← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 102

Sashe 31

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan angama su yaya rauda suka raba kayayyakin da suka tanada zasuba mutane, zarah dai mamakine yacikata cikin ranta tace nasan zaku aika tunda dai khairy tamatsa sai anyi wa'azi, chan kuma sai tayi murmushi cikin ranta ta ji dad'in hakan.

nan mutane suka watse kowa yana fad'in albarkacin bakinsa.

_*RANA BATA K'ARYA SAIDAI UWAR 'DIYA TAJI KUNYA*_

A yau juma'a masallacin juma'a da yake anguwarsu zarah cike yake da jama'a dan saida aka rasa masaka tsinke saboda yawan mutane anguwar cika tayi sosai dan har memartaba saida yahallara wajen.

Bayan anfito masallacine aka d'aura auren *Yarima Suhail Ahmad Umar* da *amaryarsa Fatima Zarah Musa* akan sadaki naira dubu d'ari,

a chan tsakiyar taron nahango ango da shaheed, ango yasha kyau har ya gaji sanye yake cikin shaddarsa fara wadda tasha aiki da bak'in zare, hularsa da takalmansa duka jajayene nan mutane sukaita zuwa suna gaisawa tare da yi masa Allah yasa alkhairi shidai yarima yana murmushi ne kawai dan saboda memartaba kawai ya amince yazo d'aurin auren.

takeaway aka shiga rabama mutane kowa yaci yasha aka watse cike da farin cikin auren nan masu tsegumi sunayi masu murna nayi.

gidan su zarah cike yake da 'yan uwa da abokan arzik'i abbah yayi k'ok'ari sosai wajen ganin anyi abinci na azo gani wanda kowa zaici yasan yaci hatta naman kaji sunyi kuka sosai a ranar.

A chan tsakiyar gadon mama nahango zarah zaune ta ci kwalliya ta had'e cikin less d'inta pink colour mai ratsin blue head ne blue a saman kanta tayi kyau sosai sai sharar k'wallah take gefenta su yaya rauda ne da Khairy suna lallashinta dan ita gani take duk wasane auren saida tajiyo hayaniyar mutane suna gud'a ana and'aura aure sannan ta tabbatar dagaskene.

mama ce tashigo d'akin taganta cikin wannan halin tace haba zarah miye abun kuka hak'uri zakayi domin shi aure haka yake.

zarah cigaba tayi da sharar k'wallarta ganin haka yasa mama taficce tana fad'a,

zarah da take kuka jin sallamar mutane da tayi yasa tashare fuskarta cike da mamaki take kallon jama'a buya guda da sukazo, nima kaina natsorata saida najawo My Hafnan muka koma gefe nace kin gane mutanen nan da sukazo?

hafnan harararsu tashiga yi tace hmm nagane wasu man wacchan tawagar masu pink d'in atamfa 'yan group d'in *yarima suhail fan's* ne, sai tamurga baki tare dagwada masu anko d'in blue tace wannan kuma na *Hibbatullah* fan's ne, sannan sai masu red d'in anko *Intelligent writer's fan's* ne, sai kuma tanuna wasu tace masu green *Nazir* fan's ne, masu coffee kuma *Aufana true fan's* da *sainah true fan's*, Masu navy blue kuma *Zaynav mtz fan's* sannan *Mummyn khalil fan's*, *Surbajo fan's*, *Sadnaf true fan's* ke da dai sauransu.

rik'e baki nayi nace chab nashiga ukku my hafnan yanzu saboda Allah duk wa yagayyaci wad'annan uwayen mutanen? murya muka jiyo daga bayanmu ance yoh wa fa yagayyacesu k'wak'wace takawosu kawai, juyawar da zanyi sai ganin My blood sis aufana da mummy sainah ummun meenal nayi, dafe kai nayi nace nashiga ukku kukuma wace k'wak'war takawoku? My blood hararata tayi tace yoh mu da tun d'azun muna nan damu akaci aka sha, su Mummyn afrah, meenah abbah, k'anwarki janaf, haleemah H.A.S, sis Aysha ke dama sauran intelligent writer's duk suna nan yanzu haka sunje kar6o mana nama kinsan mummy zill da 'yar mutan zariya basa barin nama,

had'e fuska nayi nace toh wlh wannan abun kunyar ba da sis nerja'art ba dole kowa yazo yakama gabansa babu wanda zai zauna, nan nakorasu nace muje inda muka fito nima nafasa zaman, kallon zarah sukayi sukace toh gimbiyarmu sai mun dawo wani taron,

murmushi kawai zarah tayi bayan sun fita takalli yaya rauda tace wad'annan masoyanmune fa nasan basu ganekuba saisa, yaya rauda dariya tayi tace haba saisa naga rawar kansu yayi yawa saikace Maman sadiq da mrs dawud😜 ke wani abun ma sai ummie adnan da mugirat ammah basukai mummyn khadija ba, aini naji dad'i da aka korasu.

Bayan sallar magrib wanka akasa zarah tayo bayan ta fito hafnan nd Aufana makeover ne suka zauna suna shirya amarya, kwalliya sukayi mata sosai wadda ita kanta zarah da takalli madubi saida tayaba kanta, atamfa tasa riga da skirt sun mata cif sannan aka murza mata d'aurin kallabi inda kyaun nata yak'ara bayyana.

bayan sallar isha'i aka aika da motoci biyu d'aya wadda amarya zata shiga, d'aya kuma na kuyangin da sukaje sutafo da itane saboda cewa akayi babu wanda za'aje da shi kai amarya, amarya kawai za'a tafi da ita.

wajen su mama aka kai zarah sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki duk dauriyar mama kasa daurewa tayi saida tayi kwallah, zarah tana kuka aka rik'ota aka fito da ita.

'yan unguwa sunji haushi sosai domin kowa yaci burin yaje yagane ma idonsa, wasu kuma burinsu suje suga sarki, wasu kuma suje suga yarima, wasu kuma burinsu suje sugano kwakwaf, Aysha kuka tayi sosai dan taso tabiyo 'yar auwartata, dole suka hak'ura suna gani aka fito da amarya an nad'eta da lifaya, jakadiya ce rik'e da zarah sai kuyangi biyu da suka take musu baya ahaka aka shigar da ita mota tana kuka.

nan 'yan unguwa wasu sukaita tsogumi ai iyayen zarah saboda son abun duniya suka siyar da d'iyarsu babu wanda yasan inda za'a kaita

haka akaita tafiya ita dai zarah ji take kamar ba a mota takeba saboda wani irin k'amshi mai dad'i da yake ratsata da d'in motar, bata d'ago kantaba har alokacin hawaye take tana tausayin kanta da takaicin iyayenta da suka amince suka aura mata wanda bata so.

ko da aka isa da zarah gidan sarautar tana ji bushe-bushe suna ta tashi batasan lokacin da aka tsayaba saidai gani tayi anbud'e mata k'ofa

nan jakkadiya tace ranki yadad'e kifito anzo, zarah ahankali tasafko k'afarta daga motar har a lokacin fuskarta na a rufe dasauri bayi da kuyangi suka zube k'asa suna k'awar gaisuwa angaishe da gimbiya angaishe da tauraruwar mata takawarki lafiya gimbiya, zarah duk jin abun tayi wani iri saboda bata saba jin hakaba sai a film tunda ita ba zuwa gidan sarauta takeyi ba ammah yau itace ake gaishewa ta bangirma.

muryar jakadiya tajiyo tana cewa ranki yadad'e muje mana, jakkadiya da wata kuyanga suka rik'eta inda sauran kuyangi da bayi suka zagayesu aka sa su tsaka ahaka ake tafiyar har aka isa turakar dada, duk mutanen da ke wajen taga sun duk'a suna kwasar gaisuwa a wajen dada, zarah har zata duk'a dada tace a'a akawota nan tazauna.

jakkadiya takamota takaita har kusa da kujerar da dada take zaune, zarah dasauri tazauna k'asa har a lokacin fuskarta a kulle take kyarma kawai take domin gani take kamar a mafarki.

nan duk sauran kuyangi da bayi suka bar d'akin, d'akin yad'auki shuru daga dada sai zarah, dada ce tayi gyaran murya tace barkanki da zuwa wannan gida namu mai albarka fatanmu kizauna da kowa lafiya, domin kinsan gidan sarauta sai anji ank'i ji, agani ak'i gani, kizauna da kishiyarki lafiya indai kikabi sumayya sau da k'afa toh zaku zauna lafiya domin ita batada matsala ko da kema da alama daga ganinki ba zakiyi matsalaba.

itadai zarah sauraren dada take batace ufanba har a lokacin kanta na sunkuye a k'asa ahaka har dada tagama nasiharta sannan takira jakadiya domin tazo tatafi da zarah 6angarenta, zarah duk'awatayi cikin muryarta da tadashe tace nagode sosai insha Allahu ba zan kawo muku matsalaba zan zauna da kowa lafiya,

dada taji dad'in lafazin zarah a karo na farko da taji ta d'an burgeta domin taga da alamu zatayi hankali.

dada tace zaku iya tafiya, jakadiya tace to ranki yadad'e muje,

zarah mik'ewa tayi suka fito nan duk sauran kuyangi suka take musu baya suka nufi part d'inta,

bedroom d'inta aka wuce da ita aka zaunar da ita bakin gado sannan jakkadiya tace ma kuyangi sutafi nan kuyangi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen zarah itadai zarah tana jinsu batace komaiba daganan suka mik'e tare da cewa afito lafiya gimbiya, daganan suka fita daga d'akin.

nan jakkadiya tashiga toilet tahad'a mata ruwan wanka wanda yasha turaruka sannan jakkadiya tafito tad'auko towel tarussuna ta aje sannan tace ranki yadad'e ruwan wankanki sun had'u zaki iya shiga,

zarah tace a'a ba ma sai nayi wankaba,

jakadiya tace kigafarceni ya shugabata umurnin sultana ne nake cikawa kuma wannan tsarin gidan nan ne,

zarah tana jin haka tamik'e tare da janye lullu6inta, gabantane yashiga fad'uwa tana bin d'akin da kallo cike da mamakin tsaruwarsa cikin ranta tafara kokwanto anya wannan nawane?

muryar jakkadiya taji tanacewa ranki yadad'e akwai abinda zan iya taimaka miki da shi?

zarah d'aukar towel d'in tayi tare da cewa bana buk'atar komai daga nan jakkadiya tanufi 6angaren wardrobe d'in zarah,

nan zarah tacire kayanta taje tashiga toilet ko da tashiga tsayawa tayi tana k'arema tsarin toilet d'in kallo cikin ranta tace lallai idan kana duniya zakayi kallo, tsoron Allah ne taji ya k'ara ratsamata zuciya nan tashiga cikin ruwan da yayi mata dad'i dan saida tadad'e tana wanka sannan tafito.

ko da tafito jakkadiyace da wata kuyanga tsugunne a k'asa ganinta yasa suka mike cikin sauri tare da cewa takawarki lafiya gimbiya.

zarah wajen dressing mirror tanufa nan suka bi bayanta suka mik'a mata mai hadad'e mai k'amshi tashafa waccan kuyangar ce tayi mata 'yar simple makeup sannan kayan baccine masu kyau da tsada jakadiya tafito mata dasu,

doguwar rigace silk har k'asa mai hannun vest nan zarah tasaka, su jakkadiya suka dinga yi mata 6arin turaruka a jiki masu sanyin k'amshi, suka tufke mata gashinta da rubon Sannan aka sakamata had'ad'ar alkyabbar da aka tanada.

ko ni kaina da naga zarah saida nace wow masha Allah kamar ba zaran da nasani bace saboda kyaun da tayi

su kansu su jakkadiya saida sukayita santinta suna yaba kyaun da tayi itadai murmushi kawai take nan ma suka k'ara fesheta da turaruka, sannan sukace ranki yadad'e idan ba wani abu da za'ayi zamu iya tafiya.

zarah fuskarta d'auke da mamaki tace ina zamuje?

jakkadiya kanta a sunkuye yake cike da girmamawa tace d'akin yarima zamu rakaki.

zarah saida gabanta yafad'i jin an ambaci yarima dakewa tayi tace da munyi zamanmu a nan.

jakkadiya tace a'a ranki yadad'e ai tsarin sarautar gidan nan ne yau d'akin mijinki zaki kwana.
Chapter 31 · 0% Book details