← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 102

Sashe 59

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*Yau page d'in nakune my fan's mutanen saudiya, sak'onku yana zuwa a gareni nagode sosai da soyayyar da kuke nunamin saidai ince Allah yabarmu tare, jinjinar bangirma agareku Sis Aisha*_

*PAGE* 4⃣8⃣

Sultana sadiya dak'yar tasamu tad'an tsaida nutsuwarta sannan tad'an yi d'an murmushi mai kama da yak'e tace ranki yadad'e ya akayi kikasan cikine da ita kuma an tabbata shi d'inne?

Murmushi dada tayi sannan tace tabbas cikine da ita dan rannan k'arnin kifi kawai taji ammah saida tayi amai ke ko yanayinta zaki kallah sai kin gane hakan kuma ko jiya da yarima yazo gaisheni saida namatsa mai da tambaya sannan yafad'amin ashe cikin har ya kai tsawon wata hud'u, kinsan halin yarima ba komai yake fad'aba.

Sultana sadiya saida gabanta yayi wani irin fad'uwa, cikin zuciyanta tace wata hud'u??? batasan lokacin da tace hmm ai yarima ya iya munafunci.
Ganin yadda sultana bilkisu da dada suka zuba mata ido yasa tayi murmushi tace ya za'ayi ni a matsayina na mahaifiyarsa yak'i fad'amin, ai ya kamata tasamu kulawa sosai a wajenmu tunda mune matsayin dangi yanzu a wajenta saboda da mu take zaune.

Dada murmushi tayi tace tabbas maganarki gaskiya ce koda munso ace sumayya ce tafara haihuwa ammah bakomai tunda haka Allah yak'addara kuma dukkansu d'ayane tunda duk matansane,

Sultana sadiya cikin rashin nuna damuwa tace ai d'a nakowane da zarah da sumayya duk d'ayane a wajena.

Murmushi sultana bilkisu tayi tace nima haka ina sa rai nan ba da dad'ewaba my dota nima tahaifo mana baby.

Dariya sultana sadiya tayi sannan tace saidai daga baya dan mu nan ba da dad'ewaba zamu amshi jika.

Eh munji babu komai muma namu insha Allahu yana nan zuwa.

Dada ido tazuba musu cikin jin dad'i sannan tace Allah yakawo masu albarka.

Gabad'ayansu suka amsa da Ameen.

Mik'ewa sultana sadiya tayi tana murmushi tace ranki yadad'e zan wuce akwai bak'uwa da zanyi yanzu hakama ina sa ran ta iso, insha Allahu zan je induba jikin my daughter.

Cikin jin dad'i dada tace toh bakomai.
Sultana bilkisu tace sai anjima sultana.

'Dan rissinawa sultana sadiya tayi sannan tace na barku lafiya, tana fad'in haka tajuya tafita.

Nan sultana bilkisu da dada suka cigaba da hirarsu, saida maraice yayi sannan sultana bilkisu tayi ma dada sallama takoma part d'insu cike da farin ciki akan cikin zarah.

A 6angaren sultana sadiya ko da tafita bak'in cikine yatokare mata mak'ogwaro, takaici duk yacikata ita kanta ta yi mamakin yadda akayi ta iya danne bak'in cikinta a gaban su dada.

Ko da ta isa part d'inta a parlour tayada zango nan tashiga kaiwa da kawowa ahankali take furta na shiga ukku ya akayi wata daga zuwanta tariga d'iyata samun ciki, kai da sake dole ne inbi ta kowace hanya wajen ganin na zubar da shi, taya wata d'iyar talakka zata fara aje jika a masarautar nan? Ba dai hakan yana nufin plan d'in da nashirya ya rugujeba? Inaaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba wlh, Tsanar zarah sa yarima ne taji ya k'aru a cikin zuciyanta.

Cike da 6acin rai tajanyo wayarta takira sumayya, sumayya na yin picking sultana sadiya cikin d'aga murya tace ke kina ina?
Daga chan 6angaren gimbiya sumayya tace ummah lafiya naji ki haka? Ina gida.
dan ubanki kizo yanzu kisameni ina jiranki.
Sumayya cike da mamakin mahaifiyartata tace toh ummah,
Sultana sadiya bata k'ara magana ba ta kashe wayar tare da wulli da ita saman cushin.

Daga chan 6angaren sumayya da mamaki tabi wayar da kallo ahankali ta furta lafiya? Kiran me ummah take min haka cikin gaugawa? Ba abinda yafi d'aure mata kai sai jin yadda ummah tayi mata magana cikin tsawa.
Ahankali tafurta Allah dai yasa lafiya, tana fad'in haka tamik'e tasaka alkyabbarta sannan tafito tanufi part d'in mahaifiyartata.

Ko da ta isa a tsaye tatarar da sultana sadiya tana zagaye d'akin tana cize le6e, cike da rud'ewa sumayya ta isa wajenta tace ummana lafiya me yake faruwa?
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace sumayya komai ma ya faru.
Cike da mamaki sumayya tace ummana ban fahimcekiba.
Taya zaki fahimceni sumayya bayan kinyi wasa da damarki? Toh gashinan abinda nake guje miki ya faru..."sultana sadiya tafad'i hakan cikin d'aga murya"
Sumayya tsaye tayi tana kallon ummanta cikin rashin fahimtar inda tadosa.
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kishiyarki tana d'auke da cikin yarima na tsawon wata hud'u.

Wani irin fad'uwan gaba yaziyarci sumayya tsaye tayi cak tana jin abun kamar a mafarki, chan sai ta k'yalk'yale da dariya tace ummah ciki kuma tsawon wata hud'u? Kina nufin zata haihu da yarimana? Chan kuma sai ta fasa k'ara tare da furta wlh k'aryane hakan ba zai ta6a faruwaba.
Kallon ummah tayi tafashe da kuka tace ummana wlh ban yardaba babu yadda za'ayi inbar wacchan matsiyaciyar tahaihu da yarimana ummah wlh sai na kasheta saidai nima a kasheni.

Sultana sadiya jin d'iyartata tana surutai cikin d'aga murya gudun kar ajisu yasa tajanyo sumayya suka shige bedroom d'inta.

Suna shiga sumayya tafad'a jikinta tare da fashewa da kuka tace na shiga ukku ummana ya zanyi da rayuwata ummah na tsani yarinyar chan, ba zan ta6a yadda cin mutuncin da yarima yayi minba ace 'yar talakkawa yayi ma ciki wlh ya munafunceni Allah ummah Sai na kasheta saidai shima yakasheni.

Sultana sadiya rungume d'iyartata tayi cike da tausayinta tace kidaina cewa haka sumayya kinga abinda daman nake guje miki yanzu gashinan kinyi wasa da damarki.

Sumayya cikin kuka tace ummana wlh ba zan ta6a yarda a zalunceniba inma haihuwarce ai ni yafi dacewa inyita.

Sultana sadiya rik'ota tayi sukaje bakin gado suka zauna cike da tausayi tace sumayya kiyi shuru hakanan muyi magana.

Sumayya share hawayen fuskarta tayi nan tazuba ma umman ido.

Sultana sadiya tace yauwa ko kefa, yanzu dai da farko inaso kikwantar da hankalinki kinutsu kar kice zaki kawo tashin hankali a gidan aurenki dan kinsan wannan mijinnaki ba zai d'auki hakan ba, sannan indai kinsan kina planning toh kidaina kisamu kema cikin nan kiyi sa, inyaso ita zarah kibarni da ita nasan yadda zan 6ollo ma lamarin.

Sumayya tace ummah toh cikin nata fa?

Tsiyata da ke Sumayya wani lokacin baki ganewa, tunda dai nace kibarni da ita ai nasan abinda zanyi, na dai fad'a miki kar kikuskura kice zakiyi mata wani abu da kanki.

Sumayya tace toh ummah.
Yauwa kokefa.
Murmushi kawai Sumayya tayi batare da tace komai ba.

A 6angaren sultana bilkisu kuwa koda takoma 6angaren su a bedroom d'in sultan Ahmad tayada zango lokacin yana zaune yana duba wata newspaper,

Bud'e k'ofan da tayi tashigo yasa yad'aga kai yakalleta ganin yadda taketa fara'a yasa ya aje newspaper d'in tare da yin murmushi yace da alamu yau matartawa tana cikin farin ciki.

Sultana bilkisu Ida k'arasowa tayi wajensa tazauna fuskarta d'auke da fara'a tace tabbas ranka yadad'e ka yi gaskiya domin yau ina cikin wani irin farin ciki.

Rik'o hannunta yayi yace toh nima afad'amin farin cikin da ake nima intaya.

Sultana bilkisu murmushi tasakar masa sannan tace ranka yadad'e mun kusan samun jika.

Jika fa kikace?

Eh ranka yadad'e, tabbas auren zarah da yarima akwai alkhairi a cikinsa, my son ya kusan zama daddy.

Sultan Abbas kasa 6oye farin cikinsa yayi yace Alhmdllh Allah abun godia, gaskiya naji dad'i kuma nayi farin ciki dan arayuwata inason ganin jinin yarima,

Dariyar jin dad'i sultana bilkisu tayi tace was yaga yarima da d'a.

Shima sultan Dariyar yayi yace Allah dai yasafke lfy, Allah yakawo masu albarka.

Ummi cikin jin dad'i tace Ameen farin cikina.
Gabad'ayansu suka sakarma juna murmushi, jin kiran sallar magrib ne da aka fara yasa suka mik'e, sultan Ahmad yayi alwallah yawuce masallaci.

Sumayya ko da takoma 6angarensu bedroom d'inta tashige tafad'a saman gado nan wani sabon kukan yakubce mata yi take babu k'ak'autawa tausayin kanta yakamata, saida tayi mai isarta sannan tajanyo waya takira zinat.

Zinat nayin picking babu ko sallama sumayya tace baby na shiga ukku.

Daga chan 6angaren zinat tace haba baby akan wane dalili zakice kin shiga ukku, me yake faruwa ne?

Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat dole ince haka domin ina cikin matsala bansan ya zanyi da rayuwataba.

Baby kinutsu kimin bayanin abinda yake faruwa kidaina kuka.

Sumayya tsagaitawa tayi da kukan da take tace zinat wannan bagidajiyar yarinyar daga zuwanta wai har ta samu ciki, wlh ba zan ta6a yarda ba.

Zinat cikin d'aga murya tace kina nufin wannan kishiyar taki?

Toh in ba itaba wa kike tunani ni wlh kasheta zanyi kowa yahuta inyaso nima daga baya akasheni.

Zinat ajiyar zuciya tayi tace kar kice haka baby kiyi hak'uri kijira zan shigo,
Har sai yaushe zaki shigo kina nufin inbari har sai ta haihu? Cewar sumayya
A'a baby ai very soon zan shigo, kijirani zuwa next month zan shigo wlh sai munyi silar zubar da cikin.

Sumayya tace toh zan gwada inga idan zan iya hak'uri har sai kin shigo.

Zaki ma iya baby, yanzu dai nidai burina kikwantar da hankalinki kar kije ki aikata abinda zai je yadawo.

Hmm baby kenan kidaina maganar kwanciyar hankali dan ayanzu hankali ya gama kwanciya kawai dai sai anjima yanzu zan d'an huta.

tana fad'in haka bata jira jin komai daga wajen zinat ba takashe wayarta.

Mik'ewa tayi taje tawatsa ruwa tayi shirin bacci tahaye gadonta dan yau cewa tayi babu abinda zai kaita wajen yarima saidai yayi baccinsa shi kad'ai dan shi kansa haushinsa takeji,
duk yadda taso tayi baccin kasawa tayi kalmar cikin zarah yatsaya mata a rai duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi daga k'arshe saida tasha maganin bacci sannan tasamu bacci yayi awon gaba da ita.

_*Washe gari*_

Wajen 12 zarah zaune take saman cushin hannunta rik'e da waya tana chart sallamar da taji anyine yasa ta amsa tare da d'ago kai takalli mai sallamar, da mamaki take kallon sultana sadiya da take sakar mata murmushi, cikin sauri zarah tamik'e tsaye fuskarta itama d'auke da murmushi tace sannu da zuwa ummah.

Yauwa d'iyata, a'ah kice jiki ya warware, cewar sultana sadiya.
Chapter 59 · 0% Book details