← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 102

Sashe 18

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sultan Ahmad zuba ma matar tasa ido yayi yana kallonta domin yasanta akwai hak'uri duk abinda za'ayi mata batanuna 6acin ranta saidai idan ankaita bangone, Sultana bilkisu cigaba tayi da cewa tun lokacin da d'ana yayi aure baida kwanciyar hankali domin kwatakwata bai samun nutsuwa, kula da tattali a wajen matarsa Sumayya, ba wai shi yafad'a minba kawai dai nafahimci haka kaduba kaga yadda yarame koda yarima baya fad'in matsalarsa saboda zurfin cikinsa ammah yanayinsa kawai zaka kallah kagane yana cikin matsala, girgiza kai tayi tace ya za'ayi ace da matarsa ammah yana shan ruwan lipton da lemon, ranka yadad'e ina tsoron ranar da d'ana zai kasa jurewa har yafara neman mata, bawai fata nakeyi masaba kawai dai ina tsoron hakan domin shima mutum ne kamar kowa,
rik'o hannun sultan Ahmad tayi tare da durk'usawa k'asa tace ranka yadad'e idan maganganuna sun 6ata maka rai kayi hak'uri ammah ina tausayin halin da d'ana yake ciki, Sultana Bilkisu tana kaiwa nan tasake fashewa da wani sabon kukan.

Sultan Ahmad cike da tausayi yarik'o hannun matar tasa yamik'ar da ita tsaye yarungumeta yace Bilkisu nima ina lura da lamurran Suhail narasa ya zanyi ne domin ko bakomai d'iyar d'an uwana yake aure narasa ya zanyi in magance matsalarnan domin ina tsoron abinda zai samo min matsala ni da d'an uwana.

Gimbiya Bilkisu d'ago kanta tayi tana kallon mijin nata tace ammah shi d'anka fa kaduba kaga matsalar da take shirin 6ullomasa dan Allah kataimaka kaduba lamarin yarima Suhail domin yana buk'atar taimakonmu.

Sultan Ahmad rik'o hannun matarsa yayi sukaje bakin gado suka zauna yace Bilkisu nima inajin Suhail sosai a cikin raina kikwantar da hankalinki zanyi shawara muga yadda zamu 6ulloma lamarin cikin ruwan sanyi kema inaso kije kiyi tunani a kai kidaina sanya damuwa a ranki kinji.

Sultana Bilkisu cike da gamsuwa da maganar mijin nata ta jinjina kai tare da yin murmushin jin dad'i, shima Sultan Ahmad murmushin yayi sannan yashiga goge mata hawayen da suke fuskarta.

godia tayi masa tare da mik'ewa tsaye, kallonta yayi yace Bilkisu ina kuma zakije? ai nad'auka zuwa kikayi kitayani hira?

murmushi tayi tace kayi hak'uri d'ana yana parlour yana jirana bari inje insallamesa sai indawo.

Sultan Ahmad shima murmushi yayi yace toh shikenan sai kin dawo.

Sultana Bilkisu d'an rissinawa tayi cike da girmamawa tace nabarka lafiya sannan tajuya tafita tabar d'akin,

Yarima Suhail ko da yagama shan lipton d'in komawa yayi yajingine kansa da kujerar da yake zaune yana jiran mahaifiyartasa tafito anan bacci yafara d'aukesa.

Sultana Bilkisu ko da tashigo ganin d'an nata yana bacci yasa tazauna gefensa tare da d'aura kansa saman cinyarta.

ahankali suhail yabud'e idonsa sanin mahaifiyarsa yasa yasakarmata murmushi tare da maida idanuwansa yalumshe,

itama sultana Bilkisu murmushin tayi nan tashiga shafa gashin kan d'an nata cike da so da k'aunarsa, a gefe guda na zuciyarta tausayinsace ta baibayeta.

**** **** *****

mama ce da su zarah zaune tsakar gida suna k'ulla zo6o da kunun aya suna fira cike da nishad'i, Aysha ce takalli zarah tace wai yaya zarah yaushene ma zakuyi walimar saukarku ta alk'ur'ani?

Murmushi zarah tayi tace kedai Aysha kin cika zumud'i sai fa nan da sati biyu kinga ai da d'an sauran lokaci.

Mama tace kud'in ma da kikace kina buk'ata suna nan ajiye tun jiya Abbanku yabani inbaki idan kin tashi tafiya islamiyya sai kituna min inbaki kikai dan kar ma inta6asu.

Zarah cike da jin dad'i tace nagode sosai Allah yak'ara girma da rufin asiri.

gaba d'ayansu sukace Ameen, Rauda tace toh anko d'in da zakuyi fa?

Zarah murmushi tayi tace bazanyi wannan ba yaya Rauda domin bazan matsa ma kaina ba abinda nakeda hali shi zanyi saidai in naje suhanani shiga taron.

Mama tace a'a zarah baridai muga abinda hali zaiyi idan da hali ai sai ayi miki.

zarah tace a'a mama kar kud'aura ma kanku d'awainiya abarsa kawai.

Mama tace zarah kibari dai muga abinda hali zaiyi idan da rabo ai za'ayi.

Aysha tayi karaf tace aikam dai dole ayi anko d'innan dan walima zamuyi sosai, nima zan bada gudumuwata.

Dariya Rauda tayi tace jarin sana'arki zaki bamu ko?

Aysha tace sosai ma ai har nafara tari ribar nake zubawa asusu.

dariya suka sanya mata zarah tace gaskiya nagode sosai 'yar uwata da k'aunar da kike nunamin.

Aysha murmushi tayi tace wannan kuma halinkine domin ke kike nuna mana k'auna ta gaskiya.

A islamiyya zarah ce da k'awarta zaune suna d'an ta6a hira kafin malam bello yashigo, khairy kallonta tayi tace wai k'awata me kike shirya mana na walimar nan?

murmushi zarah tayi tace abinda hali yabani domin ba zan matsa ma kainaba abinda nake da halinsa shi zanyi dan ni ko ankoma bana tunanin yinsa.

Khairy zaro ido tayi tace kai zarah dan Allah kiyi anko d'in kinga kowa fa zaiyi ya za'ayi ace kekad'aice ba zakiyiba.

zarah murmushi tayi tace ba zan damuba domin kowa da bazarsa yake taka rawa, abinda Allah yahoremin shi zanyi.

Khairy jinjina kai tayi cike da gamsuwa da maganar k'awartata sannan tace toh Allah yashige mana gaba.

zarah tace Ameen ya rabb, shigowar malam bello ne yasa ajin aka nutsu daga nan aka fara darasi.

bayan angama anyi addu'a antashi zarah tace muje khairy inkai ma malam kud'in walimana,

a office suka samu malam hambali bayan sun gaishesa ya amsa musu, zarah tace malam ga kud'in walimata,

malam hambali yace zarah banda kud'in da kika biya ko k'arine muka samu?

zarah da mamaki take kallonsa tace ni kuma nabiya kud'i? da yaushe?

murmushi malam hambali yayi yace Malam bello yazo yakawo kud'inki.

Zarah da khairy kallon Juna sukayi sannan sukayi ma malam hambali sallama suka fita daga office d'in.

A wajen islamiyya suka hango malam bello tsaye ya zuba ma k'ofa ido da alamu zarah yake jira yaga fitowarta,

zarah saida suka d'anyi gaba sannan tad'auko wayarta takira malam bello tace gamu muna jiranka.

suna gama wayar malam bello yazo yasamesu fuskarsa d'auke da murmushi yayi musu sallama nan suka amsa masa tare da k'ara gaishesa.

zarah tace malam naje biyan kud'in walima shine aka shaida min ka biya nagode sosai ammah gaskiya bazanso kadinga matsama kankaba tunda kaga kaima karatu kake dan haka ga kud'inka na maido maka.

malam Bello yace a'a zarah ni dan Allah nayi miki dan haka bazan kar6aba, kuma kidaina maganar karatu nake koma me nakeyi ai dan ina da halin yi miki da ace banda su ai da bazan mikiba.

zarah tace hakane saidai ina tsoro kar asamu matsala aurenmu yak'i yuwuwa, malam Bello murmushi yayi yace kar kidamu ko da ace ban aurekiba wannan nasan *K'ADDARA CE* kuma wani baya auren matar wani dan haka kikwantar da hankalinki.

murmushi zarah tayi tace nagode sosai malam da taimakon da kakeyi min Allah yataimakake kamar yadda kake taimakona.

malam Bello yace kar kidamu ai yi ma kaine, yanzu muje inrakaki gida naga magrib ta gabato kuma k'awarki ta tafi ta barki,

zarah murmushi kawai tayi nan suka jera da malam Bello suna tafiya suna hira har saida yarakata har k'ofar gida sannan sukayi sallama yatafi itakuma tashiga gida.

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

page 1⃣4⃣

Zarah ko da tashiga gida d'akin mama tashiga ta tarar da mama tana linkin kaya ganin zarah yasa tasakarmata murmushi tare da cewa 'yan makaranta andawo?

zarah ma murmushi tayi tace eh mama dafatan mun sameki lafiya?

mama tace lafiya lau, nan zarah takama mata suka cigaba da linke kayan, cike da nutsuwa zarah tad'auko kud'in tamik'a ma mama tace mama ga kud'in da kuka bani.

mama da mamaki take kallonta tace zarah ya haka? ya naga kin maido kud'in?

murmushi zarah tayi tace mama daman da naje inbiya shine akace malam bello ya biyamin kuma na kai masa kud'in yace bazai kar6aba shi dan Allah yayi min nayi-nayi yakar6a ammah ya k'i.

mama tace Allah sarki gaskiya yana d'awainiya dayawa mungode sosai Allah dai yabiyasa, yanzu kud'in ki aje wajenki kinga sai kiyi anko d'in da su,

zarah tace toh mama nagode sosai Allah yak'ara girma da rufin asiri.

mama cike da jin dad'i tace Ameen 'yar albarka nidai fatana a kullum Allah yakawo muku mazaje nagari kuyi aure.

zarah dagudu taficce tabar d'akin cike da jin kunya, mama dariya tayi sannan tacigaba da linkin da takeyi.

tun ana saura kwana hud'u ayi walimar aka bugo Invitation card aka gayyaci mutane da dama daga cikin wanda aka kaima katin gayyata har da maimartaba.

A gidansu zarah suma shirye-shirye suke daidai k'arfinsu, Abbah bakin gwalgwado yasiyo mata abinda zata raba ma abokanta da 'yan uwa.

malam Bello ma ba'a barsa a bayaba domin carton din lemu yasiyamata yakai mata dakyar yasamu zarah takar6a.

ana gobe za'ayi walimar gidansu zarah tun dare aka fara shirye-shiryen abinda za'a raba ma mutanen da suka gayyata kasancewar da k'arfe goma za'ayi walimar.
_______________

yarima tun daga lokacin yafita harkar sumayya ganin tana neman rainasa akan hak'insa yasa yajefar da ita gefe yacigaba da hidimarsa, sumayya tun tana daurewa itama taji bata iya daurewa.

yau ma kwance take tana ta juyi saman makeken gadonta tsaki kawai takeja tana neman mafita, chan tayi nisa tace daman ace zinat zatazo da nad'an samu sauk'in abinda nakeji, ammah bari inkirata ko ta flight ce tabiyo tazo yau, wayarta tajawo takira zinat ammah kashe wayartake,

tsaki sumayya taja tare da wullar da wayar tace matsalata da ita kenan ayita nemanta ba'a samu.

Sultana Bilkisu ce zaune a turakarta tana kallon wata drama a faskekiyar TV d'in da take manne a bangon d'akin, gefenta kuyangine zaune k'asa suna jiran jin umurni daga wajen mai d'akintasu.

Sultan Ahmad ne yashigo da sallamarsa dasauri duk suka zube suna kwasar gaisuwa, cike da fara'a ya amsa musu, nan suka tashi suka ficce daga d'akin ahankali yataka yaje inda matarsa take zaune tazuba masa ido fuskarta d'auke da murmushi,
Chapter 18 · 0% Book details