← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 102

Sashe 27

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita dai sultana bilkisu tana saurarensu batace komai ba.

Sultana Sadiya tace ma dada Ranki yadad'e ai harda laifin mahaifiyarsa da ace tana yi masa magana ai da gyara.

Dada tace a'a kar kice haka rabani da suhail ni nasan halinsa natabbata ko itama bai zama dole yaji kowace maganartaba ni nasan halinsa.

Sultana Bilkisu murmushi kawai tayi, Sultan abbas yace ranki yadad'e aikin gama ai yariga da yagama addu'an zaman lafiya kawai za'ayi musu.

Dada tace hakane duk wad'annan surutan basuyi fatanmu dai kamar yadda kace sun karramaku toh muga karamcin da mutuncin atare da ita.

sultan abbas yace hakane ranki yadad'e, Sultana sadiya bahaka tasoba taso ace dada tahau tazauna tace ba zata amince ayi aurenba.

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Yau page d'in mallakinkune ku kad'ai *Umm Abideen nd Queen Meenali* hak'ik'a ina muku so na hak'ik'a, chancantar kuce taja da haka😘_

*PAGE* 2⃣0⃣

A chan gidansu zarah duk inda yakamata araba kayan baikonta anraba kowa yayi murna sosai tare da fatan alkhairi.

k'awarta khairy tsegumi tashiga yi mata akan tabar malam bello zata auri wani daban itadai zarah shuru tayi.

duk yadda khairy taso zarah tafad'a mata wanda zata aura zarah k'iyawa tayi, sai Aysha ce take fad'a mata.

khairy murna tayi sosai har da tsallenta tace da girman kujerarki gimbiya zarah ai ni wlh tun lokacin da nagansa naga kunyi matching, gaskiya guy d'in ya had'u ba k'arya gaskiya natayaki murnar samun miji irin yarima suhail ana ta shi waketa malam bello kud'i, kyau, nasaba, mulki, aji babu wanda yarima yarasa.

murmushin takaici zarah tayi tace khairy kenan bakisan micece soyayyaba wlh son da nake ma malam bello ya wuce yadda kike tunani, kuma wannan d'in da kike maganarsa bana tunanin zai soni, ko da sau d'ayane bai ta6a zuwa muka gaisaba, wannan aurenfa iyayensane suka nema masa ni, wlh nayi da nasanin walimarnan da nayi a islamiyya domin itace silar faruwan komai, kukan da take dannewane yaci k'arfinta,

khairy rungumota tayi jikinta tana lallashinta tace a'a zarah kidaina cewa haka, domin haka Allah yak'addara yarima shine mijinki ba malam bello ba kiyi hak'uri kid'au k'addara kicire malam bello a ranki kisamarma yarima matsugunni a cikin zuciyanki.

dasauri zarah tad'ago kai takalleta tace khairy taya kike tunanin suhail zai samu matsugunni a cikin zuciyana?

murmushi khairy tayi tace na tabbata zai samu domin ta ko wane fanni ya dace kisosa dan daganin yanayinsa ma ya iya soyayya.

zarah ganin abin na khairy har da tsokana yasa tashareta.

A chan 6angaren yarima zaune yake yana dannar laptop d'insa da alama wani abu me muhimmanci yakeyi gimbiya sumayya ce tashigo ba ko sallama, ko da sau d'aya yarima bai d'ago takalletaba.

daga nesa da shi kad'an tatsaya tare da yamitsa fuska tace suhail kenan gaskiya kabani mamaki ace duk mulki, kyaun da Jan ajin ammah ace d'iyar talakawa zaka aura, gaskiya najiye maka haushi ammah fa dakunya ace talakka itace zata kasance kishiyata natabbata ko matsayin baiwata bata kaiba.

yarima d'ago kai yayi yawurga mata wata irin muguwar harara wadda har saida sumayya tatsora, yace ke dad'ina da ke wani lokacin k'walwarki a toshe take in banda abinki me yahad'a kud'i da soyayya ina so kisancewa kud'i basa siyan soyayya kuma bari kiji ahaka nakesonta dan haka kifitar min daga d'aki ko in 6a66allaki ,

sumayya ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa tafita tana k'unk'uni,

tsaki yarima yaja sannan yacigaba da aikinsa a cikin zuciyansa ko yana mamakin halin sumayya da kwata-kwata ta kasa gyarawa.

shaheed a wajen mahaifinsa yakeji sunje neman aurensa baiyi mamakin rashin fad'a masa da baiyiba domin yasan halinsa,

ko da yaje yi masa Allah yasa alkhairi yarima suhail ko kallonsa baiyiba, shaheed ba haka yasoba yaso yarima yabiyemasa ko dan yaji yadda akayi yasamu mata shi da mata basa gabansa.

*BAYAN SATI BIYU*

a gurguje sultana bilkisu shiryawa tayi itada wata aminiyarta Hajiya sa'adatu sukaje gidansu zarah inda ta rok'i iyayen zarah alfarma akan subata zarah tanaso taje da ita ayi mata gyara sosai sannan akoya mata yadda zata dinga tafiya, magana, girki dadai sauransu a gidan sarauta saboda a matsayinta na matar yarima guda ana buk'atar ace ta san yadda ake komai na gidan sarauta.

dakyar tasamu su mama suka amince zarah ma harda kukanta kafin tabisu.

sultana bilkisu gidan hajiya sa'adatu sukaje da ita, zarah tun da suka shiga gidan mamaki yacikata ganin irin daular da aka zuba a gidan babban gidane sosai mai d'auke da part ukku.

part guda aka fitar mata da shi kasancewar darene akace taje tahuta gobe za'a kawo mata wad'anda zasu dinga yi mata hidima da koya mata komai, zarah dai jikinta rawa yake har saida ummi tagane halin da take ciki.

murmushi ummi tayi tare da rik'o hannunta sukaje bakin gado suka zauna, ummi kallonta tayi tace zarah kinutsu kicire tsoro a ranki ba zamu cutar da ke ba duk abinda kikaga zamuyi miki dan gudun magana ne kinsan gidan sarauta yadda yake, dan Allah kiyi hak'uri kibamu had'in kai.

zarah da kanta yake sunkuye k'asa wani irin nauyin ummi ne taji sa6anin da dasuka tafo da ita wani irin haushinsu da takeji,

batare da ta d'ago kai takalletaba cike da kunya tace toh.

ummi cikin jin dad'i tace yauwa nagode insha Allahu gobe zaku fara gudanar da komai akwai wad'anda zasu dinga kula da ke duk abinda kikeso kiyi musu magana zasuyi miki, ummi jakkarta tabud'e tad'auka waya IPhone7 tamik'a ma zarah tace ga waya akowane lokaci kike buk'atar gaisawa da 'yan gidanku sai kugaisa nima zan dinga kiranki.

zarah batare da ta k'ar6aba tace ranki yadad'e ina da waya.

murmushi sultana bilkisu tayi tace da zaki taimaka kidaina cemin ranki yadad'e da naji dad'i.

ahankali zarah tad'ago kai takalleta, murmushi sultana bilkisu tayi tace kikirani da ummi, itama zarah murmushi tayi tace toh ummi insha Allahu hakan zan dinga Kiranki.

cike da jin dad'i sultana bilkisu tace yauwa daughter toh ina wayan taki?

zarah tashi tayi tabud'e akwatin kayanta tad'auko rugwagwar nokia d'inta tace gatanan.

kar6a ummi tayi tace wannan wayan yanzu ta gama amfani bari insaka miki number d'in wayan su mamanki a wannan,

zarah tace toh ummi.

nan ummi tasaka mata number d'in mama da abbah, sannan tad'ago takalli zarah tace daughter bari insaka miki harda number d'in yarima in case ko da ace zakuyi waya.

zarah da tunda ummi ta ambaci yarima gabanta saida yafad'i dakyar tace toh.

bayan ummi tasaka numbers d'in mik'a ma zarah wayar tayi tare da k'ara kwantar mata da hankali saida taga hankalinta ya d'an kwanta sannan tayi mata bankwana tafita taje tayi sallama da Hajiya sa'adatu tatafi.

Bayan ummi ta fita zarah mik'ewa tayi tana k'arema d'akin kallo tana mamakin dukiyar da aka zuba sannan daga bisani taje toilet domin tad'auro alwallah tayi sallar isha'i da karambani tasamu tayi alwallar tafito.

bayan ta gama sallah tana zaune saman darduma aka yi knocking d'in k'ofa nan tabada izini ashigo, hajiya sa'adatu ce tare da 'yar aikinta d'auke da kuloli, nan zarah tagaisheta,

cike da sakin fuska hajiya sa'adatu ta amsa tare da cewa yi hak'uri mun barki ke kad'ai ko?

murmushi zarah tayi tace lah bakomai mummy, hajiya sa'adatu umurni taba mai aikinta ta aje ma zarah abinci sannan tace kiyi hak'uri da kad'aici, inma kina buk'atar kallo toh zaki iya kunnawa akwai komai a parlour, sannan kayan da zakiyi amfani da su duk suna cikin wardrobe

zarah tace toh mummy nagode, nan hajiya sa'adatu tayi mata sallama tafita tabar d'akin.

abincin zarah tazuba taci sannan tatashi tashiga toilet nan ma da karambani takunna shower tayi wanka,

bayan ta fito gaban dreesing mirror tazauna tashafa mai tana ta mamakin kayan kwalliyar da tagani jibgi guda a saman dressing mirror d'in,

koda tagama wardrobe taje tabud'e mamakine yakamata ganin jibgin kayan da ke akwai, doguwar rigar bacci tajawo bak'a tasaka sannan tadawo parlour tak'are masa kallo takunna kallo tana yi domin yarage mata kad'aici,

tana zaune tana kallo saida taji tafara jin bacci sannan takashe tare da mik'ewa tashige bedroom tafad'a saman makeken gadon da yake d'akin saida tayi addu'a sannan takwanta nan bacci yayi awon gaba da ita.

da safe knocking d'in da akeyine yatadata daga baccin da takeyi saboda tunda tayi sallar asuba takoma bacci, dakyar tabud'e idonta tare da safkowa tazo tabud'e k'ofar, cike da girmamawa 'yar aikin tagaisheta tare da cewa ga breakfast d'intanan saman dining sannan zata gyara mata d'aki, zarah tace toh ammah kibar gyaran zanyi.

'yar aikin tace a'a ranki yadad'e aikinane kuma umurnine daga shugabata, zarah batace komai ba takoma ciki tabar 'yar aikin tana gyaran parlour.

wanka tashiga tayi lokacin da tafito tatarar har ta gyara mata bedroom d'in,

zama tayi gaban dreesing mirror tayi simple makeup sannan tatashi tabud'a wardrobe tad'auko less riga da skirt tasaka tayi mamaki sosai ganin yadda d'inki yakar6eta kamar an aunata.

bayan ta gama parlour tadawo tazauna a dining tahad'a breakfast tayi, sannan takoma bedroom tad'auko wayanta takira su mama domin sugaisa,
tana cikin wayan ne taji anbud'e k'ofar anshigo juyowar da zatayi taga hajiya sa'adatu ce dan haka tayi sallama da yaya rauda da suke waya tare da tsinke kiran, cike da ladabi taduk'a tagaisheta.

fuskar hajiya sa'adatu d'auke da fara'a ta amsa mata tare da tambayar ta tatashi lafiya ya kuma bak'unta?.

murmushi kawai zarah tayi batace komai ba, hajiya sa'adatu tace dafatan dai kinyi breakfast?

zarah tace eh mummy,

hajiya sa'adatu tace yauwa haka nakeso, nafison kisaki jikinki kidaina bak'unta domin nan ma gidane,
zarah tace toh mummy.

hajiya sa'adatu tace idan kin gama kisamemu a parlour muna jiranki.
zarah tace toh nama gama,

bayan hajiya sa'adatu tabiyo suka fito parlour, mamakine yakama zarah ganin wasu mata sanye da kaya iri d'aya su ukku sai wata mata zaune saman kujera.
Chapter 27 · 0% Book details