← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 102

Sashe 64

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallar isha'i suna zaune suna hira zarah handbag d'inta tabud'e tad'auko dubu d'ari biyu tamik'a ma abbah tace gashinan Abbah ko kayan kitchen anfara siya mata.

Abbah girgiza kai yayi yace a'a zarah akwai kud'i hannuna dan na ware wanda zan cika incanza mana gida, kud'in da suka rage ne nasamu nabud'e shago ina kasuwanci dasu nakeso inmata siyayyarta.

Zarah cikin jin dad'i tace hakane Abbah ammah dan Allah kataimaka ka amsa kuk'ara sai asamin albarka.

Kar6a yayi nan sukaita sa mata albarka.

Aysha da take cikin d'aki tana waya fitowa tayi takalli zarah tana murmushi tace Aunty zarah kizo kugaisa da malam bello yana nan k'ofan gida.

Zarah girgiza kai tayi tace a'a Aysha kinga ban tambayaba, marairaicewa Aysha tayi tace iyakarki fa zaure nan zaku gaisa,,,tafad'i haka tare da mik'ama zarah gyalenta.

Zarah kar6a tayi tayafa ba dan tasoba tamik'e tabi bayan Aysha.

Daga waje suka hangosa tsaye zarah wajen k'ofar gidansu tatsaya, malam bello kallo d'aya yaimata yad'auke kai fuskarsa d'auke da murmushi yak'araso wajen da suke yana mai cewa a'ah ashe yayarmuce.

Murmushi zarah tayi tace malam ina wuni?
Lfy lou zarah ya gida da mai gidan.

Cikin jin kunya tace kowa yana lafiya, kallon Aysha tayi da taketa murmushi tace malam ga dai amanar k'anwatanan akularmin da ita.

Dariya malam bello yayi yace kar kidamu yayarmu insha Allahu zanyi iya bakin k'ok'arina.

Zarah cikin jin dad'i tace Allah yasa malam mungode sosai, Allah yakaimu lokacin.

Gabad'ayansu sukace Ameen.

Daidai lokacin motar yarima ta iso wajen da suke, yana yin parking saida gabansa yafad'i ganin zarah tsaye da wani, baima lura da Aysha ba datake gefe, suna had'a ido da zarah wata irin harara yawurga mata, zarah saida gabanta yafad'i cikin ranta tace nashiga ukku, dakewa tayi tataka ta isa inda yake fuskarta d'auke da murmushi tabud'e mai k'ofan tace sannu da zuwa.

yarima wani irin kallo yaimata yace wanene wancan kuke tare da shi?

Koda ta tsorata da hararar da yai mata ammah tadake tayi murmushi sannan tace mijin da Aysha zata aurane...shine dan bakida hankali kike tsaye da shi ke kad'ai kina ta yimai dariya?

Zarah da mamaki takallesa tace bafa ni kad'ai bace baga Aysha chan ba.

Sai a lokacin idonsa yakai ga su Aysha dasuke tafowa inda suke, ajiyar zuciya yasafke sannan yafito daga motar daidai lokacin su Aysha suka iso wajen da suke,

malam bello cikin girmamawa yarussina zai gaishe da yarima.

Cikin sauri yarima yarik'o hannunsa sukayi nusabaha fuskarsa a sake yace Allah yasa alkhairi ango,
Malam bello duk'ar da kansa yayi cikin girmamawa yace Ameen ranka yadad'e nagode,
Aysha ce tace yayana ina wuni?

Kallonta yayi fuskarsa a sake yace k'anwata kin wuni lafiya? Sai mukaji labari, Allah yasa alkhairi,

Aysha cikin jin kunya tarufe fuskarta, malam bello ne kawai ya amsa da Ameen.

Dariya zarah tayi tace magulmaciya kawai.
Yarima kallon zarah yayi yace menene kuma abun gulma? Daga tana jin kunyan yayanta.

zarah fari taimashi da ido.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta yace k'anwata bari mushiga ciki ingaishe da su abbah.

Aysha murmushi tayi tace toh yayana afito lafiya.

Zarah jerawa sukayi da Yarima suka shiga gida inda sukabar malam bello da Aysha suna ta hirarsu.

Koda sukazo shiga yarima ja yayi yatsaya, zarah kallonsa tayi tana shirin yin magana yace muje mana.

Zarah murmushi tayi sannan tawuce gaba yarima yabi bayanta har suka shiga cikin gida, har a lokacin su mama suna zaune tsakar gida, zarah tabarma tad'auko tashimfid'a mashi yazauna cike da girmamawa yagaishe da su abbah,

Fara'a bayyane a fuskarsu suka amsa mashi tare da tambayarsa mutanen gida, yarima saddar da kansa yayi k'asa yace Alhmdllh, Ya hidima?

Alhmdllh,,cewar su abbah.
Masha Allah, Allah yasa alkhairi, Allah yakaimu lokacin.

Cikin jin dad'i suka amsa da Ameen y rabb.

Yaya rauda kallonsa tayi tace ranka yadad'e barka da dare.

Murmushi yarima yayi yace yayarmu anwuni lfy?

Yaya rauda tace lafiya lou Alhmdllh, y hak'uri da mu?

Murmushi kawai yarima yayi.

Zarah mik'ewa tayi taje tad'auko abinci takawo mai, ganin haka yasa su abbah suka tashi suka bashi wuri dan yasamu yaci.

Bayan su Abbah sun tashi zama tayi gefensa dan tazuba mai, kallonta yarima yayi yace kindai san bana cin abinci da dare.

Zarah ma 6ata fuska tayi takallesa kamar zatayi kuka tace abincin gidan namu ma bazakaciba?

Yarima kallon kunun ayan da takawo mai yayi yace zuba min wannan dai.

Toh tace sannan tatsiya mai a cup tamik'a mai, kar6a yayi yafara sha kad'an kad'an, wayarsa da ya aje gefe zarah tad'auka tana wasa da ita, yarima baice mata komai ba ahaka har yashanye, kallonsa tayi tace ko ak'ara ma?
Girgiza kai yarima yayi sannan yace kije kiyi ma su mama sallama kizo mutafi dare yakeyi.

Mik'ewa Zarah tayi, yarima kallonta yayi yace wai ke yau kin ma ci abinci?

Zarah yamitsa fuska tayi tace na dai ci awara.
Shuru yarima yayi baice komai ba,

wucewa tayi taje tasanar da su mama zasu tafi nan tafito tare da su mama,
Nan suka yi sallama suka fito daidai lokacin Aysha zata shigo gida, kallonsu tayi tace ba dai tafiya zakuyiba.

Yarima murmushi yayi yace ko mukwana?
Dariya Aysha tayi tace eh ranka yadad'e.

Zarah kallonta tayi tace ina angon har ya tafi?

Susa kai Aysha tayi cikin jin kunya tace uhm.

Dariya Zarah tayi nan Aysha tarakasu har wajen mota sukayi bankwana takoma gida.

Tunda suka fara tafiya tsit motar tayi, ahankali yarima yajuyo yakalli zarah da tajingine kanta a sit d'in da take zaune ta zuba ma waje d'aya ido kamar mai tunani, janye idonsa yayi daga killonta yacigaba da tuk'insa duk sai yaji babu dad'i yanayin da yaganta.

Ahankali yace akwai abinda kike buk'atane?

Zarah juyowa tayi takallesa taga ba ita yake kalloba idonsa yana a titi, shuru tayi tana kallonsa jin tayi shuru yasa yarima yad'an juyo yakalleta karaf suka had'a ido, zarah duk'ar da kanta tayi sannan tace ice cream nakeson sha.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace meyasa kikeson shan kayan sanyi, ya kamata kidaina tunda yanzu ba ke kad'ai bace.

Zarah 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace toh.

Yarima saida yabiya yasiyo mata sannan suka wuce gida, yana yin parking Zarah tabud'e tafita, kallonta yarima yayi yace wannan fa wa zai kawo miki?

Murmushi Zarah tayi tace sorry mancewa nayi nan tad'auka sannan tawuce cikin gida.

Yarima ma fitowa yayi yawuce fada dan sugaisa da memartaba.

___________

A 6angaren sultana sadiya ranta a 6ace takoma part d'inta a parlour tatarar da sumayya zaune tana jiranta dan sumayya tunda taga shigar sultana part d'in zarah yasa tafito tazo turakar iyayenta dan tasamu labari wajen ummanta idan tadawo,, ganinta yasa sumayya tamik'e cikin murna tace ummana angama komai ko?

Kallonta sultana sadiya tayi tare da jan tsoki tace sumayya wanchan banzan mijin naki ya 6ata min duk wani plan nawa.

Sumayya a tsorace tadafe k'irji tace ummah kar dai kicemin asirinmu ya tonu?

Sultana sadiya zama tayi saman kujera cikin 6acin rai takwashe komai tafad'a ma sumayya duk abinda yafaru.

Sumayya ajiyar zuciya tayi sannan tace ummah wlh banji dad'in faruwar hakanba, yanzu saboda Allah ido zansa mata har tahaihu? Yanzu ita zata aje ma yarima magaji?,,,sumayya tafad'i haka tare da fashewa da kuka, cikin kuka takalli sultana sadiya da abun duniya yadameta tace ummah ko kid'au mataki ko kar kid'auka wlh ba zan ta6a barin zarah ba sai naga bayanta.

Sultana sadiya jawota tayi tazaunar da ita gefenta tace sumayya banaso kije kiyi abinda zai jawo abinda za'ayi da ansani,

Sumayya shigewa tayi jikin ummanta tana kuka tace ummah a kullum ina fad'a miki bandamu da abinda zai faruba indai burina ya cika.

Sultana sadiya d'ago kan sumayya tayi tana share mata hawaye tace kidaina cewa haka sumayya kibari abi komai a sannu, sumayya mik'ewa tayi tana ja da baya tace a yaushe duk za'ayi hakan bayan ta haihu? Girgiza kai tayi tace ummah kibarni kawai, tana fad'in haka tajuya tafita daga d'akin.

Sultana sadiya k'walah mata kira tashiga yi ammah ina sumayya tafiyarta tayi.

Dafe kanta sultana tayi tace wannan wace irin rayuwa ce?

Sumayya koda takoma part d'inta batabi ta kuyanginta da suke gaishetaba dagudu tashige bedroom d'inta tamaida tarufe, jingine kanta tayi da k'ofar tashiga rusa kuka, tana jin wayanta tana ringing tashare tacigaba da kukanta, daga k'arshe takoma saman gadonta takwanta nan tak'ara sautin kukanta saida taji kanta ya fara ciwo sannan tatsagaita kukan nata.

Wasa-Wasa ciwon kai da zazza6i suka rufeta haka tajanyo blanket tarufa ahaka tayi ta juyi har cikin dare sai daga baya bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe ko da kuyangarta zabba'u tazo tayita knocking jin shuru yasa tatura k'ofan tashiga cikin sauri ta isa inda Sumayya take k'udundune da bargo tana rawan sanyi,

Kallonta zabba'u tayi a firgice tace ranki yadad'e mi yasameki?

Sumayya dakyar tabud'e baki muryarta na fita ahankali tace je kikira min yarima.

Cikin sauri zabba'u tamik'e tace toh ranki yadad'e.

Yarima zaune yake yana breakfast inda zarah take gefensa tana shan ruwan lipton wanda yasha kayan yaji, knocking d'in k'ofa akayi zarah kallon Yarima tayi da yature cup d'in tea d'insa gefe yamik'e saida yabaro dining area sannan yace yes,

Guards d'insane yabud'e yashigo saida yad'an russuna sannan yace ranka yadad'e gimbiya sumayya ce tayo aike,

Yarima saida yazauna saman cushin sannan yabashi izini yabarta tashigo.

Kuyanga zabba'u koda tashigo zubewa tayi k'asa takwashi gaisuwa wajen yarima, hannu kawai yarima yad'aga mata, zabba'u k'ara duk'an da kanta tayi tace ranka yadad'e daman gimbiya sumayya ce batada lafiya tana chan kwance yanzu haka ita ta aikoni inzo insanar da kai.

Zarah jin an ambaci sumayya batada lafiya yasa tamik'e tabaro dining area,
yarima nuni yayi mata alamun tatafi, zabba'u k'ara duk'awa tayi takwashi gaisuwa sannan tamik'e cikin sauri tabar d'akin.

Zarah kallon yarima tayi da yamik'e cike da jin tausayi tace meyake samunta?

Shima yarima kallonta yayi yace bari inje indubata, Zarah bayansa tabi tace muje tare.

Yarima baice komai ba nan suka fito suka nufi part d'in sumayya duk inda suka ratsa bayi da Kuyangi duk'awa suke suna kwasar gaisuwa,

ko da suka shiga parlournta nan ma kuyanginta suka zube suka gaishesu, hannu yarima yad'aga musu cikin sauri suka fita sukabar d'akin.
Chapter 64 · 0% Book details