Sashe 16
Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....✔*
_Jinjina agareku sis Mugirat marubuciyar *KISHI KO HAUKA* da sis Ummie Adnan marubuciyar *HAUWA JIDDAT* gaskiya inajin dad'in novels d'inku basirarku da k'wazonku suna burgeni kunyi namijin k'ok'ari a wajen rubutunku Allah yak'ara basira da zak'in hannu acigaba da sambad'o mana, *KISHI KO HAUKA DA HAUWA JIDDAT* duk Wanda bai karantaba anbarsa a baya dan haka kugarzaya kukaranta, muje zuwa😍👍_
_~Gareka *DR ZAIN* 👍 ina jin dad'in novels d'inka Allah yak'ara basira da zak'in hannu, nagode sosai da kyautan pages d'in da nasamu, *'YAN GUDUN HIJIRAH* labari maicike da darussa duk wanda bai karantaba anbarsa a baya~_
_*Yau page d'in nakune Mummyn Afrah nd Meena Abbah Wlh ina ji daku irin sosai d'innan, jinjina agareku marubutan *NI DA MIJIN YAYATAH gaskiya kunyi namijin k'ok'ari a cikinsa Allah yak'a basira da zakin hannu I heart u all😘*_
page 1⃣2⃣
Ko da suka isa nan ma maigadi bai hanasu shigaba saboda ya san Rauda sosai.
hango Alh munir sukayi a parking space yana shirin shiga motarsa ganin Rauda tare da zarah yasa yatsaya yana kallonsu fuskarsa d'auke da murmushi har suka iso wajen da yake su dukansu fuskarsu a d'aure take,
Washe baki Alh munir yayi yace Rauda kece tafe tare da sister d'inmu? ya dai ko itama tana cikine? ai daman na fad'a miki kud'ine abokan rayuwa nasan daman itama zata amince, yanzu dai mushiga daga ciki muyi magana ko tafiya zakiyi kibarni da ita?
Rauda cikin fushi tace ni ba wannan yakawomuba nazone in shaida maka ina d'auke da cikinka tsawon wata biyu.
Alh munir saida yafirgita jin ta ambaci ciki ammah yadake yayi 'yar dariya ta rainin wayau yace ciki kuma? Haba kina big gurl ya za'ayi kibari kiyi cikin shege kuma dan kin rainani shine sai kice cikinane?
zarah cike da k'ulewar dariyar da yayi musu tace idan ba cikin ka bane toh na uban wanene?
Alh munir tsagaitawa yayi daga dariyar da yakeyi yace ke kardai kisaki kizageni naga kamar kunya bata ishekiba,
Zarah dariya tayi tace girma dai ya riga da ya fad'i akwai marar kunya bayanka? kabaro iyalanka kazo kana 6ata rayuwar 'ya'yan wasu kuma ciki dole kakar6esa dan baida uba bayan kai.
Alh munir cikin 6acin rai yace baku isa kulik'a min d'an shegeba ita ai tasan wad'anda take bi saitaje tagano wanda yayi mata ciki ammah ni wlh babu wanda ya isa yace cikinane kuma barakiji rauda daga yanzu kar ma kik'ara nuna kin sanni ko da ahanyane, motarsa yabud'e yad'auko kud'i yamik'a masu yace ga wannan kinje kisamu kicire cikin tunda daman kwad'ayi yaja miki sannan kufitarmin daga gida tun kan ranku ya6aci.
Zarah kallon Rauda tayi da taketa aikin kuka ran Zarah ya 6aci sosai, sannan tamaida kallonta ga Alh munir takar6i kud'in tawatsa masa a fuska tace karik'e kud'inka bama so, eh dole kace haka tunda ka ci moriyar ganga, saidai inaso kasan wani abu kaima kana da 'ya'ya kuma kana da mata dan haka kasaurari naka, kar kamance Allah ba azzalumin bayinsabane kuma fad'an ubanginine abinda kayi sai anyi maka, murmushin takaici Zarah tayi kwallah duk ta cika mata ido tace alhaki kwikwiyone muje zuwa, rik'o hannun Rauda tayi har sun fara tafiya sannan tatsaya batare da ta juyoba tace kuma ciki ba zamu ta6a zubar da shiba sai ta haifesa anan zamu gane wanene ubansa kuma ko jinin wanene dole mukai ma matarsa tareni cikin shege.
Tana gama fad'in haka taja Rauda suka fita sukabar gidan.
Hankalin Alh munir ya tashi sosai domin tunda yaga zarah yasan zata iya yin komai ma, chan kuma sai yayi murmushi yace naga ta yadda za'ayi inkar6i dan shege, yana gama fad'in haka yakoma cikin gida fitarma yafasa
Suna fitowa Rauda duk'ewa tayi k'asa tacigaba da kuka, zarah share k'wallar idonta tayi tace yaya Rauda kinga abinda nake guje muku kingani ko yanzu gashinan dukansu babu wanda takar6i cikin kowa ya ce banasa bane.
Rauda tsagaitawa tayi daga kukan da takeyi tace tabbas zarah nagani kuma nasan *NATAFKA BABBAN KUSKURE* da na'amince nabi son zuciyana yanzu gashinan najawo ma kaina babar matsalarma bansan ya zanyi intunkari su mama da cikiba bansan ya zasu d'auki lamarinaba, zarah kawai kitafi gida.
Zarah cike da tausayi tad'ago yayartata daga tsugunnin da tayi tace haba yaya rauda meyasa zakice haka duk abinda yafaru kid'aukesa a matsayin *K'ADDARA CE* kar kidamu nayi miki alk'awali ni zan tsaya miki ga su mama har sai sun fahimceni *KIYARDA DANI* yaya Rauda.
Rauda kallon k'anwartata takeyi cike da gamsuwa ta jinjina kai domin tasan zarah tana da hankali zata iya shawo kan iyayen nasu, share hawayenta tayi tace shikenan Zarah na yarda da ke ammah naga illar abinda na aikata.
Zarah murmushi tayi tace kikwantar da hankalin yaya Rauda nidai fatana kidaina wannan rayuwar da kikeyi kikoma mutuniyar kirki
Rauda tace zarah insha Allahu nadaina domin nakoyi darasi tun a nan yanzu dai muje gida fatana su Abbah su fahimceni.
Mai adaidaita suka samu suka fad'a masa inda zai kaisu har k'ofar gidansu yasafkesu suka sallamesa.
Rauda tsaye tayi takasa shiga gidan ganin haka yasa zarah tarik'o hannunta suka shiga lokacin Abbah da mama Suna zaune tsakar gida Suna cin abinci, jin sallamarsu yasa Aysha tafito daga d'aki rataye da d'an k'aramin veil da alama fita ma zatayi.
Mama ce tace Rauda har kun dawo? yanzu daman muke maganarku da malam muna cewa shuru har yanzu baku dawoba.
Zarah da Rauda tsaye sukayi suna kallon juna kowa hankalinsa a tashe, mama da abbah zuba musu ido sukayi suna kallonsu domin daga ganin yanayinsu babu alamun gaskiya a tattare da su, jikin Mama ya yi sanyi tace Rauda lafiya naganku haka?
Rauda kuka tafarayi tare da zaunawa k'asa tace mama kuyafemin wlh na cutar da rayuwata tabbas ban d'aukoma kaina hanyar da zata 6ulleba a yau nayi nadamar dukkan mugun halin da nayi a baya na cuci kaina ina tsoron had'uwata da ubangijina.
Mama cikin tashin hankali tace Rauda meyake faruwa? Zarah kuyi min bayani menene yafaru?
Zarah murmishin takaici tayi tana hawaye tace mama tarbiyar da kukabamuce kar kuzargemu duk abinda yafaru tunda kwad'ayi da son abun duniya gareku.
abbah tsawa yadaka musu yace kuyi mana bayani mana me yake faruwa? sai wani kwana-kwana kukeyi mana
Rauda ce tad'ago kai takallesu tace Abbah mama kuyi hak'uri ina d'auke da ciki tsawon wata biyu.
Mama dafe k'irji tayi dak'warai tace Rauda ciki? Abbah ma yace ciki? ??
Aysha cikin tashin hankali tace yaya Rauda ciki kuma?
Zarah kallon iyayen nasu tayi tace eh ciki gareta.
Mama k'asa tasulale tazauna tace nashiga ukku Rauda gidan ubanwa kikayi ciki
Yaya Rauda ta kasa cewa komai face kuka da takeyi.
Abbah hularsa yacire yafara fifita yace idan baki fad'amin inda kika samo cikiba sai na karyaki a cikin gidan nan.
Rauda cikin kuka tace Abbah kar kuga laifina duk abinda yafaru ku ma kuna da naku laifin a ciki domin baku bamu tarbiya tagari ba, ko da nafara wannan rayuwar ko da sau d'aya bamu ta6a ganin kun nuna rashin jin dad'in hakan ba saboda kwad'ayinku da son abin duniya
tabbas ayanzu nayi takaicin kasancewarku iyayenmu nayi Allah wadai da hali irin naku, wlh nayi nadamar abinda na aikata natuba insha Allahu daga yanzu na sauya rayuwata, kallon Zarah tayi da take tsaye ta jingine da bango idonta a lumshe hawaye kawai suke fita, Rauda tace kukalli baiwar Allahn nan itace kawai tafita zakkah a cikinmu kawai kasancewarta mutuniyar kirki yasa muka tsaneta muka hantareta ammah baiwar Allahn nan hakan baisa tak'imuba a kullum k'ara jawomu take a jikinta tana mana wa'azi a k'arshe ma sai munemi muci mutuncinta ammah hakan baisa tabarmu ba, muna mata kallon bagidajiya ashe itace wayaiyar tamu tabbas Zarah rayuwarki ta burgeni natayaki murna da son zuciya bai rud'ekiba har kika fad'a wannan mummunar rayuwar da iyayenmu sukaja muka fad'a, tabbas yanzu nagane *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka.
Rauda nisa tayi sannan tamaida kallonta ga Aysha tace Aysha kitaimaki kanki kema kigyara rayuwarki tun kan rayuwa tajuya miki baya domin a yau nagane mecece rayuwa kowane saurayi naje ma maganar ciki saidai yawulak'antani yacimin mutunci a k'arshe zarah ce taso takwatar min 'yancina.
Aysha dasauri tacire veil d'inta tare da duk'ewa kasa tafashe da kuka tace wlh yaya rauda nad'auki darasi a wajenki nima nadaina abinda nake, maida kallonta tayi ga su Abbah da sukayi jugum tace tsakaninmu da ku Allah ne kad'ai zai mana *SAKAYYA* domin bamu dace da iyaye nagariba dakanku kuke turamu muna aikata 6arna wlh da ace ana canza iyaye da babu abinda zai hanani canza nawa
Zarah dasauri tabud'e idonta tana kuka tace kun gani ko mama? Abbah kunga halin da kuka jefamu a ciki kuma wlh ranar lahira sai Allah ya tambayeku game da kiyon da yabaku, yanzu gashinan duniya ta juya muku baya, idan yaya Rauda tahaihu kundinga kallon abinda tabari kutuno kuskuren da kuka tafka, girgiza kai tayi cike da takaici tace da ace akwai inda zamuje da muntafi munbar muku gidanku muje muyi rayuwa mai tsafta.
Mama fashewa tayi da kuka tace wlh son zuciyane da sharrin shaid'an suka ja mana kuma insha Allahu muma mundaina kuyafe mana,
Aysha mik'ewa tayi tazo inda Zarah take tace yaya zarah tabbas kin ciri tuta a cikinmu duk abinda muke aikatawa baisa kin k'yamacemuba sai ma soyayyar da kike nuna mana, Dan Allah kiyafe min abinda nayi miki.
zarah murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace bakomai Aysha Allah yayafe mana gaba d'aya.
Rauda mik'ewa tayi tsaye tace dan Allah kuzo muje mubar musu gidan nasan ba zamu rasa wajen zama ba Allah yana tare damu. Aysha tace hakane yaya Rauda mun amince mutafi.
mama k'ara fashewa tayi da kuka tace nashiga ukku dan girman Allah kar kutafi kubarmu wlh muma mun tuba, mama kallon Abbah tayi da yayi jugum sai zufa yakeyi tace haba malam dan Allah kace wani abu mana kar sutafi.
Abbah dakyar yabud'e baki yace Zarah, Rauda, Aysha kudawo kuzauna muyi magana,