← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 102

Sashe 62

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sultana sadiya maida kanta tayi ta jingine ga kujerar da take tana murmushin mugunta.

_Comment_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah my friendy *Sadiya Sidi S* Ina tayaki murnar fara sabon novel d'inki mai taken *RAYUWAR MATA* yadda kika fara lafiya Allah yasa kigama lafiya, Allah yabamu ikon d'aukan darasin da yake cikinsa, kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, I hrt u over dear😘_

*PAGE* 5⃣0⃣

Sultana sadiya tana nan zaune tana sak'e-sak'e a ranta a k'allah ta ci kusan minti goma sha biyar a haka, zuwan da baiwarta tayine yasa tabata izini tashigo.

Baiwar shigowa tayi d'auke da wata kula a hannunta cikin sauri tazube k'asa tana kwasar gaisuwa wajen sultana sadiya.

Sultana yatsine fuska tayi sannan ta amsa ciki-ciki, baiwar k'ara duk'ar da kanta tayi sannan tace ranki yadad'e na cika umurninki.

Sultana kallon kular tayi sannan tace bud'e mugani,
Cikin sauri tabud'e mata, tana addu'a cikin ranta Allah yasa kar sultana tace baiyiba dan tana tsoron wulak'ancinta.

Ta6e baki sultana tayi tace tashi kitafi.

Cike da jin dad'i baiwar tace toh ranki yadad'e nabarki lafiya, tana fad'in haka tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.

Mik'ewa sultana sadiya tayi taje tad'auko maganin tazuba tamotse sannan tayi murmushi tace yau dai dole kicisa zarah, k'ulle maganin tayi tamaida ma'ajinsa sannan tadawo tasaka alkyabbarta tasa wata kuyangarta tad'aukar mata kular suka fito suka nufi 6angaren su zarah.

Zarah lokacin kwance take saman 3 seater tana ta juyi saboda wata irin yunwa da takeji gashi ta kasa cin komai, wayarta tad'auko takira yarima har tatsinke baiyi picking ba.

Haushine yakamata ta aje awar tana ta jan tsaki kad'an kad'an, bayan minti biyu sai ga kiransa ya shigo.

Zuba ma wayar ido tayi har tatsinke batare da tayi picking ba.

Daga chan 6angaren yarima da yafito wanka mamakine yakamasa ganin batayi picking ba kuma tsakanin kiran da tayi mai zuwa lokacin baifi 2 minutes ba, har zai k'ara kiranta a karo nabiyu sai chan 6angare d'aya na zuciyansa yace ba ajinka bane kak'ara kiranta, tsaki yaja ya aje wayan yacigaba da shirinsa ammah kuma duk da haka a cikin ransa yana jin ba dad'i dannewa kawai yakeyi dan shi abun har mamaki yake bashi ganin yadda yake ma zarah ko sumayya bata samun haka.

Lokacin da sultana sadiya ta iso part d'in zarah har a lokacin zarah tana kwance, ganin sultana sadiya yasa gabatanta yayi wani irin mummunan fad'uwa cikin ranta tsarin ubangiji take nema, koda sultana sadiya yau ma kamar jiya fuskarta a sake take.

Zarah cikin sauri tamik'e tsaye, murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace ummah sannu da zuwa.

Sultana sadiya ma maida mata martanin murmushin tayi saida tazauna sannan tace yauwa zarah.

A k'asa zarah tazauna cikin girmamawa tagaisheta.

Amsa mata sultana sadiya tayi tace ya k'arfin jikin naki?

Zarah duk'ar da kanta tayi tace Alhmdllh ummah.

Kuyangar da sukazo tare da sultana sadiya duk'awa tayi tagaishe da zarah.

Cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan sultana ta amshi kular tace tafita tajirata a waje, ahankali tace anganma ranki yadad'e sannan tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.

Sultana sadiya kallonta tamaida ga zarah da take wasa da yatsun hannunta tace yau ma dai ga kwad'on na kawo miki dan nasan masu ciki akwaisu da kwad'ayi bare ma irin wad'annan kwad'on ganyukan...tak'arashe maganar tana 'yar dariya.

Murmushi zarah tayi tace toh ummah nagode sosai.

Sultana sadiya tace haba zarah ai bakomai ke da sumayya duk d'aya nad'aukeku.

Zarah ahankali tace hakane ummah Allah yasaka da alkhairi.

Ameen, kibud'e kigani man,,,cewar sultana sadiya.

Zarah bata musaba tajanyo kular tabud'e saida tahad'iyi yawu saboda kwad'on ya burgeta kamar taitaci dan ganinsa yasa yunwar da takeji ta tashi, maidawa tayi tarufe takalli sultana sadiya da tatsareta da ido tace ummah ya yi min sosai kuma nagode Allah yasaka da alkhairi.

Murmushi sultana sadiya tayi tace kar kidamu zarah, kici kawai naga kamar yunwa kikeji.

Gaban zarah saida yafad'i jin sultana ta ce taci cikin ranta tace Allah yaimin tsari da abinda kuke shiryawa akaina, itama murmushin tayi tace ummah zanci sai zuwa anjima yanzu bana jin cin komai.

Fara'ar da take fuskar sultana sadiya raguwa tayi tace haba zarah yau fa dakaina nayi kwad'on kuma nayo tattaki nakawo miki ai bai dace kik'i ciba.

Zarah marairaicewa tayi tace ummah zan ci ai inason kwad'on kawai dai nafiso sai zuwa anjima.

Sultana sadiya cikin ranta tace wannan d'iyan akwai d'an banzan wayau anya batagane abinda nayimataba? murmushi sultana sadiya tayi tace hakane ammah ko kad'anne kid'anci kiji.

Zarah kallon sultana sadiya tayi, gyad'a mata kai sultana tayi alamun taci.

Zarah ido tazuba ma kwad'on tarasa yadda zatayi tana tsoron taci asamu matsala, d'ago kai tayi takalli sultana.

Sultana sadiya tasakar mata murmushi tace kici man.

Zarah har ta kai hannu zata d'iba sai ga yarima ya shigo da sallamarsa da mamaki yake kallon sultana sadiya itama ido tazuba masa tana kallonsu dan kwata-kwata bataji dad'in zuwansaba.

Zarah hamdala tayi tare da janye hannunta daga cikin kular.

Sultana sadiya murmushi tasakar mai tace ranka yadad'e ashe kana nan ai ban saniba da na aiko ankiraka mun gaisa.

Yarima batare da ya ce mata komai ba yasamu waje yazauna, kallon Zarah yayi da take zaune gaban kula sannan yamaida kallonsa ga sultana sadiya, ahankali kamar wanda baya son magana yace ummah barka da rana?

Sultana sadiya washe baki tayi tace yauwa yarima dafatan na sameku lafiya? Ai na ji labarine wajen dada ashe amaryarmu batada lafiya shine nazo ind'an dubata.

Jinjina kai kawai yarima yayi batare da yayi maganaba,

Haushine yakama sultana sadiya cikin ranta tace ka ji dai da abunka munafuki, chan sai tace ya jikin nata?

Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh

Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa janye idonsa yayi yamaida ga kallon dramar da ake a TV d'inta.

Wajen shuru yayi ba wanda yak'ara magana, ammah gabad'aya yarima hankalinsa yana ga zarah dan ransa ya bashi dakyar inba wani abu sultana sadiya take son shiryawaba.

Sultana sadiya ko ta cika ta yi fam takaicinta shigowar da yarima yayi batare da tasamu zarah ta ci kokad'an bane, ji take kamar tarufe yarima da duka, ganin baida niyar basu waje yasa takalli zarah tasakar mata murmushi tace dota bari intashi intafi Allah yak'ara lafiya.

Itama zarah murmushin tayi sannan tace nagode ummah, sultana sadiya kallon yarima tayi tawurga ma k'eyarsa harara sannan tace ni na wuce.

Yarima batare da ya juyo ya kalletaba yace toh ummah mungode.

Wucewa sultana sadiya tayi zata fita cikin sauri zarah tamik'e tabi bayanta koda suka fito sultana sadiya kallon zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace zarah kikoma kar kibar mijinki shi kad'ai.

Zarah duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya tace toh ummah mungode sosai Allah yabada lada,

Sultana sadiya tace Ameen.

har zarah ta juya zata tafi sai jin sultana sadiya tayi ta kira sunanta, tsayawa zarah tayi tare da juyowa.
Murmushi sultana tasakar mata sannan tace dan Allah kitabbata kinci kwad'on nan ko kin d'an samu k'arfin jikinki dan daga ganin yanayinki yunwa kikeji, na san zai taimaka miki sosai idan kikaci kinga badad'i ace kina zama da yunwa.

Zarah murmushi itama tayi sannan tace toh ummah insha Allahu zan ci.

Cike da nuna kulawa sultana tace kin tabbata?

Zarah d'agamata kai tayi alamun eh.

Murmushin jin dad'i sultana sadiya tayi tace yauwa Allah yaimuku albarka.

Zarah tace Ameen ummah, nan suka k'ara bankwana sannan zarah tajuyo tadawo part d'inta, yarima har a lokacin yana zaune inda tabarsa, ahankali tace sannu da zuwa?

Yarima batare da ya kalletaba ya amsa

Wucewa tayi tad'auki kwad'on sai a lokacin yarima yajuyo yakalleta yace ina kika sami wannan abun?

Zarah kallon kular kwad'on tayi sannan tace ummah ce takawomin.

Ta6e baki yarima yayi sannan yace kinci?
Girgiza mai kai kawai tayi alamun a'a.

Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace ban amince kiciba.

Zarah fuskarta d'auke da mamaki tace saboda mi?

Yarima juyowa yayi yawurga mata harara sannan yace saboda hakan nayi ra'ayi.

Shuru zarah tayi batace komai ba, cikin zuciyanta tace daman ai ba ci zanyiba, chan kuma tace anya yarima baisan wani abuba game da matarnan?

Muryar yarima taji ya ce meyasa da nakira wayanki bakiyi picking ba?

Zarah cikin zucinta tace kujini da mutum saikace ba ni nakirasa bai d'aukaba, kallonsa tayi taga idonsa yana a kan tv, ahankali tace bana kusa da wayanne.

mik'ewa yarima yayi yana kallonta yace akwai abinda kike buk'atane?

Zarah kallonsa tayi tace inason cin faten tsaki.

Toh ai zaki iya sa ma'aikatanki suyi miki ko?

Zarah gyad'amai kai tayi alamun eh.

Wucewa yarima yayi zaifita cak yaja yatsaya batare da ya juyoba yace wannan abun kije kizubar a shara sannan ko nan gaba ban amince a aiko miki wani abu kiciba, duk abinda kike buk'ata kisa ma'aikatanki suyi miki indai bakya iya yi dakanki.

Zarah cike da mamakin maganarsa tace Toh.

Wucewa yarima yayi yai tafiyarsa yabar zarah nan tsaye rik'e da kula.

Bayan ya fita Wucewa tayi tashek'a ma zogalen ruwa saida tawankesa tass sannan tak'ulle a leda takira wata kuyangarta tace taje tazubar a bola ammah kar tabari kowa yaganta.

Kuyangar duk'awa tayi tace Toh ranki yadad'e sannan tamik'e tafita.

Zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tana mamakin yarima tace anya baisan wani abuba game da halin su sultana? Chan kuma tatuna da maganar jakadiya da tafad'a mata cewa yarima ko iyayensa bai cika bari suna sanin ta cikinsaba saboda yana da zurfin ciki sosai, jinjina kai tayi sannan tamik'e taje tahad'o coffee dan ji tayi fatenma duk ya fita ranta.

Ahankali tasamu tasha coffeeen ba laifi sannan tajanyo remote tacanza channel tacigaba da kallonta, ahaka har aka kira magri tamik'e taje tad'auro alwallah.
Chapter 62 · 0% Book details