← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 102

Sashe 15

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zarah tace dan Allah mama kibarni muje tare, mama ganin yadda zarah duk hankalinta yake a tashe dan ko abincin kirki bata samu taciba dan haka tace toh shikenan kushirya kutafi.

Mama tataimaka ma Rauda tacanza kaya, Rauda cema Zarah tayi tad'auko handbag d'inta akwai kud'i a ciki dan kar a buk'aci wani abu.

Aysha ce tafita tasamo musu adaidaita nan suka tafi General Hospital d'in garinsu.

basusha wahala ba wajen ganin likita, ko da Rauda tashiga zarah zaune tayi tana jiran fitowarta,

Rauda take zaune opposite d'in kujerar Doctor Xeey Xeey cike da kulawa doctor Xeey Xeey take mata tambayoyi ita kuma tana bata amsa nan Dr Xeey Xeey tarubuta mata taste tace taje tayi kuma tatabbatar yau ta kawo mata.

Rauda Kar6a tayi tafito dasauri zarah tamik'e daga inda take zaune tana jiran fitowar 'yar uwartata.
tace Yaya Rauda sannu.
Rauda dakyar tace Zarah taste ne tabani muje lab.

zarah tace toh yaya Rauda.

ko da sukaje lab aka d'ibi jininta sannan aka bata 'yar roba tayi fitsari a ciki nan akace sujira nan da 30 minutes result zai fito.
zama sukayi suna jira har minti talatin yacika aka basu nan Rauda taje takaima Dr xeey xeey sakamako.

Dr xeey xeey tana dubawa murmushi tayi sannan tayi 'yan rubuce-rubucenta bayan ta gama tad'ago kai takalli Rauda tace toh Alhmdllh ina tayaki murna domin kina d'auke da ciki tsawon wata biyu nasoma ace tare kukazo da mijinki.

Rauda da tunda Dr ta ambaci ciki tarikece cikin d'aga murya tace doctor ciki?
Dr xeey xeey tagyad'a mata kai tace of course dan haka za'a maida miki folder d'inki a ANC kidinga zuwa awo tunda har yakai kusan 2 months batare da anduba lafiyarsaba zaki dinga zuwa awo.

Rauda zufa ce tafarayi dasauri taduk'e k'asa tare da fashewa da kuka.
da mamaki Dr xeey xeey take kallonta tace menene abin kuka? kyautar da Allah yabakice bakyaso ko mi?

Rauda cikin sheshek'ar kuka tace Dr dan girman Allah kitaimaka kiciremin cikin nan wlh bana sonsa.

Dr xeey xeey fara'ar da take fuskarta tagushe cikin fad'a tace akan wane dalili zaki cire ciki idan ke bakyaso toh mijinkifa? ni gaskiya bana zubar da ciki.

Rauda cike da tashin hankali tace Doctor yadda Allah yataimakeki nima kitaimaka min wlh bana son cikin nan idan nakoma da shi gida bansan da wane ido zan kalli iyayena ba.

Doctor da tunda Rauda tafara maganar tazuba mata ido tana kallonta cike da 6acin rai tace idan na fahimceki kina nufin cikin nan na shegene baida uba ko?
Rauda shuru tayi batace komai ba.

ganin haka yasa Doctor tacigaba da cewa toh bari kiji ni bazan ta6a zubar miki da cikiba k'ara ma kiyi hak'uri kihaife abinki ammah kuma kin cuci abinda yake a cikinki domin kin samesa ba tahanyar da tadace ba, k'arama kiyi hak'uri kihaifesa domin kar zunubin yak'aru dan haka tashi kije nidai nabaki shawara haihuwar shi zai fiye miki.

Rauda dakyar tamik'e jiki ba kwari tafito daga office d'in doctor.
tana fita kallon zarah tayi nan hankalinta yak'ara tashi sai alokacin taji wata irin kunya tsaye tayi takasa k'arasawa wajen da zarah take tsaye.

ganin haka yasa zarah tamik'e cikin sauri ta isa inda Rauda take cike da tashin hankali tace yaya Rauda lafiya naganki a haka me yake faruwane?

Rauda hawaye suna zuba daga idonta dakyar tabud'e baki tace zarah ciki gareni.

Zarah a firgice taja da baya cike da tashin hankali tace yaya Rauda ciki kuma?

Rauda gyad'a mata kai tayi tare da mik'a mata takardar da doctor tabata, jikin zarah yana kyarma ta amsa taduba, aiko nan tafashe da kuka tace yaya Rauda meyasa kuka za6a ma kanku irin wannan rayuwar? meyasa kuka za6i son abun duniya kuka 6ata rayuwarku, kingani ko yanzu gashinan kiyi cikin shege cikin da ke kanki bakisan ubansaba kun d'auki alhakinsa idan kika haifesa me zaki ce masa?

Rauda da take kuka dasauri tarik'o hannun zarah tace zarah wlh nima bansan ya zanyiba yau ne karo nafarko da nafara nadamar abinda nake aikatawa dan Allah kizo muje murok'i wata doctor d'in tacire min shi.

zarah fizge hannunta tayi daga rik'on da Rauda tayi mata tana ja da baya tare da girgiza kai, cikin kuka tace yaya Rauda badani za"a had'a bakiba ayi kisan kai meyasa kikeso kikashe ran da baida alhakin kowa saima shi da yake da naku?
kiji tsoron had'uwarki da ubangiji ga laifin zina ga na kisan kai, kituna tsayuwar ki gaban Allah ranar gobe k'igama, baki tsoron garin zubar da cikin kije kirasa ranki?

Yaya Rauda wani irin nadamane taji ya zo mata nan tak'ara fashewa da wani sabon kukan tare da rik'o hannun zarah da itama take kuka tace zarah nafasa zubarwa wlh nayi nadamar abinda na aikata a yanzu kuma ba zan zubar da cikinba.

zarah cike da jin dad'i tace nagode sosai Yaya Rauda da kika fahimceni.

Yaya Rauda d'an tsagaitawa tayi da kukan da take tace saidai kuma inaso kiyimin taimako guda.

zarah dasauri tace Yaya Rauda kifad'i abinda kikeso zanyi miki.

Rauda tace inaso kafin muje gida kifara rakani wani waje

zarah da mamaki take kallonta tace yaya Rauda ina zamuje?
Rauda rik'o hannunta tayi tace muje kawai zarah.

zarah batayi musuba tabi bayanta.

mai adaidaita tatsaida musu tafad'i anguwar da za'a kaisu zarah dai shuru tayi tana mamakin inda zasuje.

Rauda ce tadinga gwada ma mai napep hanya bayan sunzo anguwar, bakin gate d'in wani gida aka safkesu nan Rauda tabiyasa kud'insa sannan tayi Knockin d'in k'ofar maigadi ganin Rauda ce yasa yabud'e saboda daman ya saba ganinta nan suka shiga ciki, ita dai zarah binta kawai take

cikin wani parlour suka shiga da sallamarsu ammah bakowa ciki Rauda kallon zarah tayi tace Zarah shigo muzauna,

zarah girgiza kai tayi tace a'a yaya Rauda nan gidan wanene.
Rauda ganin zarah duk ta rikice yasa tace kar kidamu bawani abu inaji suna ciki kizo kizauna.

Zarah a tsorace tabi Rauda suka zauna nan Rauda tad'auko wayarta tayi kira itadai zarah kawai ji tayi ta ce gani cikin gidan ka sannan takashe wayar.

zarah a tsorace tace yaya Rauda wai nan gidan wanene me zamuyi?

Rauda har ta bud'e baki zatayi magana sai ga wani mutum ya fito daga cikin gidan, da kallo duk suka bisa fuskarsa d'auke da murmushi yazo yazauna d'aya daga cikin kujerun d'akin tare da washe baki yace baby daman kina tafe baki fad'amin ba? kallon zarah yayi da itama take kallonsa yace sannu 'yanmata halan ke sister d'intace naga kuna kama?

duk tambayoyin da yayi musu babu wanda yatanka mushi sai ma ido da suka zuba masa.

Rauda fuskarta a d'aure tace Alh umar nazone infad'a maka ina d'auke da cikin wata biyu.

nan fara'ar da take fuskarsa tagushe yace ciki kuma rauda?

Rauda hawayene suka fara zuba daga idonta tace eh ciki.

dariya yayi irin ta rainin wayau yace lallai Rauda toh garin yaya kika bari har ciki yashigeki? toh wai ma wanene yayi miki cikin?

Rauda da mamaki take kallonsa tace Alh Umar in bakaiba wanene nake huld'a da shi? ai kaine uban d'an saisa nazo nafad'a maka.

d'aure fuska Alhaji umar yayi tare da daka mata tsawa yace ke banason sakarci kingama zuwa kinbi 'yan iska sannan kizo kice d'a nane,

Rauda cikin kuka tace wlh d'ankane

Alh umar a harzuk'e yamik'e tsaye yace toh bari kiji duk wanda yatsaya miki a garin nan bai isa yasa in amshi cikin kiba a matsayin d'ana kije dai kigano uban cikinki dan haka kutashi kufitar min daga gida.

Zarah ranta ya 6aci sosai jin kalaman da Alh umar yake jifan yayarta dasu ga Yaya Rauda kuka kawai takeyi, cikin 6acin rai tamik'e tsaye tare da nunasa da yatsa tace kai malam kar karaina ma mutane wayau kana nufin k'arya akeyi maka ba cikin naka bane? ai ni wlh naga wautar yaya Rauda da ta iya ba jakki irinka kanta, ni ai ko a k'afa aka d'aura min kai sai na kwance.

Alh umar ransa ya 6aci sosai cikin fushi yake ke karkinemi kigaya min magana wlh yanzu insa ad'aureki ni nace tabani kanta ba kwad'ayi yaja mataba?

zarah cikin d'aga murya tace kai kar kasaki kak'ara d'agamin murya kuma idan bakasa and'aureniba toh ba'a haifekaba.

Alh Umar a zuciye yad'aga hannu zai mari zarah cikin zafin nama zarah tagoce.
yaya Rauda da take zaune tana mamakin yadda zarah take balbala fad'a tabbas tasan ankai zarah k'arshe domin zarah tana da hak'uri sosai, da sauri Rauda tamik'e tare da rik'o zarah tace zarah ki kyalesa tunda dai har ya k'aryata alhali kuma ya san gaskine toh yaje shi da Allah.

Zarah fizge hannunta tayi tace yaya Rauda kikyaleni ya za'ayi mutum yana akan gaskiyarsa a tauye masa hak'i wlh dole yakar6i cikin nan.

Alh umar dariya yayi yace ke yanzu har kina tunanin zan kar6a ko? toh muzuba agani wanene zai ci nasara.

Rauda cikin kuka tace umar *LAIFI NANE* da na amince na mallaka maka kaina ammah inaso kasani ba zan d'auki matakiba saidai kaje kai da Allah domin shine kad'ai zai kwatarmin hak'k'ina kuma kai shedane kaine karabani da budulcina kayaudare kace zaka aureni, wlh a yanzu na tsaneka kaje kawai

rik'o zarah tayi tace zarah wuce mutafi zarah har ta bud'e baki zatayi magana Rauda tadaka mata tsawa tace kiwuce nace miki!

Zarah ba dan tasoba tabi bayan Rauda suka fita suka bar Alh umar a tsaye cike da takaicin bak'ak'en maganganun da suka yada masa.

Ko da suka fita zarah kallon Rauda tayi cikin 6acin rai tace haba yaya Rauda ya za'ayi kina da gaskiyarki sannan kibari atauye miki hak'i.

Rauda cikin kuka tace zarah ina kokwantone domin bansan ainahin cikin na waneneba.
Zarah cikin tashin hankali tace ban fahimcekiba yaya Rauda.

Rauda share hawayen fuskarta tayi sannan tace zarah ba zan 6oye mikiba wlh mutum biyune kawai nasan ina mallaka ma kaina.

zarah tace yaya Rauda wannan wace irin rayuwace toh wanene gudan?

Alh munir ne wlh bayan su bana huld'a da kowa.

Zarah tace toh yaya Rauda me zai hana shima muje wajensa?

Rauda jinjina kai kawai tayi nan suka samu mai adaidaita Rauda tafad'a masa anguwar da zai kaisu........

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
Chapter 15 · 0% Book details