Sashe 12
Yarima Suhail Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zarah ce zaune tana tsifar kanta, wayartace tashiga ringing nan tad'auko ganin sunan malam Bello da yabayya a screen yasa tayi picking tare da yin sallama,
daga chan 6angaren ya amsa mata, nan suka gaisa, sannan malam Bello yace dear gani a k'ofar gidanku kifito inganki please.
zarah jim tayi nad'an lokaci sannan taduba agogo taga k'arfe biyar d'in marece. muryasa taji yana cewa zarah ya kikayi shuru ko bakiso nazoba?
zarah tace bahaka bane malam gani nan zuwa batare da tajira jin abinda zai ce ba takashe wayarta,
nan ta tufke kanta da ribbon sannan tajanyo hijab tasaka saida talek'a ganin ba kowa tsakar gida yasa tayi hamdala sannan talalla6a taficce.
A k'ofar gida tasamesa tsaye ya zuba ido domin yaga ta ina zata fito, suna had'a ido dasauri zarah taduk'ar da kanta k'asa tare da yi masa sallama.
fuskar malam Bello d'auke da murmushi ya amsa mata yace zarah na tadoki ko batare da nasanar da ke zuwana ba.
zarah ahankali tace bakomai malam nan tagaishesa ya amsa,
kallon da yakeyi mata duk sai ya gundureta tad'ago kai tad'an kallesa,
murmushi yasakar mata yace kiyi hak'uri wlh ji nayi yau idan ban gankiba ba zan samu sukuniba tunda ko a islamiyya 6oyemin kanki kike bakya ko bari mugaisa, kinsan dai yadda nake sonki.
Zarah murmushi tayi batare da ta ce komai ba.
malam Bello yace shurun da kikeyi fa yana cutar da ni dan Allah kimin magana.
zarah d'ago kai tayi takallesa har ta bud'e baki zatayi magana sai ganin Abbah sukayi tsaye.
A tsorace zarah takallesa bakinta yana rawa tace Abbah sannu da zuwa, wani irin kallo Abbah yawurga mata.
malam Bello dasauri yaduk'a tare da cewa Abbah barka da rana ina wuni?
Abbah yace da ace ban wuniba da ka ganni?
Me yakawoka wajen 'ya ta? duk hure mata kunne da kakeyi a islamiyya bai ishekaba sai ka biyota gida?
malam Bello kansa a k'asa yace kayi hak'uri Abbah wlh ba haka bane,
Abbah yace toh yaya ne?
Malam Bello yace wlh ni tsakani ga Allah son zarah nake kuma ina da burin aurenta.
Abbah yace a haka? Minene aikinka?
Malam Bello yace eh toh gaskiya ni karatu nake ammah ina tsare shago ana biyana.
Abbah yace kana karatu ammah dan rigima kace kana son 'ya ta toh bari kaji d'iyata ba irinka zata auraba domin kwata-kwata baku daceba, bakada abinda zaka iya aurenta dan haka tashi kabar min k"ofar gida.
malam Bello yace kayi hak'uri Abbah insha Allah zan iya rik'on zarah.
Zarah tace dan Allah Abbah kayi.... tsawa Abbah yadaka mata yace wuce kishiga gida ko ranki ya6aci, dasauri zarah tawuce tashige gida tana hawaye.
Abbah kallon malam Bello yayi yace tashi kabar nan kuma kar ka kuskura kak'ara takomin k'ofar gida, Abbah na gama fad'in haka yawuce yashige gida. .
malam Bello yamik'e tsaye daga tsugunnen da yake yatafi yana jin ba dad'i cikin ransa.
Zarah saman katifarsu tafad'a tafara rusar kuka, Abbah ne yashigo gidan yana ta fad'a.
mama ce tafito daga d'aki tace malam lafiya?
Abbah yace ina fa lafiya wlh yarinyar chan idan batayi wasaba sai na sa6a mata a cikin gidan nan, mama tace wa kenan?
Abbah yace zarah mana wai ace tarasa Wanda zata tsaya da shi sai talakka d'an uwanta da baida komai inba wahalaba babu abinda zata tsinta a wajensa.
mama tace hmm malam kenan ai wlh indai zarah ce toh kad'an kagani ita kwata-kwata batada tunani ai ni wlh ban ma San lokacin da tafitaba da bazan bartaba,
mama wucewa tayi tanufi d'akinsu zarah a bakin k'ofa tatsaya tare da d'age labulen d'akin, kallon zarah take da taketa faman kuka cikin fad'a tace ke dan kin raina ni watau da narabaki da wancan yaron baku rabuba ko? shine yanzu dan anyi miki magana shine kike kuka, toh bari kiji ko da ace zakiyi kukan jini bazaki auresaba kuma dole kurabu inma bakiyi hankaliba islamiyyar ma sai inhanaki zuwa, butulun banza inba ma asaraba me zakiyi da d'an uwanki talakka duk kyaun naki baida amfani wlh, hatta k'anwarki tafiki sanin daidai.
zarah dai tana jin mama tana ta fad'anta har tagama tatafi itadai kuka take.
kiran Sallar magrib da akayine yasa tatashi taje tayo alwallah har lokacin fuskarta babu walwala.
bayan sallar isha'i kwance take saman katifa gefenta Aysha ce kunnenta d'auke da earpiece da waya a hannu da alama kallo takeyi.
zarah wayarta tad'auko talalubo number d'in malam Bello takirasa, tana fara ringing yakashe yakira,
zarah tana d'aga wayan yayi mata sallama.
jin muryarsa yasa taruntse ido tana jin wani iri acikin zuciyarta sai a lokacin taji kunyar abinda Abbah yayi masa.
muryarsa ta tsinkayo yana cewa hello zarah bakya ji na?
zarah cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace malam dan Allah kayi hak'uri akan abinda yafaru
murmushi malam Bello yayi yace kar kidamu zarah wlh bakomai kawai dai ina tunanin anya zan iya rabuwa da ke? domin ni kaina nasan ina miki wani irin mahaukacin so.
zarah ajiyar zuciya tayi tace malam Bello wlh nima ina sonka kuma ina ji a raina akwai lokacin da iyayena zasu amince mana muyi aure.
malam Bello yace hakane ammah ni fatana kitaimaka kirik'e min amanar kanki har ingama karatuna muyi aure.
zarah tace kar kadamu nariga na amince maka kuma insha Allahu idan da rabo zamuyi aure.
cike da jin dad'i malam Bello yace nagode sosai zarah Allah yamallakamin wannan tauraruwar yarinyar.
dariya zarah tayi daga nan suka shiga yin hira, sai da sukayi kusan awa d'aya sannan sukayi sallama suka kashe wayoyinsu kowa yana jin dad'i a ransa, nan zarah tanemi damuwarta tarasa.
________________
Gimbiya Sumayya lokacin da jirginsu ya safka zinat ce tazo tatarbeta cike da farin ciki suka rungume juna daga nan suka nufi inda motar zinat take suka shiga suna ta hira, zinat tace baby yanzu gida zamu wuce ko boutique din zan kaiki kifara ganowa? Sumayya jingine kanta tayi a sit din da take zaune tace dear muje gidanki kawai yanzu agajiye nake, murmushi zinat tayi tace toh ranki yadad'e angama.
dariya sukasa gaba d'ayansu Sumayya tace abun ma har da tsokana kenan, daidai lokacin tayi horn maigadi yazo yabud'e mata gate tacinna motarta a ciki a parking space tayi parking sannan suka fito suka d'unguma cikin gida.
bedroom suka wuce Sumayya tafad'a saman gado tare da cewa wash.
dariya zinat tayi tace baby keda kikazo ta flight ammah shine har kin gaji? kokuma namance ku jinin sarauta bakwa motsawa dayawa saidai ayi muku komai.
harararta Sumayya tayi tace ke dai kika sani da tsokana, ni yanzu dai taimaka kisa ahad'a min ruwan wanka infarayi tukun,
zinat mik'ewa tayi tanufi k'ofa tafara kwalah ma 'yar aikinta kira, dasauri tazo tare da russunawa k'asa ranki yadad'e gani, zinat yamitsa fuska tayi tace shiga toilet kihad'a ruwan wanka, dasauri tatashi tashiga tahad'a ruwan sannan taficce tabar d'akin.
Zinat kallon sumayya tayi tace baby kitashi kije kiyi wankan ko intaimaka miki,
sumayya mik'ewa tayi tad'auki towel tacire kayan jikinta tawuce tashiga bathroom.
bayan ta fito kwalliya tayi tashirya cikin English wears riga da skirt tafeshe jikinta da turare, kallon Zinat tayi da tatsareta da ido tace dear wannan kallon fa?
Zinat tace Mrs yarima kinyi kyau sosai.
gimbiya sumayya ta6e baki tayi tace har kin tunomin da wannan d'an jin kan, nidai muje inyi lunch domin yunwa nakeji yanzu.
Zinat mik'ewa tayi suka fito suka nufi dining nan Zinat tayi serving d'insu suna ci suna hira.
bayan sun gama saman 3 seater suka dawo suka yada zango, sumayya wayarta tad'auko tace bari inkira su ummah inshaida musu na iso lfy tun kan surigani kira,
Zinat tace hakan fa zaifi.
nan sumayya takira sultana sadiya da dada tafad'a musu ta sauka lafiya.
bayan sumayya ta gama wayar zinat tace toh baki kira miskilin mijin nakiba.
ta6e baki tayi tace kibarsa kawai wannan d'an rainin wayaun ai wlh indai bashi yakiraniba toh ba zan kirasaba _(lallai sumayya kin mance wanene yarima suhail)_
Zinat tace ai wlh kina ma hak'uri da shi ai ni kwata-kwata ban tunanin zan iya zama da irin su mijinkiba.
sumayya tace hmm nima dai dan ina sonsa ai da ban iya zama da halinsa, ke kafin fa intafo jiya saida mukayi drama, yanzu dai tashi muje inga boutique d'in dan na k'agara ingansa.
zinat murmushi tayi tace baby ai nad'auka sai ansallameni sannan zamuje kinsan fa nayi missing d'inki dayawa.
sumayya 'yar dariya tayi tace kidai bari mudawo tukun dan ni yanzu hankalina ya fi karkatuwa da zuwa.
zinat tace ke Alhaji Jamilu fa yana nan Abuja ai kinsan na fad'a miki.
sumayya yamitse fuska tayi tace wanene kuma jamilu,
harararta zinat tayi tace ammah fa ke 'yar iskace baby yanzu Alhaji jamilu kika mance?
yamitsa fuska sumayya tayi tace hmm zinat kenan ai ban mance da shi ba dan mugunta kikaja nabasa kaina shine namijin da yafara sanina,
dariya zinat tayi tace ammah ai lokacin mun samu abinda mukeso, ke ni yanzu haka in kinason ganinsa nasan gidansa sai muje inrakaki.
sumayya harararta tayi tace Allah yakyauta ke nifa yanzu namiji Indai ba mijinaba bana jin zan k'ara amince ma wani,
zinat da mamaki take kallonta tace saboda me? sumayya cikin rashin damuwa tace haka kawai mazan basu gabana.
zinat tace toh wlh ko da sau d'ayane ki amince muje gidan Alhaji jamilu domin yana ta tambayata ke, kinga mun k'ara jari.
sumayya mik'ewa tayi tsaye tace nidai kitashi muje ko mun dawo domin inaso inhuta.
zinat tace toh nima dai kenan yau ba tani akeba, sumayya rik'o hannunta tayi tace haba baby ai ke ta dabance nima fa nayi missing d'inki, muje dai mudawo ai muna tare daga yau har next week.
A motar Zinat suka fita ko da sukaje boutique d'in sumayya ta yaba sosai da kayan da zinat tazuba ciki, nan zinat ta gabatar da sumayya ga ma'aikatan wajen cike da girmamawa suke gaisheta sumayya a wulak'ance take amsawa nan tad'an d'auki kaya set biyu tace tana sonsu.
daga nan suka zagaye gari sai dare sannan suka koma gida, gaba d'ayansu saman gado suka fad'a suna hutawa, zinat kallon sumayya tayi tace baby muje muyi wanka,