← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 102

Sashe 28

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana fitowa matan suka duk'a suna gaisheta, zarah duk sai taji wani iri ganin irin gaisuwar ban girman da suke yi mata kasa amsawa tayi, nan itama zarah ta duk'a tagaishe da matar, nan ta amsa mata cikin sakin fuska tare da kallon hajiya sa'adatu tace ranki yadad'e wannan ce?

hajiya sa'adatu tace eh itace,

matar kallon zarah tayi tana murmushi sannan tamaida kallonta ga hajiya sa'adatu tace ranki yadad'e tunda dai ku customer's d'inane kawai kubiya 1.5 million, domin banason inyi jayayya da ku tunda ni nakema 'ya'yanku gyara, ko in antashi bikkinsu ninake zuwa ina musu duk abinda yadace kuma kunsan aikina, bana son intsaya ciniki da ku saisa nace abani hakan.

murmushi hajiya sa'adatu tayi tace shikenan za'a baki mudai fatanmu kifito mana da ita kinsan matar yarima ce.

dariya matar tayi tace ai hajiya tafad'a min komai dan haka bakuda matsala ai kunsan aikina cikin k'ank'anin lokaci nakeson incanzata domin daga ganin yanayinta ba zamusha wahala ba,

hajiya sa'adatu tace hakane Allah yataimaka ynz kibada account number d'in da Za'a turo miki kud'in ko kinfi son cash?

matar tace a'a kudai min transfer d'in fa wannan account number d'in da nata6a turo miki.

hajiya sa'adatu tace toh badamu sannan takalli zarah tace zarah ina fatan zaki bata had'in kai kuyi komai kugama lafiya.

zarah kanta yana sunkuye k'asa tace insha Allahu mummy.
hajiya sa'adatu tace yauwa d'iyata, sannan hajiya sa'adatu tanuna matan ukku da suke tsaye tace wad'annan kuyangin sultana bilkisune ita taturosu domin sudinga miki hidima dan haka duk abinda kikeso zasuyi miki Allah yataimaka.

gaba d'ayansu sukace Ameen.

bayan hajiya sa'adatu ta fita matar kallon zarah tayi tace sunana hajiya kubra nice wadda zan dinga koya miki kwalliya, girki, yadda zaki dinga tafiya irin ta k'asaitattun mata sannan kula da miji, kissa da duk wani abinda yakamata, sannan zan miki gyaran jiki sosai dan haka kid'aukeni a matsayin 'yar uwarki domin zaki kasance tare da ni natsawon wani lokaci, dan haka tun daga yau zamu fara.

zarah murmushi tayi tace toh Aunty kubra nagode.

hajiya kubrah tace kar kidamu aikinane dan haka yanzu zamu fitar da lokacin da zamu dinga gudanar da lecture d'in,

zarah cike da jin dad'i tace toh.

tun daga ranar hajiya kubrah tatsara yadda zasu dinga gudanar da komai,

tafara koya ma zarah yadda zata dinga tafiya mai aji, ita kanta zarah yanayin tafiyar ta burgeta, batasha wuyaba wajen ganin ta koya.

idan zarah tayi wanka zama take hajiya kubra tana mata kwalliya tana gwadamata kayan makeup d'in da amfanin kowane d'aya, idan tagama mata sai hajiya kubra tatambayeta amfanin kowane daga cikinsu, tans mamaki sosai ganin yadda kan zarah yakeja dan tana da saurin fahimta.

alkyabba ma sai da tadinga koya mata yadda zata sanyasu, da yadda zatayi tafiya Idan tana sanye da alkyabba dan har sa kuyangi hajiya kubra take suna takema zarah baya tayi tafiya tagani.

duk bayan sallar la'asar suke zama tana koya mata yadda zatayi magana, da shagwa6a da yadda zata dinga tarbar miji da yi masa rakiya, da yadda zata dinga narke masa kai hatta kwanciyar aure saida tadinga koyama Zarah, zarah tun tanajin kunya tana ma hajiya kubra kallon marar kunya har daga k'arshe tad'an sake mata.

girki kala-kala hajiya kubra take koya ma zarah dan a rana sai suyi girki kusan kala goma gobe kuma sai tasa zarah tamaimaita kuma tana maimaitawa lafiya lau.

A 6angaren gyaran jiki tana yi mata sosai zarah ta canza sosai dan ita kanta tana mamakin kyaun da tak'ara da haske fatarta Idan kata6a kamar jini yazubo saboda ja da tsantsi duk inda tagifta k'amshi take fitarwa medad'i .

turaren tsugunni ma ana had'amata tana yi, hajiya kubra bata wani d'irka mata magungunaba tace saboda ita budurwace da ni'imarta bata buk'atar k'ari saidai tana sata tana cin 'ya'yan itatuwa (fruits) sosai sai kuma dahuwar 'yan shila da takeyi mata akai akai

a gurguje *BAYAN SATI UKKU*

Nan da nan komai na zarah yazanza idan kaganta sai kad'auka 'yar gidan wani mai muk'ami ce, ita kanta hajiya sa'adatu ko da tazo taganta tayi mamaki sosai ganin canjin da tayi cikin k'ank'anin lokaci,

ita kanta zarah tana jin dad'i idan taduba taga yadda takoma saidai duk lokacin da tatuna saboda Wanda akeyi mata gyaran mutumin da baisan da zamantaba baisan wacece itaba, duk sai taji haushi da takaici sun kamata tarik'a ji ina ma ace malam bello ne, saidai ta6oye tasha kukanta ita kad'ai.

kusan kullum sai sunyi waya da su mama da 'yan uwanta. da sultana bilkisu dan sultana bilkisu ta WhatsApp taturo mata pics d'in kayan d'aki tace taza6i design d'in da takeso da colour d'in da takeso, lefe kuma cewa tayi zarah tayi hak'uri domin ba za'a je kai lefentaba za'a aje mata a gidanta saidai kayan da zatayi hidimar bikki za'a aika mata da su,

A cikin satin ne hajiya kubra tak'ara zage damtse wajen gyaran jikin zarah kasancewar a yanzu saura sati guda yarage ayi bikkinsu,

akwati guda aka kai gidansu zarah cike da kaya kala ashirin, kayane na azo agani da alkyabba da shoes nd bags akace wanda zarah zatayi hidimar bikkine saboda masarautarsu ba'a kai lefe saidai a ajema amarya kayanta a gidanta, kowa ya yaba sosai da kyaun kayan ana ta santinsu, ko da su yaya rauda suka kira zarah a waya nan suke fad'amata kayan da aka kawo mata, zarah dai bata damuba saboda ita aganinta basu take buk'ataba burinta abarta taje taga iyayenta. da 'yan uwanta.

ko da sultana bilkisu tayo mata waya nan take tambayarta idan akwai events din da takaeso tayi, zarah cewa tayi bazatayi komai ba ko ma I.V card bazata rababa domin batada abokai sosai, sultana bilkisu bata takuramata ba saboda ko da tatuntu6i yarima da maganar shima cewa yayi ba dai halarci party ko d'ayaba, sultana bilkisu kyalesa tayi tace tunda dai ka amince da auren ai babu matsala.

kud'i sosai yarima suhail yadunk'ula yaba sumayya domin tayi amfani da su, gimbiya sumayya runtse ido tayi tace bazasu ishetaba, dan haka saida yak'ara mata sannan tatafi tana cewa idan ban amsaba ai wata zakaje kaba.

sultana bilkisu ganin har bikki saura sati guda ammah yarima baidamu da yaje yaga matar da zai auraba ko da sau d'ayama baya maganarta ko ma ita tayi masa maganarta sharewa yake dan haka wayarta tajawo takirasa tace yasameta tanason magana da shi.

sultana bilkisu ko da yazo matsa ma yarima suhail tayi akan dole sai yaje yaba zarah kud'i wad'anda zatayi hidimar bikki da su, yarima saida yaga ran ummi yana neman ya6aci sannan ya amince zai je gobe idan Allah ya kaimu.

yarima ko da yakoma 6angarensa zama yayi saman kujera takaici duk ya cikasa, tsaki yaja yace sai asa mutum yayi aure kuma amatsamasa dole sai yaje, wayarsa yajawo yakira shaheed bayan shaheed yayi picking yace ranka yadad'e ina mik'o gaisuwa.

tsaki yarima yaja yace kaiwai bakasan kayi ma mutane sallama ba.

dariya shaheed yayi tare da yin sallama,
nan yarima ya amsa masa, daga nan kuma bai k'ara cewa komaiba.

ganin yarima baida niyan yin magana yasa shaheed yace kaifa tsiyata da kai sai kakira mutum kuma kakasa yin magana.

tsaki yarima suhail yaja yace gobe idan Allah ya kaimu kashirya muje wajen wannan yarinyar ka san ummi ce ta matsamin sai naje dole.

cike da jin dad'i shaheed yace Allah yakaimu, _domin shima yana burin ganin matar da yarima zai aura_, chan sai yace kai yarima bakada dama yanzu matar da zaka aurace kake cema yarinya?

tsaki yarima yaja tare da kashe wayarsa domin shi yanzu haushin kowa ma yakeji.

murmushi shaheed yayi tare da bin wayar da kallo yace yarima kenan jin kanka ya yi yawa.

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_I dedicated this page to my fan's, thank you for love nd concern, I really appreciate it😍😘_

*PAGE* 2⃣1⃣

Da daddare sultana bilkisu takira zarah bayan sun gaisa nan take fad'amata zuwan da yarima zaiyi gobe,

zarah saida gabanta yafad'i ammah tadake tace ummi Allah yakaimu.

A ranar kasa baccin kirki tayi, tunani da fargaba duk suka cikata.

wanshe kare shaheed shiryawa yayi yanufi gidan yarima, lokacin da yaje part d'in yarima nan guards d'insa suka gaishesa sannan d'aya yashiga yasanar da yarima zuwan shahid nan yarima yabada izini abarsa yashigo.

ko da shahid yashiga parlourn tsaye yayi bakin k'ofa yana kallon yarima da yake kwance saman 3 seater cike da mamaki yace haba yarima kaifa kacemin after la'asar zamuje ammah jibeka baka shiryaba.

yarima batare da ya d'ago kai ya kallesaba cike da rashin damuwa yace ina kenan?

cike da jin haushi shshid yace au kana nufin ka mance inda zamuje? yanzu saboda Allah amaryartaka ce kamance da ita ko me?

ta6e baki yarima yayi saboda shi shaf ya ma mance da maganar zuwan da zasuyi wajen zarah.

shahid jinjina kai yayi yace lallai yarima ka cika d'an wulak'anci.

harara yarima yawurga masa yace toh ina ruwanka ai sai kazauna kajirani inshirya,

dariya shahid yayi yace ba fa ruwana ranka yadad'e yanzu dai kaje kashirya kafito muje dan Allah kar kadad'e.

ko kallonsa yarima baiyiba yashige bedroom d'insa.

tashi shahid yayi yakunna kallo sannan yabud'e freezer yad'auko maltina yazauna yana sha yace kafin wannan d'an rainin hankalin yafito.

bayan minti ashirin yarima suhail ne yafito sanye cikin dakakkiyar shaddarsa blue wadda tasha aiki, kansa sanye da hula kalar shaddar, kamshin turarensane ya ankarar da shahid daga kallon da yake dasauri yajuya yazuba masa ido yana kallonsa yace kai yarima wannan kyau haka saikace yau zaka angwance? gaskiya kayi kyau sosai natabbata ita kanta amaryar bazata ganekaba kar fa karikita d'iyar mutane,

yarima suhail wayoyinsa yad'auka batare da yace ma shahid komai ba yawuce zai fita,
Chapter 28 · 0% Book details