← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 102

Sashe 20

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sultana bilkisu kallon mahaifin zarah tayi dasauri shima yaduk'a yagaisheta domin yanayinta kawai da yagani da dogarawan da suke tare da ita yasa yagane daga babban gida take.

sultana bilkisu cike da fara'a ta amsa.

malam musa yace ranki yadad'e ko dai wata zarah d'in ce kuke nema?

murmushi sultana tayi tace zarah dai taka, munaso kayi mana izini mushiga ciki sai mutattauna abinda yake tafe da ni.

malam musa jikinsa yana 6ari yace bismillah kushigo,
dasauri dogarawa sukazo suka bud'e mata murfin motar tafito nan kuyangi suka take mata baya, akabar dogarawa tsaye wajen motocinsu,

malam musa yana gaba har cikin gida, suna shiga yafara k'walama mama kira yana zainabu! zainabu!!

dasauri mama tafito daga d'aki tana malam lafiya? ganinsa tare da wasu mata yasa tayi tsaye tana malam bak'i mukayi?

malam musa yace kinyi wani tsaye kiyi sauri kid'auko musu tabarma mana, ina yarannan suke? .

mama tace basunan sunje gidan kitso sannan takoma d'aki tad'auko sabuwar tabarma tazo ta shimfid'a tace bismillanku.

sultana zuwa tayi zata zauna dasauri kuyanginta suka k'ara kakkafe tabarmar suna cewa ranki yadad'e azauna lafiya sarauniya, bayan ta zauna nan kuyanginta sukayi tsaye gefenta.

ganin haka yasa su mama suka ida fahimtar koma daga ina wannan tafito toh motar wani babbace, Dan haka mama tazo taduk'a tagaisheta.

fuskar sultana d'auke da murmushi ta amsa, nan kuyangi suka d'auka 'sultana ta amsa gaisuwarki kema angaisheki'

malam musa jikinsa yana 6ari yace bari inje insamo musu ruwa susha.

sultana murmushi tayi tace kabarsa nagode kazauna kawai muyi magana akan abinda yakawoni.

dasauri mama taje tad'auko wata tabarmar tashimfid'a ita da malam musa suka zauna.

sultana kallon kuyanginta tayi tace mero kubamu waje zamuyi magana.

dasauri duk suka zube sukace angaisheki sultana atashi lafiya sannan suka tashi suka bar wajen.

sultana kallonta tamaida ga su malam musa tace kune iyayen zarah ko?

malam musa da mama sukace eh ranki yadad'e .

sultana bilkisu tace toh Alhmdllh ni matace ga d'an sarkin garin nan, agaskiya ba zan 6oye mukuba tun lokacin da mukaga d'iyarku wajen walimarsu da sukayi a islamiyya nan muka ganta kuma mun yaba da halinta da tarbiyarta dan haka muke neman ma d'anmu *yarima suhail* aurenta.

ba mamaba hatta shi kansa malam musa ya firgita a tsorace suka d'ago kai suka kalli juna jin an anbaci yarima suhail Wanda suke jin sunansa a bakin mutane, dasauri suka maida kallonsu ga sultana bilkisu,
atare suka had'a baki sukace zarah ta auri yarima suhail?

sultana gyad'a kai tayi tace indai kun amince zaku bamu aurenta.

shuru sukayi na d'an lokaci sannan malam musa yace ranki yadad'e kiyi hak'uri gaskiya ba zamu iya amincema buk'atarkiba.......

_*Comments d'inku shine k'warin gwiwana Indai babu more comments toh hakan zai tabbatar min da baku tare da ni dan haka nima zan dakata da rubutawa daga wannan page d'in, dan haka muje zuwa*_

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Jinjina agareki My Dala inaso kisani akoda yaushe ina ji dake😘*_

_Sak'on gaisuwa agareka *Mu'az* a duk inda ka kasance wannan *page* d'in mallakinkane kayi yadda kakeso da shi nagode sosai da kulawa_

page 1⃣5⃣

Malam musa yace gaskiya ba zamu iya amincewa da buk'atarkiba domin kunfi k'arfinmu ku masu kud'ine mu kuma talakkawane, kinga ba zaiyuwuba ace masu sarauta kamarku sun had'a zuri'a da muba.

sultana bilkisu tace kar kudamu ai anzama d'aya kar kumance da talakka da maikud'i duk Allah ne ya haliccesu kuma shi yakeba Wanda yaso yahana wanda yaso, jahiline kawai zai iya gudun talakka, ammah duk wanda yasan abinda yakeyi toh ba zai gujesaba domin yasan wake azurtawa da hanawa, a lokaci guda Allah zai iya maida talakka mawadaci sannan yamaida mawadaci talakka, toh tayaya kuke tunanin zamu gujeku? saidai idan kuna tunanin d'iyarkune kar mucutar da itane, insha Allahu ba zamu nuna banbanciba zamu kula da ita kamar yadda zamu kula da 'ya'yanmu da muka haifa a cikinmu, burina kutaimaka ku amince kubamu auren zarah.
mu musulmaine munsan girman alk'awali dan haka nayi muku alk'awali zamu kula da ita bakin gwalgwado.

gaba d'ayansu shuru sukayi suna saurarenta, yanayin yadda sultana tayi maganar yasa suka yadda da ita, kuma sunsan adalci da kirki irin na sarkin garin indai shi zuri'arsa suka biyo mutunci toh ba zasu samu matsalaba.

chan Abbah yakalli mama yace tataso suje suyi shawara dan haka mama tatashi suka shiga d'aki suka bar sultana zaune wajen tana dannar waya,

a chan d'akin abbah yakalli mama yace zainabu abun nan yad'aure min kai kina ganin zai yuwu mubasu d'iyarmu? nifa ina tsoron su wulak'anta mana ita domin su masu arzikine mukuma talakkawa.

mama jinjina kai tayi tace nima abinda nake tunani kenan gaskiya kar mubasu domin bamusan yadda gaba zata kasanceba, ace duk matan garin nan surasa wadda zasuce sai zarah, so suke sujamana zagi da surutun mutanen gari.

malam musa jinjina kai yayi yace ni bama dai wannan ba kiduba kiga bayanin da tayi mana tabbas daga gani tasan daraja da mutuncin mutane daga jin kalamanta, ta ni bandamu da surutan mutaneba saidai inajin tsoron su wulak'antamin zarah domin yarima suhail ya wuce ajin zarah wajen komai, ammah kuma ina jin nauyinta bana iya hanasu zarah.

ummah tace hakane malam ko dan matsayin da darajar da ke garesu kaduba kaga bata nuna mana k'yamaba nima wlh ta wajena babu matsala domin halayyarta ta yi min kuma nasan indai d'antane takeson hadawa da zarah toh bamuda matsala saboda da alama zai kasance mai irin kyawawan halinsu saidai ba a nan takeba matsalar tana wajen zarah.

malam musa jinjina kai yayi yace tabbas zarah itace matsalar ina tsoron taki amincewa saidai nasan zarah akwai biyayya zata iya bin ra'ayinmu ko da ace bataso, dan haka idan kinga hakan ba matsala toh muje mu amsa mata,

mama tace toh nan tabi bayan malam musa suka fito, yadda sukabar sultana haka suka dawo suka taddata, suka koma mazauninsu suka zauna.

kallonsu sultana tayi tace dafatan kun yanke hukuncin da kuke ganin ya dace wlh Indai baku aminceba zamu iya hak'ura domin ta yuwu zarah ba matarsa bace.

malam musa yace ranki yadad'e mun ma amince domin darajarki da martabanku yasa bama iya ji zamu iya hanaku zarah fatanmu dai zaku rik'eta kukular mana da ita tsakani ga Allah.

sultana bilkisu tunda taji ya ambaci sun amince wani irin farinciki yakamata kasa 6oye murnarta tayi tace gaskiya naji dad'i kuma nagode sosai insha Allahu zamu kular muku da ita, sannan zanje muyi magana da iyayensa koma dai mekenan zamuyi waya, takalli mama tace bani number d'in wayanki nan mama takaranto mata sannan sultana bilkisu takira kuyanginta suka dawo, fuskarta d'auke da fara'a tace naso ace naga d'iyartawa ammah tunda batanan zamu had'u wani lokacin.

mama tace a'a ranki yadad'e ai sai inje inkirata tana chan bayan layin nan sunje kitso, sultana tace a'a kibarta kawai zamu gaisa wani lokacin, kar6ar jakkarta tayi a wajen d'aya daga cikin kuyanginta tazaro 100k ta aje musu sannan tamik'e tace bari inwuce.

Abbah yace a'a kibar kud'inki mu dan Allah mukayi.

sultana murmushi tayi tace karkadamu nima dan Allah nayi domin babu kud'in da zasu iya sayan zarah, kuyi hak'uri kyautace.

Abbah da mama sukayi godia, har wajen mota suka rakata saida sukaga tafiyarta sannan suka dawo cike da farin ciki.

Mama kallon Abbah tayi tace malam toh yanzu ya kake ganin za'ayi idan zarah tadawo? kana tunanin zata amince?

Abbah murmushi yayi yace kar kidamu kibar komai a hannuna.

mama tace toh Allah yashige mana gaba.
Abbah yace Ameen.

daidai lokacin su zarah suka shigo gidan suna dariya, mama da Abbah kallon juna sukayi sannan suka maida kallonsu ga 'ya'yan nasu suna murmushi, su zarah isowa sukayi tare da duk'awa sukayi ma iyayennasu barka da rana, mama tace 'yan albarka har kunyo kitson?

sukace eh mama, gaba d'ayansu suka mik'e zasubar wajen, abbah yace kudawo kuzauna munason magana da ku.

A tare suka zauna suna jiran Jin abinda iyayennasu zasu ce, Abbah ne yayi gyaran murya yace duk inda kuka tsinci kanku kukasance masu dogaro ga Allah, kurik'e gaskiya sannan duk mijin da Allah yaza6a muku kukar6esa hannu biyu domin ita rayuwa ta yuwu abinda mukeso ba alkhairi bane wanda bamuso zai iya kasancewa shine mafi alkhairi, gaba d'ayansu shuru sukayi suna sauraren mahaifin nasu da suka kasa gane dalilinsa nayi musu wannan nasihar,

mamace tacigaba da cewa ku 'ya'ya matane ba zaku dauwama a k'ark'ashinmu ba wata rana dole kubarmu kukoma k'ark'ashin mijinku a kullum addu'anmu Allah yahad'aku da mazaje nagari kuyi aure.

Abbah yace tabbas zancenki hakane zainabu sannan yamaida kallonsa ga zarah yace saidai kuyi hak'uri domin munyi wani karambani a matsayinmu na iyayenku munyi abinda muke gani kamar daidaine saidai a wajenku bansan yadda zaku d'aukesaba musammanma ke zarah!

gaba d'ayansu mamakine yacikasu sun ma rasa gane inda zancen abbah yanufa, zarah ce ta nisa tace Abbah bana tunanin akwai abinda zakuyimin yazama laifi wlh duk hukuncin da kuka d'auka kaina daidaine domin kun cancanci hakan.

Abbah dogon numfashi yaja yace hakane zarah ammah kiyi hak'uri da maganar da zata fito daga bakina, zarah munyi miki miji.

zarah a razane tad'ago kai takalli abbah muryanta yana kyarma tace abbah miji kuma? Aysha da Rauda sukace miji!!!

Abbah gyad'a kai yayi cikin rashin damuwa yace tabbas miji kuma nasan zaki sosa kema bakowa bane face d'an sarkin garinnan *Yarima Suhail*

zarah a tsorace tamik'e tsaye tare da ja baya tace abbah aura min wani zakayi ba malam bello ba?

Abbah yace zarah kidawo kuzauna inyi muku bayanin komai,

zarah hawaye tafara tare da dawowa tazauna, nan abbah da mama suka kwashe labarin zuwan sultana bilkisu da yadda sukayi da ita babu abinda suka 6oye masu hatta kud'in da tabasu.

Zarah fashewa tayi da kuka tace Abbah kuyi hak'uri wlh bana sonsa shima nasan ba zai soniba dan Allah kubarni in auri wanda nakeso wlh malam bello shine za6ina.
Chapter 20 · 0% Book details