← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 102

Sashe 46

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hararta safiya tayi cikin wasa tace aikam dai daruwana tunda kika hana babban abokin ango zuwa dinner, mutane suna ta nemansa.
Da munsa rai tare zakuzo sai mukaji shuru ashe kina nan kin rikitamana prince dan tunda naga gayun da kikayi nasan dak'yar idan prince zai iya barinki kitafi batare da wani abuba

Ta6e baki Zarah tayi tare da tashi zaune tace kinsan dai halin yarima indai yasa kansa toh babu wanda zai iya hanasa dan haka nidai bani nahanasa zuwaba daman chan baiyi niyaba.

Safkowa tayi taje tashiga toilet tayi wanka bayan ta fito zama tayi tatsantsara kwalliyarta sannan tad'auko super English blue colour tasaka nan tamurza d'aurin kallabinta, sark'arta ta gold tasaka nan kyaunta yak'ara fitowa.

da k'arfe biyu daidai aka d'aura auren rahma da shaheed, auren da mutane dayawa suka hallara.

Saida su zarah sukayi sallar azuhur sannan suka shiga cikin gida da yake cike da jama'a.
Safiya jan Zarah tayi suka shiga part d'in sultana sadiya dayake a chan rahma tazauna,

A parlour suka tarar da sultana da sumayya sai wasu abokan sultana sadiya a zaune suna hira.
Cike da girmamawa su zarah suka gaishesu, nan abokan sultana sadiya suka amsa ammah banda ummah da sumayya da suka had'e rai.

Safiya ce takalli sumayya tace Aunty sumayya ina adda rahma?
Ta6e baki sumayya tayi tare da cewa kin bani ajiyartane?
Safiya murmushi tayi tace yi hak'uri dan naga tare kukene saisa natambayeki.
'Daya daga cikin k'awayen ummah ne tace kai sumayya miye nabak'ar magana? Kikasani ko k'awayen amaryane?

yamutsa fuska sumayya tayi tace nasan baku gane wacchan ba? tanuna zarah
Eh gaskiya bamu santaba wacece ita?

Ummah ce tace toh wacece banda munafukar kishiyarta.
'Daya daga cikin matan ne tace tace wlh sumayya banga laifinkiba toh waima ubanmi tazo yi mana a nan?
Sumayya tsaki taja tace gulmar da tasaba ko?

Safiya da zarah tsaye suke suna kallon ikon Allah , k'arama zarah da bata wani damuba dan tasaba da wulak'ancinsu Ummah.

Safiya ce tace haba bayin Allah daga tambaya sai cin mutunci? Sumayya cikin 6acin rai tace ke safiya kikiyayeni ko ranki ya6aci.
Ta6te baki safiya tayi tace Allah yabaku hak'uri sannan takama hannun zarah suka wuce wani room da taga wata abokiyar rahma ta shiga.

A chan saman gado suka hango amarya zaune taci k'walliya tasha kyau har ta k'oshi, gefenta k'awayentane suka zagayeta sunata hira.

Safiya jan zarah tayi sukaje suka zauna bakin gadon.
Zarah fuskarta d'auke da murmushi tace sannunku? ina wuninku?
Gabad'ayansu suka amsa sannan tacema rahma amarya kinsha kyau Allah yabada zaman lafiya.
Murmushi rahma tayi sannan tace Ameen nagode sosai,

'Daya daga cikin 'yan matan amaryace tace gimbiya wannan ma friend d'inki ce?
Girgiza kai rahma tayi tace matar Bro ce.
Kallonta sukayi sukace ba dai yarima ba?
Shi man amaryarsace 2 months kenan yanzu da aurensu, cewar rahma.

Gabad'ayansu suka juyo suka kalli zarah d'aya daga cikinsu tace ashe matansa biyu, masha Allah gaskiya tana da kyau sosai kamar prince.
Wata tace saisa baya kallon mata ashe yasan ya aje mata kyawawa a gidansa.
Sai tayita haifo mana kyawawan yara, cewar safiya.
Zarah da kanta yake sunkuye d'ago kai tayi tagallah ma safiya harara.

Dariya safiya tayi tace daga fad'in gaskiya sai harara?
shuru zarah tayi tak'yaleta, tanajib wasu daga cikin 'yan matan suna ta maganar yarima har taso taji haushi, sai daga baya suka canza hira.

Saida sukayi sallar la'asar sannan suka fito sukaje part d'in dada basu wani dad'eba suka koma na ummin yarima nan suka zauna suna hirarsu.

Saida akayi sallar magrib sannan aka d'auki amarya aka kaita gidanta da yake kusa da masarautar, zarah cikin motarta sukaje gidan amarya, kowa saida yayaba tsari da kyaun gidan anzuba mata gaya na'azo agani dan room nd bedroom 3 akayi mata, nan akaita santi daga k'arshe kowa yayi Allah yabada zaman lafiya sannan aka watse aka bar amarya da wasu abokanta.

Shaheed kallon yarima yayi da yake shirin barin gidansu yace haba yarima yanzu kana nufin bazaka rakani wajen amaryataba?
Harararsa yarima yayi yace akace maka dole sai naje? Idan su muhammad sukaje ai ya wadatas,
Cike da jin haushi Shaheed yace shikenan duk yadda kayi daidaine daman jiya k'in zuwa dinner kayi.
Wai kai baka ganin rahma k'anwace agareni akanme zan dinga shige muku.
Ta6e baki Shaheed yayi yace nikuma abokine wanda bakada kamarsa, toh laifine dan kaje?
Rik'o hannun yarima yayi yace please yarima kataimaka karakani d'akin amaryata.

Murmushi yarima yayi yace toh shikenan naji jeka ka ida shiryawa kazo muje dan ni yau dawuri nakeson komawa gida saboda agajiye nake.
Shaheed yace angama ranka yadad'e.

Wajen k'arfe tara suka raka Shaheed gidansa, Tunda suka shiga d'akin da amarya take yarima bai d'aga kai yakalli kowaba dannar wayarsa kawai yake, nan abokansu da na amarya sukaita tsokanar ango da amarya, duk yadda wasu sukaso yarima yayi magana ko sunsamu shiga ammah baiyiba dan nunawa yayi kamar baisan da zamansu, nan aka k'ara yi musu nasiha sannan suka tashi sukabar gidan,
yarima yana shirin shiga motarsa saiga wasu mata biyu sun iso cikin kwantar da murya sukaimasa sallama.
Rik'e yake da murfin motar ya amsa musu ciki-ciki.
Ahankali d'aya tace dan Allah in bazaka damuba munaso kayi dropping d'inmu.
Ta6e baki yarima yayi sannan yace ba hanyarmu d'ayaba kudaije wajen wad'anchan su k'ila hanyarku sukayi.
Matan kallon juna sukayi sannan d'aya tace toh please zamu iya samun phone number d'inka?
Wani irin kallo yarima yayi musu sannan yashiga motarsa yaja yabarsu nan tsaye.
A k'arshe saidai suka koma wajen sauran abokan ango suka shiga motocinsu Cike da takaicin abinda yarima yayi musu.

Yarima ko da yakoma gida wanka yayi sannan yabi lafiyar gado yakwanta.

Zarah ko daman koda tadawo dak'yar tasamu tayi wanka takwanta batayi tunanin daman zuwa part d'in yarima ba dan agajiye take.

_Toh mudai saidai muce amarya rahma da ango shaheed Allah yabada zaman lafiya_

*BAYAN SATI 'DAYA* 'yan bikki duk suka watse zarah tayi missing d'in safiya dan 'yan kwanakin nan da sukayi sun saba sosai, yanzu saidai zaman kad'aici kuyangintane suke d'ebe mata kewa tahanyar bata labarai masu dad'i.

Yau kasancewar girkin zarah ne kwance take saman bed d'inta kanta yana kallon ceiling da alamu tunani take, ringing d'in wayantane yakatseta ganin mai kiranne yasa tasaki murmushi dan rabonta da yarima tun lokacin bikki, saida takusan tsinkewa sannan tayi picking, yarima baijira tayi maganaba yace kihad'o min coffee yana fad'in haka yakashe wayarsa, fuskar zarah d'auke da murmushi tamik'e tanufi kitchen dan ko bakomai tasan yau zata sakasa a idanunta.

Bayan tagama had'a masa hijab d'inta tasaka kasancewar daman har tayi shirin kwanciya,

Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga yarima dasauri yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kansa yacigaba da dannar laptop d'insa, zarah k'arasawa tayi kusa tashi tare da zama gefensa sannan tace ga coffeen.
Yarima batare da ya kalletaba yace ina zuwa,
Haka yabar zarah rik'e da cup har kusan 5 minutes sannan yakar6a,
Mik'ewa zarah tayi zata tafi, batare da ya kalletaba yace ina zakije?
Murmushi zarah tayi tace zanje inkwanta ne.
Ban baki iziniba, cewar yarima da yake dannar laptop.
Marairaicewa tayi tace wlh bacci nakeji.
Ko inda take yarima bai kallaba.
Zarah turo baki tayi sannan takoma tazauna,
Yarima tagefen ido yana kallon yadda take ta fushi.

Zarah ita kanta har tagaji da zaman cikin ranta tace lallai mutumin nan ya raina min wayau miyake nufi da ni ne? Chan kuma sai tayi murmushi tare da cire hijab d'inta nan gashinta yabazu kallon yarima tayi da ya aje cup d'in yana cigaba da dannar laptop, amsar laptop d'in tayi ta aje gefe, yarima binta yayi da kallo cike da mamaki Ahankali tafad'a jikinsa tare da rungumesa cikin shagwa6a tace please kazo muyi bacci kaga har 11 fa tayi.
Wani iri yaji a ransa ammah yadake yace kikwanta mana ni sai nagama abinda nake.
Zarah d'ago kai tayi tana kallon cikin idonsa ahankali takai bakinta cikin nasa yarima daman kamar jira yake nan yacafke nan suka fara rikita junansu sun dad'e a haka sannan zarah tazare jikinta takwanta tare da jawo yarima jikinta dak'yar yasamu yakashe gloves.

yau makara sukayi sallar asuba har saida gari yafara haske sannan zarah tafarka duba time tayi taga 6:15am zaro ido tayi sannan takalli yarima da yake kwance yana bacci har takai hannu zata tadasa sai kuma tafasa, rigarta tajanyo tasaka sannan tafara k'ok'arin janye blanket d'in da yake rufe ciki,
Jin ana jan blanket yasa yafarka, zarah saida tasafka daga saman gadon sannan tace katashi yau munyi late.
Tana fad'in haka tazura hijab inta tafita tabar d'akin.

Yarima janye blanket d'in yayi cikin sauri yamik'e yashiga toilet yana mamakin yadda yamakara yau baisamu jam'i ba, chan kuma yaja tsaki da yatuno basuyi bacci da wuriba.

Zarah ma ko da takoma part d'inta saida tatsarkake jikinta sannan tayi sallah, bayan tagama kitchen taje tashiga nan tafara tunanin me zata had'ama yarima na breakfast, chan kuma sai tayi tunanin tahad'a mai kunun gyad'a dan tasan yana sonsa sosai.

Nan tad'aura ruwan kunun sannan tafere doya tadafa, bayan ta dafu tadaka tayi yamball.
Bayan ta gama wanka tashiga tayi da tafito tashirya cikin swiss less d'inta, veil tayafa sannan taje tad'auki basket d'in taba wata kuyangarta tarik'e suka nufi part d'in yarima

A gaban dressing mirror tagansa tsaye yana fesa turare, d'an rissinawa tayi tagaishesa, tacikin mirror yarima yake kallonta saida yagama fesa turaren sannan ya amsa.
Fuskarta d'auke da murmushi tace breakfast d'inka na dining,
Shuru yarima yayi har ta juya zata fita ahankali yarima yace kije kishirya in ajeki gida.
Dasauri zarah tajuyo cike da jin dad'i tace yanzu?
Eh, ammah idan baki shirya zuwaba shikenan.
Zarah cikin sauri tace na shirya kagani?
Yarima kallonta yayi sannan yazo yawuce yafito yanufi dining,
Chapter 46 · 0% Book details