← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 102

Sashe 60

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zarah cikin Jin kunya tace bismillah ummah kizauna.
Zama sultana sadiya tayi har a lokacin fuskarta tana kan zarah, cike da jin kunya zarah tazauna k'asa tace ummah ina wuni?
Lafiya lou dafatan kina Lafiya, ya k'arfin jikin naki.
Cikin jin kunya zarah tace ummah ai na warke,
toh masha Allah, Allah yak'ara sauk'i, ai ba a fad'amin bakida lafiya ba sai jiya naji wajen dada.

Zarah shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta tana murmushi, ahankali tamik'e tace ummah bari inkawo miki ruwa.
Murmushi sultana sadiya tayi tace kibarsa kawai saikace wata bak'uwa.

Wucewa zarah tayi tace ummah bari dai inkawo miki, sultana sadiya binta tayi da wani irin kallo har tashige kitchen, ahankali tafurta tabbas yarinyar nan cikine da ita.

Zarah ko da tashiga kitchen dafe k'irjinta tayi tare da safke ajiyar zuciya dan ta tsorata sosai da fari da taga ta shigo sai daga baya da taga ba da wata manufar tazoba sannan taji dad'i, ahankali tafurta Allah yasa umman sumayya ta shiryu.

Nan tacigaba da had'a mata kayan marmari da drinks kala-kala a saman tray ta d'aura tad'auko tafito.
A gaban sultana sadiya ta aje tace ummah kifara da wannan kafin ingirka miki abinci.

Murmushi sultana sadiya tayi tace a'a zarah keda bakida lafiya kibarsa kawai dan ni nan a k'oshe nake,
Zarah ruwan inibi tatsiyaya a cup tamik'a mata tace ummah toh ko yayane kisa albarka.

Kar6a sultana sadiya tayi tana murmushi tace nagode zarah, kur6a d'aya tayi ta aje sannan tace zarah kiyi hak'uri akan abinda nayi miki wlh sai daga baya nagane hakan ba daidai bane,

Murmushi zarah tayi tare da d'ago kai takalleta tace ummah bakimin komai ba wlh dan ke matsayin uwa kike a wajena.

Nagode sosai zarah, Allah yaimiki Albarka, Allah yasafkeki lafiya.

Zarah kasa amsa mata tayi saboda wata irin kunya da tarufeta.

Mik'ewa sultana sadiya tayi tace toh ni zan wuce.

Ummah tun yanzu?

Haba zarah me zan zauna inyi ni da nake matsayin suruka, yanzu dai indai kinsan kina buk'atar wani abu kidinga aikawa ana fad'amin insha Allahu ni kuma zan samo miki koma menene, yanzu haka ga zogale chan nasa ana dafawa na baro sun kusan gamawa, Indai angama zan aiko miki da ita nasan zakiso cinta..

Murmushi zarah tayi cikin jin dad'i tace toh ummah nagode.

Haba minene abun godia ai keda sumayya duk d'aya nad'aukeku, zansa a ma k'wad'a miki da k'uli-kul'i dan akwai wata baiwata data iya irin wad'annan k'wad'on masu dad'i ita zansa tayi miki.

Zarah duk'ar dakanta tayi tace nagode sosai ummah, Allah yak'ara girma da d'aukaka.

Sultana sadiya tace Ameen sai na aikon, tana fad'in haka tawuce nan zarah tarakata har wajen part d'inta tare da k'ara yi mata godia.

Sultana sadiya tace bakomai, nan tawuce cike da farin ciki dan ta san tarkonta ya kama kurciya...

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah my dota *hafnan* Ina tayaki murnar kammala novel d'inki maisuna *FATALWAR MIJINA* hak'ik'a kin zuba basira sannan kin koyar da darasi a cikinsa gaskiya salon novel d'in ya burgeni, Allah yabaki ladar abinda kika fad'a daidai kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, ur mommo love you more😘_

_~Masoya sak'onku yana isowa agareni ina godia sosai Allah yabar k'auna, mutanen katsina ku ma sak'onku ya iso agareni nagode sosai nima ina gaisheku~_

*PAGE* 4⃣9⃣

Haka sultana sadiya ta isa 6angarensu farin ciki fal a zuciyanta, cikin sa'a ko da ta isa tatarar angama dafa zogalen, nan tasa wata baiwarta tak'wad'a mata, sannan tawuce cikin bedroom d'inta inda tad'auko k'ullin maganin da tasa aka samo mata.

Bayan an gama kwad'on a parlour aka kawo mata cike da jin dad'i tabud'e taduba saida tad'ibi nata sannan tazuba ma sauran maganin tamotse yadda ba za'a ganeba sannan tajuye a cikin wata kula mai kyau, murmushin mugunta tayi tace zarah kinyi babban kuskure da kikayi saurin yarda da ni dan bakisan wacece ni ba,

Sallamar da akayine daga wajen d'akin yasa ta amsa saida tagama abinda take sannan tabada izinin ashigo, jakadiya ce tashigo cikin sauri taduk'a tagaishe da sultana sadiya cike da girmamawa.

Sultana sadiya kallonta tayi a wulak'ance saida tayamutsa fuska sannan ta amsa.

Jakadiya k'ara duk'ar da kanta tayi k'asa tace ranki yadad'e daman dada ce ta aikoni wajenki.

Shuru sultana sadiya tayi na d'an lokaci sannan tace ina saurarenki.

Jakadiya ledar da take hannunta ta mik'a mata tace gashi tace akawo miki.

Kar6a sultana tayi tabud'e batasan lokacin da Murmushi yakubce mataba ganin wata had'ad'ar sark'a da dada ta aiko mata da shi, cikin sakin fuska sultana sadiya tace kice mata nagode.

K'ara duk'awa jakadiya tayi tace Allah yaja da ranki nabarki lafiya,

Gyad'a mata kai kawai sultana sadiya tayi,
Har jakadiya ta wuce zata fita sultana sadiya takirata.

Cikin sauri jakadiya tadawo taduk'a tace ranki yadad'e na amsa kiranki.

Sultana mik'a mata kular tayi tace gashi kikai ma gimbiya zarah.
Cikin sauri jakadiya takar6a cike da mamaki tace ranki yadad'e gimbiya zarah ko gimbiya sumayya?

Harara sultana tawurga mata cikin fad'a tace zarah nace miki ko sumayya?

Jikin jakadiya yana rawa tace kigafarce ranki yadad'e gimbiya zarah zan kaimawa Allah yahuci zuciyanki.

K'ofa sultana sadiya tanuna mata, cikin sauri jakadiya tad'auki kulan tafito.

A chan 6angaren zarah bayan sultana sadiya ta tafi komawa tayi saman cushin tazauna tare da dafe kanta mamakin sultana sadiya duk ya kamata dan yau ne karo nafarko da tafara ganin fara'arta, tunowa tayi da duk wulak'ancin da take yi mata a baya, murmushi zarah tayi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa.

Jakadiya tafiya take ammah mamakine yacikata ahankali take furta miye had'in sultana sadiya da gimbiya zarah? Miyasa batace inkai ma gimbiya sumayya ba sai zarah? Anya ba wata k'ullalliya da matarnan take shiryawa?
Bari dai inje sai inji daga bakin gimbiya.

Lokacin da ta isa a parlour tasamu zarah zaune tana shan fruit salad, cike da girmamawa taduk'a tagaishe da zarah, cikin sakin fuska zarah ma tagaisheta tare da tambayarta su dada.

Murmushi Jakadiya tayi tace suna lafiya sannan tamik'a mata kular tace ranki yadad'e gashi daga sultana sadiya tace inkawo miki.

Murmushi zarah tayi batare da ta kar6a ba tace bud'e mugani.

Cikin sauri Jakadiya tabud'e, zarah lek'awa tayi tace ba laifi kwad'on ya min kyau saidai ba zan iya ciba.

Murmushi Jakadiya tayi tace ranki yadad'e wai miye tsakaninku dan nayi mamakin ganin ta bada kwad'o akawo miki.

Itama zarah murmushi tayi sannan takwashe komai tafad'a ma Jakadiya.

Jinjina kai Jakadiya tayi tace duk tak'are cikinki ne da taji ance kina da shi takeso taga bayansa.

Ta6e baki zarah tayi tace koma mekenen ta Allah ba tataba dan ni nafi k'arfinsu, ban yarda da kwad'on ba aje kawai azubar da shi a 6oye inda wani ba zai ganiba bare yaci.

Jakadiya tace angama ranki yadad'e, Allah yatsare mana ke.

Zarah jingine kanta tayi da kujera nan jakadiya tamik'e tafita tabar d'akin.

Bayan fitarta Zarah mik'ewa tayi tashiga bedroom d'inta, saman gadonta takwanta tana mamakin halin sumayya da mahaifiyarta, ji take da ace sumayya zata amince suyi zaman lafiya da zatayi farin ciki da hakan dan ita da zuciya d'aya take zaune da ita.

Tunowa tayi da gogon nata nan tayi murmushi dan ita kanta ta san tayi missing d'insa rabonta da shi kusan 3 day's kenan, wayanta tad'auko talalubo number d'insa, lokacin yarima yana cikin duba patients d'insa ganin me kiransa yasa yamaida wayan silent yacigaba da aikinsa dan lokacin gab yake da yatashi yakoma gida.

Zarah ganin ta tsinke baiyi picking ba yasa ta aje wayar tare da maida idanuwanta tarufe dan tasamu tad'anyi bacci, ammah gefe guda ji take tana buk'atar son cin zogale da balango dan tunda taga wadda sultana sadiya ta aiko mata taji tana kwad'anta.

Mik'ewa tayi tafito parlour dan tasa asamo mata, daidai lokacin sumayya tashigo d'akin babu ko sallama.

Zarah tsaye tayi tana kallonta cike da mamaki dan sumayya had'e rai tayi sosai ba alamun fara'a a tare da ita daga gani kasan ba mutunci yakawotaba.

Ta6e baki zarah tayi tace haba baiwar Allah ya za'ayi kishigo min d'aki babu ko sallama saikace kin shigo d'akin arna.

Wata uwar harara sumayya tawurga mata cike da 6acin rai tace tunda gidan ubankine ai dole inyi sallama, ke ni nan bai min kama da d'akiba sai dai kongo dan haka ank'i ayi sallamar banza matsiyaciya, kuma cikin da kike tak'ama da shi indai ina numfashi bazaki ta6a haifesaba ke gidannan ma dole kibarsa dan yarima ba ajin aurenki bane, ni banga abinda yagani a jikinkiba har ya amince ya aureki, banza 'yar matsiyata.

Murmushi zarah tayi cikin rashin damuwa tace sumayya ni yanzu banada lokacinki abinda yake kaina ya isheni, kuma ciki da kike magana Allah ne yabani baki isa kiyi min abinda Allah baiyi min ba.

Cikin k'araji sumayya tace kar kikuskura kiyi min gori dan wlh zansa kiyi nadamar da bakita6a yiba a rayuwarki, kinci sa'a ina rangwanta miki ammah wlh da tuni kinbar gidannan kuma cikine kirufa ki aje sai nayi silar zubar da shi.

Zarah shafa cikinta tayi tace malama kinfa dameni da haukanki, kifita kiban waje ko yanzu insa afitar min da ke.

Ta6e baki sumayya tayi tace duk yadda kikayi daidaine ammah inaso kisani ni sumayya na tsaneki, tsanarki bazata ta6a fita daga zuciyana har sai ranar da naga na cika burina, tana fad'in haka tajuya tafita daga d'akin a harzuk'e.

Zarah tsaye tayi tabita da kallo har ta fita, ahankali tafurta Allah yashiryeki sumayya.

Ringing d'in wayanta da tajiyo yasa cikin sauri takoma bedroom d'in tad'auko, ganin mai kiranta yasa tasaki murmushi tare da zama gefen gado saida tasaita nutsuwarta sannan tayi picking.
Chapter 60 · 0% Book details