaki muryar, ahankali yad'ago kansa yasafke idonsa akan zarah da take karatu a nitse, kallo d'aya yayi mata yajanye kansa bai k'ara kallontaba har tagama sannan tamik'a lasifikar tare da mik'ewa tabar wajen.

gaba d'aya aka d'auki kabbara daga nan aka cigaba da kiran saura suna fitowa sunayi har aka gama.

bayan angama aka kira wasu daga cikin d'alibai sukayi drama ta larabci, da suka gama aka kira zarah tayi tafsirul alk'ur'ani kowa na wajen ya jinjina mata, da tagama nan aka d'auki kabbara, yarima suhail magana yayi ma iyayensa sannan yasa aka kira masa shugaban makarantar yadamk'a masa kud'i daganan yawuce yashiga motarsa yabar wajen.

daga bisani aka fara raba kyautukan da aka tanadar ma wad'anda sukayi walimar.

ko da akazo kan zarah, Sultana Bilkisu ce akakira tazo tabata itama ta azamata kyauta ta musamman sannan akayi musu pic's.

zarah har da k'wallarta ganin kyautukan da tasamu dan ko na makaranta kusan guda ukku tasamu sannan wanda mutane sukayi mata.

bayan angama raba kyautuka nan akayi d'an bayani sannan aka rufe taro da addu'a aka fara watsewa,

sultana bilkisu kallon d'aya daga cikin kuyanginta tayi tace taje tatafo mata da zarah,

ko da taje tafad'ama zarah zarah bata musaba tabiyota.

tun da suka tafo sultana bilkisu tazuba mata ido ganin yadda take tafiya a nutse har suka iso nan zarah taduk'a ta gaishesu, cike da fara'a Sultan Ahmad da Sultana Bilkisu suka amsa mata, sultana tace 'yanmata ya sunanki?
ahankali tace zarah,
sultana tace nice name, nan sultan Ahmad yad'auko 50k yabata.

cike da ladabi zarah ta amsa tare da yi masu godia sannan tawuce tabar wajen itadai Sultana Bilkisu binta kawai take daga kallo daga bisani suka tashi suka koma gida.

Zarah tattara mutanenta tayi tatafi dasu gisansu tabasu abinci na musamman sannan taraba musu kayan da tatanada, ita kanta ta jinjina ma 'yan gidansu ganin namijin k'ok'arin da sukayi dan sufitar da ita kunya, bayan anci ansha nan aka watse kowa yana murna.

nan zarah tad'auko kyautukan da tasamu taba iyayenta nan aka bud'e ana gani ana murna, kud'in da tasamu tadamk'a ma iyayenta rabi, sauran taraba taba 'yan uwanta rabi tad'auki sauran rabin, nan sukayi ta mata godia,

___________

Sultana Bilkisu ce zaune gefen Sultan Ahmad suna hira chan ta nisa tace Daddyn suhail wlh walimar da mukaje ta burgeni da alama makarantar akwai karatu sosai.

murmushi sultan Ahmad yayi yace nima ta burgeni sosai

sultana bilkisu tace ka san wani abu wlh yarinyarnan ta yi min sosai,

sultan murmushi yayi yace ai naga alama saisa kika aika aka kiramiki ita,

sultana bilkisu d'an guntun murmushi tayi tace inama yarima ya amince ya aureta, wlh da naji dad'i domin daga ganinta kasan ta fito daga gidan mutunci wlh inason yarinyar takasance surukata, kallon sultan Ahmad tayi taga yana ta dannar remote yana canza channel, hannu takai taruk'o remote d'in nan yajuyo yakalleta kwallah duk ta cika mata ido.

sultana bilkisu murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace daddyn suhail nasan sumayya d'iyar d'an uwankace ammah kataimaka ka amince da yarima ya auri zarah domin inaji ita alkhairi ce, ina ji ajikina aurenta zaisa yarima yasamu nutsuwa da kwanciyar hankali.

sultan Ahmad rik'e hannun sultana yayi yace Bilkisu ba wai na k'i bin maganarkibane kawai dai ina tsoron abinda zaije yadawo, kina tunanin suhail zai amince yasota? kina tunanin su memartaba zasu aminta da hakan?

murmushi sultana bilkisu tayi tace insha Allahu zasu amince yarima bamuda matsala da shi domin mu muka haifesa, indai su memartaba sun amince toh komai ya yi daidai, kabani izini inje gidansu yarinyar mugana da iyayenta inyaso daga baya sai muyi tunanin yadda zamu 6ullo ma lamarin.

dogon numfashi sultan Ahmad yaja yace toh tayaya kike tunanin zasu amince batare da ansha wuyaba?

murmushi sultana tayi tace kafara bani izini inje gidansu yarinyar ingana da iyayenta, muji idan zasu amince mana subamu aurenta.

shima sultan murmushi yayi yace nabaki izini Allah dai yashige mana gaba.

cike da jin dad'i sultana tace Ameen.

_*BAYAN SATI 'DAYA*_

Sultana Bilkisu ce naga tayi shiga ta alfarma ta yi kyau sosai bayanta kuyangi biyar ne suka take mata baya, wajen wata dank'areriyar mota daga cikin jerin motocin ukku da take tsakiya naga ta nufa tunkan ta isa aka bud'e mata baya, dan haka tana shiga aka maida aka rufe.

kuyanginta d'ayar motar suka shiga nan aka tada motar, dasauri maigadi yahangame musu k'aton gate d'in suka fita daga Amir palace.

bayan 'yan mintina suka isa islamiyyarsu zarah,

a mota sultana bilkisu tazauna tatura dogari yaje yayi mata magana da shugaban makarantar.

bayan kamar minti ukku sai ga dogarin ya fito bayansa shugaban makarantane yana ta zuba sauri.

duk'awa yayi yana gaishe da sultana bilkisu cike da fara'a ta amsa, nan kuyangi da dogarawa suka d'auka sultana ta amsa gaisuwarka kaima angaisheka,
sannan sultana tace inason k'arin bayani akan d'alibarku mai suna zarah musa.

dasauri d'aya daga cikin dogarawan yace sultana tanason sanin wacece ita, ina ne gidansu.

shugaban makaranta washe baki yayi yace toh toh zarah musa ai gidansu yana chan gaba da nan kad'an.

sultana bilkisu signal tayi ma driver da ido.

driver yace yimin kwatancen gidan yadda zan gane, nan shugaba yayi masa kwatance saida yafahimta sannan yaduk'a yace angama ranki yadad'e

sultana bilkisu kallon kuyanga tayi tace tamik'o mata jakkarta, dasauri kuyanga tamik'o mata nan sultana tad'auko bandir d'in 'yan 1k tamik'a masa tace ga wannan kun k'ara wajen hidima.

jikin shugaba yana kyarma ya amsa tare da duk'awa yana godia nan suma dogarawa suka hau yi ma sultana godia.

sultana izini tabada aka tayar da motar suka kama hanyar gidansu zarah.

ko da suka isa driver tsayawa yayi yatambayi wasu matasa da suke zaune a majalisa, basusha wahalar gane wadda yake nufiba kasancewar kusan kullum zarah ta gabansu take wucewa taje islamiyya kuma tadawo, sukace yak'ara gaba kad'an yashiga hannunsa na dama gida na ukku, nan yayi musu godia sannan sukacigaba da tafiya.

A k'ofar gidansu zarah yayi parking, daidai lokacin malam musa ya dawo gida, ganin dank'areriyar mota k'ofar gidansa yasa mamaki yacikasa dasauri ya ida isowa, daidai lokacin driver yafito daga motar, malam musa sallama yayi mashi yace wani gida kuke nemane?

driver yace eh gidan su wata zarah musa.

malam musa yace toh toh ai nan ne nine mahaifinta.

driver zuwa yayi daga bayan mota yayi knocking d'in glass d'in, jin knocking yasa sultana bilkisu tawane glass d'in.

driver duk'awa yayi yace ranki yadad'e nan ne ga ma mahaifinta nan.
Chapter 19 · 0% Book details