← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 102

Sashe 73

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Memartaba d'aga masa hannu yayi yace dakata bana buk'atar jin komai daga wajenka abinda idona yagane min ya isheni.

Daddyn yarima kallon yarima yayi cike da takaici yace suhail ka ban kunya kana gani yadda nake zaune da d'an uwana lafiya ammah karintse ido kakarta min rashin mutunci har haka, yanzu da wane ido kakeso ink'ara kallonsa.

Girgiza kai yarima yashiga yayi yace kayi hak'uri daddy wlh nima ba a son raina hakan takasanceba.

Memartaba a hankali yafurta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, kallon kowa yayi d'aya bayan d'aya sannan yamaida kallonsa ga dada yace kin gani ko? Ni yanzu banma san wane hukunci zan yanke masaba ko zan samu d'an sauk'i a raina.

Dada kallon yarima tayi sannan tace ma memartaba ranka yadad'e kaga ita tagaban goshin tasa tana chan tana hutawa babu abinda yadameta bata ma san wainar da ake toyawaba ita ga 'yar gaban goshi me ciki.

Jinjina kai memartaba yayi sannan yace nasan abinda zanyi, kallon Rahma yayi da take kuka yace ke jeki kisamo min takarda da biro, mik'ewa Rahma tayi tafita.

Nan kowa yayi jugum yana jira yaji hukuncin da memartaba zai yanke.

Bayan kamar minti biyar sai ga Rahma ta dawo rik'e da takarda da biro, tsugunnawa tayi gaban memartaba tamik'a mai,

Kar6a memartaba yayi yace yauwa, sannan yakalli yarima da yake zaune har Lokacin bai d'ago kansa mik'a masa memartaba yayi yace kar6a.

'Dago kai yarima yayi yakalli takardar sannan yamaida kallonsa ga me martaba, a karo na biyu memartaba yace kar6a mana.

Hannu yarima yamik'a yakar6a tare da tsare memartaba da ido yana jira yaji abinda zai ce.

Shima memartaba kallonsa yake sannan yace inaso karubuta ma wacchan matar taka itama saki ukku.

Gabad'aya d'akin d'agowa akayi aka kalli memartaba cike da mamakin kalmar sakin da ya ambata.

yarima ko gabansane yayi wani irin fad'uwa saida biron takubce daga hannunsa, tashin hankaline k'arara yabayya a fuskarsa.

har a lokacin memartaba kallonsa yake fuskarsa ba alamun wasa yace indai kana son cigaba da zama a gidannan toh dole kasaketa saboda hakan shi zaifi dacewa karabu da kowace d'aya daga cikinsu.

Dada gyad'a kai tayi tace tabbas ranka yadad'e ka kawo shawara mai kyau inma cikin da yake jikintane yake ma rawar kai toh taje gidansu da abinda tacigaba da raino zamu dinga aika mata da duk abinda take buk'ata har sai ta haihu, intaso tashayar da abunta inkuma batasoba tabamu abunmu a haka zamu sami wacce zata kular mana da shi.

Ummi ita kanta saida gabanta yafad'i dan ita jin abun take kamar a mafarki tabbas ta san d'anta akwai dalilin da yasa ya saki sumayya saidai miskilanci da zurfin jikinsa bazasu ta6a barinsa yafad'aba.

Abban sumauya ne yaduk'ar da kansa yace ranka yadad'e ataimaka a sassauta ma yarima wannan hukuncin yai masa tsauri.

Sultana sadiya da take gefe takaici duk ya cikata tana ji kamar tashak'e yarima yamace kowa yahuta, jin maganar da mijinta yayi yasa tawurga masa harara, sai a lokacin tace ranka yadad'e tabbas wannan hukuncin da kayanke shine daidai dan yarima ya tozarta min d'iya,,,, d'aga mata hannu sultan abbas yayi yace ke banason hauka na san duk abinda yaima sumayya toh tana da laifi a ciki dan na san sumayya bata ji.

Sultan Ahmad ne yai k'arfin hali yace ma sultan Abbas kadaina cewa haka domin yarima bai kyautaba.

Memartaba gyaran murya yayi nan kowa yanutsu, sannan yace duk naji k'orafinku saidai inaso kusani babu wanda ya isa yasa incanza maganata dan ku kanku kunsani ni kaifi d'ayane bana magana biyu.

Duk'ar da kansu sukayi sukace Allah yaja da ran sarki me adalci.

Memartaba kallon yarima yayi da duk sanyin A-C d'in da take d'akin ammah bai hana yayi zufaba, murmushi Memartaba yayi sannan yace suhail ina saurarenka dan kaji abinda nafad'a.

Aunty husna ce tad'auki biro d'in da tafad'i tamik'a mashi.

Cikin sanyin jiki yarima yak'arfi biro d'in yad'aura saman paper, nan kowa yazuba mai ido ana jira yarubuta.

Ido yazuba ma paper tare da d'aura biro d'in kamar zaiyi rubutu nan gabansa yashiga dukan ukku-ukku jinsa yake wani iri gabad'aya komai ya kwance masa, yarasa cikin biyu wane zaiyi shin sakin zarah zaiyi ko kuma ya amince yarabu da family d'insa, runtse idanunsa yayi yana jin wani irin k'unci a ransa........

_Shin yarima zai amince yasaki zarah?_

_Ko zai amince yarabu da family d'insa kamar yarda memartaba yafurta?_

_*Muje Zuwa dan jin yadda zai kasance*_

_Comment_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Nagode Sosai da kulawarku agareni masoya, gaskiya naji dad'i dan naga k'auna zallah daga gareku, banda abinda zanyi inbiyaku saidai ince Allah yabar k'auna da dank'on zumunci😘*_

*PAGE* 5⃣7⃣

Ahankali yabud'e idanunsa da gaba d'aya suka canza launi, ji yake kamar yarubuta ma zarah saki sai kuma yaji bazai iya aikata hakanba dan shi kansa ya san idan yasaketa bai mata adalciba.

'Dago kai yayi yakallesu d'aya bayan d'aya har a lokacin idanunsu suna a kansa,,,Yarima kallonsa yasafke ga memartaba cikin sanyin jiki muryarsa tana rawa yace kagafarceni ranka yadad'e bazan iya rabuwa da matataba.

Gabad'ayansu a firgice suke kallonsa hatta shi kansa memartaba yayi mamakin furucin da yafito daga bakin yarima.

Murmushi memartaba yayi sannan yace suhail idan na fahimceka toh kana nufin ka za6i matarka akanmu ko?

Cike da damuwa yarima yagirgiza kai yace ranka yadad'e ba haka nake nufiba kawai dai... katseshi memartaba yayi yace kawai dai me!!! Toh bara kaji indai har bazaka iya rabuwa da itaba toh mu yazamar mana dole murabu da kai, dan haka kaje kawai na cireka daga cikin masarautata yanzu ka fita daga cikin iyalaina dan haka na baka awa d'aya kaje duk wani abu da kasan mallakinane kaje kakawo min sannan kafita kabarmin masarauta, inkuma ba hakaba zansa a fitar da kai a wulak'ance.

Gabad'aya d'akin shuru sukayi kamar ruwa ya cisu dan sunsan tunda har memartaba yafurta toh tabbas ba wanda ya isa yacanza.

Yarima runtse idonsa yayi yana jin yadda maganar memartaba take dukan dodon kunnansa wani irin d'acine yakeji a ransa

Ummi ko rufe fuskarta tayi da alkyabbarta tana goge hawayen da suka taru a idonta, gabad'aya lamarin ya rikitata.

Daddy ma shikad'ai yasan abinda yakeji a ransa game da maganar da mahaifinsa yafurta, kawai dai ya dakene bai nuna ba.

Dada ce takalli memartaba tace ammah ranka yadad'e ba... d'aga mata hannu memartaba yayi yace banason jin maganar kowa daga cikinku dan ni nariga da nagama magana yanzu lokacin da nabaka zai fara aiki.

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, ahankali yamik'e jiki ba k'wari kamar wanda kwai yafashe mawa a ciki haka yake tafiya har yafita daga d'akin.

Rahma da Aunty husna ko kuka sukeyi ahankali, inda sumayya take kuka akan mutuwar aurenta.

Yarima ahaka ya isa part d'insu, bakin gadonsa yazauna yadafe kansa shi kad'ai yasan abinda yakeji gashi an hanasa yai magana, tunani yashiga yi shin in ya bar gidansu ina zaije? Tunowa yayi da maganar memartaba da yace ya fara cin lokacin da yabasa, dan haka yajanyo wayarsa yakira wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking,

Yarima k'ok'arin saita nutsuwarsa yayi suka d'an gaisa sama-sama sannan yace Dr Mu'az kana gari?
Daga chan 6angaren wanda aka kira da Dr mu'az yace eh ranka yadad'e.
Ohk, please kaje kasamar min hotel maikyau yanzu zan shigo Abuja.
Cikin jin dad'i Dr mu'az yace angama ranka yadad'e Allah yakawoka lafiya.

Ameen yarima yace sannan yakashe wayar,
Sannan yakira yasa ayankar masa ticket na mutum biyu yace yanzu yakesonta, kasancewar sanannene nan suka amsa masa, bayan sungama wayar yai musu transfer d'in kud'insu, bayan ya gama Dr khalil yalalubo bai wani 6ata lokaciba yai picking

Yarima ko gaisawa bai bari sunyi ba yace Dr khalil kana ina yanzu?

Daga chan 6angaren Dr khalil yace ranka yadad'e ganinan wajejan anguwarku gidan Auntyna.

Ohk, please kazo yanzu akwai inda nakeso kakaini.

To ranka yadad'e ammah ya naji muryarka haka? Lafiya dai ko?

Yarima kashe wayarsa yayi batare da ya bashi amsaba,,,,mik'ewa yayi yaje yafara had'a duk wani abu da yasan ba mallakinsa bane yaware ma daddy da memartaba nasu sannan yad'auki nashi, wajen wardrobe d'insa yaje yabud'e nan yafara fitar da kayansa yana sawa a trolly, cikin trolly guda yazuba duk wani abu da yake buk'ata sannan yajawo,

Tsaye yayi yana k'are ma room d'insa kallo yana jin k'unci a ransa, janyo trollyn yayi yafito cikin sauri guards d'insa suka zo suka kar6a nan yace suwuce masa da shi waje.
Cike da ladabi suka amsa masa.

Daga nan part d'in zarah yawuce kallonta yayi har lokacin tana kwance, ita kanta zarah yanayinsa kawai tagani tasan yana cikin tashin hankali,

Yarima batare da ya janye idonsa akantaba yace tashi kihad'a kayanki,

Zarah saida gabanta yafad'i tace na'am.

Shareta Yarima yayi yawuce wajen wardrobe d'inta yabud'e nan yafara zuba mata a trolly duk abinda yasan zata buk'ata saida yazuba mata a ciki, bayan ya gama juyowa yayi yakalli zarah da tatsaresa da ido yace tashi muje.

Zarah k'wallah ce tacika mata ido tace ina zamuje?

Tsawar da Yarima yadaka matane yasa tamik'e ba shiri tajanyo veil d'inta tayafa nan Yarima yawuce gaba tana biye da shi, wata kuyangarta ce cikin sauri takar6i trollyn da yake hannun Yarima

Zarah tana biye da yarima gabad'aya kanta ya d'aure gashi yarima bai bata fuskar da ma zata iya tambayarsaba ahaka har suka fito harabar gidan, da mamakinta sai gani tayi sun nufi turakar su memartaba.

mamaki bai ida kamataba saida suka shiga d'akin taga gabad'aya family d'in yarima suna a ciki, bata lura da yanayin da suke cikiba, dasauri tatsugunna tagaishesu, gabad'ayansu babu wanda ya amsa mata,

Ta d'auka basujiba nan tak'ara gaishesu, dady da abbah ne kawai sukayi k'arfin halin amsa mata,
Chapter 73 · 0% Book details