← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 102

Sashe 87

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan aka shiga da su sumayya cikin d'akinta dan gudun kar wasu sugani, sumayya tafara kwanciya dan ita bata tsorata da bulalar da akace za'ayi mataba ita dai burinta ubangijinta da iyayenta suyafe mata, bulalar farko wata irin k'ara tasaki koda akan adalci yayi musu ba kamar wadda za'ayi ma namijiba su ya d'an safsafta musu saboda matane, bai kyaletaba saida yayi mata tamanin tun tana iya motsi har takasa daga k'arshe sumewa tayi ahaka aka gama tana a sume, sannan yadawo kan zinat itama tana ihu da hargagi ahaka aka gama aka barta kwance bata iya motsin kirki.

Memartaba gudun kar suji k'ara yasa aka kunna tv tare da cika volume ammah duk da haka sunaji sama-sama, ummi, dada, sultana sadiya kuka kawai suke ahankali cike da takaicin abinda sumayya ta aikata

Bayan dogarin ya fito nan yatabbatar ma da memartaba ya yi kamar yadda ya umurcesa nan memartaba yasallamesa yatafi.

Sawa yayi aka rage volume sannan yakallesu cike da damuwa yace yanzu ya duniya zata d'aukeni? Da wane suna za'a kirani? Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un wannan wace irin *k'addara ce* yanzu duk mutuncina da darajata sun zube a idanun mutane

Sultan abbas cike da damuwa yace ranka yadad'e ni kaina narasa ya akayi ina zaune da sumayya ammah bansan abinda take aikatawa ba, kokuma ni k'arani kan waccan uwar banzar da akodayaushe take tare da ita ammah batason laifinta sannan ace batasan duk wani motion d'in d'iyartaba toh wannan wace irin soyayyace takeyimata, wannan ba so bane haukane tunda baki iya tarbiyar da d'iyar cikinki dan haka daga ke har ita kutafi kuban waje bana buk'atarku a cikin rayuwata.

Sultana sadiya k'ara fashewa tayi da sabon kuka tace nashiga ukku idan karabu da ni ina kakeso inje inji dad'i bayan banida kowa bayanku dan Allah kayi hak'uri kayafe min wlh bansan sumayya tana wannan mummunar halayyarba.

Cikin d'aga murya sultan ahmad yace kai miye haka kakeyi idan rai ya 6aci ai baidace zuciya ta6aciba yakamata kadawo hayyacinka ita kuma sadiya miye nata laifin aciki? Itada ba ita tayimakaba shine zaka had'a da ita?

Girgiza kai sultan abbas yashigayi yace kubarni nikad'ai nasan abinda nakeji su dukansu banason ganinsu.

Memartaba jinjina kai yayi yace babu inda zasuje, sannan yakalli sultana bilkisu yace jeki kigano min su sumayya.

Mik'ewa sultana bilkisu tayi cikin sauri tanufi part d'in sumayya tana shiga yanayin yadda taga sumayya saida tatsorata dan batada banbanci da matatta, zinat ko numfashi take fitarwa sama-sama tana jan jiki daga kwancen.

Cikin sauri ta isa inda sumayya take tashiga jijjigata ganin bata motsi yasa tamik'e taje tad'ebo ruwa tamakaka mata, wani dogon numfashi sumayya taja ahankali tashiga motsa hannunta nan hawaye suka shiga malala daga idanunta, ahankali tabud'esu tasafke akan ummi da itama take hawayen, muryar sumayya ciki-ciki tace ummi kice min mafarki nake ba gaske bane, wlh ummi nayi nadama nadaina kuyafemin.

Ummi rungumo sumayya tayi a jikinta tace shikenan sumayya yanzu dai bari ingasa miki jikinki kinga duk ciwone.

Murmushin k'arfin hali sumayya tayi tace ummi ciwon da nakeji a zuciyata yafi radad'in bulalarnan dan Allah kitayani ba su abbah hak'uri.

Ummi sharemata hawayen fuskarta tayi tace kar kidamu yanzu dai muje kifara gasa jikinki,,,,haka ummi taje tahad'a mata ruwan d'umi ita tataimaka mata tagasa jikinta tayi wanka sannan tashiryata takwantar da ita saman gadonta saboda jikinta yad'au zafi sosai.

Juyowar da ummi zatayi nan taga zinat tana d'aukar kayanta tana bin bango dakyar take tafiya har tafita daga d'akin.

Ai tana fitowa parlour tacikaro da su memartaba rikicewa tayi tasaki jakkarta tare da duk'awa tace dan Allah kuyafemin wlh natuba bazan k'araba.

Murmushin k'arfin hali memartaba yayi yace dole ki amsa hukunci tunda kece silar lalacewar sumayya, kuma kece silar rugujewar duk wani farin ciki na masarautar nan dan haka yanzu zansa akaiki gidan yari kid'an kwana biyu.

Zinat sake fashewa tayi da sabon kuka tace dan Allah kuyi hak'uri wlh ba zan sake dawowaba.

Memartaba wayarsa yad'auko yai kira, cikin mintuna kad'an saiga wani k'aton barde yashigo nan memartaba yace atafi da zinat gidan yari duk wani aiki me wahala asata kar a sassauta mata .

Cike da girmamawa yace angama ranka yadad'e, nan yatusa zinat gaba tana kuka tana rok'onsu ammah ahaka aka fita da ita babu wanda yasaurareta.

Sultana bilkisu fitowa tayi tashaida musu halin da sumayya take ciki ammah kowa shareta yayi yace baruwansa, dada ma cewa tayi tamutu mana ina ruwan wani, sultan ahmad ne kawai yatausaya mata nan yakira family doctor d'insu.

Memartaba da takaici ya isheshi mik'ewa yayi batare da yayi ma kowa maganaba yawuce yaficce nan dada tabi bayansa.

Ganin haka yasa sultan abbas ma cike da 6acin rai yatashi yawuce part d'insa, sultana sadiya ma tashi tayi tabi bayansa dan gabad'aya hankalinta atashe yake addu'a take cikin ranta akan Allah yasa kar aurenta yamutu.

Sultan ahmad da sultana bilkisu ne suka cigaba da zama har doctor yazo yaduba sumayya yabata drugs tasha, nan sultan ahmad yatafi yabar sultana bilkisu wajen sumayya tana cigaba da kula da ita tare da kwantar mata da hankali har dare sannan tafara shirin komawa turakarsu, sumayya ba dan tasoba haka tahak'ura tabar ummi tatafi.

bayan ummi ta tafi nan tadasa wani sabon kukan cike da nadamar abinda ta aikata, ji take ina ma tabud'e ido taga duk a cikin mafarkine komai yafaru saidai inaa *k'addara ta riga fata* haka tayita juyi tana kuka har wajen k'arfe d'ayan dare nan tatashi dakyar jiki ba k'wari taje tad'auro alwallah akaro na farko a rayuwarta da tafara tunanin yin nafila, nan taita sallah tana neman yafiyar ubangiji har wajen k'arfe ukkun dare, tana zaune a saman darduma tana lazumi ahaka bacci yai awon gaba da ita.

Sultana sadiya koda tabi sultan abbas part d'insa tana ganin ya zauna bakin gado nan tazo tatsugunna gabansa cike da nadama, cikin kukan tace Dan Allah kayafemin wlh zan canza rayuwata, duk abinda na aikata wlh akan kuskure da *SON ZUCIYA* na aikatasa, tabbas a yanzu nasan ba gata bane nanuna ma sumayya, dan Allah kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko nasamu d'an sauk'i acikin raina.

Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kin aikata babban kuskure wanda tabonsa ba zai ta6a gogewaba a raina, na aureki ina gani kamar zaki taimaka min wajen ganin mungina rayuwarmu da ta 'ya'yanmu cikin tsafta, ashe bahaka bane ni kad'ai nake haukana ke kin riga kin tsara taki rayuwar, toh me yayi saura a yanzu? Me zakice min?

Cikin kuka tashiga girgiza kai tace kayi hak'uri wlh tsautsayine insha Allah yanzu zan gyara.

A wulak'ance yakalleta yace kar ma kigyara dan ba matsalata bane dan haka kitashi kifita kiban waje tun kan ranki ya6aci.

Cikin sauri sultana sadiya tamik'e tare da cewa Allah yahuci zuciyanka sannan taficce tabar d'akin tana waiwayensa.

Memartaba koda yakoma turakarsu cike da tashin hankali tare da nadamar abinda yayi ma yarima suhail maganganun da yayine akansa yadinga dawo masa a k'wak'walwa, jiyake ina ma ace ya tsaya yai bincike kafin yakori jikansa dayafi k'auna a rayuwarsa Memartaba harda 'yar k'wallarsa, dada ita kanta koda tana cikin tashin hankali ammah haka tadanne tashiga lallashin mijin nata dan soyayi yaje yafara neman yarima a lokacin, dakyar tasamu taja ra'ayinsa yafasa zuwa dan darene,

A 6angaren ummi ma koda takoma part d'insu kuka taci sosai har sultan ahmad yashigo yatarar da ita, cike da tausayinta yazauna gefenta d'ago kai tayi takallesa cikin kuka tace kagani ko suhail d'ina baida laifi dan Allah kasa baki memartaba ya amince sudawo gida.

Rungumota yayi jikinsa cikin lallashi yace sultana kikwantar da hankalinki suhail zai dawo agaremu tunda baida laifi a ciki, na tabbata memartaba zai sa anemo masa shi dan shi kansa yana cikin damuwar rashin suhail.
Kicigaba da addu'a kinji ko?
'Daga masa kai tayi alamun eh, nan yacigaba da kwantar mata da hankali daga k'arshe suka kwanta.

Gabad'aya family d'in babu wanda yasamu yayi baccin kirki dan kowa hankalinsa atashe yake.

_Comment_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣5⃣

Asubar fari sumayya tafarka koda daman ba wani baccin kirki bane tayi, alwallah taje tad'auro tazo tagabatar da raka'atanil fijir sannan tazauna tayi ta tasbihi da istigfari kafin atayar da sallah.

Bayan ta gama sallah alqur'ani tad'auko tashiga karanta abinda ta iya acikinsa har saida gari yai haske sannan tayi addu'a takoma takwanta ammah bacci yace d'aukarni inda kika barni, haka tayita juyi ga baccin tanaji ammah ba dama, saidai hawaye kawai da suke fita daga idanunta.

A ranar haka tawuni cikin d'akinta bata fitaba saboda kunyar iyayenta da takeji, ko breakfast batasamu tayiba koda tana jin yunwa dan rabonta da abinci tun jiya da rana.

A 6angaren memartaba ko tun dasafe yatura aje abinciko masa yarima duk inda ake tunani za'a gansa anje babushi har gidansa da yagina saida akaje ammah babu labarinsa har marece yayi ana nemansa sannan daga baya akazo aka shaida ma memartaba.

Memartaba baiji dad'iba cikin daren har so yayi yafita dakansa yak'ara bincikawa ammah su sultan ahmad suka bashi baki dak'yar sukasamu yahak'ura.

Sumayya ko sallah ce kawai take tashinta daga saman gadonta cikin d'an k'ank'anin lokaci duk tatsure tarame kamar ba itaba, chan wajen marece ummi tashigo ganin sumayya a wannan yanayin saida tatausaya mata nan tasa aka kawo mata abinci dak'yar tasamu tad'anci kad'an sannan tak'ara yi mata nasiha da wa'azi, sumayya kuka tayi sosai sannan tace ummi dan Allah kuyafemin wlh bazan k'araba, sharrin shed'anne nadaina, k'ara sautin kukanta tayi tace ummi ina jin tsoron had'uwana da ubangijina.
Chapter 87 · 0% Book details