← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 102

Sashe 25

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zarah tsagaitawa tayi da kukan da take tace bakaji abinda nace bane? miji fa akayi min?

Malam bello daurewa yayi cikin rashin damuwa yace najiki mana, toh menene Zarah? dole kiyi hak'uri kibi za6in iyayenki domin ba zan ta6a yadda inbaki shawara akan kibijire ma iyayenkiba, Allah daman ya k'addara ba matata bace ke, ita rayuwa duk yadda tazo maka kayi hak'uri kakar6eta domin shi aure nufine na ubangiji babu mai auren matar wani kar kimance mune muke haukanmu ammah Allah yariga da yatsara ma kowa yadda rayuwarsa zata kasance wlh nabaki goyon baya kiyi ma iyayenki biyayya insha Allahu zakici ribar biyayyar da zakiyi musu kema kuma Allah zai baki wad'anda zasuyi miki biyayya domin su iyaye sun wuce abin wasa yakamata muguji fushin iyaye, ni yanzu shawarar da zan baki itace kiyi ma iyayenki biyayya insha Allahu zakici moriyar hakan.

Zarah da tunda yafara maganar tazuba masa ido hawaye kawai suke zuba daga idonta dakyar tabud'e baki tace yanzu kana nufin ka rabu da ni?

malam bello murmushi yayi wanda iyakansa baki sannan yace tabbas Zarah narabu da ke domin ko nine bazan iya bujirema umirnin iyayenaba saidai inaso kisani sonkine da nake yajawo hakan kuma har abada bazan daina sonkiba saidai inyi addu'an Allah yarage min sonki a cikin zuciyana, fatana Allah yasa wanda zaki aura yasoki fiye da yadda nake sonki, kema inaso kiyi min alk'awali d'aya shine zai tabbatar min da kina sona.

Zarah cikin kuka tace wane irin alk'awali kakeso inyi maka wlh indai shi zaisa kagane ina sonka toh na amince koma minene kafad'a.

malam bello d'an guntun murmushi yayi sannan yace inaso kiso mijinki fiye da yadda kike sona sannan kinuna masa kulawa kar kisa6a masa kiyi masa biyayya indai ba hanyar Allah yanemi yakauceba.

Zarah girgiza kai tashiga yi tace bana tunanin zan iya son wani fiye da yadda nake sonka bazan iya d'aukar alk'awalin da nasan bazan iya cikawaba.

malam bello juyawa yayi cikin dabara yagoge hawayen da suke shirin zubo masa sannan yace wannan zai shaida min da cewar bakya sona.

Zarah girgiza kai tashiga yi tace malam kar kace haka wlh ina sonka shikenan na amince zanyi duk abinda kace.

malam bello juyowa yayi yace dagaske kin d'aukar min alk'awali?

gyad'a masa kai tayi tace eh saidai kayi hak'uri ba zan iya tursasa zuciyana taso wani fiye da yadda take sonkaba.

murmushi malam bello yayi yace natabbata zaki ma soshi indai ya amsa sunansa namiji wanda yadace mace taso, dan haka ina miki fatan alkhairi zarah idan nasa6a miki kiyafemin domin inaso wannan takasance had'uwarmu tak'arshe.

zarah fashewa tayi da wani sabon kukan tare da durk'ushewa k'asa cikin kuka tace nagode sosai malam bello hak'ik'a kai masoyinane nagaskiya tabbas duk macen da ta aureka tayi dacen miji fatana Allah yabaka wadda zata soka fiye da ni, bazan ta6a daina yi maka addu'a ba domin kabani gudunmawa sosai a rayuwana wlh *K'ADDARA CE* kawai tarabani da kai ammah ka cancanci kasancewarka mijina.

malam bello murmushi yayi yace kar kidamu zarah daman kyaun kowane musulmi ya yarda da k'addara me kyau da marar kyau, ina miki fatan alkhairi nabarki lafiya .

juyawa malam bello yayi yatafi yana jin wani k'unci acikin ransa ji yake inama yayi kuka ko yasamu sauk'in abinda yake ji, yana jin kukan zarah tana ta kiransa ammah yak'i juyowa gudun kar shima yaga yanayin da take yayi kuka.

zarah da take tsugunne tana kuka tare da k'walah masa kira saida taga yayi mata nisa sannan tatashi takoma gida tafad'a saman katifarsu tacigaba da kukanta.

Tun daga ranar zarah da malam bello suka daina waya saidai text shima na gaisuwane kawai sukeyi, daurewa kawai take tacigaba da addu'a akan Allah yaza6a mata wanda zaifi zama alkhairi, su yaya Rauda su suke k'ara kwantar mata da hankali da tayi hak'uri tacigaba da addu'a.

**** ***** ***** ****

memartaba kamar yadda yafad'a hakan kuwa akayi domin kiran yarima suhail yayi yace yafad'a ma iyayen yarinyar zuwa gobe zasu aiko da komai na neman aure domin basuson aja lokaci dayawa.

yarima suhail a firgice yad'ago yakalli memartaba yace ranka yadad'e duk dawuri za'ayi haka? nad'auka za a bi Komai ahankali.

murmushi memartaba yayi yace suhail kenan toh me zamu jira? k'ara dai muyi komai dawuri domin banaso ana d'aukar lokaci dayawa ammah indai iyayen yarinyar suka nemi aja lokaci toh lafiya lau saidai bazanso hakaba

yarima yace toh ranka yadad'e.

memartaba yace koma mi kenan kaje kuyi magana da waziri domin shine zaije yanemo maka auren sai ku yanke shawarar yadda zaku tafiyar da komai.

duk'awa suhail yayi yakwashi gaisuwa sannan yayi ma memartaba sallama yatashi yafita yanufi 6angaren iyayensa.

yana shiga daidai lokacin daddynsa yana shirin fita ummi tana bayansa cike da girmamawa yagaishesu sannan suka koma suka zauna, nan yake fad'a musu yadda sukayi da memartaba gabad'ayansu sun nuna farin cikinsu.

ummi tace toh zan kira iyayen yarinyar infad'a musu halin da ake ciki, sannan driver d'in da yakaini shine zai kai su waziri.

suhail ahankali yace toh ummi.

daddy murmushi yayi yace son kaima ai yakamata kaje kagano matar taka domin baidaceba ace baka san wadda zaka auraba.

yarima suhail sosa kansa yayi yace ranka yadad'e ba ma sai najeba hakan ma lafiya lou zan zauna da ita, ko da ace ban santaba a yanzu, zan santa bayan aurenmu.

ummi tace haba suhail ammah..... hannu da daddy yad'aga matane yasa tayi shuru, daddy yace shikenan zaka iya tafiya.

yarima godia yayi ma iyayensa sannan yatashi yafita cike da jin haushin auren had'in da ake shirin k'ara masa a karo na biyu.

daddy kallon ummi yayi bayan yarima ya fita yace kibarsa kawai tunda ya amince zai aureta kar mumatsa masa akan dole sai yaje yaganta.

ummi jinjina kai tayi tace hakane ranka yadad'e fatana dai suhail yasota domin zarah ta cancanci kowane namiji yasota.

murmushi sultan Ahmad yayi yace zai ma sota insha Allah yanzu dai bari inje muyi magana da waziri yadda za'a tafiyar da komai.

cike da jin dad'i Sultana Bilkisu tace adawo lafiya ranka yadad'e.

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Yau Ranar takuce *'yar mutan zariya mummyn uswan nd Mummyn Fadyl* wlh ina ji daku irin sosai d'innan😘_

*PAGE* 1⃣9⃣

ummi kiran mama tayi a waya lokacin mama tana zaune tsakar gida ita da abbah suna cin abinci, mama jin wayarta tana ringing yasa tad'auko ganin sunan sultana bilkisu da yabayya yasa tazaro ido tare da cewa malam sultana ce take kirana.

Abbah yace toh toh d'aga muji abinda zatace, mama saida ta saita nutsuwarta sannan tayi picking d'in call d'in tare da yin sallama.

daga chan 6angaren sultana bilkisu ta amsa mata cike da fara'a, nan suka gaisa cike da girmama juna, ummi tace ya su zarah dafatan duk suna lafiya?
mama tace lafiya lou, nan ummi take shaida mata akan maganar neman auren zarah da za'a zo gobe.

mama kallon abbah tayi da yake sauraren firar tasu, alama yayi mata da tace toh.
mama tace toh ranki yadad'e Allah yakaimu.
cike da jin dad'i ummi tace Ameen mungode sosai, ammah idan mahaifinsu yana kusa kiban shi inaso muyi magana inkuma baya kusa idan yadawo zan kira,

mama tace ranki yadad'e yana ma kusa gashi, nan tamik'a ma abbah waya.

Abbah kar6a yayi tare da yin sallama nan suka gaisa cikin mutunta juna, sultana bilkisu tace yauwa daman akan tsaida rana ne agaskiya mu a Royal family d'inmu ba'a yin baiko ad'auki lokaci shine nakeson in rok'eka alfarma dan Allah kar asa lokaci dayawa,

Abbah Jim yayi yakasa cewa komai.
sultana bilkisu tace kayi mamakin jin haka ko? kuyi hak'uri wlh tsarin masarautarmu ne haka.
Abbah cike da damuwa yace ranki yadad'e gaskiya hakan bazai yuwuba domin mu ba halinmu d'ayaba idan mukace ayi bikkin cikin gaugawa toh gaskiya zamu cutu tunda bamu fara tara komaiba da dai ataimaka asa ranar da d'an nisa domin musamu muyi mata abinda Allah yahore mana.

daga chan 6angaren ummi murmushi tayi tace kar kadamu ni zan d'aukema zarah duk wani abu da iyaye yakamata suyi ma 'ya'yansu wlh ko da ba d'ana zata auraba zan iya yi mata haka.

Abbah yace a'a ranki yadad'e kar hidimar tayi yawa kibari dai zamuyi.

ummi tace kar kadamu tunda nace zanyi kubarsa kawai wannan yazama sirri tsakanina da ku domin bana fatan wani yasan da hakan saboda gori da wulak'anci

maganarta tayi ma abbah dad'i sosai ganin yadda take Royal Family ammah bata d'auki kanta komai ba tasan abinda yadace da wanda bai daceba, muryar sultana bilkisu yaji tana cewa bawai ina nufin naraina k'arfinkuba wlh ko d'aya ko da ace ba zarah bace zan iya yi ma wata barema zarah da zata auri jinina dan Allah ka amince ma buk'atata a karo na biyu, malam yace toh ranki yadad'e mungode sosai Allah yabiyaki da gidan Aljannah,
ummi tace Ameen nice da godia da kuka amince min sai kunjimu, agaishe da su zarah.
malam yace haba bakomai ranki yadad'e, su zarah zasuji.

bayan sun gama wayar Mams kallon Abbah tayi tace malam toh yanzu ya za'ayi? wannan neman aure ba ko shiri.

Abbah yayi murmushi yace gaskiya mutanen nan suna da kirki sosai bamuda abinda zamu biyasu da shi saidai muyi musu addu"a.
Chapter 25 · 0% Book details