← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 102

Sashe 17

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsaye sukayi sukak'i motsawa zarah ce tayi k'arfin halin cewa yaya Rauda kuzo muje muzauna.

A tare sukazo suka zauna har a lokacin mama kuka takeyi, Abbah ne yayi gyaran murya sannan yace.......

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah *Mummyn Afrah nd Meena Abbah* ina tayaku murnar kammala novel d'inku mai suna *NI DA MIJIN YAYATAH* hak'ika kun wa'azantar, kun fad'akar sannan kun Nishad'antar damu, gaskiya tsarin rubutunku da fasahar da kuka zuba ta sun burgeni, Allah yabada ladan abinda aka fad'a daidai, kurakuren da suke ciki Allah yayafe muku, inaso kusani ina muka son so, Allah yabar k'auna my Aunties😘_

page 1⃣3⃣

Abbah gyaran murya yayi sannan yace maganar barin gida duk bata tasoba a yanzu muma mungane kuskurenmu tabbas duk abinda mutum yashuka shi zai gir6a wlh banga laifinkuba tabbas bamu dace da mukasance iyayenkuba, Abbah girgiza kai yayi yace kaicona da nabari son abun duniya yarud'eni har nawatsar da tarbiyar yarana alhali ni iyayena bahaka sukayi min ba, son zuciya da kwad'ayine suka ja mana dan Allah kuyi hak'uri da mummunar d'abi'ar da muka d'auraku akanta, wannan ya zama darasi a garemu ayi hak'uri a yafi juna.

mama cikin kuka tace dan Allah kuyafe mana insha Allahu yanzu zamu gyara tsarin gidanmu da komai zakuyi alfahari da mu.

Zarah ce tace bakomai wlh mun yafe muku duniya da lahira muma kuyafe mana.
kallonta tamaida ga su Rauda da basu da niyar yin magana tace yaya Rauda dan Allah kuyafe ma su mama tunda sun gane kuskurensu.

Rauda da Aysha cikin kuka sukace shikenan mun yafe musu Allah yayafe mana gaba d'ayanmu.

gaba d'aya suka amsa da Ameen.

sannan Abbah yace toh Alhmdllh da Allah yataimakemu muka farka tun kafin lokaci yak'ure mana naji dad'in hakan, insha Allahu zanyi k'ok'ari duk wani hak'inku da yarataya kaina inga na safke muku shi, saidai matsala d'aya yanzu cikin da yake jikin Rauda bansan ya zamuyi da Shiba.

Mama ma tayi nisa sannan tace mezai hana azubar da shi?

Zarah da sauri tagirgiza kai tace a'a mama bai dace azubar da shi ba karfa mumanta shi fa d'an baida alhakin kowa sai ma su da yakeda alhaki akansu da suka samesa ba ta hanyar halak ba, ga laifin zina ga na kisan kai ai k'ara tahak'ura tafauwala ma Allah lamurranta saboda Allah yana sane da halin da take ciki kuma komai rubutaccene ya riga ya tsara ma kowa yadda rayuwarsa zata kasance, shin baku tsoron wajen zubar da cikin tarasa rayuwarta? idan taje me zatace ma ubangijinta ranar gobe k'iyama? Shin kunsan yadda rayuwa zata kasance a nan gaba ko kuna tunanin nan gaba zata k'ara haihuwa? yakamata mumik'a lamurranmu ga Allah ubangijinmu mucigaba da rok'onsa tare da neman gafararsa Allahu gafurur rahim ne.

Dukkansu jinjina kai sukayi alamun gamsuwa da bayanin Zarah, Abbah yace tabbas Zarah nagamsu da bayaninki Allah yayafe mana kuskurenmu wlh ke d'iyar kirkice, kekuma Rauda Allah yasafkeki lafiya.

Gaba d'ayansu sukace Ameen, mama tace Allah yayi muku albarka Allah yaraya mana ku.
cike da jin dad'i sukace Ameen mamanmu,
muma muna alfahari da ku Allah yabar mana ku.

daga nan suka shiga tsara yadda zasu tafiyar da rayuwarsu, Aysha da Rauda 'yan kud'in da suke hannunsune suka tattara suka ba iyayen nasu sukace asiyo kayan abinci,

tun daga ranar suka rabu da samarinsu gidan yagyaru, inda Aysha takoma islamiyya suna zuwa tare da Zarah, Rauda kuma tacigaba da rainon cikinta, a gida Zarah takeyi masu k'arin karatunsu Rauda da Mama.

cikin ikon Allah Abbah yasamu d'an aikin da ake biyansa duk wata da taimakon Allah yake samu yana rik'e gidansa gwalgwadon k'arfinsa,

su kansu a yanzu suna jin dad'in sauyawar da suka samu ta rayuwa.

_______________

Yarima Suhail yau tunda yatashi jinsa yake wani iri ga tsananin buk'atar sumayya da yakeyi daurewa kawai yake tsawon wata biyu kenan rabonsa da ita.

yau bayan yadawo wajen aiki yayi wanka ya shirya cikin shigarsa ta alfarma fitowa yayi yanufi part d'in sumayya domin yau ji yake hak'urinsa ya k'are baya iya cigaba da daurewa

Yarima d'akinn sumayya yashiga lokacin sumayya tana zaune a parlour tsakiyar kuyanginta suna ta mata hidima.

ganinsa yasa dukansu suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baibi ta kansuba yashige bedroom d'in sumayya, da harara sumayya tabisa sannan tamik'e tabi bayansa.

tana shiga ta tarar da shi zaune saman gado batare da ta tanka masaba taje tazauna itama kusa da shi nan wajen yad'au shuru.

ganin baida niyar yin magana yasa sumayya tace lafiya?

Harara yarima yawurga mata tare da cewa lafiyar kenan, hak'ina nazo kibani.

'yar dariya gimbiya sumayya tayi sannan tace sai a yau za'a waiwayeni? ai nad'auka anrufe shafina, ko ka mance lokacin da nazo d'akinka kakoreni? ai nad'auka nagama amfani a wajenka ashe ina da sauran amfani.

yarima suhail wata muguwar harara yawurga mata cikin 6acin rai yace sumayya da ace akwai yadda zanyi inguje ma kusantarki da nayi domin nima ba dan nasoba nake nemanki domin kwatakwata ke ba ajina bace dandai *K'ADDARA CE* kawai tasa na amince ma aurenki, wlh kikiyayi ranar da zaki kaini k'arshe domin zan d'auki mummunan mataki akanki.

Sumayya ta6e baki tayi cikin rashin damuwa tace kai fa matsalata da kai bakasan arzik'iba sai kanaso ataimaka maka maimakon kalalla6ani shine kakemin fad'a da gori. wlh nima ashirye nake nakad'auki kowane irin mataki nasan dai duk abinka ba zaka ta6a k'ara aureba dan su dada ma nazasu amince ba.

yarima har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayansa tafara ringing ganin ummi ce yasa yasaita nutsuwarsa sannan yayi picking tare da yin sallama.

chan 6angaren sultana sadiya ta amsa masa tare da cewa yarima kazo kasameni inason ganinka.

yarima suhail cike da ladabi yace ummi lafiya dai ko?

Ummi tace lafiya lou kawai inaso mutattauna ne akan kayan da kace aware akai gidan marayu da gajiyayyu.

yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toh ummi ganinan zuwa, nan yakashe wayar tare da mik'ewa ko inda sumayya take bai k'ara kalloba yaficce yabar d'akin.

sumayya haushi yakamata saboda ba haka tasoba taso ace sai tagama ja masa rai sannan zata amince masa domin itama buk'ace take da shi kawai dai tana daurewane domin tanuna masa kuskurensa na wulak'antata da yayi, tsaki taja tare da mik'ewa tsaye tace nasan dai dole zai dawo gareni.

yarima ko da yafita direct turakar iyayensa yaje a parlour yatarar da k'anwarsa Gimbiya Rahma a tsakiyar kuyangi sun zagayeta suna mata fifita da tausa inda ita kuma take waya.

ganinsa yasa gaba d'ayansu suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, Rahma ma dasauri tamik'e tsaye tare da d'an rissinawa cike da girmamawa tace barka da shigowa.

Yarima batare da ya tanka musuba yayi musu nuni da k'ofa alamun sufita.

gaba d'ayansu suka mik'e suka fita daga d'akin, Rahma ma har zata fita yace ke dawo.

Rahma dawowa tayi tazauna kujerar da take opposite d'in wadda yake zaune, kallon yayan nata take taga baida niyar yin magana gashi duk ya canza, ahankali tace yaya suhail bakada lafiya ne?

Yarima suhail ahankali yamaido kallonsa gareta kamar ba zaiyi magana ba sai kuma can yace tashi kije kihad'o min ruwan lipton da lemun tsami kar kizuba komai ciki.

Rahma mik'ewa tayi tare da d'an rissinawa sannan taffice daga d'akin.

Yarima jingine kansa yayi akan kujerar da yake zaune tare da lumshe idonsa shi kad'ai yasan abinda yake ji.

ummi tana fitowa daga d'akinta ganin yarima a haka yasa tayi tsaye tana kallon d'an nata ahankali tace suhail daman ka shigo shine baka fad'a min ba?

Yarima suhail ahankali yabud'e idanuwansa da suka rikid'a suka koma launin ja yasafkesu akan fuskar ummi tare da yin d'an guntun murmushi yace sorry ummi ban dad'e da shigowaba.

ummi tsaye tayi tana kallon d'an nata yanayinsa yasa saida gabanta yafad'i a rud'e tace suhail me yake damunkane bakada lafiya?

Yarima murmushi yayi yace lafiya ta lau ummi.

ummi kasa cewa komai tayi saidai binsa take da kallo tana nan tsaye Rahma tashigo da wani plate d'auke da ruwan lipton da lemon a gefe, gaban ummi ne yashiga fad'uwa ganin Rahma ta aje gaban yarima tare da duk'awa tana matsa lemon d'in cikin cup d'in,

tausayin d'antane yakamata domin tabbas tasan abinda take tunani shi yakasance, ahankali taga yarima suhail yad'auki cup d'in yana sha yana yamitsa fuska duk Wanda yagani yasan ba dan dad'i yake sha ba kawai dai dan ba yadda ya iya.

ganin haka yasa ummi tawuce tana jin wani iri a cikin ranta bata zarce ko'inaba sai turakar mijinta bata damu da gaisuwar da akeyi mataba domin kwatakwata ma hankalinta ba anan yakeba.

ko da tashiga lokacin yana zaune saman gado hannunsa rik'e da newspaper yana dubawa, jin anbud'e d'akin yasa yamaida kallonsa ga k'ofa, yanayin yadda yaga matar tasa ta shigo yasa ya aje newspaper d'in da take hannunsa yazuba mata ido.

Sultana bilkisu itama tsaye tayi tana kallonsa ta bud'e baki zatayi magana kenan sai hawaye suka fara zuba daga idonta, Sultan Ahmad cike da rud'ewa yamik'e yanufo inda matar tasa take yace bilkisu lafiya me yake faruwane?

Sultana Bilkisu fashewa tayi da kuka tace ranka yadad'e kagafarceni akan abinda zan fad'a domin hak'urina ya k'are ace d'ana tunda yayi aure baida kwanciyar hankali kaduba kaga duk mulki, sarauta, kyau, dukiya babu wanda *YARIMA SUHAIL* yarasa saidai abu d'aya shine kwanciyar hankali.
Chapter 17 · 0% Book details