← Book details Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 102

Sashe 6

Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin k'ank'anin lokaci ya isa gidan gona horn yashiga yi dasauri maigadi yazo yahangame masa gate yashiga da motar yana yin parking fitowa yayi yashige ciki bai ma kula da gaisuwar da ma'aikatan gidan sukeyi masaba.

shahid numfashi yake maidawa cike da jin dad'in sunzo lafiya domin bai kawo ma ransa zasu iso lafiya ba, daga k'arshe dai yabud'e motar yafito nan yatsaya saida suka gama gaisawa da ma'aikatan sannan yawuce cikin gidan.

A parlour yatarar da yarima kwance saman kujera idanuwansa a lumshe ya yi matashin kai da hannuwansa,

shahid tsayawa yayi gefensa yace wai yarima meyake faruwa ne naga tun da kadawo daga kiran da dada tayi maka fara'arka tagushe?
kuma dan mugunta kadinga gudu da mu toh idan kai bakason ranka toh ni inason nawa.

yarima idanuwansa a lumshe bai tanka masaba.

shahid tsaki yaja tare da zama yace kai nifa matsalata da kai kenan sai anayi maka magana kashare mutane kamar ba da kai akeba.

shidai yarima suhail baice komai ba saida yayi kusan minti biyar sannan yabud'e baki dakyar yace shahid wlh sumayya batada mutunci yanzu saboda Allah duk mutuncina ammah tana nema tazubar min dashi.

shuru yayi nad'an lokaci sannan yacigaba da cewa ni duk abinda takemin ban ta6a kai k'ararta ga kowaba ammah ita da mun d'an samu sa6ani toh sai kowa ya sani, ya za'ayi matar aure kuma matar yarima kamarni ace wai nabarta tana business har dada tagoya mata baya ai sai aja mutane suzageni.

Shahid cikin ransa yace ai indai wannan marar mutuncin ce zata aika domin bazan ta6a mance rashin mutuncin da tayi minba ranar da nazo wajenka.

chan kuma sai shahid yace kayi hak'uri kasan mata sai da hak'uri kacigaba da hak'urin da nasanka da shi.

yarima bud'e idonsa yayi da suke a lumshe yayi murmushin da yafi kuka ciwo sannan yace shahid kallon da akemin nine macuci cutar sumayya nakeyi babu Wanda yata6a tambayata yadda zaman aurenmu yake ammah wai ni zan saki matata tadinga yawon kasuwanci garuruwa.

shahid cike da tausayi yake kallon abokin nasa domin yasan ba'a ta6a jin matsalarsa saboda zurfin cikinsa ammah yau shine yake fad'a masa abinda yake damunsa tabbas yasan ba k'aramin 6ata masa rai akayiba, shahid yace dan Allah yarima kacigaba da hak'uri kadinga yi mata fatan alkhairi kar kad'auki mataki insha Allahu dakanta zata daina abubuwan da take.

Yarima shahid maida idanuwansa yayi yalumshe yana jin wani iri a ransa,

ganin haka yasa shahid yatashi yafita yana zagaya gidan gonar....

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwata agareki aduk inda kika kasance my Aysha hak'ik'a ina yinki irin sosai d'in nan, ina tayaki murnar sabon novel d'inki da zaki fara mai suna *K'AUNACE SILA* Allah yasa afara lafiya agama lafiya my dear, Happy Birthday in advance🎊🎉🎈_

_*Ba zan gaji da sadaukar muku da page ba Masoya ina jin dad'in comments d'in da nake samu daga gareku a group's da masuyimin ta pc wlh ina yinku over, wannan page d'inma kuje da shi nabakushi a kyauta👌 sis Nerja'art tana sonku irin sosai d'in nan😍*_

page 5⃣

yarima duka wayoyinsa yakashe dan kar adamesa da kira dan yasan confirm ne sai maimartaba ya nemesa,
bayan sallar isha'i suka bar gidan gonar, shahid ne yakar6i key d'in motar yayi driving d'insu domin cewa yayi ba zai yarda yarima yatuk'asuba gudun kar yak'ara irin driving d'in da yayi d'azun shidai yarima baice komai ba yamik'a masa key d'in.

ko da suka isa yarima cema shahid yayi yazo sufara shiga fada sugaishe da sarki, shahid bai musaba yabi bayansa a jere suka shiga fad'a nan duk mutane suka zube suna kwasar gaisuwa ahaka har suka iso gaban sarki,

dasauri wani dogari yad'auko wani had'ad'en carpet yashimfid'a musu nan sauran dogarawa suka zo suka baza manyan rigunansu suka kare su yarima daga ganin mutane suna cewa azauna lafiya yarima, saida suka tabbatar da sun zauna sannan suka matsa nan su yarima suka gaishe da sarki, sarki fuskarsa d'auke da fara'a ya amsa nan fadawa suka d'auka angaisheku yarima mai jiran gado sarki ya amsa gaisuwarku Allah yaja da ranka.

sannan yarima suka gaishe da su daddy da abban sumayya, nan ma fadawa suka d'auka da angaisheku kuma,

maimartaba kallon yarima yayi da yake durk'ushe k'asa yace yarima tun d'azun nake aikawa akira min kai ammah sai adawo acemin tunda kafita baka dawoba.

yarima suhail murmushi kawai yayi.

ganin bashida niyar yin magana yasa shahid cewa ranka yadad'e munje gidan gona ne tun d'azun muna chan.

maimartaba murmushi yayi irin nasu na sarakai sannan yace Alhmdllh gaskiya ina jin dad'in hakan kuma duk ayyukan alkhairi da kukeyi a gari yana dawo min a kunnena tabbas nasan ko bayan raina nabar magajin da zai gadeni Wanda zai so kuma yatausaya ma jama'arsa tabbas kaine yafi cancanta da kakasance *Sarkin sarakai*

yarima dasauri yad'ago kai yakalli mai martaba har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa,

gaba d'aya fadawa suka d'auka angaishe da yarima mai jiran gado, angaishe da kwarzon namiji, angaishe da namijin zaki sarki ya gaisheka.

yarima da shahid k'ara gaishe da sarki sukayi sannan suka mik'e dasauri sauran jama'a da fadawa suma suka mik'e nan suka shiga yi ma yarima kirari har saida yafita daga fadar sannan suka zauna.

shahid saida yaraka yarima har wajen turakarsa sannan yayi masa sallama yatafi gida.

yarima yana shigowa dasauri dogarawa suka zube suna kwasar gaisuwa sannan suka mik'e suka take masa baya suna masa kira, takawarka lafiya yarima, Takawarka lafiya babban dodo mai rikita 'yan maza, takawarka lafiya sarkin sarakai, nan bayi da ma'aikata sukaita fitowa suna gaishesa tun yana amsawa har yagaji yakoma d'aga musu hannu ahaka har ya isa part d'insa dasauri wani dogari yabud'e masa d'akin,nan suka d'auka ashiga lafiya yarima, batare da yarima ya juyoba yad'aga musu hannu nan duk suka duk'a sukace munbarka lafiya yarima akwana lafiya, nan suka tashi duk suka watse, sai guards d'insa kawai suka rage yarima yana shiga bedroom d'insa kawai yawuce.

wanka yayi sannan yakwanta.

tun daga ranar suka rage had'uwa da gimbiya sumayya saidai idan tana son wani abu wajensa sannan take zuwa d'akinsa, yarima bai damuwa da rashin zuwanta hidimar gabansa kawai yake sai inyaji yana buk'atarta sannan yake zuwa d'akinta idan ma yaje sai yayi da gaske yake samu tana amince masa cikin 6acin rai suke rabuwa.

A sibitinsa da aka gina masa yana bada gudunmawa sosai baya bari ana wulak'anta masa patients kamar yarda baya bari awulak'anta masa staffs, hatta talakka idan yazo asibitin ana kar6arsa sannan kud'in magani rabi ake kar6a ana yafe musu rabi nan da nan asibitin yayi suna a garin da wajen garin.

Gimbiya sumayya business d'insu suke kud'i suna shigo mata sosai ammah har lokacin bataje tagano boutique d'in nasuba da yake a garin Abuja inda zinat tazuba ma'aikatan da suke kular musu da kayan kullum tsegumi take ma gimbiya akan rashin zuwanta tagano boutique d'in,

yau ma dai kiran gimbiya tayi a waya, gimbiya sumayya da take kishingid'e bayinta zagaye da ita tuface ake bata a baki tana ci ahankali inda gefenta baiwace take karanta mata labarai anutse, wayarta da tahau rurine yasa kowa yanutsu wadda take rik'e da wayar tatsugunna tace ranki yadad'e gashi ana kira,

gimbiya sumayya yamutsa fuska tayi tace wake kirana?
jikin haule yana kyarma tace bestie naga ansa, harararta gimbiya tayi tace ashe ke kin d'anyi karatu ba laifi ai na d'auka jahilace irinsu indo, indo da take tsaye tana ma gimbiya fiffita murmushi kawai tayi batace komai ba,

gimbiya sumayya d'aukar wayar tayi tare da cewa my zinat dafatan kina lfy?
daga chan 6angaren zinat ta amsa da lfy lou kema dafatan haka sarauniya mai jiran gado
'yar dariya sumayya tayi tare da cewa ke ni har na hangoni ko nazama sarauniyar, Allah dai yakaimu lokacin
zinat tace am wai yaushe zakizo yau fa kusan 5 months ammah shuru bakizo kikaga yadda komai yake tafiya ba? saidai kawai kiji alert d'in kud'i.
gimbiya k'ara gyara kishingid'ar tayi tare da cewa zinat wlh nima inso inzo kawai ina tsoron wulak'ancin yarima.
tsaki zinat taja tace ke wlh kina bani mamaki sai kace ba big gurl ba? yanzu saboda Allah duk class d'inki ammah kizauna wai sai yadda miji yayi dake, ke ya dai kamata kizo munfayi customers sosai kuma akwai kayan da nakeso ink'ara d'auko mana saboda haka kifitar da rana kizo,

gimbiya sumayya dogon numfashi taja sannan tace toh shikenan baby kar kidamu zanzo nima ai daman nayi missing d'inki,

dariya zinat tayi tace koma dai mekenan saidai kinzo, kinga sai kimin ko 2 weeks ne,

gimbiya sumayya tace ina ma dai laifi kice 1 week, shima sai munyi daga da yarima sannan zan samu yayarda, koma dai mekenan zamuyi waya.

nan sukayi bankwana, gimbiya sumayya tunani tashiga yi yarda zata samu tatunkari yarima da maganar batare da yak'i amincewaba.

chan kuma sai taja tsaki cikin ranta tace dolema ya amince dan babu yadda za'ayi yak'unsheni cikin gida shi yana yawon gararanbarsa a gari. bari ma yadawo.

gimbiya sumayya kallon haule tayi tace yau inaso kisamin ido ga yarima idan ya shigo kiyi min magana?

haule cike da ladabi tace tau ranki yadad'e umurninki shine abun cikawata.

wajen k'arfe tara gimbiya tagama shirinta cikin kayan baccinta sannan tad'aura alkyabba daga sama tafeshe jikinta da turare mai k'amshi sannan tafito dasauri ma'aikata da bayi suka hau gaisheta tare da yi mata kirari,

gimbiya sumayya sai yatsina take tana ji suna k'ara mata girman kai, baiwarta haule kawai tace tazo tarakata nan haule cikin sauri tataso tatake mata baya har sukaje 6angaren yarima nan ma dogarawa suka shiga gaisheta sannan suka bud'e mata k'ofa, kallon haule tayi fuskarta ba yabo tace zaki iya tafiya.

haule durk'usawa tayi k'asa tace toh ranki yadad'e atashi lafiya,
Chapter 6 · 0% Book details