← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 102

Sashe 29

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dasauri shahid yamik'e yabi bayansa, ko da suka fita nan guards d'insa suka take masu baya, wajen da aka tanadar musu motocin da zasu fita da su suka nufa tun kan su ida isa naga anbud'e musu bayan wata dank'areriyar mota bak'a da take tsakiyan sauran motocin, saida suka shiga aka maida aka rufe sannan cikin sauri guards d'in sukaje suka shiga sauran motocin.

A chan 6angaren zarah Aunty kubra sata tayi tashirya, sosai tayi kwalliya had'ewa tayi cikin material Black colour mai ratsin marron nan tamurza d"aurin kallabinta tare da yafa veil marron, takalmanta da jakkarta ma duk maroon colour ne.

ba ita kantaba hatta su Aunty kubra sun yaba ma kyaun da zarah tayi, 6arin turaruka akayi mata sosai a jikinta.

ko da su yarima suka iso mai gadi hangame musu gate yayi motocinsu a jere suka shigo; dasauri guards d'insa suka fito daga cikin motocin da suke sukazo suka bud'ema su yarima murfin mota, ahankali yasafko k'afarsa sannan daga baya ya ida fitowa daga cikin motar, cike da tafiyarsa ta k'asaita yake takonsa shaheed yana gefensa nan wasu daga cikin guards d'insa suka take masu baya har part d'in mummy sa'adatu, daga wajen parlour guards d'in suka tsaya inda yarima suhail da shaheed suka shiga ciki da sallamarsu lokacin mummy sa'adatu tana shirin tafito taje ta tarosu,

ganinsu yasa tayi murmushi tare da cewa marabanku da zuwa, yarima murmushi kawai yayi shaheed ne yace yauwa mummy sa'adatu shidai shaheed kansa a d'aure yake har suka zauna domin yayi tunanin d'iyar mummy sa'adatu ce yarima zai aura, shidai yarima daman ummi ta fad'amasa zarah tana nan gidan hajiya sa'adatu kuma ta ce yabiya gidansu zarah yagaishe da iyayenta saisa baikawo komai a ransaba.

bayan sun zauna nan suka gaisheta cike da girmamawa, ta amsa cike da kulawa tare da tambayarsu mutanen gida sukace kowa yana lafiya, nan da nan aka cika musu gabansu da kayan tand'e-tand'e da shaye-shaye, mik'ewa hajiya sa'adatu tayi tare da cewa son kugama cin abinci sai inkira muku ita.

shaheed ne yatsiya musu ruwan inibi yamik'a ma yarima sannan yace mummy wlh a k'oshe muke abincin bazai shigaba.

murmushi mummy sa'adatu tayi tace ku daman ina rik'e da ku bakwacin abincin ginnan, kokuma ma ai bazuwa kukeba duka wannan zuwanku na ukkune shima duk ta dalilin umminku, bakwason zumunci ko?

yarima suhail murmushi yayi yace insha Allahu zamu gyara, tace kullum wak'ar kenan bari inje inkira muku ita toh tunda kunk'i cin abinci.

ko da hajiya sa'adatu tafita shaheed apple yad'auka yana ci tare da kallon yarima da yake rik'e da cup d'in ruwan inibi yace kasha mana,

yarima batare da yayi maganaba ya aje cup d'in tare da jawo wayarsa yana operated d'inta, shaheed murmushi yayi tare da ci gaba da cin Apple d'insa.

Hajiya sa'adatu lokacin da tashiga part d'in da su zarah suke tun daga bakin k'ofa tafara washe baki tana kai daughter wannan irin kyau haka?

zarah dai murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da kanta domin gabanta fad'uwa kawai yake,

Hajiya sa'adatu tace yauwa toh yanzu kitashi kije parlour na suna chan suna jiranki.

kallon Hajiya kubra zarah tayi, Hajiya kubra tace kitashi mana.

idanuwanta nan suka ciko da k'wallah, Hajiya kubra tace a'a zarah dan Allah kar kiyi kuka ki6ata kwalliyarki.

zarah murmushi tayi tace Toh Aunty kubra, nan kuyangin da ummi ta aiko mata da su suka take mata baya tafiya take cikin takunta mai aji hango motocin su yarima da tayi da sauran guards d'insa saida gabanta yasake fad'uwa duk tsoro da fargaba suka cikata har ta isa parlour nan guards d'in da suke tsaye wajen k'ofar suka gaisheta ahankali tabud'e labulen dakin tashiga inda tabar kuyangin tsaye waje.

cikin 'yar siririyar muryatarta tayi sallama, shaheed ne ya amsa mata tare da d'ago kai yakalleta zaro ido yayi yace wow masha Allah matarmu bismillah mana.

ahankali zarah tatako tazauna saman kujerar da take opposite d'insu cike da nutsuwa tagaishesu, shahid ne kawai ya amsa mata domin yarima har lokacin bai d'ago ya kalli inda takeba barema asa ran zaiyi magana.

Shaheed kallonta yayi yace amaryarmu gaskiya kin had'u, dafatan mun sameki lfy? , murmushi zarah tayi tace lafiya lou ya gida?

shahid yace kowa yana lafiya, sannan yamaida kallonsa ga yarima da yake zaune kamar baisan abinda akeyiba, murmushi shahid yayi yace ranka yadad'e kayi shuru bakace komai ba,

Zarah ahankali tad'ago kai takalli mutumin da tunda tashigo baiyi maganaba dannar wayarsa kawai yakeyi saida gabanta yafad'i, batare da yad'ago kai ya kalletaba yace akawai event d'in da zakiyi ne?

shuru zarah tayi tana kallonsa, ahankali yarima yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido, dasauri yajanye idonsa daga kallonta yace kamar nawa kike buk'ata inbaki?

zarah dakyar tabud'e baki tace bana buk'atar ko naira, ta6e baki yarima yayi, ganin haka yasa shahid yace a'a amarya kar kice haka kifad'i yadda kike buk'ata nagama kamar kunyata kukeji kowa yakasa magana bari inbaku waje kuyi magana.

Yarima yace no nima ai tafiya zanyi yanzu, harararsa shaheed yayi yace toh ai sai kugaisa dan naga ko gaisawa bakuyi ba kar ace ni nahana nabarku lafiya, yana gama fad'in haka yaficce yabar musu d'akin,

nan d'akin yad'auki shuru ba'ajin motsin komai zarah wasa kawai take da yatsun hannunta, jin baida niyar yin magana yasa tad'ago kai takalli yarima dayake ta dannar wayarsa kamar baisan da zaman mutum ba a wajen, zarah wani k'ululune taji ya tsaya mata a mak'oshi, janye idonta tayi ga kallonsa mamakinsane yacikata cikin ranta tace mutumin nan ko dai kurma ne? chan wata xuciyantace toh kuma ai yanzu taji ya yi ma d'an uwan nasa magana, chan da tagaji da shurun ahankali tace ina wuni?

shuru yarima yayi bai amsaba jin shurun da yayi yasa tad'auka baijitaba nan tak'ara d'ago kai takallesa har lokacin dannar wayarsa yake, sai a lokacin ya amsa mata cikin muryarsa mai dad'i, zarah mamakine yakamata domin bata d'auka miskilancin nasa yakai hakaba, ahankali tace lallai wannan mutumin d'an wulak'ancine, jiyo muryasa tayi yace magana kikayi?

cike da k'ulewa tace ni bance komaiba,

d'ago kai yarima yayi yakalleta kallo d'aya yayi mata yad'auke kai tare da mik'ewa tsaye, takawa yayi yaje inda take ya aje mata cheque a gefenta sannan yace gashinan idan basu ishekiba sai kiyi magana.

zarah ida k'ulewa tayi ganin baima jin zai iya bata saima ajemata yayi, cike da jin haushi tace kabarsu kawai ba abinda zanyi da su.

yarima kallonta yayi cikin rashin damuwa yace indai nafitar da kud'i bana maidasu idan basu ishekiba zaki iya yin magana, yana gama fad'in haka yawuce yafita yabar d'akin,

tsaki zarah taja tare da mik'ewa tabi bayansa domin suyi sallama da shaheed, ganinta yasa shaheed yatafo wajenta yana murmushi yace amaryarmu yanzu nake shirin zuwa muyi sallama.

Murmushi itama tayi tace nima cewa nayi bari nazo muyi sallama, yarima gaba yayi aka bud'e masa mota yashiga saida suka iso wajen motar sannan zarah tayi musu sallama takoma ciki tana mamakin halin yarima, cikin ranta tace ashe akwai babban aiki a gabana.

ko da su yarima suka kama hanya shahid kallon yarima yayi yana murmushi yace gaskiya yarima ka iya za6en mata kaga yadda kukahad'e kukai matching? yarima batare da ya kallesaba yace bawani dacewa ai wlh kai yakamata ma ace anma dole ka yi aure, dariya shahid yayi yace nima fa abin yana damuna ganin har kana shirin yin na biyu ammah ni ko d'aya banda ita, yamitsa fuska yarima yayi yace nima ba ason raina nayi aure yanzuba dan banma shirya yinsaba by my age, kaduba kaga duka yanzu fa 28yrs ammah mata har biyu tsaki yarima yaja cike da takaici yace ina ma amfanin hakan.

dariya shaheed yayi yace ai abun jin dad'ine hakan kuma matsayinka ya kai hakam, nima insha Allahu kwanannan zan faso zan baku mamaki,

ta6e baki yarima yayi yace wajen surutunka kayo yarinya ko?

shahid gyara zamansa yayi tare da cewa haba dai kabari zakasan ko wacece nan gaba jira nake agama wannan hidimar auren naka nima in6ullo kai dan bama zanso asa sama da wata d'ayaba,

yarima suhail jingine kansa yayi da sit din da yake zaune tare da lumshe idonsa,

ganin haka yasa shahid yaja bakinsa yayi shuru dan yasan maganarce ta ishi yarima.

tunda suka kama hanya basu zarce ko inaba sai gidansu zarah saboda tun dare sultana bilkisu ta kira iyayen zarah ta shaida musu yarima yana nan zuwa zai gaishesu, dan haka tun da safe suka dinga hidindimu kaji shidda baba yasiyo akayi pepper da ukku aka soya ukku, had'add'ar wainar shinkafa su mama sukayi da miyar ganye sannan suka had'a kunun aya wanda yasha madara, bayan sun gama duk suka shirya suna jiran zuwan yarima dan su Aysha sun k'osa sosai suga mijin zarah.

A gaban gidansu zarah sukayi parking d'in motocin dasauri guards d'in sukafito daga motocin da suke ciki sukazo suka bud'ema su yarima k'ofa tare da cewa ranka yadad'e nan ne,

yarima batare da yafitoba yadinga k'arema gidan kallo cike da mamaki, shima shahid mamakine yacikasa ganin gidan da yarima yanemi aure.

malam musa da yake zaune cikin gida jin k'arar mota yasa yakalli su mama yace ina tunanin sun iso bari inje induba,
cike da jin dad'i Aysha tace yauwa Allah yasa sune.

malam musa ko da yafito yaga jerun motoci cike da fara'a yanufo wajen, ganinsa yasa yarima yafito daga motar, nan guards d'insa suka shiga gaishe da malam musa.

malam musa hannu ya mik'a ma su yarima suka gaisa yace maimakon kushigo sai kukayi tsaye? shaheed ne yace daman yaro muke nema mu aikasa yayi mana sallama da kai,
malam musa yace ayyah Allah sarki toh bismillanku.

batare da sunyi musu ba sukabi malam musa suka shiga har cikin soron gidan, saman tabarma suka zauna.

cike da girmamawa suka gaishe da malam musa ya amsa musu tare da tambayarsu mutanen gida, shaheed ne yace suna lafiya lou, sunce agaisheku

malam musa yace muna amsawa sannan yakalli yarima da tunda yagansa yagane shine mijin da zarah zata aura, malam musa yace ya su mahaifiyartaka?

murmushi yarima yayi kansa yana sadde a k'asa yace lafiya lau suke.

malam musa yace toh masha Allah, mik'ewa yayi yace ina zuwa nan yashiga gida.
Chapter 29 · 0% Book details