← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 102

Sashe 54

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.

Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.

Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.

Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.

Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad'a min matsalarki ni nayi alk'awali zan taimaka miki kid'aukeni a matsayin uwa,
Zarah d'ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k'ullamin sharri da angama wanchan sai afad'a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak'ura da auran inkoma gidanmu,
Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a'a ranki yadad'e kar kice haka dan Allah kifad'amin abinda yake faruwa nayi alk'awali zan taimaka miki.

Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad'a ma jakadiya,

Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya,
Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka?
Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.

Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak'ura da auren inkoma gidanmu.

A'a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had'ine ba auren soyayya bane sukayi.

hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k'ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.

Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.

Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d'akin najuyo magana k'asa-k'asa a bedroom d'in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik'on k'warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d'a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d'in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.

Zarah cike da rud'ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d'iyarta.

Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad'an daga cikin halayyarta dan tun yana k'arami idan yaje part d'inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad'e ni da idan nafad'a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad'aice lokacin da abun yafaru.

Toh ba'a gane taba? Cewar zarah.
Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud'e cikinsa yafad'aba wannan halinsane tun yana k'arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene,
indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad'annan abubuwan.

Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad'e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.

Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.

Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad'e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had'a kinga ai bakowa bane zai iya k'in yarda, yanzu dai abu d'aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad'a min.

nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d'insa sufad'i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba,
Zarah tace anya kina tunanin zai amince?
Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k'aryaba,

Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak'ik'a kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,

Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.

Zarah saida gabanta yafad'i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.

'Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k'addara ta riga fata,

Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba?
Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad'ewaba, jakadiya tana fad'in haka tamik'e tare da d'an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.

Zarah d'aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.

Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik'e sirrin maganar da nafad'a miki.

Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.

Jakadiya tace nagode, nan sukayi sallama tafita, zarah tsaye tayi tana tunani cike da jinjina ma sumayya da mahaifiyarta sannan daga baya tawuce tashige bedroom d'inta takwanta, nan hawaye suka cigaba da fita daga idonta tana tunanin hukuncin da yarima zai yanke mata akan laifin da ba ita ta aikata shiba, fashewa tayi da kuka tace ya ubangiji kakawo min d'auki, kuka tayi sosai saida taji kanta ya fara ciwo sannan tadaina haka taita juyi saman gadon daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima bayan zarah ta fita zama yayi saman gadonsa tare da dafe kansa cike da takaici, mamakin zarah ne yakamasa dan baita6a tunanin haka daga garetaba tun daga yanayin tarbiyarta, ya dad'e zaune yana jinjina lamarin dan abun ya d'aure masa kai sosai dan idan ya ce ba ita bace toh wanene zaiyi hakan?, tsaki yaja cike da takaici sannan yakwanta abu guda yatsaya masa a rai kalmar da tafurta ta nima ina da wanda nakeso, haka kalmar yaita jinta a kunnensa tana masa yawo har daga k'arshe bacci yad'aukesa..

A chan 6angaren sumayya kiran sultana sadiya tayi tana yin picking bata bari tayi ko sallama ba cikin jin dad'i tace ummah na aiwatar da komai kuma ina tunanin nasara a cikin aikin namu, daga chan 6angaren sultana sadiya dariya tayi tace gaskiya naji dad'i daughter ai ina fad'a miki ta ruwan sanyi zatabar gidannan dan makirci kala-kala babu Wanda ban iyaba idan akayi wani baiyiba sai acanza wata hanyar, cikin jin dad'i sumayya tace saisa nake k'ara sonki ummana dan duk abinda nakeso kema kinasonsa na rabbata yanzu yarima zai zama nawa ni kad'ai.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kar kidamu d'iyata farin cikinki shine nawa, saisa nake burin kihaifo min jika wanda zai gaji masarautar nan ammah kinkasa fahimtar inda nadosa, Indai kinsan kina yin planning toh kitaimaki kanki kidaina tun kan waccan munafukar tafara haihuwa,
Gaban sumayya saida yafad'i dan bata ta6a yin tunanin hakaba, ahankali tace hakane kuma ummah insha Allahu bama zata haihuba zata bar gidan.
Sultana sadiya tace na dai fad'a miki kirufa ma kanki asiri kidaina.
Cikin shagwa6a sumayya tace toh ummah na ji.
Uhm Allah yasa dagaske, cewar sultana sadiya.
Ameen ummana.
Yauwa toh yanzu kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Toh ummah ko mi kenan sai kinjini, nan sukayi sallama suka kashe wayoyin.
Sumayya fad'awa tayi saman gadonta cikin murna tace yes nasan zuwa gobe waccan munafukar zata koma kongon gidansu, ahaka tayi bacci cike da farin ciki.

Cikin dare zazza6i da ciwon kai suka tashi zarah daga baccin da take nan taita juyi saman gadon daga k'arshe k'asa tasafka takwanta, ciwon cinta yake babu wanda zata iya kira dan ko hannunta kasa d'agawa tayi daga k'arshe, tana nan tana juyi ahaka aka kira sallar asuba.

Har aka gama sallah akan kunnenta ammah takasa tashi dakyar tasamu tamik'e tana dafa bango har tashiga toilet, saida tahad'a ruwan d'umi tayi wanka sannan tad'auro alwallah daga zaune tasamu tayi sallah sannan talalubo paracetamol tasha, nan saman darduman tayi kwanciyarta har saida gari yafara yin haske sannan tamik'e tajanyo alkyabbarta tasaka, cikin rashin k'warin jiki tafito duk wanda yaganta ya san batada lafiya, ko da kuyanginta suka gaisheta hannu kawai tad'aga musu taku take dak'yar tana dafa bango tana tsayawa tahuta ahaka ta isa part d'in yarima.

Tana murd'a k'ofar bedroom d'in yarima tsaye tayi tare da jingine kanta jikin k'ofar tana maida numfashi,

Yarima da daidai lokacin yasafka daga saman gadonsa tsaye yayi yana k'are mata kallo ko da cikin fushi yake da ita ammah hakan bai hana yaji wani iriba da yaganta cikin yanayin.
Chapter 54 · 0% Book details