← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 102

Sashe 4

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sumayya gyara zamanta tayi tace ai lafiya lou miskilanci kau saidai abinda yayi gaba, zinat tace ke ya batun first night d'inku,

dariya gimbiya sumayya tayi tace ai babu abinda yagane game da hakan kinsan nayi amfani da magungunan da kikasa aka had'a min wlh har tausayi yabani ganin bai gane komai ba.

ta6e baki zinat tayi tace ke inbanda abinki wa yace miki ana tausayin maza indai kina lalla6a miji ai sai yarainaki, shawarace zan baki daga inda miji yafara d'aga miki murya ke kinuna masa kinfi sa hauka,

sannan ba kowane lokaci zaki dinga ba mijinki kankiba saboda idan kika saba masa da haka toh sai kin gunduresa yaji ya gaji da ke daga k'arshema sai kiga kishiya

zaro ido sumayya tayi tace kishiya kuma? zinat gyad'a kai tayi tace eh man ai wlh namiji ba a basa amana ke nifa saboda tsoron halin maza yasa nakasa aure nake cin karena babu babbaka dukiya ce natara bakin gwargwado a lokacin da kuma naji ina buk'atar namiji ga mazanan birjit sai na za6a, inma macen nake buk'ata kema kin sanni.

dariya sumayya tayi tace hakane k'awata wlh kin kawo shawara mai kyau, ke nima fa sonake inga natara dukiya dan ban had'a kud'i da komai ba tunda ga mulki ga miji kinga dukiya yarage dan haka business zan fara. saidai anya zamu kwashe lafiya da yarima?

harararta zinat tayi tace kefa matsalata da ke wani lokacin baki da ganewa ammah asannu zan ganar da ke yadda zaki fahimta, ammah nagargad'eki da lallashin miji bare ma wannan mijin naki idan yashareki kema kifita harkarsa ke da nice da nasan yadda zan juyasa yakoma a tafin hannuna,

gimbiya sumayya tace hmm ba dai yarima ba anya akwai macen da zata iya juyasa?
zinat tace kefa matsalata da ke kenan bakida ganewa, kedai kigwada kigani dakanki zaki bani labari, yanzu dai taso mushiga daga ciki.

mik'ewa sumayya tayi tana dariya zinat tana binta a baya suka shige bedroom,
a ranar haka zinat tawuni gidan gimbiya sumayya tana k'imsa mata makirci iri-iri har saida taga gimbiya sumayya ta hau ta zauna sannan tabarta.

Tun daga ranar gimbiya sumayya tadaina shiga sabgar yarima shima shareta yayi yacigaba da hidimar gabansa,

yarima tun bai damuwa har abun yazo yafara damunsa yanzu tsawon wata d'aya da aurensu tun satin farko rabonsa da gimbiya domin ko d'akinsa bata zuwa.

yau da dare kasa daurewa yayi dan haka yatashi yasaka alkyabbarsa yafito yanufi 6angaren gimbiya sumayya, da key d'insa yabud'e direct bedroom d'inta yashiga chan tsakiyar gado yahangota ta baje sai baccinta take ahankali yataka yaje yahau saman gadon.

gimbiya sumayya da take bacci jin ana shafata yasa tafarka, da mamaki take kallon yarima, chan kuma sai tad'aure fuska tace lafiya?

yarima cigaba yayi da abinda yake kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace sumayya yanzu saboda Allah hakan da kike min kina ganin kin kyauta? hak'k'ina nazo kar6a,

gimbiya sumayya janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tana jin dad'in shawarar da k'awarta tabata ganin yau dakansa ya aje girman kan yazo d'akinta,

ganin yarima suhail yana shirin rikitata yasa tajanye jikinta gefe tace haba dan Allah yarima wai menene haka nifa a gajiye nake.

da mamaki yarima yake kallonta yace haba sumayya saikace wadda tayi wani aiki nidai yanzu kibari inyi inyaso daga baya sai kiyita baccinki.

gimbiya sumayya komawa tayi takwanta tare da juya masa baya tace ni ba zan iyaba gaskiya, yarima binta yayi yana lallashi dakyar ta amince masa shima saida taita masa k'orafin ta gaji kan dole a k'arshe yahak'ura yabarta batare da ya ida samun nutsuwaba,

toilet d'inta yashiga yayi wanka sannan yadawo yakwanta tare da juya mata baya cike da mamakin yadda sumayya tasauya hali .

gimbiya sumayya ko murna takeyi ganin ta d'an ci nasara har Yarima suhail ya zo d'akinta yau, kuma ya aje girman kai da sarautar ya lallasheta.

Tun daga lokacin yarima shi yake biyota d'akinta ko da ace ya yi mata wulak'anci a wani wajen ita kuma sai ya nemeta take ramawa sai ya-yi dagaske yake samun hak'insa a wajenta ahaka suka haura wata shidda ammah ko 6atan wata bata ta6a yi ba,

dada ta fi kowa damuwa domin tisata gaba take a d'aki tana tambayarta ko akwai abinda take sha ita dai gimbiya a'a take cewa, dada tace a'a gimbiya indai akwai abinda kikeyi, gimbiya saidai tayi dariya tace dada inda ina yin wani abu ai da kun gane, dada saidai tace toh Allah yakawo.

ko da yarima yazo yagaishe da dada bayan sun gaisa dada tace yarima wai har yau ba wani labari?

yarima shuru yayi saida yayi kusan minti biyu sannan yace dada labarin me kuma?

dada tace hmm ciki mana.

murmurshi kawai yayi yace dada ai haihuwa lokacine, idan da darabo zamuyi.

dada tace toh Allah yakawo mai albarka yarima yace Ameen.

sannan yarima yatashi yafita dogarawansa da suke tsaye bakin k'ofa suna ganin ya fito nan suka fara masa kirari yana gaba suna biye da shi tun kan ya isa wajen jerin motocinsa da yasa aka tanadar masa dan yafita dasauri aka bud'e masa dank'areriyar motarsa da take tsakiya nan yashiga baya yahakimce sannan dogarawa suka shiga sauran motocin akasa tashi a tsaka nan aka kama hanya.

asibitoci yaje yakai ziyara yaduba marassa lfy yayi musu kyauta sannan yawuce gidan marayuwa yabada kayan abinci kowa yaji dad'in ziyarar da yakawo domin daman halinsane kyauta,

daga nan suka kama hanyar gida, ko da suka isa bai shigaba saida yatsaya yasa aka tara ma'aikatansa yaraba masu kud'i nan suka zube suna ta godia daganan yawuce part d'insa yana shiga yacire kayan jikansa yafad'a toilet yayi wanka, bayan ya shirya saman gado yafad'a yana hutawa bud'e k'ofar da akayine yasa yabud'e idonsa dayake a lumshe,

ganin gimbiya sumayya ce yasa da mamaki yakalleta domin yasan bata shigowa d'akinsa sai idan tana buk'atar wani abu, maida idanunsa yayi yalumshe,

takowa tayi tahau saman gadon tazauna gefensa ganin baida niyar bud'e ido yasa tace ashe har kadawo tun d'azun nake aikowa adubomin idan kana nan,

yarima batare da ya bud'e idanunsaba yace ya akayi kika shigo min d'aki ba'a fad'a miki nace kar wanda yashigo ba? gimbiya sumayya murmushi tayi tace yanzu dan zan shigo d'akinka har sai anbani izini a matsayina na matarka?

banza yarima yayi yakyaleta, ganin baida niyar tanka mata yasa takwanta a jikinsa ta d'auka zai gwalisheta ammah taji ya yi shuru baice komai ba, dan haka takai hannu tana shafa fuskarsa daga nan tafara kissing d'insa daman abu ga mai nema nan yarima yabiye mata,

ya yi mamaki yadda yau bata hanasa kantaba domin yasan hali da ya fara zata fara cewa ta gaji, ammah yau saida yagaji dan kansa sannan yabarta.

rungume take a jikinsa cikin shagwa6a tace my sweetheart dan Allah inaso kabani 2 million,

yarima baiyi mamakin jin hakan daga garetaba, domin daman yasan za'a rina ba zata ta6a bashi kantaba sai da dalili,

bud'e idonsa yayi yasafkesu akan fuskarta kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace mezakiyi da kud'i?

Sumayya batare da damuwaba tace business nakeso inyi kaga zaman hakanan ai baya yuwuwa zamu had'a jari da k'awata zinat zata dinga zuwa tana saro mana kaya, zamu bud'e babban boutique a chan Abuja.

yarima tunda tafara bayanin yatsareta da ido har takai aya sannan yace yanzu ke bakiji kunya ba kice zakiyi kasuwanci akwai abinda narageki da shi ne?

gimbiya Sumayya d'aure fuska tayi tace kai fa matsalata da kai kenan to shi business dole sai marar wadata yakeyinsa?

yarima janye jikinsa yayi yace idan ke bakida hankali toh ni ina da shi kuma ba zakiyi ba, yana gama fad'in haka yawuce yashige toilet domin yayi wanka.

gimbiya Sumayya binsa tayi da kallo cike da takaici tace tsiyata da kai bakasan arzik'iba saida nagama baka kaina sannan kanemi kawulak'antani toh wlh baka isa kahananiba dan haka muzuba mugani,

tana gama fad'in haka tajanyo kayanta tasaka tatashi fuuuuu tafita tabar d'akin.

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*~Sak'on gaisuwata agareki Mummyn khalil fatana Allah yabaki lafiya, Allah yasa zakkar jikine~*_

_kuna ina Kuzo yau ranar takuce wlh ina ji daku har cikin zuciyana *My k'anwa Safiyya Aliyu, Mrs Abubakar, Ma zeenart, Hafsat Kanty, Cool Angel, Chubby, Asma'u Yusuf Beji, Husnah, Mugirat Musa, Maman Sadiq, My k'anwa Khairyy, Maman Haidar, Hadiza Abubakar, Maman Amira, Kubcy Auwal, Dr Xeey Xeey, Aisha Baba Audu, ummu walid nd Abdul, Maman khaleesat, Sadiya Abubakar, Billy....* da ma sauran wad'anda ban lissafoba, wannan page d'in nabakushi Allah yabar k'auna😘_

page 4⃣

tana fita daga d'akin yarima part d'inta tawuce ko ta kan su jakkadiya batabiba da suke tsugunne suna ta kwasar gaisuwa wucewa tayi tashige bedroom d'inta, wayarta tad'auka takira zinat, zagaye d'akin tashiga yi tak'agara zinat tad'aga wayar ammah har tatsinke bata d'agaba, tsaki gimbiya taja tace itafa matsalata da ita ayi ta kiranta sai taga gama take d'auka,

k'ara Kiranta tayi bugu biyu tad'aga
ko gaisawa basuyiba tace zinat kinajin wancan d'an rainin hankalin wai bazai barni inyi business d'inba

zinat cikin tsawa tace what! shi har ya isa yahanaki kuma kihanu? gambiya tace hmm yoh ke kina tunanin ma zan hanu?

zinat dariya tayi daga chan 6angaren tace wlh innice yanemi yaraina min hankali tuni zan nuna masa iyakarsa ke ak'arshema zan iya kashe auren tunda dama dashi yake tak'ama,

gimbiya zaro ido tayi kamar tana gaban zinat tace kirufa min asiri ai wlh ba zan iya rabuwa da shi ba saidai nasan ta inda zan 6ullo masa kibarni da shi.

zinat tace toh shikenan nidai ina jira cikin week d'innan inga alert saboda so nake inje ingama komai dawuri indawo,

gimbiya sumayya tace toh shikenan kar kidamu, nan sukayi bankwana.

suna gama wayar gimbiya ummanta takira saida takusan tsinkewa sannan sultana sadiya tad'aga da sallamarta, sumayya ko gaisheta batayiba tace ummana wlh yarima baida mutunci
Chapter 4 · 0% Book details