← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 102

Sashe 44

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toh ai bansan wajen da za'ayiba.

Kar kidamu ni nasani sai muje.

Harararta zarah tayi tace keda ba garin kikeba ina kikasan wajen.

Dariya safiya tayi tace Allah dagaske, jiya munje mungano wajen, yanzu dai kiyi sauri kigama nasan anfara yanzu.

Zarah saka sark'a take tace ke banfa tambayi yarima ba.

Chab har ma sai kin tambayesa? Kizo kawai muje ai yasan hidima ake.

Mik'ewa zarah tayi tad'auki veil d'inta tayafa sannan tace bari inzo, bata jira Jin abinda safiya zatace ba tafita.

Ko da ta'isa part d'in yarima itama saida taji wani iri dan rabonta da d'akinsa kusan 5 day's kenan, ganin baya parlour yasa tawuce bedroom nan ma baya nan.

Fitowa tayi takoma part d'inta wayarta tad'auka takirasa har tatsinke bai d'agaba, mamakine yakama zarah nan tak'ara dialing d'in number d'insa sai da takusan tsinkewa sannan yarima yad'aga lokacin yana gidansu shaheed.

Zarah naji ya d'auka bata bari yayi maganaba tace ina wuni?
Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa jin muryar zarah, sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace ina jinki.

Zarah ma wani sanyi taji aranta saida tazauna saman gado sannan tace am dan Allah inaso zanje wajen kamu,

Sai kindawo, yarima yafad'a tare da kashe wayarsa.

Zarah murmushi tayi tare da mik'ewa tsaye, had'a ido sukayi da safiya da take tsaye itama tana murmushi, dariya zarah tayi tace kekuma fa?

Itama safiya dariya tayi tace ina kallon yadda ake waya da habiby, harararta zarah tayi tace nidai wuce muje sarkin 'yan sa ido,
Dariya safiya tayi tace gaskiya zanso inga soyayyarki da prince, na sansa da jin kai ku ma matansa yana yi muku? fad'amin sirrin.

Zarah d'aukar hand bag d'inta tayi da key d'in mota tawuce gaba, bayanta safiya tabi tana mata dariya har suka fita sukaje wajen motar zarah,

Zarah bud'e k'ofar tayi tashiga tazauna saida tayi addu'a sannan tatada motar abun yabata mamaki ganin yadda tatada motar batare da tsoron komai ba saboda wannan ne karo nafarko da tafita da mota dan tun lokacin da aka koya mata rabon da tashigeta, ahankali tajasu suna tafiya suna hira ammah duk hankalinta yana ga driving d'in da take ahaka har suka isa babban hall d'in da aka tanada.

Motocine duk inda kaduba gefe guda tasamu tayi parking sannan suka fito suka shiga daga chan gefe suka samu waje suka zauna daidai lokacin amarya da ango suka iso sunyi gwanin kyau, nan abokan amarya sukaje suka tarbosu aka kaisu har wajen da aka tanadar ma ango da amarya,

Daga gefen amarya sumayya ce zaune tayi kyau sosai itama sai yatsina take tana nuna isa, dan ma bawanda yadamu kowa hidimar gabansa yake,

Shaheed ne yaketa baza ido ammah baiga yarima ba ahankali yaduk'o yace ma rahma kinga yarima baizo ba ko? Bayan munyi da shi shiryawa zaije gida yayi.

Murmushi rahma tayi tace indai Bro ne zai aika wlh,
hmm barni da shi, wayarsa yad'auko yashiga kiran wayar yarima,
Yarima da yake shirin fitowa daga part d'insa ganin kiran Shaheed yasa yayi murmushi sannan yawuce yafita,

Lokacin da ya isa hall d'in abokan amaryane a fili suna ta kwasar rawansu shigowar yarima da abokinsa Dr khalil ne yasa gaba d'ayansu suka zuba masa ido, sanye yake cikin boyel milk colour wanda yasha d'inkin zamani ya yi masa kyau sosai kansa babu hula gashin kansa yasha gyara, nan MC yafara masa kirari
Daga chan gaba suka samu table d'in da ba mutane suka zauna, nan maza sukaita zuwa wajensa fuskar yarima a sake suke gaisawa.

Shaheed ne yayi ma MC magana nan mc yazo inda yarima yake cike da girmamawa yagaishesa sannan yace ranka yadad'e ga wajen da aka tanadar maka chan.

Yarima kallon saman high table yayi sannan yace no nan ma ya yi min, MC har yabud'e baki zaiyi magana nan yarima yad'aga masa hannu cikin sauri yawuce yabar wajen.

A chan nahango sumayya tunda yarima yashigo tafara washe baki dan duk a tunaninta wajenta yarima zaizo yazauna sai taga akasin haka ga 'yan mata sai wucewa suke tagaban su yarima ko Allah yasa sutaya, sumayya da take kallon matan murmushin mugunta tayi tace yau duk wacce tanemi tataya mijina za'ayi bura'uba wajen nan.

A chan 6angaren zarah ma safiya hira take yi mata ammah hankalinta gaba d'aya yana wajen yarima tun lokacin da yashigo, ganin matan da suke bi tagabansa yasa tacika fam ji take kamar taje tashak'esu.

Shidai yarima tunda yazauna bayan sun gama gaisawa da mutane dannar wayarsa yake baisan wainar da ake toyawaba.

nan aka fara kiran babban abokin ango yashiga fili ammah yarima ko motsawa baiyiba ganin haka yasa shaheed yace ma MC akira muhammad abokinsa dan yasan babu wanda ya isa yasa yarima yin abunda baisa kansaba, a k'arshe dai saidai muhammad yakoma madadin yarima.

Bayan yashiga yayi rawa sannan aka ce kowa yafita yanzu filin yakoma na amarya da ango.

Shaheed rik'o hannun rahma yayi suka tashi suka safko daga high table suka shiga tsakiyar fili yana rik'e da ita suke d'an takawa ahankali, sumayya ce tamik'e taje tafara watsa musu kud'i nan abokansu ma suka take mata baya aka dinga watsi da kud'i.

Dr khalil yana murmushi yace ranka yadad'e kataso muje muyi ma aboki da k'anwa lik'i.
Ta6e baki yarima yayi yace ba zan iya shiga wajen chan ba saidai kai idan zakayi.

Haba yarima ammah dai da baka kyautaba, yarima bandir biyu na 'yan 1000 yafiddo ya aje gaban dr khalil yace idan kai zakaje sai kawakilceni.

Zaro ido Dr khalil yayi yace ni kuma? A'a kai dai yafi dacewa kaje da kanta.

Banza yarima yayi masa yacigaba da dannar wayarsa,
Ganin haka yasa Dr khalil yamik'e yatafi dan yasan tunda dai har yarima yafurta a'a toh bawanda zaisashi yace eh, nan yashiga yi musu lik'i yace ma shaheed, yarima ne yawakiltashi yayi masu lik'e madadinsa.

Rahma da shaheed kallon juna sukayi sukai murmushi shaheed yace lallai yarima halinsa sai shi.

Safiya kallon zarah tayi tace Mrs prince muje muyi ma adda rahma lik'i,

A'a Safiya kije nidai ina nan,
Rik'o hannunta tayi tace haba Mrs prince dan Allah kitaso muje kinga ba dad'i.
Zarah ba dan tasoba tatashi suna rik'e da hannunsu suka nufi filin.

Kud'i suka ciro daga cikin jakunansu suka fara yi ma amarya da ango lik'e, zarah ji tayi ta bayanta ana zubo mata kud'i itama, dasauri tawaiwaya wani guy ne tagani fuskarsa d'auke da murmushi,

Harararsa zarah tayi tace dallah malam menene haka?
Fuskarsa d'auke da murmushi yace duk cikin sonkine baby kiban izini ingabatar miki da kaina,

Zarah Zaro ido tayi dasauri takai kallonta ga yarima da shima idanuwansa suna wajensu, ai yarima tunda yaga mutumin yana ma zarah lik'i wani irin abune yaji ya tokare masa zuciya wata irin harara yashiga wurga ma zarah,

Zarah saida 'yan cikinta suka kad'a ganin hararar da yarima yayi mata, cikin sauri tafito daga wajen, mutumin ma binta yayi yana ta mata magana ita kanta batama san me yake cemata ba har takoma mazauninta tazauna.

Shima zama yayi gefenta yace haba baby wai menene haka wulak'ancifa baida dad'i daga na ce ina sonki sai ki6ata rai?

Zarah cike da tashin hankali tace dan girman Allah kakyaleni ni fa matar aurece,
Murmushi saurayin yayi yace nima mijin aurene.

Zarah kallon yarima tayi da yake kallonsu idanuwansa sun kad'a sunyi jawur, shima mutumin kallon inda take kallo yayi dan yaga duk ta ida daburcemasa ganin yarima yasa yayi murmushi yace baby kinsan prince ne?

Zarah mik'ewa tayi cikin d'aga murya tace malam na ce kafita harkata ni matar aurece!
Tana fad'in haka tawuce tanufi inda yarima yake zaune ya cika fam.

Kujerar da take kusa da shi taja tazauna rau-rau tayi da ido kamar zatayi kuka tace wlh bani nace yabi niba kuma nafad'a masa ni matar aurece.

Yarima ta6e baki yayi sannan yace wani abu kikaji na ce?
Girgiza kai zarah tayi.

Cikin nuna rashin damuwa yarima yacigaba da dannar wayarsa yana d'an murmushi, nan ko zuciyansa cike take da bak'in ciki,

Daidai lokacin Dr khalil yadawo yaja kujera yazauna, fuskarsa d'auke da murmushi yace amaryarmu watau kinzo kin tsare mijinki dan kar wata tayi miki k'wace ko?

Murmushi zarah tayi sannan tace ina wuni?

Lafiya lou amarya ai da nahangoki nad'auka irin 'yan matan nan ne suka samu kar6uwa wajen yarima ashe amarya ce tazo takasa tatsare abinta, hakan da kikayi yayi kyau nabaki goyon baya dan na lura da 'yan matan amarya sai rawar kai suke akansa sunaso suyi masa magana ammah ya yi mu k'warjini.

Murmushi kawai zarah tayi.

Yarima kallon Dr khalil yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace Dr gaskiya ni nagaji kazo kawai muwuce.

Haba Dr tun yanzu zamu tafi?
Hmm bakaga time d'in sallah ya kusaba? Yarima na fad'in haka yamik'e tare da cewa idan ba zaka tafiba toh ni na tafi dan ko 1 minute ba zan k'araba anan, kallon zarah yayi yace kitashi mutafi.

Zarah ma kallonsa tayi tace da mota nazo, yarima mik'ama Dr khalil key d'in motarsa yayi yace gashi katafo da ita,

Kar6a Dr khalil yayi tare da mik'ewa yace nima ai bazan zaunaba.
Yarima kallon zarah yayi yace muje.

Zarah mik'ewa tayi tabi bayansa, wajen motarta suka nufa nan tamik'a masa key d'in.

Tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi, yarima gudu kawai yake da motar, ahankali zarah tajuyo takallesa gani tayi ya wani had'e rai babu alamun fara'a a fuskarsa, janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tace kai dai kasani.

Suna isa gida yana yin parking key d'in motar ya aje mata sannan yabud'e yafita batare da yayi mata magana ba, itama zarah bud'ewa tayi tafita tabi bayansa tana shiga direct part d'inta tawuce.

Saman cushin tazauna tare da jan numfashi tace Allah ya taimakeni da mutumin chan ya ja min bala'i wajen yarima, chan kuma cikin zuciyanta tace bayan basonki yakeba bai damu da ke ba to akan me zaiyi kishinki? Jinjina kai tayi k'wallah duk ta cika mata ido tace hakane kuma, wayarta tad'auka takira safiya nan tashaida mata da ta tafi gida.
Chapter 44 · 0% Book details