← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 40

Chapter 15&16

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Da sallama ya shiga part d'in, ba kowa a palour dan haka direct d'akin xaljamil ya nufa, ganin yarda take juyi tana murk'ususu yareema jawad yaji hankalinsa ya tashi, da sauri ya k'arasa gaban ta ya fara bud'e first aid box, sarki mai mirabus da fulani da momy suka fita dan barin yareema jawad yyi aikinsa.


"Nawal na gefen xaljamil tana ta mata sannu, xaljamil idonta a runtse yake tana hawaye. A hankali yareema jawad ya fara duba xaljamil, kallon ta yareema jawad yyi dan ya fara xargin ciwon cikin da xaljamil keyi na k'aryane kawai pretending ne.idan ran jawad yyi dubu sai da ya b'aci, dan haka ya tattara kayansa ya fice daga d'akin ransa a b'ace. Yana fita ya dan saisaita yanayin fuskarsa sannan ya karasa inda su sarki mai murabus suke xaune duk hankalin su a tashe, jawad ya ake ciki? Jiyayi gaba d'aya sun bashi tausayi, lallai yarinyar xata gane kurenta. Murmushin takaici jawad yyi eh na mata allurar bacci sai dai ku bari gobe kwaxo ku ganta. Shikenan yareema jawad Allah ya bata lpy, bai amsa ba yasa kai ya fice daga palour xuciarsa da bak'in cikin xaljamil.


"Part d'insa ya nufa, yana shiga palour bala ya tashi da sauri ya karb'i first aid box d'in. Barka da xuwa ranka ya dad'e, yareema jawad bai kalli bala ba dan gaba d'aya ransa a b'ace yake, bedroom d'insa ya nufa yana takun k'asaitarsa. Bala na biye dashi a baya, suna shiga bala ya cirewa yareema jawad labcourt a ajiye a cikin wardrob.


"Xama yareema jawad yyi a kan carpet tare da bawa Bala umarnin xuba masa abinci. Durkusa Bala yyi ya jawo tray d'in ya fara xuba masa,jellop spagetti wanda taji kayan lambu,sai farfeson kaxa, mixed fruit d'in da Bala yake had'a masa dan bayasan shan ko wane irin juice, xuba masa yyi ya ajiye, tashi yyi ya koma gefe.


"Kamar bayaso haka ya dinga cin abincin, har ya kammala, Bala ya tattare wajen ya gyara komai.Pajamas bala ya dakkowa Yareema jawad ya ajiye a gefen bed ya masa sai da safe ya fita. Kayan ya saka ya haye luntsumeman gadonsa, yana runtse idonsa ya tuna alkawarin da yyi wa nawal na ice cream, tunawa yyi yana dashi a fridge dama saboda ita yake ajiyewa, nd kuma yana san kara ganin kyakkyawar fuskar xaljamil, duk da dai ta b'ata masa rai d'axu.


"Tashi yyi ya cire pajamas d'in ya xira jallabiya, wayarsa ya dauka ya kira layin momy, bugu d'aya ta d'aga kiran, hello yareema jawad wallahi fushi nake dakai, wato ta xaljamil kawai kake ka manta momy ko? Murmushi yareema jawad yyi yana shafa sajen fuskarsa, i'm sorry momy na kinsan mara lapia na bukatar a bashi kulawa shine kawai amma kun kwanta ne? A'a dan dad d'in naka ma bai dawo ba yana chan wajen sarki farouq da mai martaba. Daria yareema jawad yyi cike da kasaita, eh lallai baxaki ganshi da wuri ba. Nawal ta tafi ne? A'a tace tare da xaljamil xata kwana dan fulani taxo duba xaljamil amma nawal taki binta, murmushi yareema jawad yyi eh lallai yarinyar nan wai menene manufarta ne? Momy gani nan. Ok sai kaxo.


"Fridge ya bud'e ya ciro rubar ice cream guda biyu ya nufi part d'in su xaljamil, da sallama ya shiga palour, mom na xaune tana kallon labarai a aljaxeera, cike da fara'a ta amsa ya shigo ya xauna a gefen momy. Hira sosai sukeyi suna daria abin sha'awa.


"Xaljamil da nawal xaune a bed suna hira, aunty xaljamil dan Allah ki tashi muyi pillow fight, haba nawal ki bari sai gobe mana, plx aunty ki tashi muyi, nawal ta bata fuska kamar xatayi kuka, karki mini kuka tashi muyi.


"Yes, dats my aunty, tashi tashi suka dauki pillow suka fara guje guje a d'akin, daria suke sosai xuciar su cike da nishadi.


"Yareema jawad ne ya kalli momy, mom ina su nawal? Tana d'akin xaljamil, ok bari naje na dubata,mikewa yyi ya nufi d'akin, tun kan ya bud'e d'akin yaji hayaniyar su, nawal ta biyo xaljamil da gudu ta nufi hanyar k'ofa yareema jawad ya murda handle d'in ya bud'e, da sauri xaljamil ta durk'ushe a wajen ta rike cikinta. Baki da hanci yareema jawad ya bud'e yana kallon xaljamil cike da mamakin wannan alamari,nawal kam da gudu ta nufo jawad ta rungume shi, I miss u sooooooo much uncle jawad, miss u 2 baby.


"Ice cream d'in hannunsa ta karb'a yawwa uncle thanks, baice komai ba xaljamil kawai yake kallo, da yaga ta kasa d'aga kai ballantana ta tashi daga inda take. Juyawa yyi ya murda handle ya fita, still momy na xaune a palour, dan haka ya mata sai da safe ya fice.


"Bedroom d'insa ya shiga ya chanja kaya ya haye gado, wayarsa ya jawo yana dubawa yaga missed call din " xahra" tsaki ya ja ya gyara kwanciyar sa yyi rigingine, tunani ne iri-iri ya addabi brain d'insa. Phone d'inshi ce ta fara ringing, dubawa yyi yaga "xahra" kamar baxai dauka ba sai da ta kusan katsewa sannan ya daga. Shiru yyi yana sauraronta, hello! Yareema jawad ykk? Tunda ka tafi baka nemeni ba, idan na kira baka d'agawa, sanin halinsa ba tanka mata xaiyi ba yasa ta cigaba da xancen ta, ya kakeso inyi da rayuwata, batun yau ba na fada maka ina sanka, wallahi yareema jawad I can't do without u, kuka ne yaci karfin ta, shiru tayi tana sheshekar kuka. Da kyar ya iya bud'e baki cike da ixxa, xahra xahradden, mai yasa kike san takura wa rayuwata? Mai yasa kike san abinda baxai taba sanki ba, baki da muhalli a xucia ta, bakya cikin type din matar dana keso na aure, so plx ki taimakeni ki fita a rayuwata, kinsan halina ai, tsaki yaja ya kashe wayar cike da takaicin xahra, gaskia matan ynx sun lalace, ace wai macece xatayi ta bibiyar namiji akan ya sota. Ajiyar xucia ya sauke ya lumshe idonsa ya kuma gyara kwanciyar sa ya lula duniar tunanin rayuwar sa a london.


SUMYNBASH CE💋

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P. M. L. W


A romantic love story
2017


Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ


I proud to dedicate dis page 2 u hyxarana halliru, thanks 4 love nd care, I really appreciate. Much love 😍💕💕💕💕💕
Chapter 9 · 0% Book details